Showing 18001 words to 21000 words out of 26971 words

Chapter 7 - KASAITA BOOK 1 COMPLETE PDF BY MARYAM KABIR MASHI.doc

sarauta da filillikan ta biyu. Gefe Waya kuwa wani irin kafet ne, amma ba wai irin wanda ni kaina na sani ba, tabbas wannan ya fi kafet Win tsakiya laushin gaske.

Bangon gidan kuwa Waukar ido kawai yake yi, wanda na yi imani da Allah ba tayal ba ne ba saboda yanda yake Waukar ido. ?aya Wakin kuwa, shi ma an zuba masa wani irin gado, wanda kan shi kawai ma abin kallo ne, sai kujeru ?waya uku da ke gefe, sai kuwa rukunin tebir Win kayan Na'ura mai ?wa?walwa (Computer).

BanWakin Wakunan kuwa shi ma wani sabon gida ne, saboda shiga ka ke yi ?wamin wanka tamkar ka shiga ramin wanka (Swimming pool) saboda ?asa ya shafe, kuma sam ba ka ganin mai ke ?asan ?wamin ne,ko kuwa irin abin da ke manne a bangon gidan ne? Oho, sai dai zaka ga yana ta gudu, tamkar ka shiga ?orama.

Sannan an rubuta zafi da sanyi a jikin wani bango da yake tsaye shi kaWai a can tsakiyar kusa da ramin wanka, shi kan shi ramin wankan ka tattaka matattakalar bene,amma shi sai mu ce kamar za ka gidan ?asa, sannan ka shiga ciki.

Wasu green da blue Win abubuwa ne li?e da Wan dandamalin inda za ka ajiye hannuwanka in ka shiga, wanda aka rubuta sabulu da soso, ma'ana su za ka danna su fito da kansu,in ka gama ma su koma da kansu.

?aton madubi ne wanda za mu iya cewa ya kai rabin bangon banWakin, shi ne ke kallon ka in ka shiga, da in ka fito. Tsayawa ?arasa bayanin ma na san abu ne mai Waukar lokaci.

Da ka buWe ?ofar da ke cikin Wakin,za ka ga gaban gidan, wanda yake kallon ga??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ban wani gida wanda na ga Faysal tsaye jiya da daddare,da ka gangaro matattakalar benen,sai ?aton falo, wanda zan iya cewa tsayawa fassara shi Sata lokaci ne, sai dai a?wai Wakuna biyu shi ma a ?asan da banWakinsu.

In ka fita cikin gidan,za ka samu bene ne zagaye da shi kamar ?wabo, sai filin tsakiyar,in ka fita ?ofar shigowa kuwa za ka samu ragowar rariyar gidan, waje kenan inda ke da lambu in ka dawo ta gaban gidan kuma doguwar baranda ce kamar ta asibiti, amma wannan yanayinta kamar ?aton fayif Win ruwa.

Tun da zagaye take da shukokin fulawoyi,in kana ciki kamar kana cikin inuwa, ita za ta Wauke ka har ka shiga gidan Faysal, wacce kamar nan naWe take da wayoyi, sai dai akwai ?ofa biyu in ka zo tsakiyar ta.

?aya ?ofar za ta fitar da kai filayen wasa na gidan, wanda gaba Wayan zagayen gidan ciyawar nan ce ?wantacciya mai kama da kafet Win ?asa, filayen wasa ne kala-kala, akwai na ?wallon ?afa, ?wallon raga, ?wallon ?wando, ?wallon hannu,?ar ?wallon rami da sauran wasanni kala-kala.

Daga can nesa da wajen kuma wani dutse ne wanda ?asanshi duk ?ananan duwatsu ne, ga ruwa mai ?yau yana gudanya a ?asansa, wanda za mu iya cewa wajen sha?atawa, wajen ya yi mini daWi da sanyi-sanyi. ?aton dutsen kuwa malale yake, tamkar an shinfiWa a kai wanda sai ka taka kamar ?ananan duwatsu uku, sannan ka haye shi.

Ba zan iya cewa ga inda wannan ruwan ke nufa ba, saboda gabanshi duk daji ne,wato dogayen itatuwa ne, masu kama da iccen turare,ko ko iccen fulwaya za mu ce, shi kuwa ruwan kana hango ?asanshi garai-garai, wanda ?ananan duwatsu ne ke aiki.

Muna isa wajen kuwa, na tattaka na haye saman dutsen nan,a nan take sai na ji ai ni na samu wajen zama in dinga hutawa, duk da an keSe wajen hutawa a cikin wajen filin wasan. ?aya hanyar kuwa, Sangaren lambu ne,babu abin da babu,a cikin wajen, wanda sai da muka zagaya shi sosai, sannan muka fita, shi ma a cikin shi akwai duwatsu, sannan an tanadi wata rumfar gargajiya a ciki, wacce ta sha shimfiWu a inda daga nesa da ita akwai wani Wan ?aramin gida mai ?yan gaske, sai dai sun ce gidan hutawar Yarima ne.

Saman dutsen nan mai ruwa shi ne ?arshen zagayen gidana, tunda ni ba abin da zai kai ni gidan Yarima. A nan na umarce su da su Wan kawo mini darduma,zan zauna a saman dutsen,dama ni ba gwanar Wan ?wali ba, sannan ga ni da son ?ananan kaya (English wears) duk da dama ?an Jos haka muke,mun fi baiwa ?ananan kaya muhimmanci a kan kayan gargajiya.

Doguwar riga ce kuwa jikina, wacce take Salalliya daga ?asa, ba ta wuce ?waurina ba, sai dai ?aramin hannu gare ta, iya cinyar hannuna, na sa suka Webo mini ?an ?ananan duwatsu don kawai in dinga jefawa a cikin ruwan.

Na samu tsayin awa Waya a wajen nan,ni da Mansura da Muslima, sai ga jakadiya cikin hanzari ta zube a can ?asa, sannan ta nemi iznin hayowa, na bata,a inda ni kuma na kishingiWa a Wan tuntun da suka kawo mini.
*?ASAITA BOOK 1*


*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*


Page 10


"Allah ya taimaki Gimbiya,Yarima ya ce a ce miki yau ?arfe huWu na yamma ki same shi gidanshi,za ku gaishe da Sarki, da mahaifiyar shi,dama haka al'adar take, domin su ga ya ku ka ?wana."

Na yi shiru, sannan na nisa na fara magana.

"Ki ce masa ina da ?ar hidima a gidana, amma shi in ya shirya yazo ta gidana mu tafi in kuma ba damuwa ma iya haWewa a can, ina da ?ar rakiya." Sai na ga tana rausayar da kai.

"Shikenan jakadiya."

"To,to,to, Gimbiya ai ba gardama, abin da ki ka ce shine."

Ta mi?e ta gangara ta tafi,ni kuma na cigaba da harkokina, wanda suke yi mini daWi, ga ba rana ko kaWan a ganina sai ma iska da ke ratsa jikina, irin ta sanyin damuna.

?arfe biyar na yamma na farka daga baccin da ya ?washe ni a kan abin sallah ta wanda na tashi da mamakin jikina ba hijabin da na saka na yi sallah, sannan an Wora mini kaina a saman filo.

Cikin Wan hanzari da faWuwar gaba na mi?e, saboda tunawa da na yi cewa mun yi da Yarima za mu gidansu. BanWaki na shige na watsa ruwa da saurina, ina fitowa Waure da tawul na le?o ta barandar sama, ta cikin falo, na kira Mansura,wai dama in tambaye ta cewa Yarima ya aiko,ko ya zo? Ai sai kawai muka yi ido huWu da shi.

Ya yi tsaye a maimakon in kira Mansura, ganin ya cire gilashin da ke manne a fuskarshi, ya ?ara Wago idanuwanshi a kaina, ya tuna mini cewa jikina ba riga, na yi saurin shigewa cikin Wakina, tare da ?wallawa Mansura kira.

Ta shigo da sauri, "Ya daWe da zuwa?" Tambayar da nayi mata kenan.

"Eh, ya daWe."

"Tun yaushe ya zo?"

"Tun ?arfe huWu, na zo gaya miki sai na same ki kina bacci, shi ne na gaya masa,ni dai na ga ya hayo saman da kanshi, sai ya sauko ya zauna a nan,mun kawo masa kayan marmari da lemu, amma bai ko kalle su ba."

Na yi tsaki, "maimakon ki ce masa ya tafi zan zo daga baya?"

Na ga ta zaro idanuwa da sauri.

"Allah ya huci zuciya,ai ba a mayarwa da Yarima magana, yanzun ka ?wana a yari." Nan take sai na tuno yarin nan,nima na taSa zuwanta, ta tsawon awa goma.

"Ke ki ka cire mini hijabin jikina ki ka sa mini fulo a kaina?"

"A'a"

Haushi ya kama ni, "wa ya ce ki ka barshi ya shigar mini Waki?"

Ta yi saurin sunkuyar dakai, ba ta ce komai ba, "fita ki bani waje ki turo mini masu kula da kayana!"

"Ai sun ajiye Gimbiya, Allah ya huci zuciya,ga su nan sun fito da su." Ta nuna saman kujera da Wan yatsa, sannan ta yi waje.

Boyal ne mai ruwan makuba (Coffee Color) wanda ya amsa sunansa, wanda ya sha aikin surfani a wuyansa da hannayensa, amma hannun bai wuce cinyar hannuwana ba, sai rigar kuwa da kaWan ta wuce ?uguna, amma buWaWWiya ce, wacce ake kira da Stella Style.

Zanin kuwa ya sha ado, wanda zai Waukewa jama'a hankali,ni kaina mai kayan sai da na ji sun birge ni, na zauna a jikin madubin da ke kusa da gadona, na gyare fuskata.

Takalmi da jaka ruwan ?asa ne nasa a ?afata, wacce jakar iya silin hannu kawai ake rataya ta, da gani ka san desginer ce,wata siririyar diamond na saka a wuyana,inda zobunan hannuwana da Wan kunnan duk kalar sar?arce, zobe ?waya biyu kacal ne a hannun nawa.

?an ?walin Boyal Win ne aka naWo shi, tamkar naWin gwaggwaro, amma a matsayin Waurin Wankwalin yake. Turaren (Network) na zuba a jikina, ban tsaya wani make-up ba a fuskata,saboda gaishe da sirikan dole zan je, sai dai na san dole ta sha farar hoda da Wetlips mai she?i,farcena kuwa sun sha fenti ruwan ?asa suma.

Taku WaiWai nake yi na sauko daga ?afar bene inda takalmin ?afata ke fitar da sauti cikin nutsuwa, saboda malalen kafet da ya baje gidan, shi ya hana su ?ara mai fitar da sauti da ?arfi.

Babu kowa a falon sai Faysal shi kaWai da jarida a hannunsa,jin takuna yasa ya ajiye jaridar, amma ba tare da ya kalli inda nake ba, har sai da na iso daidai da shi, sannan na ga ya Waga kai ta gefe Waya ya kalleni,mayar da kan da ya yi ya sunkuyar ya yi daidai da fitar maganarshi a hankali.

"Something is missing."

Na ?ara kallon jikina sosai, ban ga abin da na manta ba.

"What?" Na faWa cikin jan aji.

"Mayafi,ko kin manta yanzu ke matar aure ce?"

Na tsaya na ?are masa kallo, amma shi ko motsi bai yi ba,a hankali na nufi inda na san zan ga su Mansura, sannan na yafito ta, ta iso da gudun saurinta, sannan na umarce ta da ta Wauko mini mayafi wanda yake iri Waya da takalman da jakata, cikin rawar jiki ta ce to.

Ko kallon inda yake ban yi ba, na wuce zuwa waje abina,bai ce ?ala ba, shi ma na ga ya taso ya biyo bayana. Wani abun al'ajabin kuma shi ne dakarun tsaron shi suna nan tsaye ?am suna jiran shi, a zuciyata na ce lallai wannan mutumin da mulkin masifa yake.

Limousine motar nan mai ?ofa uku, wacce ta bugeni a titin Ahmad Bello Waya, ita aka buWe mini na shiga cikin takaicinta, ta gefe Waya na ga ya shigo shi ma,a inda bai fi sakan biyu da zama ba, na ga labulaye ba?a?e sun sauka da kansu, kenan an rufe mu,ko direban ma bana gani.

Kujerar gefenmu ba kowa, sai tsakiyarta naga ?aramar talabijin na aiki,sanyi na ji ya sauka a lokaci Waya, tare da wata fitila mai kalar duhuwa ita ma a zuciyata na ce lallai dole a dinga kaWe ?a?an talakawa ba a sani ba.

Yanda ya shige ?wanar kujerar da yake,ni ma haka na ?wanta linkif a cikinta,tsawon mintuna goma sannan na ga ya cire gilashin fuskarsa da ?yar, sai ga wani Wan tebir ya Sullo daga ?asa da ?walaban lemu amma ba irinsu fanta ba,da kofunansu, wasu ?walaben ne abin kallo, don ma ina ?ar gidan masu da shi, da sai in ce giyoyi ne ba lemo ba.

Ya Wora gilashinsa a sama, sannan yasa hannu ya janyo gaban tebirin, sai na ga ashe Wan firji ne ya zaro robar Ice Cream da Chukulat, ya ajiye a gabana, sannan ya Waga ?walba ya tsiyaya lemo a kofi, ya ajiye a gabana, sai na ga shi ma ya tsiyaya.

Sai da ya kurSa sau biyu, sannan ya ajiye ni kuwa sai bin shi nake da kallo ta wutsiyar idanuwana.

"Na aiko da gaisuwata Wazu, amma ban ji gamsasshiyar amsa ba, wanda ke ce mace a ?ar?ashina ki ke,ke ya cancanci ki aika mini da ita,ko kizo ki gaishe ni." Ya yi shiru ya ?ara Waukar kofin ya kurSa lemun.

"Ki sha mana,sarkin shan za?i."

Na Wago na kalleshi a zuciyata na ce wa ya gaya masa ina son waWannan kayayyakin, ban amsa masa ba sai naga ya Wan sunkuyo kaWan ya Wauki Ice Cream Win ya buWa ya mi?o mini.

"KarSi."

Na girgiza kaina alamar a'a, saboda mamaki da al'ajabi ya hana ni motsi, ashe ya iya magana mai sanyin gaske ko don bai cika yin magana ba.

"Yasmin!"

Na juyo sosai na kalle shi domin mamakin yanda aka yi yasan sunana, ya Wan yi murmushin ?ASAITA, ya ?ara mi?o mini,na sa hannu zan karSa, sai na ga yasa Wayan hannunsa ya ri?e hannuna, ya kama ?an yatsuna, sannan na ji ya yi magana.

"Daga yau don Allah kada ki ?ara shafa irin wannan fentin, ina son kisa a yanke miki faratan gaba Wayansu,ni ba na so, Allah ma baya so."

Na zame hannuna, "Dole ne ki bi umurnina, saboda ina mijinki, ba ki da wata hanyar rabuwa da ni, tunda kin zo hannuna."

Na yatsina fuska. "Ka manta da ina da abin da zan iya tona maka asiri da shi?"

Ya yi murmushi, "Ai yanzun kan ki zaki tonawa asiri, tunda duniya za ta kira ni da mijin Yasmin ne Wan iska mai bin mata. Amma duk da haka ina ro?on ki ?onasu,bana so mu Sata ran mahaifanmu."

Na yi murmushi na juyar da kaina gefe Waya.

"Zan ?ona su, amma sai ka bi dokokina."

"Bama za ki same su ba,ki yi shiru kawai."

Bai yi wata magana ba, na ga ya koma ?wana ya ?ara gyara ?wanciyarsa.

Ni dai ?ar bi ce kawai, saboda ban san ko'ina ba a gidan, har muka iso wani falo. Wata ?yak?yawar mata ce kishingiWe a saman wani tudu kamar na katifa, wanda ya sha shinfiWun dardumai wanda kalolinsu ba sa ?irguwa. Sai da muka isa kusa da matar, sannan na ga na ma taSa ganin ta. ?asa na ga Yarima ya zauna cikin ladabi, nima sai na yi yanda ya yi.

Cikin Wan lokaci ?an?ani, na ga matan da ke zagaye da ita suna kawo mana gaisuwa,suna ficewa waje.

"Barka da yamma Mama."

"Barka ka dai yarona."

Nima sai na faWi yadda ya ce, "Barka da yamma Mama."

"?iyata barka da yau, ya ba?unta, ina fata baya Sata miki rai?"

"A'a Mama, lafiya ?alau."

Sai na ga ya tashi ya haye shinfiWar ya zauna, ya fara wata magana irin ta shagwaSa, mamaki ya kama ni,nan take na ce lallai iyaye, iyaye ne ashe da wanda Faysal ke wa magana lafiya ?alau ba ta?ama.

"Mama ni har yanzun Sarki ya hana ni zuwa Malesiya,Mama don Allah ki sa baki ya bar ni in tafi gobe."

"Ba fa zai yiwu ba,in dai ka tashi zuwa Honey Moon ne to na san ba zai hana ka ba."

"Mama don Allah." Ya ?ara matsawa kusa da ita har da ri?e mata hannu.

"Kana da naci Yarima a kan abin da ka san ba zai taSa yiwuwa ba. Yanzun ka tashi ka je ku gaisa da Sarki naji an ce ya shigo, kuma na san saboda kai kawai ya shigo. Baby Yasmin ku je ku gaishe da Babanku, ga shi can ya shigo gida,ki ?yale wannan shagwaSaSSan mijin naki,kin gan shi nan kullum bai girma ji yake kamar a mayar da shi ciki ma."

"Mama, kada ta raina ni,ni bana yi mata wasa."

"A'a,lallai ni tashi ka wuce ka ba ni waje,marar kunya."

"Mama." Ya faWa a daidai lokacin da shi kuma ya sauko muka tafi.

Tabbas sarauta sai Wanta, Sarki kam yana mugun ?aunar Faysal, saboda yanda ya nuna lokacin da muka shiga. Mun shiga Faysal ya sunkuya har ?asa ya gaishe da Sarki,a inda ni ma na yi yanda na ga ya yi, sannan muka zauna gabansa.

"Faysal na ji aikenka har karo biyu, amma na bayar da amsa Waya, ita ce a'a, yanzun ma a gabanka na ce a'a, ba wai don in Sata maka rai ba, a'a saboda yanzun ba da bane ba, yanzun kana da nauyin iyali a kanka, ya kamata a ce ka tsaya ka kula da su na tsawon lokaci kafin ka yi wata tafiya.

Faysal ban haWa ku aure da sunan in zalunce ku ba,mu iyayenku mun haWa ku aure ne, saboda muna ganin ku ?a?a ne nagari masu tarbiyya, hakan yasa ni nayi tunanin wacce ta dace da kai ta Sangaren ko'ina rayuwar duniya nan, har izuwa lahira, na ga ba wacce ta dace sai wannan yarinya.

Wallahi! Wallahi!! Wallahi!!! ?acin ranta zai iya shafar tsakaninmu da kai,ko da kuwa labari na samu,ka ri?e ta tsakaninka da Allah, shi so da ka ke gani, a hankali yake shiga cikin zuciya, har ya ratsa gangar jiki,in kuka yi ha?uri da juna, wata rana sai kun yi murna. Saboda mu ma duk haka aka yi mana,ga shi yanzun ya zame mana alheri."

Daga nan ya ci gaba da yi mana nasihohi, sannan ya sallame mu.

Muna fitowa daga ?aton falon Sarki,Yarima ya yi gaba ya bar ni a baya,a zuciyata na ce ni dama cewa ka yi in tafi gidanmu,ni ya fiye mini alheri, tunda nima saboda mahaifina kawai nake zaune a gidanka.

Ina isa falon mahaifiyarsa na ga ban gansu ba, sai na nufi wata ?ofa nima in nemi inda suka shiga sai na jiyo muryar Yarima.


*?ASAITA BOOK 1*


*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*


Page 11


"Mama wallahi yarinyar nan ba ta sona ?wata-?wata, nima har yanzu ban ji ta ?wanta mini ba sosai. Mama ta?ama gareta ga jiji da kai."

"Kai ka fara yi mata,ka manta labarin da ka ba ni a baya cewa yi fa tana burge ka,tun ranar da ka fara ganinta."

"To Mama ai burgewa ba so bane ba."

"To yanzun me ka ke so inyi maka?"

"Mama ki yi mata faWa, ita ma ta rage jiji da kai."

"Kai ka yi mata."

"Wallahi Mama tun da ki ka ce kada in yi mata wallahi ba na yi mata."

"Haba Faysal na san ka fa."

"Mama ko yanzun fa da zamu zo nan ni na je har Wakinta, sai da ma na jira ta tashi daga bacci. Mama ai kuwa na yi."

"Shin wai waya gaya maka rana Waya so ke shiga,a hankali in kuna tare zaka ji kana sonta, amma na gaya maka dole kai ne za ka yi ?asa ka dinga lallashinta,?iyayyar mace ba ta da tsanani."

"Mama ni wallahi da an bar ni nayi tafiyata kawai."

"Bana son haukan nan naka fa,kullum ana koya maka hankali, amma ka ?i

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login