Showing 9001 words to 12000 words out of 26971 words

Chapter 4 - KASAITA BOOK 1 COMPLETE PDF BY MARYAM KABIR MASHI.doc

tambaya, amma sai na ga ta kawar da kanta, na taSe bakina na haye sama, zuwa Wakina.

Bayan kamar mintuna goma sha biyar, sai ga Mamee ta shigo Wakin da nake ta mi?o mini wasu riga da zani na Wanyan ?watin less (Cotton less) mai launin kore wanda ya chiza wato ruwan kayan sojoji (Amry colour) da takalma ruwansa, amma mai haske (light green) da file Wan?walin sa?i, da abin sagalawa a wuya, duk ruwan takalman. Da wani irin English Gold wai duk in saka a jikina.

Tambayar Mamee nake, amma ta ?i ba ni amsa, sai dai faman shirya ni take yi hatta shimi da siket Win duk kalar kayan ne,ni kaina na san nayi ?yau, balle raba gashina biyu da Mamee ta yi ta sakko mini su a gaban ?irjina, wanda ya sauko mini har kusan rabin cikina.

Fuskata kuwa ta sha gyara,ni kaina ban san Mamee ta iya ?walliyar kece raini ba, sai yau, tun da ita Mamee ba ta ?walliya,iyakacinta ta murza hoda kawai da Wan ?walli a idanuwanta. Ta umarce ni da in biyo ta,na bi bayanta a hankali wanda take ce mini taku WaiWai zan dinga yi.

Dama ni sarkin iya ?ASAITA, shi na dinga yi. Mun isa falo na ga matan da ke zaune duk sun ruWe, na yi zaton iya nan kawai za mu tsaya, amma sai na ga an nufi sashen (Sitting room) Win Dad,Wakin sha?atawarshi da ni.

Muna kai wa ?ofar Wakin na ga Mamee ta ?ara fesa mini wani Desginer Win turare, sannan ta ce.

"In kin shiga da kin kai tsakiyar falon ki dur?usa ki gaishe su, amma da harshen Turanci, ban da sakarci, ban da shagwaSar da ki ka saba yi wa My dear,kina ji na?"

Na ce, "To Mamee,wai su waye,me suka zo yi?"

"Baki da amsa yanzun sai sun tafi."

Na Wan kaWa kai na shiga.

"Tafiyar nutsuwa." Haka na ji Mamee ta ce.

Yawan mutanen falon Dad su suka sa na fara rikicewa wajen tafiya, amma tunanin kada in kunyata iyayena,shi yasa na yi saurin sanyawa jikina nutsuwa a take, hankalina kam ya tashi, sai dai ban yarda na nuna ba, saboda ganin dattijon mutum da na yi a hakimce a saman kujerar kishingiWewa, har da sa masa darduma mai laushin gaske a saman kujerar.

Ban da mutane biyu da ke tsaye a kan shi, suna sama da ?asa da wani ?aton abu mai gashi, faWin shi kamar ?aton faifan bakacan masara, sai dai bazar gashin jikinsa da kalar ja da yalo da ke jikinsa da mari?in da suka fito da shi, zai nuna maka mafici ne.

Amma na fi ganin shi a cikin talabijin, shi ma sai in an nuno wani sarki. A zuciyata na ce dan kinibibi duk A.C Win da ke falon Dadyna, amma sai an yi masa fifita.

Yanda Mamee ta ce inyi haka na yi,bacin duk dama hankalinsu ya dawo kaina tun da na shigo. Dad Wina ne ya iso ya kama ni ya tashe ni tsaye, sannan ya fara magana.

"Your Highness this is My daughter Yasmin."

Ya tafi da ni har gaban wannan mutumin,ya tsugunnar da ni.

"?iyata Wago da kanki."

Na Wago.

"Very fine lady,na tabbatar Wana zai yaba da ita."

"Haka ne, haka ne, ai ba ja."waWannan mutane na tsaye bayansa suka faWa.

Sannan ya kama hannuna muka mi?e tare da shi, shi wannan mutumin ya juyar da ni na kalli ragowar mutanen da ke baje a ?asa, sai dai wasu uku da ke zaune a kujera daban-daban.

"Wannan ita ce matar da na zaSawa Wana Faisal, ina fatan ta yi?"

"Ta yi, tayi."

"Waziri ta yi?"

Ta yi,ta yi."

Sai na ji wazirin ya ?wala kira, amma ban ji yanda ya kira sunan ba, sai na ga wasu mata su huWu sun shigo Wauke da farantai lulluSe da kaya a ciki, da wani farin gyale sun ajiye gabana.

"?yauta daga waziri." Inji wani ya faWa.

Aka dinga shigowa da kaya kala-kala,ni dai ina daga tsaye, daga a ce ?yauta daga wa ne, sai daga wane, bayan kamar minti ashirin aka sallame ni na tafi. Raina a Sace na shiga falon Mamee ba?in da na gani da waWannan mata, shi yasa na Wan saki fuskata, sannan na sunkuya na yi masu sallama na haye sama.

Komai cillar da shi nayi daga tsaye, takalma,tuntun saman kaina,sar?ar,awarwaron, na faWa a gado.

"Me ye wannan?" Na tambayi kaina.

"Me su Dad ke nufi da ni,?yautar da ni suka yi ko kuwa siyarwa? Yanzun manufarsu in rabu da Anwar Proposed Wina? Mutumin da nake ?auna.

Mamee fa ta san yanda nake son shi, shine zata je ta yadda a haWa ni da wanda ban taSa gani ba, hawaye suka gangaro mini,shi kenan rayuwata ta raunana, tun da za'a aura mini wanda ba na so, yanzun ba za'a barni in zaSa ba kamar yanda Aunty Salwa ta zaSa?.

Kenan an nuna mini a gidan nan an fi son Aunty Salwa da ni, yanzu duk ?aunar da na ga ana nuna mini,ashe duk ?arya ne, ashe iyaye ma na yaudarar ?a?ansu,anya kuwa ma su suka haife ni? Ban yarda ba,?ila dai ru?ona suke yi, shi yasa za su haWa ni da Wan gidan sarauta ko sarautar wane gari ce ma? Oho. Ko dai cikin dangin Mamee ne waWanda ba su Musulunta ba, na ga suma ?yansu ya yi yawa irin nata. Tashin motocin da na ji, shi yasa na rarrafa daga gadona na Waga labule ina le?ensu.

Suna wucewa na sauko ina dire-dire na kuka, na shige banWaki,dama na sani da ban tafi da wayata ba, duk ita ta janyo mini, da bata nan ai da ba za'a kira ni in zo ba. A banWaki nake wannan tunanin da kuka mai fitar da sauti, to an fa tuno da Allah duk da dama muna kiyayewa mu a gidan nan.

Nan take na yi alwala na fito,ai sai sallah, kafin a kira sallar magriba na yi nafila ta kai goma, ina ji Mamee ta le?o Wakina ta koma,ganin ina sallah.

?arfe ta?was saura minti huWu,Mamee ta shigo ta ce in je inji Dad.

Na Wago kaina, na kalle ta kawai, na mayar.

"Ba ki ji ni bane?"

"Na ji Mamee yanzun zan je."

Tana fita,nima na bi bayanta. Bayan kamar minti biyar.

Yana kishingiWe a inda ya saba hutawa, duk bayan sallar isha'i, Mamee na daga ?afarshi zaune tana yi masa matsar yatsun ?afa.

"Yauwa,autar Daddy zo nan."

Na isa na zauna ?asa Wan nesa da shi.

Ya Waure fuska, irin alamar in babba zai yi maka maganar da yake ganin so yake yaro ya Wauke ta da muhimmanci na gaskiya, sannan ya kira sunana.

"Yasmin." Sai na ga Mamee ta tashi ta fita, sannan ya ci gaba.

"Yasmin,kin san kowanne uba yana son ya ga ?a?anshi sun fi na kowa Waukaka,?yau, asali, tarbiyya, miji nagari, idan mata ne,in maza ne mata nagari. To balle ku ?a?ana da ku ke a zuciyata tun ranar da na haife ku har izuwa yau. Ku kanku kun san ba wanda nake so a duniya in har suka wuce iyayena sai kuwa ku da mahaifiyarku, kamar yanda nake ?aunar Manzon Allah (S.A.W) haka na koya muku sonshi da ?aunarsa,a matsayinku na ?a?ana, na horar da ku tarbiyyar bautawa Allah da bin sunnar Manzon Allah (S.A.W).

Kamar yanda ku ka san ba wanda zai ba ka ladan bautar Allah,sai shi Allah, haka ba Wan da ya isa ya biya iyayenshi ladan tarbiyya da haihuwarshi da suka yi sai shi Allah, amma ana son a yi masu biyayya, ga duk abin da aka ga suna so da wanda suka umarta idan dai har an tabbatar bai saSawa shari'ar Muslunci ba, da abin da Manzon Allah (S.A.W), ya zo mana da shi.

Ko da kuwa sun zama suna masu tsanar abin da suka umarce su, da ?iyayya mai tsanani to yin biyayya ga abin da suka faWa Win nan, shi zai sa su sadu da rahamar Ubangiji, wata rana kuma su ?aunaci abin,su yi wa iyayen godiya ta musamman da addu'a idan sun riga sun rasu.

Yasmin,kin san dai duk cikin ku ukun nan,ba wacce nake ?auna da so, sai ke. Ke ce ?ar da take ?wance a cikin zuciyata a koda yaushe,ke ce ?ar da nake ganin nan gaba za ki ?aunace ni, ki kula da rayuwata.

Ki tuna na haife ki, nayi miki tarbiyya tagari, na baki ilmi, na wadata ki da abinci mai ?yau, na kawo gida mai ?yau na gina na saka ku,ya na same su, wacce wahala na yi? Oho,ni dai ku ji daWi,yau rana ta zo ta ki nuna mini Waya daga cikin son da ki ke yi mini,ki nuna mini iri-irin biyayyar da zaki iya yi mini ko da bayan raina ne.

Ki sani Addini ya yarjewa iyaye su zaSawa ?a?ansu mazaje na gari, idan har ?an mata ne, ko samari, amma in sun zama aure ne na biyu, bazawara,ko bazawari, shari'ah ta ce a bashi dama ya zaSa, ba wai don ba zai iya zaSa da farko ba, a'a saboda Allah kaWai ya san hikimar da yake nufi a nan.

Yasmin yau na zauna a ?asanki ina ro?onki wata alfarma ?waya Waya, amma girmanta ya fi ?arfin Najeriya gaba Wayanta, nauyinta kuwa ya fi ?arfin teku, amma a gare ki in kin yi,abu ne mai sau?i da rashin nauyi.......


*?ASAITA BOOK 1*


*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*


Page 6


Kada kiyi tunanin na yi miki haka ne don in cutawa rayuwarki,a'a na yi ne domin ina ganin na isa a gare ki, kuma na san ke yarinya ce mai biyayya, mai ?aunata, na yi ne domin in sakaki jin daWi da annashuwa a nan gaba, ranar da hankali ya huda miki jiki.

Ke kin san dai yanzu nafi ?arfin a kalleni ace zan je ?waWayin wani abin duniya,ko zan kai ?a?ana domin ?waWayin wani samu na duniya ke kanki kin san nafi ?arfin haka, sannan kin san na mallaki abin da zan iya ciyar da ku har ?arshen rayuwarmu,ko na riga ku mutuwa, zan yi alfahari da cewa na bar muku abin da za ku tafiyar da rayuwarku har ku bini inda na tafi.

Yasmin na san kina son Anwar,na san zakiyi farin ciki yau a ce shi zan aura miki a matsayin miji a gareki, amma ki sani yawancin abin da ka fi so,in har ba ka same shi ba, to ba alheri ba ne a gareka, ta yiwu alherin na ga wanda ba ka son nan.

Yasmin ni mahaifinki nake son baki ha?uri a kan hana ki auran wanda ki ke so Anwar,Ina neman alfarma a gareki da ki yi mini biyayya zan haWa ki aure da Wan Sarki Jafar,ki yi ha?uri na san da takurawa. Yasmin ki taimaka ki fitar da ni kunya, sannan ki sani,ni ba irin iyayen da suke kai tallan ?a?ansu ba ne ba, na fi ?arfin haka nan.

Ko kuwa kuna da yawa a gabana, balle ku biyu ne, da kansu suka zo har gidan nan neman wannan alfarmar, ban sani ba, sai yau, ban taSa jin labari ba, sai dai ganin su nayi sun zo, ban san abin da ke tafe da su ba, sai da suka faWa,ban san wanda ya ba su labarin ina da Wiya ba, sai da suka faWa cewa wajen taron bikin gidan Alhaji Kabir suka ganki.

Shi ne Sarkin yasa aka dinga cigiyar ke ?ar gidan waye, ba su samu ba sai wannan satin, shi ne Sarkin ya zo da kansa wai gudun kada in ga da wasa ake yi. Ban san ko waye ba a cikin ?a?ansa ba, sai dai ya ce zai turo shi cikin satin nan ya zo ku gaisa,ku daidaita kafin nan da lokacin bikin. Wannan da ki ke gani shine Sarkin nan garin na musulmi."

Gabana ya faWi shi kenan gidan cin mutane ma za'a kai ni, saboda waWannan mutane na gidan yarin in ba cin su ake ba,ai ya isa a sake su su koma gidajensu, da gani ma sai an shanye jininsu, sannan a cinye tsokar a yanda na ga sun bushe a tsaye.

Nan take na yi dana sanin kin gayawa Daddy abin da Yarima ya yi mini wata uku da suka wuce, da na sani wata Waya da wani abu da ya wuce da ban Wauki fansa da kaina ba, da na faWa an Waukar mini,na san da yanzu Dad ba zai yarda ya aurawa wani Wan gidan ba ni ba.

Shi yasa aka ce ta yaro ?yau take, amma ba ta ?arko, ga shi dai ni yanzu ba damar in faWa Daddy ya ga kamar zan tozarta shi ne a idon duniya.

"Yasmin na ji kin yi shiru."

"Dad ai na san ba zaka zaSa mini abin da ka san zai cutar da ni ba, saboda haka na amince da zaSinka matsawar in ka amince da in naga abin cutarwa zan zo in sanar da kai, kuma zakayi saurin Waukar matakin gaggawa a gareni,ka ba ni gudummawar ka ta uba."

"Na yi miki wannan al?awari, sannan ni ma kin tunasar da ni zan faWa masu da wuri tun kafin akai ki, na gode Allah ya yi miki albarka, ya baki ke ma ?a?an da za su yi biyayya a gareki,ki yi ha?uri na san na takura miki."

Na ce, "Ba komai." Na mi?e na koma cikin gida.


**** **** ****

Shi kenan,Rayuwata ta raunana, tun daga ranar da Daddy ya gaya mini maganar aurena, har zuwa yau,?wanaki tara kenan, ba ni da wata walwala,in ma naWan yi ta, to gabansu iyayena ne,gudun kada su yi wani tunani na daban.

Amma ni a Wakina,ko motsin kirki ma bana son yi saboda tsananin tunani da kuma rabuwa da masoyina Anwar,wanda muka rabu muna kuka ga junanmu. ?wanaki huWu da suka wuce, amma har yanzu Win nan sai da ya bugo mini waya, kullum kuwa ri?e nake da kan wayata ina kallon hotanshi wanda shi ne (Screen Saver) Win wayata,hoton fuskar wayata.

Na kasa fita ko ina yawon da na saba, balle in isa gidan Aunty in gaya mata halin da nake ciki,ko gidan Fatima amarya da na yi niyyar buga musu waya kuwa, sai in ga matsalar tafi ?arfin faWa a waya.

?arfe huWu da rabi ina zaune a kan abin sallah ta, sai na ji ?wan?wasawar ?ofa, da ?yar na ce a shigo. Yaya Habib, na yi tsalle na ruga na rungume shi, ina yi masa oyoyo, madadin mu koma ?asa, sai na janyo shi cikin Wakina na mayar da makulli na kulle ?ofata.

"Yaya zauna tambayoyi zan yi maka,dama ina neman ka, saboda ina cikin tashin hankali, amma kada ka gayawa su Mamee, ba na nunawa a gabansu."

"To ina jin ki."

Nayi saurin tsugunnawa a gabanshi, shi kuwa yana saman gado zaune.

"Yaya su Mamee kuwa su suka haifeni ko ri?ona suke yi?"

"Kina da hankali kuwa, da tambayar taki kenan ta mahaukata?"

"Yaya don Allah ka da ka juya mini baya, kai dai ka amsa mini,zan gaya maka dalili."

"Eh,su suka haife ki."

"Kana da wayo sosai a lokacin da Mamee ta haife ni ina jaririya,kana ganin tana ba ni nono a gabanka?"

"Wai ke yau ko kin yi gamo da aljanu ne?"

"Wallahi Yaya da hankalina,kai dai ka amsa mini don Allah."

"Zan iya tuna lokacin da take shayar da ke, har ma nake cewa ki sam mini nono in sha, ana yi mini dariya, har in je in kai ?ararsu ga Daddinmu."

"Kuma ka ga suna so na?"

Ya mi?e tsaye, "bana son sakarcin banza, zan yi miki duka yanzun nan."

"Don Allah Yaya ka yi ha?uri."

Sai nasa kuka.

"Wai Yaya wai Wan Sarki Jafar za'a aura mini,ban san ko waye ba a cikin ?a?an nasa, shi ma Dad wai ya amsa shi zan aura,ni kuma bana son shi, koma waye a cikin su, duk azzalumai ne fa."

Na saka kuka na mi?e na cakume shi.ina ji ya saukar da ajiyar zuciya, ya Wago kaina.

"Haba Yasmin ?ar ?anwata,ki yi tunanin irin son da Dad yake nuna miki yanzun haka in za ki buWe zuciyar Dad shima baya so, Amma,zan je in tabbatar da me yake faruwa."

"Kada ka gaya masa cewa na ce bana so."

"Ba zan faWa ba,kin ji ?anwata."

Ya goge mini hawayen fuskata,sannan ya juya ya fita.

Bayan mintuna hamsin ne Yaya ya shigo, ya yin da ya nuna mini sai dai in ta addu'a kawai, saboda aurena ba fashi, yanda yake gaya mini ma har sun tsayar da ranar Waurin aure, da sarki Jafar,nan da wata biyu shi ma domin mu samu sha?uwa da juna.

Iya bayanin da Yaya ya yi mini kenan, ya fita shi ma jikinsa a sanyaye, ban taSa shiga tashin hankali ba tun da nayi wayo sai a cikin ?wanakin nan tara, ban taSa tunanin za'a samu abin da zai girgiza min zuciya ba, amma yanzu ga shi na samu wanda Yake neman kawar mini da tunanina.

Yau ?wana goma sha bakwai da zuwan sarki Jafar kenan ya rage saura ?wanaki arba'in da uku yinin bikina, sai yau ne aka ce ai ga Faysal wanda zai zama angona, duk da sanyin da ake yi, amma sai da na ji tamkar an watsa mini ruwan zafi.

Mamee ta shigo ta umarce ni da in shirya in isa falon Daddy na yi ba?o, lallashi, nasihohi,Mamee ta dinga yi mini na kada in nuna masa halayyar sakarcina. Ni kuwa ba ta san gani nake ma ba ta ?aunata.

Dogon siket da riga ne,?irar ?asar Japan nasa a jikina, dogayen hannu gare su har idon hannuwana,buWaWWan wuya gare su tamkar irin Winkunan da ake ya yi yanzu a Najeriyarmu, sai dai tare yake da Wan ziririn mayafinsu wanda za mu iya cewa iya wuya kawai ya tsaya.

Mamee ta lulluSa mini shi, ta sako leSe Waya a gaban ?irjina,Wayan kuwa ya nufi bayana, gashin kaina kuwa yana can baya aka tattara shi, sai ?an ?wayoyi da ta Wan gyara mini su ta sako su gefen fuskata, wanda ya bi ?irjina ya ?wanta.

Na sha turare da gyaran fuska, abin ka da kalar ruwan ?asa mai cizawa ne,siket Win sai ya yi mini ?yau,rigar kuwa ba?a ce mai ?yal?ali a gabanta, Wan mayafin kuwa kalar siket Win ne,ba?a?en takalma na saka a ?afata, waWanda suka yi daidai da rigar, na Wauki ba?ar wayar hannu na ri?e a hannuna.

Kafin in yi sallama in shiga, sai da na le?a ta kafar labule,jiri ne yasa na koma baya da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login