Showing 3001 words to 6000 words out of 26971 words

Chapter 2 - KASAITA BOOK 1 COMPLETE PDF BY MARYAM KABIR MASHI.doc

tana digiri Win ta a kan Education, shekararta ta farko.

Shi kuwa yana shekarar ?arshe ta kammala digiri Winsa,a lokacin yana Wan shekara talatin da biyar kenan. A shekara sha Waya ya je Jos, ya yi shekara Waya ashirin kenan, suka yi ya?i da jahilci shekara biyu, Sakandire shekara shida, shekara biyu sharar fagen shiga jami'a, Diploma kenan, sai haWa digiri shekara uku, sai kuma kammalawa da bautar ?asa ya Wauke shi shekara biyu.

Tunda Allah ya haWa Momeena da Dad Wina, Mahaifinta ya nema masa aiki a ma'aikatar (NNPC) ta Jos, ya kama masu wajen zama. Mameena gidan Dad ta kammala karatunta na digiri, da tana aiki a ma'aikatar Ilimi (Ministry of Education), amma daga baya Dad ya hana, saboda maza da suka dame ta. A hankali har Allah yasa komai nasa ya bun?asa, amma har yanzu sana'ar shigo da kayan Gwanjo tana nan Dad na yin ta,irin tasu ta manya-manyan ?an kasuwa.

Saboda yanzun haka, ba ya aikin gwamnati, sai dai siyar da motoci da harkar Gwanjo da ta safarar kayayyaki ?asashen duniya. Amininsa abokinsa Wan uwansa, wanda suka fara harkar tare shi ne Alhaji Kabir babansu Aminiyata ?ar uwata Fatima Kabir.

Mahaiyata Mamee, wacce sunanta na gaskiya Sharifat,iyayenta ?an asalin Syria ne,mahaifinta ne yazo aikin wakilcin Syria a Nijeriya (Ambassador) ya zo da su Mamee suna ?an mata,a inda Mamee ta gama makarantar gaba da Secondary a Najeriya ta fara karatun digiri Win ta a jami'ar Jos.

Mahaifin Mamee ya zo Najeriya tun shekara ta 1973, a lokacin mulkin Gen.Gawon, a inda ya ji daWin zaman Najeriya, ya yanke hukuncin zama a cikinta,a lokacin da ya kammala aikinshi. Su Mamee su biyu ne a wajen iyayen su, ita da ?aninta Saifullah.

Shekarar iyayenta goma sha Waya kenan da komawarsu Syria,a lokacin kuwa ina da wayona sosai, saboda ina ?ar shekara sha biyu a inda suka tafi da Yaya Habib can ?asar,a wata jaha wacce take mai albarkar noma da kiwo. Kenan zan iya cewa kakannina Fulanin Larabawa ne, yanzun haka su kan zo lokaci-lokaci,mu ma mukan je masu ziyara.

Mu uku ne kacal su Mamee suka haifa,Aunty Salwa ita ce yayarmu, shekara biyar ta baiwa Yaya Habib. Ni kuma shekara biyar Yaya Habib ya bani, kenan Aunty Salwa shekararta talatin da uku,Yaya Habib ashirin da ta?was, sai ni ?ar auta ashirin da uku.

Dukkanmu mun yi digiri, amma Aunty Salwa a gidan mijinta ta yi shi,tana ?ar shekara sha takwas aka yi mata aure, ta gama makaranta da shekara Waya kenan, yanzun haka ?a?anta uku. Shekarar ta sha biyar da auran Uncle Abdul?adir,amma suna zamansu lafiya.

?an ta na farko shekararsa shida, sai ?ar yarinyarta mai shekara biyu Haulatu, har yanzun kuma shiru, amma Uncle ya hana ta yin aiki, sai dai tana yin kasuwancin siyar da injinan sa?a da na keken Winki, da na hawa, kuma mijinta Uncle yana da abin hannunsa sosai.

Yaya Habib yanzun yake digirinsa na biyu a jami'ar Syria,wanda ya yi karatunsa ne gaba Waya a can ?asar,wajen iyayen Mamee. Yana karantar (Agronomy) karatun fitar da tsiro daga cikin ?asa.

Alhaji Fahat shi ya zaSa masa wannan fannin,wato mahaifin Mamee kenan. Yaya ba mazaunin gida ba ne, sai dai in yazo hutu.

Ni kuwa na yi primary Wi ta a Al-Imam School of Science nan Jos,na yi Sakandire Wina a Minna,amma nan Jos na kammala makaranta ta, inda a can ne na haWu da Anwar tsawon shekara huWu muna tare da shi.

Mahaifinmu Alhaji Sani Sa'id, yana nuna mana ?auna fiye da tunanin kowa, shi yasa mu ma muke ?o?arin yi masa abin da zai ji daWi, balle ga girma ya tunkaro shi, saboda mutum Wan shekara sittin da takwas a duniya,ai mun san dattijo ne, sai dai jin daWi yasa ba'a gane tsufan jikinsa.

Ina da ?yau,ko ni na sani, sai dai farina irin na Larabawa ne wato fari mai haske. Structure Win jikina kuwa na burge ni,ga manan ?irjina daidai ne, yawancin ?awayena suna cewa ina yanayi da ?ar ?asar Indiyar nan wato Pretty Zeenta,sai dai wai na fita fari mai ?yau, kuma gashinmu ba iri Waya ba ne,ni irin mai laushi ne irin na Larabawa, ita kuwa nata mai tauri ne,ko kuwa a ce bazar yake.

A unguwar Refin Rizont gidan iyayena yake,gani ?ar gata gaba da baya, saboda ?auna da ake nuna mini,balle kuma ni ce auta.

**** **** ****

Hidima kamar ta yi mini yawa, balle yau ne ranar walimar iyaye da abokan arziki (Dinner party). Rana ce wacce da iyaye da ?a?a da abokanan arzi?i ke haWuwa, to balle hidima irin ta manya haka.

Yau ne mahaifin Fatima, wanda yake abokin wasa ga Dad yake yin party Win Wiyarshi ta uku, wacce take ?ar'uwata, Aminiyata ga ta ?awata. Biki kuwa irin na manya, kowa ya san shuwagabannin kasashe ke taruwa ban da Sarakunan duniya.

Tabbas sun taru a yau. A hotel Win jero wanda shi ne Hotel na biyu a Jos a duk faWin Jos. ?an gidajen rediyo da talabijin kuwa ba zan iya ?irga yawansu ba, ballantana kuma dama kowanne shugaba in zai zo da tawagarshi, zai taho ne da ?an Waukar hotansa, ban da ?an Waukar hotan kaset (Camera man) da ?an gidan rediyo na garinshi.

Shi hall Win kuwa,an jera masa kujeru na alfarma, amma za a iya cewa duk tebir Waya mutum uku ne zagaye da shi, suna kallon saman Wakin taron, manyan sarakuna da shuwagaban ?asashe kuwa su ne irin lafiyayyun kujerun nan da ake keSewa (VIP Cushion).

Kowa ya san in an haWo irin wannan taro a kan Wauki lokaci ana gabatar da shirye-shirye tun da akan gayyato mawa?a kala-kala, da ?an wasan ?wai?wayo na Turanci, da na yare, sai an gama irin wannan sha?atawa sannan ma ake buWa fili da ?an surutai, da kuma sannu da zuwan ba?i wanda uban ango da na amarya ke yi.

Da waWanda aka Wora a matsayin ba?in taro,a kan ba ango da abokinshi fili su yi godiya. Ango kenan abokin ango ya gabatar da halayen ango masu ?yau, haka ?awar amarya ma takan yabi ?awarta. Amarya kuwa godiya kawai take yi da nuna murnarta.

Yau ne duk ranar yin haka, wanda tuni Wakin taro ya cika ma?il da jama'a, kafin komai ya fara bayyana kaset Win kiWa mai fitar sauti a hankali (Slow music) a lokacin kuma ?an mata masu rabon abinci ke ratsa mutane suna ajiye masu ?an kayan lasawa, kafin a gama a fara kawo abinci.

A cikin ?an matan kuwa har da mu ?awayen amarya, wanda muka dinga yawo da ?an farantai a hannu muna raba madara mai ?an?ara da lemun ?wali da ruwan doguwar roba (Ice Cream,Lemon juice, and Swan water).

Ni kaina na san duk Wakin taron nan mutum Wai Wai ne wanda hankalinsa ba ya kaina, shi ma sai dai in bai hangoni ba, saboda ?yau da Allah ya yi mini. Riga da wando ne a jikina, amma ruwan ba?a?e, sannan kuma masu Wauke idanuwa, saboda yadin mai she?i ne tamkar madubi.

Wando ne har ?asa, amma daga ?asa a buWe yake, sai rigar kuwa ?ar iya ?uguna, wanda hannunta kuwa na shimi ne, Wan siririn gaske, amma doguwar riga mai buWaWWan gaba da dogon hannu ita ce a saman shimin nan, wanda Wan abin Salle doguwar rigar dai dai saman cibiyata yake.

Gashina ya sha gyaran kanti, wato (salon), amma na taje shi gaba Waya ya bi bayana, sai she?i yake,dama Tubarakallah! Ga shi ba?i??irin, tamkar izgar ba?in doki,dama asali ni ba mai Waura Wan?wali ba ce ba, saboda haka ma baya cikin tunanina, sai dai na Wan yanko ?alilan daga cikin gashina ya sauko gefen fuskata, wanda yake Wan saka ni aikin gyara shi idan na du?a ajiye ?an kayan lasawa a gaban mutane.......



*?ASAITA BOOK 1*


*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*


Page 3


Fararan takalma ne a ?afata, sannan sar?a da ?an kunne ne a wuyana, amma na (Diamond), wanda duk sun ?unshi agogon hannuna da zobunan hannuna guda huWu, ba?in fenti ke li?e a farcina na (Lamp paint), haka ba?in jam baki ne manne a leSSuna na, wanda ke she?i.

Lallai ni kaina na san na yi ?yau, wannan ?yau nawa kuwa ina ta?ama da shi,ga takalma na masu tsinin gaske ko'ina na kai (Ice Cream) Win nan sai sun yi mini magana,ni kuwa dama ba mace ba ce mai son magana, wannan yasa sai dai in yi musu murmushi wanda ?ar lotsawar gefen kumatuna ke bayyana (Dimple).

Ina cikin rarrabawa ne kuwa har na kawo wani tebir a tsakiyar Wakin taron, na ajiyewa na gabana,na ajiyewa Wayan na kusa da shi, sai na ji mutanen nan biyu na cewa.

"Allah ya ja da ran Gimbiya,Yarima na gaishe ki."

Na samu na gyara gashin da ya rufe mini fuska. Gabana ne naji ya yi mummunan faWuwa a daidai lokacin da na Wago kaina na ga mutumin da motarshi ta bige ni,a tsakiyar titin unguwar Ahmadu Bello way,wanda tamkar ya banke akuya shi ne kishingiWe a cikin kujera ko motsi ma ya kasa yi don mulki zan ce ko ?ASAITA.

Na yi masa kallo wanda ya kai na minti uku, a inda na ?ara karantar fuskarshi,a cikin kallon da nake yi masa ne naga da ?yar yasa hannu ya cire farin gilashin da ke manne a saman idanuwanshi, sannan na ga ya lumshe idanuwansa duka biyu, sannan ya buWe.

Da hannunsa mai gilashin nan ya Wan yi masu nuni kaWan, sai naji sun ce, "Yarima na amsa gaisuwar ki."

Nayi murmushi da ke bayyanar mini da asirtaccen ?yauna, wanda na yi shi ne don haushi da takaici da nuna masa cewa nima fa na isa,?yau yake ta?ama da shi, nima a?wai wanda ya fi nasa a jikina.

Na rausayar da gashin kaina, ya shafi fuskarshi, sannan na sunkuya na Wauke kayan lasawata,ice cream da lemuna har ruwana, na mayar a gaban na kusa da shi, sannan na mi?e na yi gaba abina,a zuciyata na ce, sai dai wata ta kawo maka ba dai ni ba, nima nan da ka ke ganina sarauniyar kaina ce, iyayena kawai nake wa shagwaSa sai kuwa yayyena.

Tsakanina da Dad da a?wai nisa, sannan ga shi cikin jama'a yake, waWanda suke manyan mutane ne. Wannan ne ya hanani in isa wajen Dad in nuna masa azzalumin mutumin da ya kaWe ni, sannan ga tsoro ina ji, kada in tafi wajen tsurkun nunawa Daddy shi, wani ya ce yana sona a cikin mutanen da yake tare da su,ni kuwa sai angona Anwar.

Bayan Wakin taro ya nutsu ne aka bayar da umarnin cewa amarya da ango su shigo Wakin taron, cikin mintina goma (Martina Desginer) jikina da ?walliyar dark blue les mai dige-Wigen fari, musamman domin ta gyarawa ?an matan amarya jiki aka Wauko mana ita.

Gwaggwarona kalar fari, haka takalmana, da jaka ?ar sagale a hannuna,?ar siririyar sar?a ce mai kalar fari a wuyana, wacce zamu iya kiranta da suna Diamond, gashin kaina kuwa nannaWe shi na yi waje Waya, tamkar naWin da Indiyawa ke yi wa gashinsu.

Wetlips ne kawai a laSSana, sai dai zagayan saman laSSan nasa masu jagira mai kalar fara. Kowa ya hango ni, sai ya yi zaton ni ce amaryar, sai dai don ita amarya ta sha bamban a duk inda take, gefen amarya nake, shi ma abokin ango a gefen angon yake, kenan mun jera layi a kan mutane huWu-huWu, maza biyu mata biyu.

Dole Wakin taron ya kaure da surutai don ma dai taron manya ne har ihu ma sai anyi, saboda ni kaina nasan mun yi ?yan da za a iya Waukarmu a matsayin (Magazine) ?inkunan zamani ne a jikinmu in ka ganmu tamkar an shirya mu ne domin a sa a Magazine Win (Ovation Magazine).

Fitowarmu ke da wuya, sautin kiWa ya canja a hankali ya soma tashi, wanda har muka isa wajen zamanmu,saman Wakin taron daga gefe Waya, saboda gefe Waya an bar shi ne saboda ?an wasa.

Abin ka ga garin da ya tara yarurruka kala-kala, wannan yasa kusan yare ashirin suka yi raye-rayensu da wa?o?in su, sannan aka koma wasan ?wai?wayo, inda ?an Legas suka yi nasu a kan zamantakewar auratayya da tarbiyyar yara.

?an wasa kuwa shahararru ne, irin su Pate Odochi,Sam Loco,Ramsy Noah,Geneve Nneji,Liz Benson,Mama G. Gaskiya wasan ya yi ?yau, dole ne ma fili ya Wauki tafi,abin ka ga mutanen da ba su da Addini duk da ita ma Jos da sau?in Addinin, amma yanda suka shirya shi ne kamar da gaske, shi ya burge ni. A nan take na ji ina son yin auren, saboda rayuwar da suka nuna.

Kamar an ce in Waga kaina, sai na hango wannan sakaran mutumin wanda ya kaWe ni ya wani ?wanta a kujera sai fizgar kai yake yi, kowa ya kewa, Oho. A zuciyata na ce yau ka faWa, da Dad zan haWa ka,kasha dukan tsiya.

Bayan fitarsu ne sai fili ya Wan ruWe kaWan da hayaniya,in Wan kalla sosai sai na ga ashe shahararrun ?an wasan Hausa ne na jahar Kano waWanda muke gani a cikin talabijin yau ga su a fili, kamar su Iyaye Alhaji Ibrahim Mandawari, Alhaji Hamisu Iyantama,Kabiru Na ?wango, Shehu Hassan Kano,Usaini Sule ?o?i,Kabir Mai Kaba. Tare suke da ?an fim Win su maza da mata. Sai iyayen fim din su mata na biye da su kamar su Hajara Usman salihar mace,Saratu GiWaWo macen da kowa ke so, Jamila Haruna kin fi kama da matar Gwamna da dai sauransu.

In na tsaya lissafawa ba zamu gama ba,sun yi wasan ?wai?wayonsu a kan samu da rashi sannan da mutuwa da kuma ?aunar iyaye da ?a?ansu, wasan kuma ya sanyayar da zukatan mutane, wanda a take kowa ka kalla ya yi la'asar, tamkar yana jiran Mala'ikun mutuwa su iso kanshi.

Bayan nan kuma Waya bayan Waya aka dinga tashi ana magana da ?o?on fitar da sautin magana da ?arfi (Microphone), iyaye,abokan arzi?i, shuwagabanni,a inda har wani shugaba a nan Jos ya baiwa ?an wasan Kano ?yauta ta motoci guda biyu, saboda yawon wasa da suke yi.

Wannan ne ya buWe fili aka dinga yi musu ?yaututtuka. A ?arshe abokin ango ya fara faWin halayyar abokinsa, ya kuranta shi, inda ni ma na tashi na yi, duk fa da harshen Turanci,dama su ni an iya turancin hanci (Slang) shi nayi a wajen. Ni kuma na san duk wanda ya ganni a tsaye ya ji turancina kuma ba zai taSa Waukar ni bahausa ba ce ba, sai dai ?ar ?asar tsallake.

Ango ya yi godiya, amarya ma haka, daga nan sai aka dinga rarraba abinci wanda duk ka ke so, sai ma an tambaye ka wanda nan kuma masu raba abincin Hotel Win ne ke aikinsu (Waiters).

?arfe biyu da rabi na dare aka tashi ba wai watsewa ba, saboda in na tashi ne ake samun damar gaisawa da jama'a na nesa da na kusa. A lokacin Wakin taron da wajen ya baje da jama'a ana ta gaisawa tare da yin hira da su a gidan talabijin.

Da ?yar na samu na je na gayawa Dad cewa na ga mutumin da ya kaWe ni, kafin in waiga in nuna masa shi ya Sace mini,wannan yasa na yi saurin jan Waya daga cikin ?awayenmu na fita wajen Hotel Win, domin in samu damar Waukar lambar motarshi.

Cikin Wan sauri-sauri muke tafiya, a inda na ci karo da wani, wanda har sai da muka haWu da juna sosai, turaren da ke jikinsa kuwa, irin mai sanyaya zuciya ne, ina jin ?arar faWuwar jakata da wani abu a ?asanmu, duk wannan bai fi cikin sakan uku ba, maimakon in kalli ko waye sai na du?a don Wauko masa wayar hannunsa, wacce ta faWi tare da jakata.

?agowa ta kuwa ta yi daidai da du?awarsa ya Wauko mini jakata yana Wagowa ina shirin ba shi ha?uri, saboda a zatona ya yi tsaran iyayenmu, sai kawai haushi ya kama ni a take kamar yanda na lura al'ajabi ya kama shi mutumin da nake faman nema in nunawa Dad Wina,shi ne muka yi karo da juna.

Na rasa me zan ce masa, na yi tsaye da wayarsa a hannuna, shi ma da jakata, ganin shi ba shi da niyyar yi mini magana, saboda tsananin girman kai, yasa nima na ?i tanka masa, sai dai na fizge jakata da ke hannunsa ta ?arfin tsiya, sannan na jefe shi da wayar da ke hannuna, ta faWi ?asa ta tarwatse.

Wannan ta yi daidai da tahowar wasu gungun shuwagabanni, za su wuce gamu mun tsare hanya,?awata Uwani ita ta janye ni cikin sauri sannan na ga ta sunkuya ?asa tana tsince masa tarwatsatstsiyar wayarsa, wanda ta bi shi da sauri don ta bashi, saboda gungun mutanen sun yi gaba da shi.

Wai sai da na Wauki mintuna biyar a tsaye sannan na yi saurin tunowa da lambarshi fa zan Wauka ta mota. Na fita cikin zafin nama ina ta waige-waige, amma ko kalar mai rigar sa ban hango ba.

Na gaji da waigena har na juya zan koma ciki, sai na ji Uwani na ?wala mini kira na yi saurin wai??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????gawa domin in gano inda take, saboda na ma san na gane mutumin nan, amma sai na ganta ita kaWai, na yi saurin taryar ta, ina tambayarta.

"Ina yake, ina yake?"

Wai tambaya take wa? Na ce mata wanda ki ka kaiwa waya. Sannan ta nuna mini motar da yake ciki wacce ta kusan fita daga hotel Win, ba kuma za a iya hangen lambar jikin motar ba, balle a Wauka.

Haushi ya kama ni na dinga yi mata faWan masifa a taron nan,a haka har aka tashi wannan taro, ina cikin Sacin ran rashin Waukar lambar motar nan.

Bayan mun je gida na sanar da Dad abin da ya faru,nan ya ce inyi ?o?arin Waukar masa lambar in na yi haka, to shi kenan in sa ido, na amsa masa tare da ?udirin sai na Wauke ta in Allah ya yarda, amma har muka gama biki ban ?ara ganin ko mai kama da shi ba. Wannan kuwa ba ?aramin takura ni ya yi ba.

**** **** ****

Bayan ?wanaki arba'in da huWu da gama bikin Fatima da mijinta Ibrahim, wacce take da mahaifinta da Dad abokan wasa suke. Ni kuwa bayan bikin ban ?ara zuwa inda take ba, sai yau ranar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login