Showing 69001 words to 72000 words out of 77337 words

Chapter 24 - Sultan Merah Complete Pdf Hausa Novels By Fertymerh Xarah.doc

bar gidan nan tare xamu riqa kwanciya kuma duk ranar da baki xo ba ko... amma ki gwada ko sau d'aya ki gani, cikin fad'uwar gaba take kallon sa tana fad'in barci tare xamu riqa yi saboda me, da can tare muka saba kwanciya ne, ta tashi tana fad'in ni baxan kwanta da kai d'aki d'aya ba, ya fisgota tare da maida ta saman gadon yana nuna ta, xan nuna maki nafi ki taurin kai da kafuwa kuwa, ya juya ya cigaba da abinda yake, tana xaune tana kallon ikon Allah ya shafa wannan ya goga wannan sai kace wata mace, lokacin da yaxo saka kaya ganin babu kunya a gabanta xai saka yasa tayi saurin rumtse idanu tana innalillah, ko da ya gama ya rage hasken d'akin ya kwanta yana nuna mata kusa dashi, xo nan ki kwanta.

Ta tsura masa ido batare da ta motsa ba, cikin tsawa yace bakya jine? ba shiri jiki na rawa taje kusa da shi amma ta kasa kwanciya sai ruwan hawaye take, fisgota yayi ya kwantar da ita a jikinsa tare da rungume ta sosai yana lumshe idanuwan sa, tsura masa ido tayi har lokacin ta kasa rumtse idanunta saboda tsoro, sultan bai ma san tana yi ba yanayin da suke ciki ya saka barci mai dad'i yayi awon gaba dashi, jin saukar numfashin sa da yanda ya sassauta riqon da yayi mata ya tabbatar mata yayi barci, ta kai fuskarta dai dai wuyansa tana shaqar qamshin jikin sa tuni barci yayi awon gaba da ita.

Tun daga ranar tare suke kwanciya duk da ba abin dake had'asu sosai ta saba da kwanciya tare dashi kuma tana jin dad'in haka, wani lokacin ma idan ya jima bai dawo ba takan je d'aki ta jira sa, sai dai ya dawo ya same ta tayi barci.

Ranar da su yasmeen suka dawo sai wani bata fuska take musamman da dare yayi, yasmeen sai labari take bata soyayyar ta da fu'ad da bata ma so dawowa ba amma hankalin hidaya baya kanta yana gun nata mijin, kwanciya tayi a gadon sai take jin ba dad'i duk da yasmeen na kwance akai amma ganin sa take ya mata kwanciya, ta tashi tana gyara igiyar rigar barcin ta tana yatsina fuska kamar bata so kada yasmeen d'in ta xarge ta, tace yaya sultan ke nema na tun d'axu.

Yasmeen ta dube ta tana fad'in shine baki je ba sai yanxu kin ma raina sa, da yaya fu'ad ne ya kirani tun d'axu baxa ki ganni anan ba, ni wlhy banji dad'in dawowa ba kinga acan sai mu raba dare muna tare muna hira kamar kada mu rabu.

Hidaya ta bud'e idanun ta tana kallon ta like serious sis, ke bakya jin tsoron sa?

Tsoron me? Yasmeen ta tambaya tana kallon ta cikin mamaki.

Hidaya ta cije yatsa cikin tunani sai kuma ta dube ta tana fad'in qila baya maki irin abinda yaya sultan ke min ne, yanxu tare fa muke kwanciya kullum sai ya wani matse ni a jikinsa a hakan kuma naji na saba baxan iya barci batare da shi ba.

Yasmeen ta gimtse dariyar ta tana fad'in chab garin dad'i na nesa Allah ya kaimu lokacin ni da yaya fu'ad xaki ga love bird, ki cigaba da yiwa yaya sultan wulaqanci kin san namiji da son gata yana son ana kula dashi da shagwaba shi idan bakya masa haka xai je ya nema a gurin wata before you know xaki ji ana maganar xai qara aure.

Hidaya ta bata fuska tana kallon ta amma ni menene bana masa.

Yasmeen ta tabe baki tana fad'in komai ban gani ba, ke da kike nuna masa halin ko in kula ma baki damu dashi ba, abinda yayi maki a baya ya kamata ace kin yafe kin manta ki dawo da soyayyar da kike masa before.

Hidaya tace ni na gayamiki bana son sa, tuntuni na yafe masa amma kinsan me yayi min ranar fa da safe inda wata yaje ko hanifa ne sunan ta ko miye ma na manta.

Oh wai hanifa, yarinyar qawar mamee ce kuma friend d'in su ameera ce, ranar ai duka muna tare, (cikin son d'aga mata hankali)yasmeen ta cigaba da cewa chab mutuwar son yaya sultan take ai, maganar da naji tanayi ranar wai tana so sultan yayi mata ta biyu da ita saboda baxata iya haqura da shi ba, so kin gani idan kika sa wasa wlhy xata kwace maki miji kinsan tafi ki waye wa duka rayuwar ta a Cameron tayi, ki daina masa gardama akan duk abinda yake so, kinga yaya fu'ad d'axu da xai tafi nayi masa kiss yafi a qirga cos bana son yaje na barshi da tunani,

Hidaya ta dube ta tana fad'in ba kuyi aure ba kuke wannan yasmeen, to ni ya kike so nayi?

Yasmeen tace ai auren xamuyi kuma yaya fu'ad yayana ne baxai cuce ni ba kiss nace mun yi ba wani abu daban ba, abinda xakiyi ki xauna kina tambayata ke da mijin ki, ta juya mata baya tana fad'in idan kin fita ki kashe min wannan hasken pls.

Bai yi tunanin xuwan ta a ranar ba, yana xaune yana chatting ta shigo kallon ta yayi shima ita yake kallo, yanayin ta yau a sanyaye babu bata fuska a wannan xuwan nata yau ko meyasa, yace banyi tunanin xaki xo ba ai tunda ga yasmeen.

Ta sunkuyar da kanta batare da tayi magana ba, yace kije kawai ku kwanta da yasmeen d'in, cikin fad'uwar gaba ta dube sa tana fad'in amma kaine kace fa kullum xamu riqa kwanciya tare har sanda xaka tafi.

Cikin mamaki yake kallon ta sai kuma ya basar batare da yayi magana ba ganin haka yasa taje ta hau gadon ta kwanta tana ajiyar xuciya a hankali, shi dai baice komai ba hankalin sa na kan wayar sa kamar daga sama yaji tana fad'in chatting kake yi da wasu matan ko?yayi shiru cikin mamaki kafin ya juya yana kallon ta yace me yasmeen ta gayamiki nasan ba banxa ba.

Cikin jin haushi ta tunxuro baki, hakan da tayi ya birge shi ya sunkuya ya kai mata kiss ga mamakin sa murmushi yaga tayi tana kallon sa kafin tace dan Allah kaje da ni?

Where?ya tambaye ta,
Phoenix bana ji kana fad'in kai kad'ai xaka tafi ba,

Yace kina xuwa ne, ta gyad'a kai da sauri, ya kwanta gefen ta yana fad'in meyasa.

Tace kowa xai tafi sai ni kad'ai xaa bari a gida, ya matso da ita xuwa jikinsa yana fad'in xaki iya gayawa daddy xaki bini, nan ma ta gyad'a kanta, yace idan an fara biki ki masa magana kina so ki bini kuma ke bakya son karatu anan sai acan, tayi shiru batasan dalili ba yau tana jin wani nishadi a tare da ita wanda ta dad'e bata ji ba tun ranar da suka rabu, ya gyara masu kwanciya yana fad'in barci hidaya itama murmushi tayi tare da sa hannu ta rungumo sa tana fad'in good nyt, shiru yayi yana kallon ta daren yau mamaki take bashi, cikin son gwada ta ya kai hannun sa cikin rigar barcin ta amma ga mamakin sa rumtse idanun ta kawai tayi tana fad'in ba kace barci xamuyi ba, da kyar yace shikenan na bari, pray for us....


*littafina na kud'i ne kada ka karanta baka biya ba xaka bada haqqi inda baka da ikon biya, idan kana so kayi magana ta wannan number 08169334980*
[11/20, 10:25 AM] Ummi Tandama: *SULTAN MERAH*

*littafina na kud'i ne kada ka karanta baka biya ba xaka bada haqqi inda baka da ikon biya, idan kana so kayi magana ta wannan number 08169334980 or? 08030811300*


41

Kallon sa tayi tana fad'in kai wane irin mutum ne da bashi da xuciya.

Bai yi magana ba ya xauna had'e da tankwashe qafafuwan sa yana nuna mata kusa dashi alamar ta xauna anan.

Na xauna kusa da kai akan wane dalili, taja qaramin tsaki ta nufi hanyar fita yasa mata qafa ai kuwa ba shiri ta fado jikinsa saura kad'an suyi baya ya taro ta, tsura masa idanu tayi kamar yanda shima ya kafe ta da idanuwa, yatsansa yasa yana xagaya lips d'in ta dashi a hankali ya soma yi qasa dashi xuwa qirjinta, ta bige mashi hannu tana qoqarin tashi ya riqe ta kyam.

Muryar baffa suka ji yana fad'in, baxaka bud'e qofar ba kaxo ka fice min a gida shashasha, ke hidaya me kike jira kika xauna sauraren sa maza fito.

Ko tunanin me sultan yayi sai ya ture ta ya tashi ya bud'e qofar ya fito, baffa na ganin sa ya soma balbalin fad'a duk kalar xagin da ya xo masa ranar ba irin wanda bai ma sultan ba, sultan ko kallon sa bai yi ba yasa kai ya fice daga gidan.

*

Aiman da kansa ya shirya ya nufi qauyen tare da jagorar fu'ad shine ma ya tuqa mota.

Sosai aiman yayi mamakin qauyen da yanda sultan ke xarya acikin sa kamar mai xuwa unguwa, dama wannan qauyen hidaya ta fito, yau gashi sanadin sultan yaxo inda bai Ma taba tunanin xuwa ba.

Baffa na ganin aiman ya tarbe sa cikin farin ciki, tabarma ya shimfida masa suka xauna duka, hidaya na jin daddy ya xo ta fito da sauri tana gaida shi sai kallon ta yake duk ta canxa kamar ba ita ba, sam hidaya baxata iya rayuwar wannan qauyen ba daga yanayin yanda jikinta ya soma komawa a yanxu.

Baffa yace ina ce ba dai kaxo kan mgnr hidaya bane dan har yanxu? ina kan bakana baxata koma ga wannan yaron ba.

Murmushi aiman yayi yana fad'in ai kana bari mu gama gaisawa kaji dalilin xuwa na tukunna, maganar komawar hidaya ya rage naka sultan matsayin d'a yake a wurin ka xaka iya bashi ko ka hana shi ban damu ba, ni naxo kan maganar karatun hidaya ne saboda admission dana nema masu ya kusa fitowa, ban sani ba ko harda karatun ka yanke mata qauna daga samun sa?

Baffa yayi shiru jiki a sanyaye da kyar ya bud'e baki yace aa ni ban hanata karatu ba domin yana cikin burina, qoqarin da kake akan hidaya Allah kad'ai xai biya ka kuma nagode sosai Allah ya saka ma.

Aiman yayi murmushi yana fad'in amin, ya dubi hidaya yana fad'in sai kika manta da daddy ko sau d'aya baki nemi kije ki gan shi ba.

Tasa tafukkan hannuwan ta tana rufe fuska cikin jin kunya, tace aa daddy kullum kana raina kuma xan xo na ganka har gida.

Allah yasa ya fad'a yana tashi tare da xaro kud'i a aljihunsa ya ajiyewa baffa yana fad'in har yanxu kud'in sadakin hidaya ne na biyo ka dasu da ka barmin ina ta ajiya, sultan xai xo xaka iya bashi sadakin ya bada takardar hidaya ni kud'i sun fita daga hannu na daga haka bai qara cewa komai ba yayi masa sallama ya fice.

Sosai ranar aiman ya bar baffa da tunani iri iri.

Dawowar da kwana biyu daga qauyen ya dubi sultan bayan ya gama breakfast yace ka d'auke qafar ka a wannan qauyen har xuwa wani lokaci, sultan ya tsura masa ido jin dalili Afiya kuwa kallon sa tayi tana fad'in aa saboda me inaji kace ka cire hannun ka a wannan al'amari miye damuwar ka yanxu da xuwan sa ko rashin xuwan sa.

Aiman ya tashi yana goge bakin sa da tissue, umarni nake bashi a matsayin mahaifi ba shawara ba kada ya taka wannan qauyen har xuwa wani lokaci, ya juya ya fice.

Mami karki ce komai please barshi dama ko bai hana ba baxan ne ba nagaji da wannan wulaqanci ni yanxu kiyi masa tafiyar komawa na, am tired of this country, ina so na koma qarshen wannan watan.

Tace shikenan ba damuwa gwanda ka koma ka huta ma ko xaka manta da wannan yarinyar, idan kaje ka kula da kanka sosai bana so ka saka wata damuwa a rai kuma.

Yace insha Allah mami...

*
Ranka shi dad'e, alfarma naxo ayimin kamar yanda ake yi ma kowa a gidan nan nima aure nake so ayi min.

Aure?sarki ya tambaya yana kallon fu'ad d'in,

Yace eh, nima granny ayi min aure kamar yanda aka yiwa sultan tunda nama girme sa fa.

Saboda sultan yayi aure kake so ayi ma aure, ina ji kasan dalilin nashi auren ko.

Fu'ad ya tunxuro baki, ni dai a duba min nima ayi min tunda dai har na buqaci hakan.

Yace gaskiya ne da kaima kaje ka d'auko abin kunya gwanda ayi ma auren kuwa, ya janyo wayar sa yayi kiran aiman cikin gaggawa kana ya kira aliyu shima yana neman sa da gaggawa.

Fu'ad ya dube sa cikin bacin rai yana fad'in meyasa xaka kira su naxo muyi magana a sirrance sai ka kira su Abba yau na shiga uku.

Na kira su ne saboda ka maimaita abinda kace, sai ka xauna anan kuma idan kayi yunqurin fita daga falon nan xan saka sarkin fada ha hukunta min kai.

Fu'ad ya d'auke kansa gefe yana qunquni, ya jima sosai a wurin kafin iyayen maza su xo, anan sarki ya saka shi maimaita abin da ya fad'a, aliyu xai yi magana aiman ya katse sa tare da kallon fu'ad d'in yana fad'in wacece kake so?

Cikin fad'uwar gaba yace yasmeen,

Aliyu yace ita amira fa me kake nufi?

Sarki kuwa sai cewa yayi xancen banxa kake duka duka yasmeen d'in tashin yaushe ce da xaa aura maka ita.

Aiman shiru yayi cike da mamaki shi yama rasa me xai ce, ko amira dake da 20 baida burin aurad da ita a yanxu ballantana yasmeen dake da 15 yana ji ko Afiya baxata yarda da hakan ba yanda take ji da yasmeen autar ta.

Fu'ad yace amma ai hidaya ma yarinya ce aka bata sultan k.... Aliyu ya bige mashi baki yana fad'in kaine xaka fad'a mana abinda yafi dacewa kome, baxaa baka yasmeen ba ko amira baxaa baka yanxu ba sai nan gaba.

Cikin tashin hankali fu'ad ya juya yana kallon merah kamar xai yi kuka yana fad'in dan Allah daddy ka bani yasmeen ni ina son ta kuma itama tana sona ka tambaye ta kaji.

Aiman yace karka damu xan baka yasmeen.

Sarki yace aa ni ban amince ba ban yarda ba a aurad da wannan yarinyar ba a yanxu.

*

Bayan kwana biyu fu'ad na xaune akan motar sa sai ga xiyada,

Yace oh baby kwana biyu kina duniyar kika bata bat.

Ta yatsina fuska tana fad'in ba dole ba tunda an guje mu, ina son sultan ya guje ni.

Yace ki bar maganar sultan ynxu cos yayi maki nisa.

Tace hakane ni wani xance ma nake ji a wurin qaseem wai da gaske sultan yayi aure.

Fu'ad yayi dariya yana fad'in yayi aure kuwa yana nan da xankadediyar matar shi fulani son kowa qin wanda ya rasa sai ma kin ganta.

Tace duk abinda nayi da tsumayen soyayyar sa dana yi duk ya xama aikin banxa kenan, kama san me nayi masa a baya wurin party d'innan dan kawai na sami hadin kansa ko xai so no.

Fu'ad ya girgixa kansa yana kallon ta galala, nan kuwa ta soma yi masa bayanin komai kafin ta qarasa fad'a ya d'auke ta da wawan mari, ya sauko daga saman motar tare da kai mata ball a qafafu ya kwashe ta sai da ta fad'i.

Da qarfi ya ja ta cikin bacin rai yayi cikin gidan da ita, dad'in abin kowa yana falo ya cillo ta yana huci.

Kai miye haka sultan ya fad'a yana kallon sa yana kallon fuskar da kamar ya Santa amma ya kasa tunawa.

Ya dube ta yana fad'in ni nama kasa magana tun d'axu xaki fad'a masu abinda kika gama fad'a min ne ko sai naci uban ki yanxu ga fad'a yana xare belt a jikinsa, sosai hidaya ta tsorata qaddara ta kawo ta gidan yanxu take dana sani, tana kuka ta sanar da su komai, Afiya ta tashi tana fad'in dama nasani ai ni dama nasan ban haifi dan iska ba amanar sa akaci kuma ke sai na sa an hukunta ki xan nuna maki qarfin ikon sarauta ko waye uban ki kuwa a garin nan, saboda sharrin da kika qulla na tashi rasa rayuwar d'ana ashe kece silla.

Aiman kasa magana yayi saboda mamaki, ya dubi sultan da yayi shiru kawai ya kasa komai yace ku d'auke ta kuje da ita wannan qauyen ta fad'a a gaban baffa da hidaya domin wanke halayar d'ana da ake son batawa sai ku dawo da ita nan fada wurin sarki shi xai hukunta ta dai dai laifin ta.

Xiyada ta d'ora hannu aka ta rusa kuka amira ta kai mata rankwashi mai xafi cike da bacin rai tana fad'in Allah ya isa annamimiya.

Haka suka xo qauyen da ita ta qara bayani a gaban baffa da hidaya, baffa bai yarda ba tabe baki yayi yana fad'in wani sabon salon yaudara aka xo dashi saboda na bada hidaya to baxan bayar ba dalla ku tashi ku bar min gida kun je kun shirya wasar ku xaku xo kuna min qarya gani marar hankali.

A fusace suka bar qauyen hidaya kuwa tuni jikin ta yayi sanyi, ta tuna halayya na sultan tabbas xaa iya masa sharri domin sultan bashi da neman mata ko kula su.

Tun daga lokacin bata qara jin ko motsin sultan a qauyen ba duk da tana cikin damuwa bata bari baffa ya sani ba har tsawon sati biyu kuwa ya d'auke qafar sa a gidan.

Bayan ta sallame sallah tana xaune akan darduma ta soma tuna rayuwar ta a gidan aiman.

Ya kula da lafiyarta da aljihunsa yayi sanadiyar farin cikin ta wanda duk duniyar nan babu wanda ya bata shi samuwar idanun ta, ya ciyar da ita, ya tufatar da ita, ya riqe ta da hannu biyu kamar yar sa ta cikin sa cikin so da qauna batare da hantara ko tsangwama ba, idan bata farantawa Merah ba bata gode masa ba, jikin ta ya mace murus ko carbin da take ja ta kasa ja, taya xata faranta masa banda ta koma gidan sa Karo na biyu a matsayin mata ga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login