Showing 6001 words to 9000 words out of 26971 words

Chapter 3 - KASAITA BOOK 1 COMPLETE PDF BY MARYAM KABIR MASHI.doc

Asabar saboda in samu Ibrahim a gida shi yasa na bari sai Asabar.

Cikin isa nake jan motata zuwa unguwar Ring Road,domin kai wa Fatima ziyara, daidai wajen bada hannu ne wajen unguwar Ahmad Bello way,na tsaya bai fi mintuna biyu da tsayawa ta ba ina jiran a ba ?an layinmu hannu, sai kawai na ga ?ato ya buWe murfin motata a gaba ya shigo, ina ?o?arin yi masa magana na ji buWewar baya,waigawar da zan yi sai naga ?arti uku zaune a cikinta, sun nuna mini bindiga, wanda na gaba ya ce mini.

"Kiyi shiru,ki ja mota kawai muke so!"

Ban tsaya gardama da su ba na mayar da hankalina ga tu?ina inda aka ba mu hannu.

"Titin hannun ki na dama za ki bi."

Haka Wayan ya ce mini. Ni dai na san ba zan Sata ba a garin nan sai dai in kashe ni za su yi, saboda haka ban razana ba.

Duk inda suka ce in nufa,nan nake bi da motata, har zuwa wani mahaukacin gida, wanda yake Wauke da yawan fitilu, duk da safe ne ba kunna su aka yi ba, amma ganin su a tsaye shi ya nuna mini yawansu.

Titin get Win gidan muka mi?e, tamkar za mu wani garin, bayan mun shiga get Win gidan waWanda yake Wauke da sojoji sun kai goma sha biyar,ni kuwa ganin sojojin ma ya ?ara mini ?warin giwar in sakin jikina ma, sai da muka dinga wuce gidaje zan ce ko gine-gine, sun kai ba?wai sannan suka ce in tsaya a ?ofar wani gida mai bene,wanda saman shi yake zagaye da barandar sama.

Da gani zagaye yake kamar ?wano kenan circle ta can sama na hango ?yallin wani mutum ta labule ya Wan Wago masu hannu, daga nan sai suka ce in yi gaba na ja mota muka nausa cikin wani daji, duk fa a cikin harabar wannan gine-gine. Bayan tafiya ta kai ta kilomita uku, sannan na ga mun iso wani gida mai dogon gini kamar ginin Choci.

Nan aka umarce ni da in tsaya in fito daga motar, ba wanda ya taSa ni cikin su, suka nuna mini hanya har cikin gidan nan. Mun wuce wurare da dama, sannan na dinga ganin ragar ?arfe da mutane a ciki, wannan ya nuna mini gidan yari ne aka kawo ni,abin da ban gane ba,shin ziyara aka kawo ni inyi ko kuwa ganin wani,ni dai na san ban yi laifin komai ba......


*?ASAITA BOOK 1*


*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*


Page 4


Abin tausayi na gidan (Yarin) gidan maza, saboda duk sun bi sun rame, sun ?are,ga su nan da ?yar suke magana, masu Wan ?arfi ne ke mi?ewa su zo su kama ?arfen suna yi mana magana wadda bana ganewa.

Matattakalar bene muka haye ni da su, wanda nan naga mata birjik a Waure a zuciyata na ce laifin me suka yi waWannan bayin Allah, har da masu tsohon ciki da masu ?a?a, ga su nan a kukkulle,ni dai ?ar kallo ce har aka kai wani Waki na ga an buWe shi wai in shiga,ban musu gardama ba muka shiga tare da su.

Gado ne ?arami irin na ?an makaranta amma wanda bashi da sama, sai Waya a kusa da shi da wata ?wance tana bacci. Ba su yi mini magana ba Waya daga ciki ya buWe wata ?ofa,nan na ga ashe banWaki ne, Waya ya buWe famfo a kusa da ni, na ga ruwa ya zo, duk dai ban yi magana ba.

Sai da na ga duk sun fita suna shirin kulle ni a ciki, sannan na yi masu magana da harshen Turanci.

"Baku gaya mini komai ba har za ku tafi."

?aya daga cikinsu ne ya ce, "ki zauna za a neme ki."

Ya juya ya tafi ban ce masu komai ba,nima na Wan kalli gidan nan na zauna.

Tsayin awa Waya, sai na ga matar nan ta tashi, tana ganina ta taso a hankali ta iso wajena ta zauna.

"Yaushe aka kawo ki?"

Naji ta faWa da Hausa. Na kalleta sosai.

"Ko ba?ya jin Hausa?"

"Ina ji,Wazun aka kawo ni."

"Me ki kayi?"

"Ba komai"

"To Allah ya taimake mu"

"Musulma ce ke?"

"Eh."

Daga nan muka dinga hira da ita.

Ina nan har ?arfe tara na dare, sannan naga waWannan mutanen sun buWe in da muke sun shigo, Waya daga ciki ne ya ce in taso, na yi wa wacce muke tare sallama mai suna Mabaruka. Tana kuka na bar ta tausayinta ya kama ni. A motata muka kuma shiga na ja har gaban gidan da muka tsaya da rana.

Muna tsayawa na Waga kaina sama sai na hango mutum zaune a barandar saman bene ya mi?e tsaye sosai ya juyo tare da dafa majinginin barandar, cewa suka yi in fito, na fito na kalleshi sosai, cikin sakan uku na gane mutumin da ya kaWe ni watanni huWu da suka wuce.

Me zan ce masa ni kuma yanzu bai yi magana ba, nima ban yi masa ba. Na girgiza kaina na juya na koma motata har na tashe ta Waya daga cikin ?artin nan masu sanye da fararan T.shirt, ya sunkuyo ta gilashin da nake tu?i ya ce.

"An baki last warning saboda haka yana gargaWinki da kada ki ?ara shiga layin gonar shi, balle har ganganci ya kai ki kice za ki ratsa tsakiyar ta, ina fatan kin fahimta?"

Na Waga masa kai kawai, na ja motata har na yi nisa na tsaya na le?o da kaina na Waga masa babban Wan yatsana ma'anata a nan za mu haWu wata rana.

A mota ne na yi tunanin ba zan gayawa Dad kome ya faru da ni ba, amma ni da kaina zan Wauki mataki wanda ko a hanya ya hango ni sai ya ce a sake wata. Har na isa gida ina tunanin hanyoyin da zan bi, amma na rasa su, saboda haka na ajiye lamarin, na dangana shi da ba aikin gaggawa ba ne.

Sai da Mamee ta Wan yi mini faWa a kan nayi dare, goma saura kaWan, na san banida gaskiya na dinga ba ta ha?uri,gudun kada ta gayawa Dad shi kuwa ba wasa a lamarin sa, idan har ka taSo shi. Kun san iyaye dai.

Bayan na yi wanka na shirya jikina ne na gabatar da sallolin da ake bina, daga nan ban iya yin bacci ba, saboda tunanin hanyar ramuwar gayyar da nake son haWawa Yarima.

Wannan dalili ne yasa na tunano da litattafan novel na Turanci na shahararren marubucin nan (James H. Chase). Na san a cikin litattafan sa akwai idea zan iya samun wata hikima a ciki. DaWi, murmushi, dariya, suka saukar mini a lokaci Waya, wannan ya sa na kashe fitilar gefen gadona na koma na ?wanta, tare da tabbacin yanzu bacci zai zo mini. Haka aka yi kuwa,sallar Asubahi ma Mamee ce ta tashe ni.

Da ?yar na shawo kan Mamee ta amince na fita, shima don na ba ta tabbacin iyakata Bookshop na nufa domin neman wasu littattafai, cikin saurin da bai fi na mintuna talatin ba na dawo,lode da litattafan James, sun kai goma sha biyar.

Tun da na haye sama Wakina ko motsi na kirki ma bana son yi, abincin rana kuwa sai da la'asar na samu na ci shi. Sai da na Wauki ?wanaki goma ina nazarin litattafan nan da birona da zungureran littafina a gefe,in ta kama in rubuta in kuwa tawa muguntar ta faWo in rubuta.

Wani lokaci a falon Dad,nake shigewa saboda kada a dameni, sai na ji dawowarshi, sannan in koma Wakina, na gama karantawa saura haWa ayyuka. To yaya kenan?.

?arfe ta?was saura na safiyar Litinin wacce ta yi daidai da ?wanana biyu da gamawa, na je na samu Katung Maigadi nan na zauna na gaya masa bu?atata, a take ya ce ai wannan duk abu mai sau?i ne, tunda da akwai shi, sannan akwai abokanansa,in zan tura da kuWi kawai su zasu kawo mini aikin da suka shirya. Na yi murna ?warai da gaske, sannan na ce ya bani ?wana Waya.

Saboda na jima ban fita ba, shi ne na tambayi Mamee zan je gidan Aunty,ta amince mini. Ina isa gidan na ce mata kuWi nake so, na dinga narke mata kamar zan yi kuka, har sai da ta bani dubu goma, na bugawa Yaya Habib waya na ce masa kuWi nake so ya ce zai turo ta account Wina wato banki.

Sai da na haWo dubu talatin, sannan na Wauki ashirin a nawa (account) Win na haWa, na zo wajen Dad kuma na dinga fadanci cewa litattafai zan siyo, ya bani, saboda ganin da yake ina yawan karanta su, ya bani talatin. To saura Mamee, na girka mata kuka tun da ita ba wasa.

Ganin duk ranar kuka kawai nake, shi ne ta tausaya mini ta dinga lallashina, har tana tambayar me nake so, shi ne na gaya mata cewa account Wina ba komai a ciki, shi ne nake son kuWi in siyi litattafai, shi ne Dad ya bani kaWan ,nan ta ce nawa ne? Na ce ashirin, ta ?irgo ta ba ni.

Bayan ?wanaki tara, ya zo ya ce mini komai ya haWu, amma aikin farko kenan,yau wajen ?arfe biyar na yamma in bi ta hanyar Bank Road saboda ruwan da ake yi na san yanzu zai kai har nan da tsayin lokaci a yanda (weather forecast) ta nuna.

Cikin ruwan sama mai tsanani na bi hanyar Bank Road,hanyar da bata cika mutane sosai ba, sannan tana da haWarin bi a lokacin ruwa, ga shi yau garin na Jos shugaban ?asa ne ya kawo mana ziyara, saboda ganewa idanunshi tabbacin zaman lafiyar da aka samu yanzu a Jos, madadin rikicin da aka samu tsawon lokaci ana yi a baya. A cikin shekara ta Wari biyu da uku (2003).

Wannan yasa sai motoci WaiWai ke yawo a garin,na laSe da motata a gindin wata babbar mota na ga motocin Yarima sun wuce cikin gudu sai da suka yi nisa, sannan na ji sun bugo mini waya da in tafi,nima in bi hanyar, cikin natsuwa na dinga tu?ina, balle kuma yanda ake tafka ruwan sama.

Ban fi tsayin tafiyar kilomita Waya ba, sai ga shi na same su motocin su sun tsaya, ga ruwa ana yi balle su samu damar Wauko wasu,ga ba motoci masu giftawa, saboda ruwa da ake yi kamar da bakin ?warya.

Tun daga Wan nesa na ga mutum a tsaye da lema yana Waga mini hannu, daidai motarshi Yariman, na tsaya na zuge gilashina,nan wannan yake mini bayanin zan bayar da motata za a mayar da Yarima gida.

"A'a ka ce masa sai dai ya fito in rage masa hanya,me ma ya samu motocin naku?"

"Kawai gani muka yi motarmu ta tsaya,mun Wan tsaya gyarawa sai ta bayanmu ta kama haya?i, ba mu lura da ta Yarima tayoyin sun sace ba sai da muka ta da ita da sunan shi a isa dashi gida."

"Ka gaya masa in ya amince, amma gaskiya bana bayar da aron motata ni in tsaya nan har sai an kaishi an dawo ba,ka tuna ni macece."

"To Hajiya."

Mayar da gilashina na yi na zuge, ina kallonsu sun Wan jima, sannan na ga sun zagayo da sauri dukkansu sun kara masa lema tare da baza babbar riga,wai gudun kada ruwa ya ji?a shi,a haka suka kawo shi har motata, inda aka buWe masa baya ya shiga.

Ya koma ya ?wanta yanda yake yi, kafin wani ya zagayo ya buWe gaba,ni har na ja motata, amma don ?ASAITA ko motsi bai yi ba, balle magana.

A Hill Station Hotel na yi fakin da motata a wajen harabar ajiye motoci, ina fita suna isowa da ba?a?en kaya dogaye suka nuna masa bindigogi a cikin motar, mutane ne sun kai goma.

"Fito!" Haka Waya daga cikinsu ya ce, cikin ta?ama ya fito a daidai lokacin da ni kuma na cire ba?in gilashin da ke manne a fuskata.

Tabbas ko ban faWa ba na san mamaki ya dirar masa a lokaci Waya don dai namiji ne mai ji da mulki, shi yasa bai nuna razanarsa a fili ba. Duk fuskokinsu manne suke da safar fuska ba?a, wanda gilashi ba?i ne ke manne da fuskarsu.

"Alhaji doka ta Waya" wani daga cikinsu ya faWa da harshen Turanci.

"Na farko za ka bi Madam zuwa sama, ba na bu?atar ka nunawa wani cewa kana tare da mu,in kuwa ka ?i." Ya Wago hoto duk dogarawansa ne tsare da bindigogi.

"Zamu Wauki rayukansu a yanzu, sannan mu Wauki naka."

Sai a yanzu ya samu ya yatsina fuska ya yi magana cikin isa a hankali.

"Okey,no problem."

Na yi gaba yana biye da ni, na waiga na ce masa.

"Ka je ka biya kuWin Waki ni nayi gaba."

Bai ko kalleni ba, ya yi wajen biyan kuWi ni kuwa na haye sama.

Tsayin minti sha biyar sai ga shi ya mi?o mini makullin da aka rubuta No.120, Waki na Wari da ashirin, ina tafe yana biye da ni har Wakin. Na buWe na shiga ya biyo bayana, sannan na juyo na fito na mayar da ?ofar na kulle. Na sauko na bawa Katung makullin.

"Ku ?arasa sauran aikinku, amma kada ku yi masa komai, kuyi komai cikin mutunci,kun san babba ne ku ?arasa haWa komai, ina fatan kun gane?" Suka amsa eh. Na mi?a masa dubu talatin a biya a Wan ci abinci.

Bayan ?wana uku na dira a hotel Win da ?arfe goma na dare, wanda su Mamee ma basu san na fito ba, na sa makulli na buWe shi yana kishingiWe a gado yana karatun mujalla ta Turanci (Tell) da ido Waya ya Wago ya kalleni.

"Za ka iya tasowa mu tafi yanzu."

Bai ce komai ba ya mi?e ya zura babbar rigarshi da ke gefe Waya ya biyo bayana.

A motata har wannan gidan da yasa aka kai ni, amma inda yake da alama dai gidansa ne,kafin in shiga sai da na rufe fuskata da wata ba?ar fuska mai tafe da kitso, sannan na Waga wata ?atuwar ambulan na ce masa.

"Ko ba?ar magana ka gaya mini sai na kai wa Sarki wannan ambulan Win da ba zaka san ko meye a ciki ba, sai nan da Wan wani lokaci."

Ya buWe murfin motar ya fita ba tare da ya ce mini ?ala ba,ya juya ya tafi abin sa, nima na ja motata sai gida.

Duk da na yi masa haka, amma ban ga alamar razana ba a jikinsa, wannan ta sani kaina na ce lallai wannan ya cancanci ya hau gadon mulki, saboda ba a san matsoracin Sarki, ga shi kuma da iya ?ASAITA, na yi dariya ni kaWai, nayi murmushi kuma sannan na haye gadona na ?wanta.

Bayan ?wana biyu ne na taka da kaina har get Win gidan sarautar nan, wajen sojojin nan muka gaisa amma a cikin Satacciyar fuskar nan, sannan na kawo ?atuwar ambulan (envelope), na mi?a masu na ce.

"Sa?on Yarima ne daga ?asar Sudan."

Suka Wan dudduba ni da motata, sannan suka ce sai na zazzage kayan ciki, na ce masu ba zai yiwu ba, amma su buga masa waya su sanar da shi cewa yana da ba?uwa ta kawo masa sa?o amma kun ce sai na buWe....


*?ASAITA BOOK 1*


*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*


Page 5


Nan take suka buga masa, sai ya ce a karSi sa?on kawai a kawo masa, ya san da shi,ni kuwa na juya na yi tafiyata gidan Auntyna.

?angaren wajen Yarima kuwa,kaset ne aka kai masa da hoto ?waya Waya. Ya sanya kaset Win,lallai ya san na isa, hoton ?wance yake ba riga a jikinsa da bargo lulluSe daga ?afafunsa zuwa ?ugunshi, sannan ?irjinsa yarinya ce ?wance a daidai lokacin da yake rungume da ita, ya kai bakin shi ya sumbaci goshinta nan aka Wauki hoton.

Kaset kuwa daga inda ya Wauki yarinyar ne har zuwa hotel Win da shiga Wakin hotel Win duk dai yarinyar Waya ce, da takarda wacce na gaya masa, idan har ya ?ara sawa aka kama ni ko ya yi ?o?arin sawa a yi mini wani abu zan kai wa Sarki kaset Win da hotunan da kaina, na yi sallama.

Tabbas ni kaina na san na gama da Yarima, saboda yanzu ba shi da wata hanyar yi mini wula?anci,sai dai ni inyi yanda nake so a garin nan, da ya nemi takura mini da na tona masa asiri da ?undin kaset Win da na Wauka a matsayin Sata masa suna. In kuwa haka ta faru, sarauta kuwa shi da ita har abada.

**** ****

Yamma ce yanzu wacce ta nuna ?arfe biyar har da wasu mintuna goma, yanayin sanyin daminar garin sun haWa sun mayar da garin tamkar dare ya yi, sanyi kuwa mai shiga cikin tsokar jiki.

Motocin da na gani a harabar gidanmu a lokacin da na shigo da motata, shi yasa na Waga hannuna na kalli agogon da ke ma?ale a tsintsiyar hannuna, tabbas waWannan koma su waye ba?in Daddy ne, da gani ka san manya ne na gaskiya, saboda ganin manya-manyan (Jeep) da na yi har wajen biyar,ban da ?ananan (Pegeout 406) ga zungureriyar motar nan irin ta Yarima Limousine Cadillae.

Don dai kalarsu ce ba Waya ba, kuma wannan mai murfin ?ofa huWu ce, kenan babbar ta Yarima ce,na samu na raSa tawa motar daga gefe Waya, sannan da Katung ya iso nake tambayarsa su waye? Nan ya nuna mini bai san ko su waye ba, amma manyan mutane ne (Big Men).

Mamee na falo ita ma da wasu mata har biyar, ina isowa na sunkuya har ?asa na gaishe su, sannan na isa ga Mamee, na sumbaci kumatunta alamar na dawo kenan har zan wuce sai na ji Mamee na cewa.

"Ai itace wannan."

Wata mata wacce take zaune ita kaWai a doguwar kujera wacce da ?yar take motsi, ita ta yi ?ar dariya ta ce mini in zo.

Ina zuwa na zauna ?asa kusa da ita, sai na ga ta shafi gashin kaina wanda yake a buWe ta ce.

"She is beautiful, she deserves to be the Prince's wife,amma daga yau ki dinga kula da rufe gashin kan ki, saboda yanzun kin zama babba."

Ta faWa da harshen Hausa, sannan ta ce in tafi. Ina tashi na kalli Mamee kallo mai alamar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login