Showing 42001 words to 45000 words out of 77337 words

Chapter 15 - Sultan Merah Complete Pdf Hausa Novels By Fertymerh Xarah.doc

acan.

Sultan ya fisge hannun sa ya nufi hidaya yana fad'in hidaya wasa wasa wasa.

Tace ni baxanyi wasa yanxu ba, makaranta xanje kaima kaje gida kayi wasa idan mun dawo xamuyi da yasmeen kaima sai muyi da kai.

Sultan ya girgixa kansa yana make kafada cikin rashin yarda kamar yanda yaga suna yi idan basu son abu ko basa son yi, suna haka sai ga merah ya fito cikin shirin sa na xuwa asibiti, kallon su yayi yanda suka yi cirko cirko har yanxu basu je ba.

Yace lafiya me kuke jira, ina driver na ku.

Yace gani yallabai, su nake jira har yanxu ranka shi dad'e.

Hidaya tayi caraf tace daddy ba wai yaya sultan bane shi sai ya bimu munje School tare, ai mun gayamasa ya xauna gida ya jira mu kafin mu dawo xamuyi wasa dashi.

Mera ya riqa hannun sultan yana fad'in, school xasu je baka ga uniform a jikin su ba, banda rigima irin ta ka fita aka saba yi da kai ne, xo muje inda Mami sai kuyi wasa tare, sultan yaja ya tsaya sai ga hawaye ya soma yi wannan dalilin ya saka hidaya xuwa ta riqa hannun sa tana kallon mera.

Daddy ni xanje dashi sai mu xauna a seat d'aya.

Yasmeen tace wlhy baxa muje dashi ba, ai friends namu dariya xasu mana mun xo da yayan mu class d'aya.

Salwa tace gsky daddy baxaa je dashi ba, teachers d'in ma baxasu yarda ya shiga class ba yayi girma.

Amira ta gyad'a masa kai cikin tabbatar wa itama bata bada goyon bayan aje da shi ba.

Hidaya tace ni baxan je School na barshi yana kuka ba, idan baxaa je dashi ba nima baxan je ba.

Mera yace duk kuxo na kaiku a mota na, I will talk to the principal, duk suka fito a motar ba dan sun so ba, hidaya kuwa farin ciki kamar me xata je da abokin wasar ta School.

Mera da kansa yayi wa principal d'in bayanin ciwon sultan, ya roqi alfarma a barshi na yau kawai.

Hidaya taja hannun sa sai farin ciki take banda harara babu abinda salwa da amira suke binta da shi.

Aikuwa suna shiga class aka soma kallon su, yasmeen ta nufi seat d'in ta, ta xauna hidaya kuwa taja hannun sa xuwa nata seat, kowane seat a class d'in na xaman mutum d'aya ne, each student per seat?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? haka tsarin skul d'in yake, sai ta xauna kad'an ta matsa mashi shima ya xauna yana bin class d'in da kallo.

Ranar littafan ta haka yabi duk yayi ta xane akan su, wasu kuma ya keta idan ta bige shi ya rama, sai dariya yasmeen ke masu, da aka tashi breakfast yaran suka xagaye shi.

Hidaya wannan yayan ki ne, tace eh, amma yana da kyau sosai, shi bashi da skul ne, meyasa kika xo dashi class d'in mu, shi baya magana ne, kurma ne shi, hidaya yayan ki dolo ne, meyasa yake abu irin na yara, shine tambayoyin da yan class da friends nata ke mata.

Da aka tashi breakfast ta riqo sa suka fito inda suke cin abinci suka nufa, abincin ta tare suka ci kasancewar baa saka dashi ba nata kawai sai duk basu qoshi ba,

Hidaya abinci babu...
Tace ai duk kaine ka cinye min nawa gashi nima ban qoshi ba, meyasa baka ce a baka naka kaxo dashi ba.

Yayi shiru yana kallon ta, ta soma tattara kayan tana had'awa sai ga yasmeen ta xo da nata abinci.

Hidaya kun cinye naku ne.
Tace eh kuma bamu qoshi ba.

Yasmeen tace gwai waya ce ki bari ya biyo ki, gashi ya cinye maki abinci ni kuma yau tare da farida xan yi breakfast tunda kika xo baki kira ni munyi tare ba.

Hidaya tayi shiru batayi magana ba, yasmeen tace kije inda su amira su bada nasu a bashi mana, hidaya ta girgixa kanta tana Jan hannun sa ta dube sa, ka gani kayi haquri idan mun je gida sai muci wani abinci yanxu babu nima ban qoshi ba.

Hidaya abinci in ci ya fad'a kamar yana son yayi kuka, ta xaunar dashi inda yasmeen ba dan ta so ba, sai ta nufi block nasu amira, sai gasu sun fito suna tafe suna dariya ko me suke ma dariyar oho.

Anty amira ta kira sunan ta, ta juyo tana mata wani kallo, menene me ya kawo ki block namu.

Tace yaya sultan ne ya cinye min abinci kuma bai qoshi ba.

To me kike so nayi, uban wa yace kixo dashi ba sai da muka ce a'a kika nace ba maxa kije ki bamu wuri cewar salwa.

Amira tace a'a yaya sultan ne fa, shikenan sai mu barshi da yunwa, aa wlhy, xo karbi nawa kije dashi kuma wlhy kika barmin food flask a skul sai na maki shegen duka ke xaki je gida da ita.

Hidaya taje karba salwa ta mata wani uban rankwashi mai shegen xafi, amira ma sai da ta dangware ta kafin ta bata, jikin ta na rawa ta karba ta juya tana hawaye saboda taji xafin sa, tana xuwa ta share hawayen nata da sauri kafin ta bashi abinci ya soma ci.

Hidaya xo ya fad'a yana kallon ta tare da nuna mata su ci abincin tare, ta girgixa kanta, kallon ta yasmeen tayi sai taga kamar tayi kuka, tace hala sun dake ki ne?

Hidaya ta gyad'a kai tana qoqarin had'iye kukan da yaxo mata, ki barsu da Allah xo muci wannan.

Bayan sun dawo gida suka cire uniform nasu suka cigaba da wasa, tun daga lokacin idan xasu je School da boye suke xuwa batare da sun bari ya sani ba, kafin ya tashi sun gama shirin su sun yi breakfast sun fice a gurguje, idan ya tashi ya fito bai same su ba yayi ta rigima kuma daga baya sai ya daina damuwa ko ya fito bai same su ba, idan ma yana nan xasu je sai ya raka hidaya da yasmeen har mota yana masu kiss a kumatu suna yi masa? bye bye wannan abin ba qaramin qona ran amira da salwa yake ba.

Ta numfasa bayan ta dawo daga tunanin da take, ire iren wannan tunanin ke sakata xama wata iri babu kuxari ko da yaushe a tare da ita sai na kewar sultan, ko yaushe xai dawo suci gaba da wasar da suke yi before oho.

A makaranta ba ta tsinana komai sai tunanin sultan da al'amuranshi, tare da tuna abubuwan da suka gudana a tsakanin su masu qara saka mata kewar shi, bata note bata maida hankali gurin teacher idan ana masu darasi kullum sai an dake ta wanda yasmeen ko kad'an bata jin dad'in sauyin hidaya a yanxu, tayi tambaya tayi rarrashi irin nasu na yara duk a banxa.

Da aka xo jarabawa ta kwaso na talatin, yasmeen tayi na uku, amira na d'aya dama can tana da qoqari sosai da kaifin basira idan bata d'auko na d'aya ba xata d'auko na biyu, sai salwa da tayi na biyar.

Banda ihu da murna babu abinda suke, sai tsokanar hidaya suke ga takkwala mai kwakwalwar kifi, bata san komai ba yar qauye da ita, she knows nothing in banda wasa da ci, wannan shine kalaman da amira da salwa suke ta jifanta dashi suna dariya, a matse suke mera ya dawo yau su bashi labari hidaya tayi na talatin.

Aikuwa yana dawowa suka je masa da labarin suna nuna masa nasu result, ya karba yana dubawa, yace ina na yasmeen ta nawa tayi, amira tace as usual daddy ta uku ta yi kasan bata wuce uku ko hud'u, ya gyad'a kansa yana kallon yasmeen, mu ga naki result d'in, ta bashi tana murmushi.

Kallon su yayi babu hidaya, yace hidaya fa me.... kafin ya qarasa tambayar har salwa da amira suna rige rigen fad'in daddy hidaya ta talatin ta kwaso har ma tana qoqarin kulle aji, suka soma dariya banda yasmeen dake kallon su.

D'agowar da mera xai yi idanun sa caraf acikin nata sai ya ganta rakube ta boye tana leqensu fuskarta sharkaf da hawaye.

Oh ni bintu, nayi bayani mutane sun kasa fahimta su dole sai nayi amfani da sarauta tunda littafin ya qunshi haka, xan duba nagani ko xai yiwu a yanxu.
[11/20, 10:25 AM] Ummi Tandama: *SULTAN MERAH*

Haske writers Association

?Fertymerh Xarah=؞?

30

After five years.......

Shekara kwana ga mai yawan rai, kwanaki ke shud'ewa a hankali su koma watanni, watanni su rikid'e su koma shekaru, cikin hikimomi da iyawar ubangiji har ya kasance a yau hidaya da yasmeen suke xana jarabawar su ta qarshe ta gama sakandire.

Farare ne sirara masu tsayi sambal, haka suka taso kamar tagwaye amma mabambanta a dabi'u da halaya.

Yasmeen fara ce sol mai hanci irin na Afiya, yarinya ce mai son huld'a da mutane tana da wayewar kai fiye da hidaya, tana da friends iri iri a school sabanin hidaya, wannan farar bafillatanar wata irin miskilar yarinya ce da wuya ka fahimci inda tasa gaba, domin fuskarta bata nuna abinda ke cikin xuciyarta, ta iya danne abu a xuciyar ta komai girman sa da muhimmancin sa, koda dannewar xata cutar da ita, shiru shiru ce bata da hayaniya bata da son shiga jama'a ko da yaushe tana d'aki kwance ko kuma tana study room tana karatu kowa ya san da ita akan hakan, ba ruwan ta da shiga shirgin kowa a gida.

Ta d'auki buri ta sakawa ranta tun daga ranar da ta mallaki hankalin kanta, ta qara tabbatar wa ta rasa wannan baffan ta rasa wannan mahaifin mai matuqar sonta fiye da kowa da komai a duniya, ta rasa wannan burin na ta na rayuwa dashi tare da d'ora idanunta akan sa, ta riqe yaren ta wanda har gobe tana alfaharin kasancewar ta bafillatana, bata bari ta bar harshen ta ko ta manta wani abu daga ciki ba, bata yarda harshen aro na hausa ya rinjayi yaren ta ba, wanda dalilin haka yasmeen ma tana ji sosai ta koya mata amma bata iya mayarwa sai kad'an kad'an.

Ta dage da son cika burin mahaifin ta na karatu, tana so ta cika masa wannan burin nasa na ganin ta xama wata a duniya da mutane xasu yi alfahari da ita, takarda da biro sune abokanta a koda yaushe, bata da lokacin kallo ko riqe waya, babu ruwanta da wani social network wanda a tunanin ta shi ke hanawa mutum karatu da kuma lalata mutum, a ganin ta waya bata da wani amfani gare ta illa bata lokaci a rayuwarta.

Sabanin yasmeen da koda yaushe tana kan waya, itace Twitter, Instagram, Facebook da sauran su.

Yasmeen ta san tun tana qarama yaya fu'ad bai damu da ita ba kamar yanda yake damuwa da amira ko hidaya, ita yana mata kallon qanwa kamar salwa da suka fito ciki d'aya, ta lura akwai boyayyiyar soyayya a xuciyar sa da yake wa hidaya Wanda ita kanta hidaya bata san yana yi ba, to amira fa?

Sai gata ta tsinci kanta a wani irin yanayi da baxata iya fassara kanta ba, son wanda yayar ta ke so, a yanxu babu wanda ta damu dashi irin sa, bata iya kwana biyu bata kira shi ko ta tura masa saqon gaisuwa ba, duk da bata nuna wata alama ta soyayya aciki ta barwa kanta wannan sirrin.

Yasmeen ta sha xama tayi tunani akan kanta, meyasa yaya fu'ad bai damu da amira ba like before duk da kowa yasan suna tare, meyasa yanxu yake nuna hidaya yake so, ko ya daina son amira ne da xai xabi hidaya akan ita da take jinin sa kuma yar'uwar sa?

Ga uwa uba yaya sultan, duk suka yi waya ko chatting a kullum xai tambaye ta hidaya sau biyar koma fiye da hakan, amma tsawon wannan shekarun hidaya bata taba nuna tana son ta karbi waya su gaisa ba idan ya nema, sai ma tayi biris ko ta sa kai ta fice daga d'akin.

Ko sau d'aya bata taba xancen yaya sultan ba, ko saka bakin ta idan ana hirar sa, bata taba tsayawa kallon ball nasa ba a duk lokacin da xasu yi wasar match idan duka gidan sun had'u ana kallo to banda hidaya, meke damun hidaya ne akan yaya sultan, bata jin ta yaya fu'ad saboda a yanxu ita take son sa, amma d'an uwan ta fa wanda a ko da yaushe cikin nuna mata damuwar sa yake akan damuwa da hidaya da yayi, duk da bai fito ya fad'a mata yana son hidaya ba a matsayinta na budurwa ta fahimci hakan.

Kamar yaya sultan har xai nuna damuwa akan ta amma bata damu ba, ita hidaya wace irin sa'a ce da ita hakan, banda abin hidaya yam'mata nawa ne masu son yaya sultan, wace irin mace ce bai gani ba acan, ya'yan sarakuna nawa aka xo dasu gidan nan akan ana son had'a su da yaya sultan, ta na so tayi wasa da damar ta tabbas xata ankarar da ita akan halin da take ciki domin tana son hidaya kuma tana son xaman ta da yayan ta akan wasu bare.

Tana cikin tunanin hidaya ta shigo da wani littafi a hannun ta, kallon yasmeen tayi kafin ta dubi wayar dake hannunta ta yatsina fuska tana jefar da littafin hannun ta, qaramin tsaki taja tana fad'in,

dama ta ya damuwa da tunani xasu barki tun da kin d'auki waya da chatting abokan huld'ar ki ko da yaushe, idan kin qaraci tunanin naki ki tashi ki shirya lokacin xuwa islamiyar mu yayi.

Kallon ta yasmeen tayi tana cire kayan jikin ta da alama wanka xata shiga, sai taji tana son mata mgnr yaya sultan, ta soma mata nasiha akan halin ko in kula da take nuna wa akansa wanda sam bata jin dad'in haka, to me yaya sultan ya maki haka da xafi da har kike masa haka bayan a baya ba haka muka taso ba, wai meke damun ki ne hidaya?

Kallon ta hidaya tayi bayan ta d'aura qaramin towel a jikin ta,

Ki jiki da wani shirme, shi ya gaya miki yana sona ko kuma ya damu dani? Miyid'a kongatta miwatta tegal joni midalimo yauti'amo (ni nace maki ina da wani lokacin shirme), kin sani duk wani shirme bana cikin sa musamman ma akan wanda ya nuna ni ba kowa bace a gurin sa, kin manta lokacin da yake hantara da duka na k.. Yasmeen ta katse ta da sauri cikin bacin rai.

Da anyi magana sai kice ya ture ki ya mare ki, wannan kad'ai ya isa ki d'ora masa qiyayya haka ne, ba yayan ki bane kina nufin bai isa akan ki bane kamar mu, ko kuma dan ba ciki d'aya kuka fito bane.

Hidaya ta bud'e idanunta sosai akan ta, you are thinking negative yasmeen, na fiki sanin shi d'in yayana ne kuma babu kamar shi a gurin mu but what about the hatred, na gani a kwayar idanun sa nagani hidaya ce baya son gani a lokacin, hidaya ce baya son ta masa magana ko tana son xama dashi.

dallah malama rufa min baki, yasmeen ta katse ta a harxuqe, ke baki da wani kwakkwaron dalili da xaki kare kanki akan sa, kuma duk wannan tsana da kike nuna masa kada ki bari iyayensa su sani ai inda alqawari ruwa baxai dafa kifi ba, just look at you please (ta fad'a tana nuna ta qasa da sama ) me kika fi shi, me xaki nuna masa da kike jin kanki wata can daban, kina tafiya haka dake kamar a busa ki fad'i, ban da so gamon jini ne me yaya sultan xai yi dake yana da xuqa xuqa yam'mata ke mai kama da yan qauyen China ma har kina bud'a baki kice baki da wani lokaci na shirme, kuma na rantse da Allah kika yi saken da ya subulce maki xakiyi nadamar da baxata yi maki amfani ba, gwanda auren wanda ke son ka akan wanda kake so.

Cikin fusata hidaya tayi kanta tana fad'in just tell me waye nace maki ina so, na taba maki mgnr wani ko kin taba gani na da wani, kowa an gayamiki irin kine da bashi da aikin yi sai neman gindin xama a gurin maza, kece waya da wannan yau gobe wani daban, yarinya ga kyau amma ba class sai iyayi kan abinda bai shafe ta ba, ban taba son sa ba, banda so na d'an uwa kuma baxaki tursasani ba tunda bake xaki d'aura min auren ba, I don't have time for your stupidity, marar aikin yi kawai mtsew.

Eh naji banda aikin yi... Hidaya ta fice da sauri tana fad'in kiyi da wani ba da ni ba nace banda lokacin ki ai, ta fice tana kwalawa d'aya daga cikin bayi kira Sophie, bata jima ba sai gata taxo cikin rawar jiki bayan ta amsa.

Hidaya tace kije ki had'a min ruwan wanka yanxu.

Yasmeen tace ai kuma baki isa ki saka baiwata aiki ba, ina ji an raba an ba kowa nasa bayin ko, ki kira naki mana.

Murmushi kawai hidaya tayi batare da ta kula ta ba ta kira Kdeey d'aya daga cikin bayin ta.

Tun daga lokacin suka d'auki gaba babu mai kula wani acikin su abinda basu taba yi ba tun tasowar su kuwa.



*littafina na kud'i ne, idan baka biya ba kada ka karanta, xaka biya haqqi inda baka da iko, mai buqata yayi mgn 08169334980*
[11/20, 10:25 AM] Ummi Tandama: *SULTAN MERAH*

Haske writers Association

?Fertymerh Xarah=؞?

31

Kwanan su uku basa magana da juna, duk sun jigata saboda basu saba ba sai suka kasa jurewa dole suka shirya kowane yana da laifi a cewar su.

Amira da salwa basa gidan suna qasar Cairo acan suke karatun su yanxu na gaba da secondary, tun bayan shekaru uku da suka wuce aka sanya su, acan suka had'u da Aryan da Arham (El'mustapha) sanin suna da alaqa ta jini da juna ya saka su sakin jiki dasu inda suka yi matuqar sabo da juna, a taqaice sun manta da soyayyar yayyun su biyu da suke so sun bud'e sabon shafin soyayya da twins d'in Jiddatulmusty.

*

Fitowar ta wanka tana tsaye bakin mirror tana tsane gashin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login