Showing 21001 words to 24000 words out of 26971 words

Chapter 8 - KASAITA BOOK 1 COMPLETE PDF BY MARYAM KABIR MASHI.doc

ka koya." Jin kamar ta yi Wan shiru yasa na yi saurin yin baya na samu ?asa na zauna.

"Haba Yasmin!"

"Na ji an faWa, na yi saurin Waga kaina. Mama ce, "Nan fa ya zama gidanku,ki saki jikinki."

"Na yi murmushi, ta zo ta zauna kujerar kusa da ni, sannan ta kama hannuna ta sa mini awarwaraye da zobe.

"Na gode Yasmin,ki je kuyi ta ha?uri kin ji ko, balle ma na san za ki samu kulawa sai na kawo muku ziyara."

Nayi godiya, sannan muka yi sallama. Ai tunda muka shiga mota ban kalli inda ma yake zaune ba, saboda ba?in ciki,wai ni Yasmin ce yau ake tambulan da ni ga Wa namijin da ba na ?auna,wai har ba shi baki ake yi da lallashi a kaina dole ne in zo in tayi masa abin da zai ji haushi, har ya ha?ura da ni,a raba auran don dole.

Safiya na yi na sa aka kira mini jakadiya,na tambaye ta wa ke tsaran gidan yari? Ta amsa mini da Sarkin tsaron gida, na ce ta sa a kira mini shi, shi da mai kula da basu abinci, wanda ta ce mini sunanshi Ma'aji.

Suna zuwa na umarce su da su shiga dafa abinci mai ?yau kamar wanda suka san ana ci su dinga ba ?an gidan yarin, kuma sau huWu a rana. Da wadataccen ruwan sha, sabulun wanka,wanki,kayan sakawa, na tabbatar zan yi masu ?yautar da ba su taSa kawowa zuciyarsu ba, sannan tabbas zan iya kai masu ziyarar bazata,a duk lokacin da na so. A take na ce masu idan Yarima ya tambaya suna iya ce masa ni na saka su, na Waga filon Win da yake kusa da ni, na Wauko bandir Win ?an Wari biyar guda huWu na basu na ce su raba.

Na kawo guda shida na basu na ce a siyi duk abinda aka san babu. Nan Ma'aji ya tabbatar mini a?wai komai, ya ba ni labarin irin kayan abincin da ke gidan nan,ya tabbatar mini za su iya ciyar da mutanen Jos da ?auyukansu har na tsawon shekaru goma, mai ?yau mai daWi.

Bayan sati biyu ta cika ne,a daren ranar sai ga jakadiya da mace Waya tana biye da bayanta,a inda ta tsugunna ta gaishe ni. Ni kuwa ina kishingiWe saman kafet ina hutawa su Mansura na gefena, ana ta ba ni labarurrukan ban dariya da nishaWantarwa.

Na ba ta iznin ta faWi abin da ya kawo ta, shi ne ta ce Yarima ne ya turo ta tunasar mini na lokacin da na Wiba ya cika, ta ajiye mini farantin hannun matar nan Waya,tana buWewa sai na ga manya-manyan kaji ne har guda uku, na Wan yi shiru na tsayin mintuna biyu, sannan na nisa.

"Ki koma ki sanar da shi cewa ni ma na san lokaci ya cika, amma ko a wancan lokacin na baya, cewa na yi ?ila, saboda haka ki mayar masa da waWannan kaya ki ce na ji sa?on shi, amma idan ya samu dama ina son ganin shi yanzun, anjima, gobe,ko duk lokacin da ya samu damar zuwa,ki gaishe shi."

Ta Wan Wauki lokaci, sannan ta mi?e, shi ma kamar ba za ta tafi ba, na juyo na kalle ta.

"Shi kenan." Ta tafi tana kiran,"To, to,ai ba gardama."

Mun samu sama da awa uku muna hira ni da ?an matan gidana,ganin sha Waya na dare ta yi yasa na sallame su,ni ma na nufi Wakina, domin kayar da kafaWata saman gado. Al'adata ce yin Sallar nafila kafin in ?wanta bacci, sannan in kawo wutirina, wanda nake ?in yi dama sai dare ya yi. Sam ban wani tsaya tunanin zuwan wani Yarima ba na haye gadona.

?arfe goma na safiyar juma'a na shirya tsab na fita,a inda na samu motocin da na bayar da umarnin a shirya mini su tun jiya. Motoci ne guda huWu, Waya ta maza ce ?an rakiyata, ragowar kuwa ?an matana ne, ba wani waje za mu ba,illa gidan yari zan kai masu ziyara in ga ko ana yi masu yanda na umarta.

Bayan na shiga mota ne, na hango Yarima saman barandar Wakinsa yana kallona, tare da al'ajabin ganin yanda na danna kaina a mota, amma abin ka da sarauta,ko ya nuna alamar ya yi mini magana, balle ya tambaye ni ina zani.

Na ji daWi ?warai da gaske, yanda na ga mutanen gidan yarin nan duk sun fara ?yan gani, duk da akwai rama a jikinsu, amma ni kaina na san ta ragu sosai, gaba Wayansu aka tara mini su,a inda na yi masu ?an nasihohi, sannan na ?wantar masu da hankali da maganganu masu daWi.

Da ganin yanda suke nunawa ka san sun ji daWi sosai,nan take na yi masu al?awarin kawo masu ?wararrun likitoci, domin a duba marasa lafiyarsu, da su kansu masu lafiyar, domin tabbatar da tasu lafiyar. Na ?ara jadadda masu cewa abinci mai ?yau kuwa yanzun ma aka fara ba su.

Sannan na ce masu za'a dinga fitar da su wajen wasanni, amma sai sun yi mini al?awarin ba za su dinga guduwa ba,in kuma na same su da cika al?awari,nima na yi masu al?awarin wani abu, amma ba zan faWeshi ba, sai idan lokacin ya yi. Bayan gama jawabina, na umarce su da su ja layi za'a raba masu wasu kayan da na zo dasu.

Tun bayan goma na safe nake cikin gidan yarin nan, amma ban fito ba sai ?arfe uku na yamma. Ina isa gida kuwa sai wanka, ban fi minti sha biyar da fitowa ba sai ga jakadiya ta russuna ta yi gaisuwa, sannan ta ce Yarima na son ganina,na bata amsa da cewa in ya shirya gani, ina nan a gida zaune.

?wana uku tsakani, amma ba Yarima ba dalilinsa, wannan ba ?aramin tayar mini da hankali ya yi ba,shin wai haka za mu yi zaman auran? Tambayar da nake wa kaina kenan daga ?wance cikin gadona, wanda tun da na yi sallar Asubahi nake cikinsa, har ?arfe Waya na rana.

Kuka kawai nake yi daga ?wancan nan, Mansura suka shigo na sanar masu cewa ba na jin daWi, ?arfe biyu saura ?wata na rana sai ga Yarima ya shigo har Wakina, ina ?udundune cikin bargo, amma ba ?udundunar rashin lafiya ba, duk ba?in ciki ne yasa na kasa tashi in yi komai.

Tsaye ya yi a bakin gadona, sai da ya Wan Wauki minti Waya, sannan ya cire gilashin fuskarsa,ni kuwa ina kallon shi da idanuwana masu fitar da hawaye.

"Ni ban san ba ki da lafiya ba, sai yanzun, sannu da jikin naki." Ya Wan yi shiru.

"Da zaki daure ki Wan saka kayanki saboda zan turo miki likita yanzu."

"Ka barshi ma, na sha magani, zan samu sau?i."

Ya janyo kujerar tebirin rubutu a gaban gado, ya zauna, ya kalleni ina kukana, amma bai iya yi mini magana ba.

Wannan zama kuwa ya Wauke shi har wajen awa Waya, sai dai ya ce mini sannu sau Waya kawai.

Bayan nan ya mi?e ya zo ya Wan dafa goshina, wanda jijiyoyin kuka suka tashi a saman shi, ina kallo yasa Wan ?aramin hankici ya goge mini hawayena,amma fa ba tare da ya yi mini magana ba.

"Zan dawo anjima." Ita kawai ya faWa ya juya ya tafi abinsa.

Haushi da takaici suka saukar mini a lokaci Waya, tare da tunano masoyina Anwar na san da shi ne, da naga ruWewa a yau, amma shi ko a tsokar naman jikinsa ma.

Sallamar da aka yi ta kai uku, sannan na amsa na bayar da umarnin a shigo,a inda nake ?wancen nan. Na ga Aunty Salwa ta shigo, ban san lokacin da na mi?e da ihu ba na duro daga gado na taryeta,sai dariya take yi ita kuwa, bayan mun zauna ne take yi mini ya jiki.

A inda ni kuma na tabbatar mata lafiya ta ?alau,ba?in ciki ne ya yi mini yawa a zuciyata,amma yanzun tunda ta iso na warke, na ?ara gyara zama, na kalle ta sosai tare da ri?e hannuwanta, kafin bakina ya motsa har hawayen da ke cikin ?wayar idanuwana sun gangaro a kumatuna.

"Aunty gaskiya ni ba zan iya wannan zaman ba,ki gayawa Dad, ya zo ya raba ni da wannan rayuwar ?iri-?iri mutum ya ce baya sona,ni ma bana son shi, amma an tursasa mu, sai mun yi zaman dole."

Na ?washe labarin duk irin zaman da na yi na tsawon ?wanaki ashirin da uku a gidan nan amma ba ruwansa da harkata.

"A'a ba ruwanki da harkarsa dai,ai shi ba laifi,yana daurewa yana kula ki,ke ce mai matsalar,ni ba ma ruwana da wannan, tsaya in dawo ga ha??insa. Shin kin san ba abin da yake ci ko sha?" Na girgiza kai.

"Kin san a inda yake ?wana,ma'ana a nan tsabtar muhallin shi?" Na kuma girgiza kaina.

"Kin taSa shiga Sangaren sa ki gaishe shi ya nuna miki baya so?"

"A'a, amma Aunty ai duk yana da masu yi masa."

"Ba ruwana da masu yi masa,ai ke dai ha??in ki zaki sauke."

"Ni wallahi Anti..."

"Ke wallahi da me? Haba Yasmin ya ki ke so iyayenmu suyi da ransu,so ki ke su kashe kansu a kanmu?"

"Aunty ki yi ha?uri abin ba na faWa ba ne."

"In ba?ya son faWa, to ki tashi ki yi wanka ki shirya jikinki,muje ki raka ni wajen Yariman mu gaisa."

"Kai Aunty in je gidansa,ai Kamar na ma zubar da ajina ne, na dai aika a kirawo shi."

"Sannu mai makaranta, saboda ai yanda ki ka Wauki kan ki ma naga alama ya wuce aji, sai dai makaranta kawai. Wallahi idan ba ki Wauki kanki da sau?i ba, zaki sha wahalar rayuwar duniya,su waWannan mutanen babu abin da Allah bai basu ba, sannan ina ki ka taSa jin auran gidan sarauta na rabuwa? Da wahalar gaske. Sai dai su auro wata su ?ara,kina kallo ya auro wata ya yi zamanshi lafiya da ita."

"Ni dai Aunty da zai sallame ni,ni ya auro huWu ma a lokaci Waya, har ya haWo da ?war?wara ma."

Nan take na ga ta daddanna wayar da ke hannunta.

"Zan gayawa Daddy halin da ki ke ciki,in ya so shi sai ya san matakin Wauka."

Na yi saurin fizge wayar daga hannunta, na kashe.

"Aunty ke daga wasa."

"To tashi ki shirya." Dole ta sa na tashi gudun kada ran iyayena ya Saci a kaina.

Riga da zani ne na wani yadi three in one mai ?yan gaske, ruwan madara ne da dishi-dishin ruwan ?asa mai duhu a jikinsa,zanan ya sha ado, kamar dai yanda ake yayi ( Wrapper Skirt ) yanzu,takalman da na sa a ?afata kuwa masu kamar silifas ne (Flat) ruwan madara ne, sai mayafi kawai da na yafa a kaina, ban wani tsaya neman Wankwalinsu ba, na feshe jikina da turare, amma ba wata ?walliya a fuskata, saboda sanyi ma da ake da ko mai ba zan shafa ba.

Farar hoda kawai na gogawa fuskata, sai kuwa man leSe da na sakawa laSSana. Jere muke da Aunty a inda na cewa su Mansura su jira in dawo. Muna isa ?ofar gidansa, mutane ne sun kai goma a zazzaune, suka yi saurin mi?ewa suka kawo gaisuwa, muka amsa sannan muka wace ciki.

Mutane ne su huWu zaune a ?asa suna ta hirarsu,falo ne shi ma ?aton gaske, wanda ba zan iya cewa ga abin da ya ?unsa ba, saboda farkon shigowa ta kenan, mutanen nan suka kawo mana gaisuwa, waWanda zan iya kiran su dogarawa. Bayan mun zauna da minti Waya sai nake ce musu su yi mana magana da Yarima.

*?ASAITA BOOK 1*


*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*


Page 12


A take Waya daga cikinsu ya ce ai ba a hawa idan har yana sama, sai dai ni ina iya hawa. Na nuna a barshi in ya sauko ma dawo. Amma Aunty ta ce sai na hau saman nan, kamar wacce zata hadu da abin tsoro, haka nake tattaka matattakalar benen, saboda na fahimci yanayin zubinsu Waya da gidana.

Duk inda na duba baya nan, har sai da na kai ga Wakinsa. A hankali na murWa hannun ?ofar gudun kada ya ji ?ara, na tura ta cikin sanWa, sannan na yi sallama, amma shiru ba wanda ya amsa mini,sai da na kai tsakiyar Wakin manufata in isa barandar gidan inda na fahimci ya fi zama.

Kamar an ce in kalli gefen Wakin, sai na ganshi ?wance a ?asa, ya yi rigingine yana bacci ba riga a jikinsa, sai dogon wando, na matso na tsugunna a hankali a gabanshi inda na ?urawa halittar Allah idanuwa.

?yau kam gashi nan a ?wance, a take sai na ji dama Anwar ne na samu a ?wance nan, amma matsala Waya ita ce hannuwanshi waje Waya ya yi filo da su, da gani kuma ka san abu ne wanda zai iya wahalar da shi.

Wai sai na tsinci kaina da son gyara masa, na mi?e zuwa gado na Wauko filo, na iso na zauna dirshen, na zare hannuwansa a hankali, abin ka da gefe nake zaune, sai kawai na ga ya yi juyin da ya iso saman cinyata, ya sa hannuwa duk biyun ya zagaye ni.

Kenan ya koma rub da ciki,a zuciyata na ce Allah ya ?ara mini,cikin ?ar dabara na samu na zame jikina nasa masa fili,wai sai na ji ina son taSa gashin kan shi inji kowanne iri ne, a hannuna na ji wani irin laushi,dama na san hakan za ta iya faruwa, saboda ba?in gashin ya yi yawa, sai dai ba shi da yawa.

Na mi?e a hankali na juya na tafi,a inda na samu Aunty na sanar da ita bacci yake yi,baccin kuma ya yi nisa, haka muka koma sashena muka ci gaba da hirarmu.

?arfe biyar na yamma na dinga haWa Aunty da Allah a kan ta sa kayan wasa mu je muyi tennis a filin wasa. Siket da riga iya gwiwa na saka,farare ?al, da ganinsu ka ga kayan wasa, saboda wuyan T.Shirt Win kore ne zagaye da ita, haka hannuwanta ma, sai bal Win matse gashi wanda na roba ne,koriyar safa ce amma farin kambos ne a ?afata.

Ita kuwa Aunty Siket Win ta har ?asa yake, sannan ta Waura Wan?walin wasa sai dai ita ma farare ne na wasa, na umarci su Mansura da su je su duba mana lafiyar filin wasan, sannan su isa da ruwa da lemo kafin mu isa, wanda tuni nasa an yi gaba da kayan wasan.

Shigar da nayi ita tasa na ji ni tamkar an yi mini albishir da Aljanna, saboda samun kaina da na yi cikin farin ciki da nishaWi,hakan yasa ma da guduna na isa filin wasan, saboda motsa jikina. Aunty kuwa ta biye mini ne kawai na san don dai ta ja ra'ayina in yi ha?uri in ci gaba da zama.

Wasa kam ya yi daWi, amma har yanzu ba wanda ya ci wani. Ikon Allah kuwa Allah ya ba ni Sa'a na ci Aunty,ban san lokacin da na dinga ihun murna ba, har da su tsalle. Kamar an ce in kai idona ga barandar Yarima, sai na gan shi a sunkuye ya dafa ?arfe yana kallonmu, kallon da nayi masa ya kai na minti Waya sannan na juyo na yi tsaki,a inda ya Wago mini babban Wan yatsa,alamar yabawa da cin da na yi.

Na kira Mansura na ce ta je ta kirawo min jakadiya ta amsa tare da tafiya da saurinta. Ban fasa wasan ba wai saboda ganin Yarima, sai dai jikina na bani kallona yake yi. Tsawon mintunan da ba su wuce ta?was ba, sai ga jakadiya da saurinta tana zuwa ta zube gefena a inda ina wasana ina gaya mata sa?o. Sa?on kuwa bai wuce ta je ta cewa Yarima ga Antina ta zo in yana da dama za su gaisa.

Gudu nake kada in ce yazo Aunty ta yi mini faWa,ni kuwa ba na fatan ?ara zuwa sashinsa,lallai zance,ko kuwa tabWijan! Ganin Yarima a filin da muke wasa, shi kaWai da silifas a ?afarshi,shin ina aka ajiye girman kan da ?ASAITAR, koda yake na lura a cikin gidan shi sau?in kai ne da shi, tunda har yana ?wanciya ?asa saman kafet,ko filo babu.

Cikin rawar jiki ?an matan nan suka sunkuya suka gaishe shi. A idona cikin mintuna biyu na ga an kafa rumfar lema da kujerunta uku amma na (Cane) irin kan Nan mai lan?waso da tebir a tsakiya, wannan duk aikin wasu maza ne, waWanda ban ga isowarsu ba, sai dai aikinsu kawai na gani. Mulki, na ce a zuciyata saboda ganin ga rumfar da aka tanada don hutawa, amma har sai da aka kafa masa wata.

Mamaki yasa na yi tsaye na ri?e ?ugu da hannuwana duk biyun, ganin yanda ya gaishe da Aunty har da Wan russunawa alamar girmamawa, yasa na dinga tunanin anya kuwa Yarima Faysal ne kuwa? Tambayar da nayi wa kaina kenan a daidai lokacin da na ga sun jera da Aunty suna tafiya zuwa ?ar?ashin inuwar lemar nan.

Har sai da suka zauna, sannan Aunty ta yi mini maganar wai in zo,a lokacin ne ma hankalina ya dawo a jikina, na iso na zauna a tawa kujerar, wacce ke gefe Waya,hakan kuwa ya yi Waya da lokacin da wani mutum ya iso da farantin kayan sha,su lemo kenan, wanda gefensu kuma tufa ce (Apple)

Hira sosai shi da Aunty. A cikin hirar na ji tana cewa, "Wai ranar da ku ka je gida Mamee ta gaya mini,cewa kun biya ta gidana ba ku same ni ba." A zuciyata na ce, Au! Ashe har gidanmu ake zuwa ba a gaya mini ba,neman shiga.

Iska ta taso mai ?arfin gaske, wanda zan iya kiranta da guguwa,jin yanayin wasu addu'o'i a bayyane yasa na yi mamaki, a inda ni kuma gashin kaina ya kaiwa gefen fuskarshi ziyara, yasa hannu ya cire shi a hankali,a inda ya ci gaba da magana da Aunty.

"Aunty ki yi mata faWa, ba ta son Waura Wan?wali ?wata-?wata, tunda ta zo gidan nan ni dai sau Waya na ganta da Wankwali, shi ma na san don gidanmu za'a."

Ta juyo gare ni, "kin ji ki daina."

"Aunty ba fa kowa a inda nake sai yaran nan su Mansura fa."

"A yanda ki ke gani ba,ni ko jiya na ji cikin dogarawana wasu na yin fasalin ?yan gashinki,kin ga kenan suna kallonki in kin fito."

Maganar da yake yi mini kuwa tana nuna cikin jin haushi yake yin ta, na kalli Aunty,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login