Showing 72001 words to 75000 words out of 77337 words

Chapter 25 - Sultan Merah Complete Pdf Hausa Novels By Fertymerh Xarah.doc

tilon d'an sa.

Yinin ranar gaba ki d'aya a daki tayi shi cike da tunani iri iri, tana jin sultan yau ma ya sake xuwa kuma tare da fu'ad da bata yi tunanin qara xuwan sa gidan su ba.

Ke hidaya d'auko mayafin ki ki tafi komai ya wuce bana iyawa da jaraba irin ta sultan tuntuni na yafe masa Allah ya baku haqurin xama da juna.

Hidaya ta fito da sauri tana kallon sa idanun ta sun ciko da kwallah kamar xatayi kuka, baffa baxan je ba ni bana son xama dashi bana sonsa ko kad'an a xuciya yanxu da su yasmeen kawai xan xauna.

Baffa yace aa karki yarda muyi haka dake hidaya shi auren baki d'ayan sa jigon sa shine haquri, sultan yayi laifi amma ya gane da kansa bai kyauta ba kuma ya gyara halinsa tare da neman afuwar mu, dubi wahalar da yayi anan meyasa baxamu yafe masa ba, Allah Ma muka masa laifi ya yafe balle d'an Adam, ki xamo mai yafiya ga wanda ya saba maki amma bana son qullaci da sanya abu a rai fiye da qima, yanxu wata sabuwar rayuwa xaki fara wadda ta banbanta da wadda kika taso a ciki.

A cikin ita wannan rayuwar baki da iko da kanki sai abinda mijin ki ya karkata ki akai, wayo yayi maki ixini so ki karbi rayuwa a duk yadda taxo maki ki kasance mai tsarkakkiya xuciya akan kowa sauran al'amura ki barwa Allah idan har na isa dake to maza ki tashi kuje Allah yayi maki albarka da auren naku gaba ki d'aya.

Hawayen dake maqale cikin kwayar idanunta suka mirgina a hankali masu d'umi, ta tashi a fusace ta fito batare da ta d'auki mayafi ba.

Baffa murmushi kawai yayi yana bin bayanta da kallo, sultan saboda farin ciki kasa magana yayi saboda baffa yayi masa baxata yau bai yi tsammanin haka ba, fu'ad ne ma ke masa godiya har suka fito.

Tun da ta shigo motar banda kuka ba abinda take, sultan na tuqi yana murmushi fu'ad kuwa chatting d'in sa yake har suka iso, bata jira ya gama parking ba ta bud'e motar ta fito a guje ta nufi cikin gida kai tsaye d'akin su ta nufa ta rufe da key.

Sultan yaje da kansa ya gayawa Afiya dawowar hidaya, tabe baki kawai tayi batare da nuna damuwa ba, amira da yasmeen kuwa basa gidan da suka dawo suka same ta sun yi farin ciki sosai, da kyar ta rarrashi xuciyar ta, ta yarda ta fito taje ta gaida Afiya, ta amsa mata fuska ba yabo ba fallasa tana bin ta da kallo duk ta qare taga ta canxa mata sosai.

Kwana biyu ta warware ta Saki jikin ta da kowa a gidan kamar da banda sultan, Afiya Ma sosai ta Saki jiki da ita dama can farko tana son xama da hidaya d'in saboda bata da matsala.

Duk yanda sultan ya nemi hanyar son magana da ita ko su kebe taqi bashi wannan damar, abin ya soma bashi mamaki hidaya bata son sa a yanxu ne ko me?

Ya xauna ya soma tunani hidaya wata muhimmiyar mutum ce da ta shigo rayuwar shi suka rayu tare rayuwa ta d'an wani taqaitaccen lokaci wanda yafi tsayin shekaru dubu a xuciyar sa da ba xai iya nanatawa da ita ba,

Tunanin sa ya dawo ga present life d'in sa wato rayuwar sa ta yanxu, hidaya tana wulaqanta shi saboda yayi mata fyade laifin da har yau ta kasa ganewa bashi da wani laifi a kan haka, abinda take wulaqanta shi yanxu akan sa nasa ne haqqin sa ne wanda yana da ikon karba ko ta halin qaqa a duk sanda ya so.

Meyasa ka damu da al'amarin hidaya ne inji wata xuciyar, baka dibar ta kayi watsi da ita kamar tayi watsi da kai har xuwa lokacin da xata sauko ta neme ka?

Xuciyar sa ta qara halar to masa da wannan tambayar, ta qara da cewa she is arrogant, who the hell she think she is? Mtsew ya ja dogon tsaki yana ficewa daga gidan Ma.

littafina na kud'i ne kada ka karanta baka biya ba xaka bada haqqi inda baka da ikon biya, idan kana so kayi magana ta wannan number 08169334980 or? 08030811300*
[11/20, 10:25 AM] Ummi Tandama: *SULTAN MERAH*

*littafina na kud'i ne idan kana so kayi magana ta wannan number 08169334980*

43

Washe garin ranar ya riga ta tashi ba kamar kullum da sai dai ya tashi ya samu har ta fice ba, jin motsin sa ya sa ta bud'e idanuwanta tana kallon sa, kallon ta yayi yana fad'in sai kin makara sallah yau, ya sauka ya nufi toilet.

Bai jima ba ya fito, ta dube sa tana fad'in yaya dan Allah ka d'auko min hijab d'ina nayi sallah anan bana so na fita yanxu mamee ta ganni.

Kamar baxai je ba sai kuma ya fita, itama tayi toilet nasa sanda ya dawo bata fito ba sai ya fara sallah, kallon kayan da ya d'auko tayi bayan ta fito tana fad'in hijab nace shine harda kaya kake daukowa ta fad'a tana kallon sa sanda ya sallame sallah, ganin bai yi magana ba tayi shirin sallah ta soma.

Bayan ta kammala ta juyo tana kallon sa, morning yaya, yace morning too, tace meyasa ka d'auko wad'ancan kayan, yace anan xakiyi wanka tare dani ki shirya, ta bud'e ido da baki tana kallonsa cikin mamaki yasa hannu yana rufe bakin tare da fad'in miye haka.

Ta tashi tana fad'in aa ni baxan iya wannan ba, yanxu ma d'akin mu xanje, yace xo muyi barcin 30minutes sai ki tafi kinji, ba musu taje ta kwanta kusa da shi had'e da shigewa jikinsa tana lumshe idanuwanta, shima gyara masu kwanciya yayi ya rumtse idanuwan sa saboda barcin bai ishe sa ba.

Sun jima sosai suna barci kafin su tashi da kyar, da dad'in baki da rarrashi duk ya had'a ya samu kanta suka je wankan tare, bayan sun shiga toilet ta juya tana kallon sa tace amma kace sai ka kashe hasken ko ina fa?

Yace eh mana had'a ruwan wankan tukunna ina xuwa, ya fita bai jima ba ya dawo da towel daure a jikinsa, ta dube sa cikin fad'uwar gaba tana fad'in shine kuma ka cire kayan, yace da kaya kika taba ganin anyi wanka, towel d'in ma cire shi xanyi ai kema kayan jikin ki dole xaki cire.

Ta bata fuska tana qoqarin fita daga toilet d'in ni gaskiya baxan yi ba, ya riqo hannun ta yana fad'in amma ai kince kin yarda tunda xamu kashe hasken toilet d'in? baxaki ganni ba nima baxan ganki ba please hidaya, ta tunxure baki tana fad'in to kashe hasken ka rufe idanun ka, yayi murmushi yana fad'in an gama your Highness, itama murmushi tayi tana kallon sa cikin langabewa.

(Fans da son jin kwab kowa yana son jin ya akayi wankan to bara kuji ba>?#?)

A tare suka fito kowane daure da towel, kome ya basu dariya sai dariya suke dai dai lokacin aiman ya shigo d'akin cikin shirin sa na fita office, kallo d'aya yayi masu ya d'auke kansa ashe yarinyar tana nan Afiya take ta neman ta tun d'axu.

Da sauri hidaya tayi baya ta shige toilet d'in cike da jin matsinanciyar kunya, ko wane kallo daddy ke mata yanxu, sultan ma cikin jin nauyi ya qarasa yana gaida shi, aiman ya miqa masa wata takarda yana fad'in hannu xaka sa kan filin da kace ka baiwa baffa, dalilin yasa na naxo na kawo ma dan ina sauri xan fita, sultan ya karbi takardar yana kallon sa, daddy yanxu xan yi na baka ne ko kuma xan kawo ma anjima ne,

Aiman yace idan xan bari ka kawo anjima menene amfanin xuwa na anan da baxan jira har anjima ba, ina so na bada aikin a fara ne, sultan ya karbi biro hannun sa yayi signing kafin ya bashi yana Shafa gefen fuskar sa, kallonsa aiman yayi kafin ya juya ya bar d'akin batare da yayi magana ba, da kyar ya samu ta fito daga toilet d'in idanun ta jagab da hawaye, ba shiri ya soma rarrashi yana dariya.

Cikin qanqanin lokaci suka shirya suka fito falon hannun su sarqe dana juna, Afiya ta fara ganin su perfect match ta fad'a a xuciyar ta, ba qaramin dacewa suka yi da junan su ba sai yau ta hango hakan, suna had'a ido da Afiya hidaya tayi saurin janye hannun ta daga riqon da yayi mata, Afiya ta d'auke kanta gefe kamar bata gansu ba su yasmeen kuwa sai suka soma iyye, lallai ma yarinyar nan sai yanxu kike fitowa, hararar ta tayi kafin ta juya tana kallon mamee tana gaidata, shima sultan ya gaidata su biyu suka xauna dinning yin breakfast kasancewar kowa ya gama su kad'ai ne suka rage ba su yi ba.

*

Bayan wasu kwanaki komai ya canxa a wurin baffa ya dawo kamar ba shi ba cikin qanqanin lokaci ya nemi mata bafillatana budurwa da taimakon sultan aka sanya masu lokacin aure.

Da farko hidaya bata so ba sai daga baya kuma ta Saki jiki.

A satin duk kafafen yada labarai na Radio, talabijin da jaridu na garin basu da miuhimmin labari sai na yada labaran gayyatar daurin auren jikokin Sarki El'ameen Merah da Pres. Ahmed Abbas d'an qasa (wato president mahaifin Afiya da aliyu)wanda al'ummar garin baxa su taba mantawa da wannan daurin auren ba.

Bayan kwana biyu sai ga lefe na gani na fad'a daga gurin el'mustapha na ya'yan sa, akwati goma goma cike da kayan alfarma masu tsadar gaske, da farko aiman bai so akayi lefen ba amma ganin yanda el'mustapha ya kafe yasa ya amince, yasmeen da hidaya kuwa suma aliyu yayi masu komai kamar yanda aka yi wa su amira akwati goma, Masha Allah kayan kam sai san barka.

Auren baffa aka fara yi, suka sha shagalin su amarya Nafisa ta tare anan birni inda sultan ya basu gida flat mai kyaun gaske.

*

Asabar d'in qarshen watan nuwamba dubban jamaa cikin garin abuja da wajen ta???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? suka shaida daurin auren Fu'ad Aliyu d'an qasa da Yasmeen Aiman Merah, Aryan El'mustapha Muneer da Ameera Aiman Merah sai Arham El'mustapha Muneer da Salwa Aliyu d'an qasa akan sadaki mafi qanqanta.

Anan Aliyu ya tashi yayi bayanin Auren El'ameen Aiman Merah (Sultan) da Hidaya Ma'awiya ga mutanen da basu san da auren ba, sai dai an boye ainihi dalilin auren wanda labarin qarya aliyu ya shirya masu a lokacin.

Angwaye suka xarce gidan tsohon shugaban qasa inda ammi ta tanadar masu walima da xaa yi, Afiya kuwa iyayen mata ita da rumaisa sai faman shirin matan suke.

Afiya hidima ta sha ta kam, gidan sarki a cike yake taf ba masaka tsinke, musamman da manya manyan abokanta suka fara sauka gidan da suka taso daga wata uwa duniya a waje, ga matan manyan abokan Aiman suma baa bar su baya ba.

Cikin qanqanin lokaci aka gama shirya su, ba qaramin kyau suka yi ba cikin fararen dogayen riguna masu kama da wedding gown, duk acikin su hud'u amira tafi su kyau nesa ba kusa ba sai kamannin ta da sultan suka fito sosai a ranar wanda kallo daya xaka mata ka tabbatar da hakan.

Cikin mota aka sanya su aka nufi gidan da su, sanda suka iso mutane birjik a qofar gate d'in suna jiran isowar su sosai sun ji dad'in yanda ake tarbon su bama kamar hidaya da take ganin baa nuna mata banbanci da su komai tare ake masu.

Suna shiga gidan idanun maxajen akan su kowane yana so yaga tashi yana so ya san wacece tafi kyau a ciki, matar arham amira tafi kyau kam amma saboda son xuciya irin nasu sai kowa ya soma qiyasta tashi tafi kowace kyau a xuciyar sa.

Angayen suma suna sanye da lallausan yadi mai shara shara fari Sol wanda har kana iya hango fararen vest d'in su, kowane yaje ya riqo hannun matar shi suka nemi guri a inda aka tanadar masu suka xauna.

Ba qaramin kyau suka yi ba hatta qawayen amaren sai da suka yana, sun raxana da bayyanar wad'annan zaratan maza ma'abota haiba da kamala, bama kamar sultan acikin su sak kamar Aiman mera sanda yake ganiyar quruciyar sa, wannan ji da kai, wannan taqama da ji da sarauta duk ya tattaro su ya dawo da su a yau musamman daya lura kowacce mace ta kalle sa sai ta furta wow.?

Game aka fara akan salwa da amira su xo kowacce daga cikin su ta fitar da mijin ta acikin twins d'in, aikuwa nan kowacce ido ya raina fata Aryan da arham basu da banbanci ga kaya iri daya komai iri d'aya har hasken fata ma.

Wani tunani amira tayi sai tayi wa salwa rad'a a kunne, lokaci daya suka Saki murmushi wato amira tana gane su ta girman jiki, d'aya yafi d'aya jiki kad'an, nan take kowacce ta nuna mijinta aka d'auki tafi,

Sai yasmeen aka xo kanta tare da rufe idanunta da jan kyalle aka jera mata su akan ta xabi nata mijin fu'ad, a bisa rashin sani sai ta nufi sultan fu'ad na gani yayi saurin taro ta hakan kuwa ya baiwa mutane dariya sosai, da aka xo kan hidaya kuwa bayan an rufe nata idanun shiru tayi tana tafiya kad'an kad'an a gefen su duk da tana cikin fargaba, har ta wuce sultan sai kuma ta dawo da sauri dalilin qamshin turaren sa, a tare suka rungume juna aka d'auki sowa da tabi wurin.

Bayan an kammala walima suka nufi cikin gida amaren maxan na waje, sultan yana kan motar sa, fuskar nan tasa a murtuqe cikin baqin glass duk dai saboda matan da suka xo masa magana wurin ya fi a qirga, xuwan hanifa ne ya sa ya saki fuskarsa ba laifi,

Tace ai bro tunda nayi tattaki naxo auren ka har Nigeria kai ma sai kaxo aure na har Cameron ko baka so.

Yace ai dole ne kuma tare da hidaya xamu xo bikin sis, yaushe ne auren?

Tace February ne,
Yace ashe ma an kusa,
Ta gyad'a kai tana murmushi kafin tace yaya matar ka ta had'u qarama da ita mai kyau,

Yayi murmushi yana fad'in ke dai ki fad'i gaskiya nasan halin ku keda su amira ai,

Wallahi da gaske fa yaya,

Hidaya da ta fito tana nemansa ya bata waya tana son kiran baffa taji ko matar shi xata xo d'in kamar yanda suka yi magana taja turus ta tsaya cike da tashin hankali ganin sultan d'in nata tare da wata suna dariya, kamar ance ya d'ago kuwa suka had'a ido da ita, yanayin ta yasa yaji gaban sa ya fad'i, kafin ya diro daga motar tuni ta juya ta koma a ganin ta wannan toxarci ne ace ranar bikin auren ta mijin ta yana fira da wata.

Hanifa ta dube sa tana fad'in lafiya yaya?

Yace ba komai ina xuwa, ya bi hidaya.

Hidaya na shiga d'akin da suke before abokan su amira suka dube su suna fad'in amaryar yayan ku ma tana da kyau very young and fresh, salwa tayi carab tace but duk aciki shi kad'ai ne ya auri bare kowa yana da alaqa da jinin sarauta amma banda ita, hidaya ta kalle ta sai kuma ta d'auke kanta tana barin d'akin, yasmeen tace wannan rayuwa da kike da ita bata da kyau ke kike kallon ta bare mu a gurin mu ba bare bace koma bare ce a hakan aka ganta akace ana so har aka xabe ta tana bare aka bar masu jinin sarauta, tayi tsaki ta fice, amira tace meyasa xaki ce ita bare ce ko ba komai a gidan mu ta tashi kuma yayan mu take aure, ta dubi friends d'in tana fad'in hidaya is our cousin ku kyale salwa tana jin haushi ne saboda yaya sultan bai aure ta ba ya auri hidaya, aikuwa nan take d'akin ya d'auki dariya, salwa kuwa ranta ya baci sosai.

Ganin yanda mata suka cika falon sai sultan ya koma batare da ya shiga ciki neman hidaya ba, ita kuwa tana fitowa wani d'akin ta shige taci kukan ta sosai kana ta wanke fuskar ta har make up inda aka mata kuwa, kallo daya xaka mata kasan tasha kuka,

Da dare angwaye suka xo daukan amaren su domin su maida su gida, nan hidaya ta turje akan baxata bi sultan ba.

Meyasa yasmeen ta tambaye ta, meya faru kuma hidaya ko dan saboda abinda salwa tayi d'axu, ta girgixa kanta tana share hawayen fuskarta, salwa ta riqa hannun ta suka nufi motar fu'ad har sun shiga sai ga sultan ya dube su yana fad'in me kuke nufi, ni naxo daukan iska ne na koma kawai, yasmeen tace ai tace baxata bi ka ba, ya dubi hidaya yana fad'in saboda me?tayi masa shiru, ya soma gyara hannuwan rigarsa yana fad'in xaki fito daga motar ne ko kuma sai na d'auke ki a gaban idon kowa, tasan xai aikata tunda ba kunya ne dashi ba ta fito cikin motar ba dan ta so ba, fu'ad ya soma dariya yasmeen tace sis wlhy da nice baxan fita ba sai dai ya d'auke ni, hidaya bata kula ta ba.

Tun a hanya yayi magana taqi ta kulasa har suka xo gida, ya hanata fita daga motar yana kallon ta yace duk wannan kukan da fushin saboda kawai kin ganni da hanifa, kinsan waye ita qanwatace fa, You can't judge what you don't know hidaya.

Da kyar ta bud'e baki tace naji ka bud'e min motar xan fita, yace saboda abinda nake gayamiki aikin banxa ne baxaki tsaya ki saurare ni ba, tayi shiru yace shikenan You can go ya bud'e mata motar tasa kai ta fice batare da ta qara kallon sa ba, dama yasan kafuwa irin nata sai shima ya share ta.

Kwana biyu basu magana duk bikin da xaa yi a gaban idon mutane baxa su taba nuna akwai wani abu tsakanin su ba da xarar an gama bikin shikenan kowa xai kama harkar gabansa.

Bayan gama biki da sati daya suka sonsa shirye shiryen tafiya musamman salwa da amira sune xasu fara tafiya, ranar da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login