Showing 15001 words to 18000 words out of 26971 words

Chapter 6 - KASAITA BOOK 1 COMPLETE PDF BY MARYAM KABIR MASHI.doc

mata suka Sanbare ni daga jikinsa. Ganin yanda nake yi ne yasa Daddy ya ce su tafi, zai kai ni da kanshi daga baya. Hakan yasa sai dai aka lulluSa wata abokiyar wasata aka fita da ita a matsayin amarya.

Ni kuwa har goma da rabi na dare,Daddy nata lallashina da ?yar na amince, shi ma sai da ya yi mini al?awarin gobe tun da safe zai je gidan,in ya ga ban ha?ura ba zai dawo da ni, kai ni kaina na san dai wayo kawai ya yi mini.

Duk da na san dai shi kanshi dole ta sa zai rabu da ni,kari da ganin hankalin Dad ya yi mugun tashi har yana zubar da hawaye ganin yanda nake kuka, har da neman shiWewa.

Da lallashi da ban magana,Daddy ya kaini har gidan Faysal, shi da kanshi ya rakani har cikin Wakin da yake nawa bayan nan ma sai da ya Wan zauna ya ?ara yi mini ?an maganganun da za su ?wantar mini da hankali, wanda sai da jama'a suka Wan ba mu fili, saboda yawa, amma duk da haka da zai tafi sai da na ji hankalina ya yi mugun tashi.

Abu Waya ya hana in bi shi, ?an'uwa da ?awayena da sauran waWanda suka isa a kaina, kamar ?annan Dad da na Mamee,da suka ri?e ni suna lallashi, dole dai ta sa na ha?ura. A wannan rana sai da aka bar mini mutane daga gidanmu suka ?wana, har da ?awayena,ganin Aunty Salwa ta ?wana,shi ma ya ?ara taimaka mini.

Sabuwar hidima ce ta Salle da gari ya waye,taro a cikin ariyar (area) gidan Sarki tamkar yau aka fara bikin, tun daga get kuwa har izuwa cikin gidana, wani sabon biki ma ni zan ce ake yi. Yamma na yi kuwa, sai hawan Daba ya tashi ranar Litinin kenan.

A al'adarsu,wai amarya da ango ke fitowa saman gidan Sarki, Sarki da tawagarsa a gefe Waya, ango da amarya a gefe Waya a sama. To sai a dinga kawo gaisuwa, dole ta sa na shirya, saboda Aunty na nan, ban da sauran dangin iyayena,?an Syria,kuwa suna can wajen Mamee suna taya ta zama.

Sai da muka kai gaisuwa wajen Sarki, sannan muka wuce ni da Yarima muka zauna, baya ga ?an bi baya da muka samu, tun daga fitowata, kafin ma in iso inda Yarima ke jira na,a nan zaune har sai da aka yi kiran Magriba, tsakani da Allah na ga girmamawa da ?auna a wajen jama'a. Wannan tasa ma na saki jikina.

Ranar Talata kuma amarya da ango ke zuwa gidan Sarki na cikin gari, amma iyakacinmu fadarshi aka gabatar da mu ga manya-manyan hakiman Sarki.

Daga nan kuma sai zuwa gaishe da iyayensa, shi Sarkin wanda dangin amarya ne ke raka ta, kuWi,?yaututtuka kuwa,wai na sha su,ni kaina na sake da irin ?aunar da ake nunawa Faysal, na san kuwa iyayenshi suka fara nuna masa ita.

Ranar Laraba,a ranar ango ke yin tashi walimar da abokanansa, saboda gabatar da amaryarsa a gare su, ita ma ta san su, sannan da ?an ?awayenta ko su goma ne,a wani babban wajen taro na manya. Iyakaci na da Faysal wajen hidimar auranmu, da mun iso gida, kowa hanyarshi yake nufa,dama kuma ba mota Waya muke shiga ba,ni da motocina, shi ma da nasa.

Ranar Alhamis ita ce ranar da na ga kowa na tafiya, wasu da safe, wasu kuwa sai yamma, amma ni ?an'uwana, sai da dare suka tafi, cikinsu kuwa har da Aunty da Fatima amarya, zan ma iya cewa su ne na ?arshen tafiya, wajen ta?was da rabi na dare, saboda sai da suka gyara gidan duk inda aka Sata,turaran wuta da sauran kimtsa amarya da ake yi kafin ango ya shigo Waki, shi da abokanansa, wanda ake kiranshi siyan baki, sai da suka sa na sake wani wankan na sake kaya, sannan suka umarce ni da in sauka ?asa,in zauna ga wata kujera ta nan ita Waya, idan sun tafi.

HuWuba, ba wacce ban sha ba a wajen Aunty,daga nan muka yi sallama suka tafi, da sunan ba zata dawo da wuri ba, saboda gidan sarauta ba a yi masa zirga-zirga,ganin na narke zan yi mata kuka ta ce wai jibi za ta dawo,ni dai na san tsarani kawai ta yi.

Na sauko daga sama a daidai lokacin da agogon bango ya buga ?arfe tara na dare, na shigo falo na yi tsaye a inda nake tunanin an bar ni ni kaWai kamar mayya, na tuna irin jama'a da suka taru a gidan nan,yau gashi rana Waya kamar an ?washe su.

Na samu ?wanar kujerar kishingiWa na ?wanta gefe, ita kaWai ta sha shimfiWun sarauta,?asan ta ma zagayayyan kafet ne (Circle) mai taushin gaske, da gani ka san ita ce kujerar zama idan mulki ya taso. A hankali na dinga bin Wakin sha?atawar da kallo, ba inda idona ya kai, sai ga ?aton hoton Faysal wanda zan iya cewa ya fi ?arfin taga, sai dai ?ofar mutan da.

**** **** ****

Ban ce ?ala ba, har ta gama, ina kallonta suka jera layi ita da ragowar ?an matanta suka yi waje sai guda biyun nan su ne suka yi saurin dawowa gefena suka zauna a ?asa, na yi murmushi na juyar da kaina gefe, sai na ji hawaye sun gangaro mini,saboda tunanin tausayawa yara ?anana da aka jera mini su,ni ina aure su suna bauta, Allah ya kiyaye.

Na Wan motsa na tashi zaune, amma na Wan kishingiWa, cikin sauri duk suka mi?e tsaye Waya ta Wauki ?afata ta gyara mata mazauni, na kalle su, ba laifi duk suna da ?yawunsu.

"Ku zauna na gode."

Suka yi saurin zama, na kalle su.

"Ya sunayenku?"

?ayar ?ar wacce ta fi ?yan ta ce mini, "Mansura." ?ayar kuma Musulum.

"A wane gari ku ke?"

"Nan gidan Sarki."

"Na sani,iyayenku nake cewa."

"Can cikin gidan Sarki, babban gidan kenan."

Nayi shiru, ina tunanin me suke nufi da haka, ban kammala tunani ba, sai na ji sallama, na juyo a hankali na kalli masu shigowa. Jakadiya Dela ce da wasu mata biyar Wauke da wasu abubuwa a rufe suna biye da bayanta, tana zuwa kusa da ni, ta ?ara zubewa a ?asa,su kuwa suka matso gaban kujerar suka ajiye kayan, suka ja da baya, suka zube ?asa, sannan suka ce.

"Gaisuwa muke, gaisuwa muke."

Na Wago masu hannu.

"Gimbiya ta amsa." Na ji jakadiya ta ce.

"Gimbiya ayi mana afuwa,muna damun ki da zirga-zirga."

"Ba komai."

"Abin da ki ka ce ba ?arya." Inji Waya daga cikin matan da suka shigo tare da jakadiya. Ta mi?e tsaye ta iso gaban abubuwan da suka shigo da su, sannan ta tsugunna.

"Allah ya ja da ran Gimbiya wannan sa?o ne daga Yarima, ya ce in kawo gaisuwa a gare ki."

Na mi?e zaune, inda su Mansura suka mi?e da sauri za su kama ni, na yi saurin Waga masu hannu, ina zama sosai, sai na ga jakadiya ta fara buWe kayan Waya bayan Waya.

Faranti ne Wan dogo, mai ruwan zuma (golden color) kayan marmari ne a ciki,lemon zai kai goma,ayaba nono Waya, sai tuffa (apple) da dabino a tsakiya, amma fa na alfarma, dole ne ma su ba ka sha'awa, saboda ?yawunsu, daga saman dabinon wani Wan faranti ne shi ma mai zagayewa.

A warwaraye ne cikinshi, tsakiyarsu da sauran kaya rakwacam, na sunkuyo na Wauki Wan farantin na Waga awarwarayen (?an hannu) sai na ga su shida ne, da sar?a ?atuwar gaske, zobuna huWu da Wan kunnayensu na zinare ne ?an Dubai Win asalin (Daham).

Na mi?awa Mansura ta yi saurin karSa ta Wora a kai, sannan aka buWe Wayan,Faranti ne shi ma kamar tsayin na farko, sai dai shi kalar ruwan silba (Silver colour) kayan sawa ne a ciki, amma da gani na bacci ne, da faranti ?aramin sama.

"Mansura mi?o mini." Na faWa.

Awarwaraye ne ?waya huWu da sar?a da Wan kunne, da zobuna biyu kacal, amma Diamond,sun bala'in burge ni, ta dinga Wagawa,sama rigunan bacci ne a ?walinsu guda bakwai, kala-kala, sai tawul ?asa da silifas, amma masu ?yan gaske, dukkansu a ?walaye suke irin ?walayen ?asashen tsallake,su kansu ?walayen abin kallo ne.

Na mi?a mata Wan farantin hannuna ta karSa, sannan aka buWe Wayan duk fa kalar faranti kalar Wan yankin da ke rufe da shi, leshi na gani na faWa, da takalmansa,jakarshi,mayafinshi,a samansu a?watina ne masu ?yau guda huWu sai Wan ?arami a sama.

Aka mi?o mini Wan akwatin na buWa, Wan zobe ne, mai ?yau na Diamond da Wan ?aramin zanen abin sarauta a jikinsa, ya yi mini ?yau sosai, na ajiye shi gefe, aka dinga mi?o mini ?an a?watinan duk turarurruka ne a cikinsu desginer na mi?a musu, sannan aka buWe na cikon na huWun,kaji ne gasassu har guda huWu masu rai da lafiya,ko a ido ka gansu sai ka yaba.

Sai ?amshi ke tashi sai she?i suke yi, da wu?a?e biyu ?anana a gefe Waya,Wayan gefen kuma cokula masu yatsu ne (Knife and fork) nayi murmushi na koma sosai na jingina.

"Gimbiya Allah ya ja da rai, waWannan kayan siyen baki ne inji Yarima." Sannan ta buWa na biyar Win bandiran kuWi ne ?an Wari biyar biyar sun kai guda goma.

"Allah ya ja da ran Gimbiya idan har baki ya siyo wannan leshin Gimbiya zata saka, sai mu tafi tare can gidan shi Yarima Win, tare da dukkan farantan nan, saboda ko za'a bu?ata a can."

Na mi?e tsaye, a daidai lokacin da jakadiya ta gama tata maganar cikin ?ASAITA na haye matattakalar bene zuwa Waki inda na ce su Musulum su zo.

Na basu umarnin da su Wauki kayan da ke saman gadona su ma lulluSe da fararan yanki, ina isowa falo, sai da naga na daidaita wajen zamana, sannan na ce da jakadiya.

"Ga waWannan ki kai masa,ki faWa masa baki ya siyu, amma Gimbiya hutawa take yi sai nan ?ila da sati biyu."

Na umarci Mansura da ta Wauko mini faranti a kicin,ta mi?e da sauri. Faranti Waya kayan sawa ne, riga da wando da babbar riga, waWanda aka Winko su daga ?asar Sinigal,a?walinsu, sai dogayen riguna guda huWu, sai gajerun wanduna huWu, duk a ?walayensu da silifas, da turarurruka huWu da tuwal Waya a samansu ne ke da zobe ?waya Waya na azurfa.

?aya farantin kuma al?ur'ani ne da abin Wora shi, Wan katakon nan da dardumar sallah mai beza mai ?yan gaske, da carbi da littafin ibada da hukunci ?waya Waya.

Farantin da Mansura ta Wauko mini kuwa, na sa hannu na Wauki kaza Waya, na Wora a saman shi, cokali mai yatsu Waya, gefe Waya na sa tufa biyu,lemo biyu,ayaba biyu, na Wauki dabino huWu na zuba, na bayar da umarnin a Wauki yanki Waya a rufe.

*?ASAITA BOOK 1*


*NA*

*MARYAM KABIR MASHI*


Page 9


Sannan na Wauki kaza Waya na baiwa ?an kawowa, tare da bandir Win kuWi.

"Jakadiya ku je ku raba,ke da abokan rakiyar ki, waWannan kuma na gaya miki ki kai masa,ki ce Gimbiya na gaishe shi baki ya siyu, amma tana hutawa har nan da sati biyu."

"Maganar ki ita za'a bi, godiya muke."

Na koma na ?wanta jikin kujerar da nake zaune, ina kallonsu suka bi layi suka fita kamar yanda suka shigo, bayan nan kuma na umarci su Mansura da su ?washe kayan su Wan Wibar mini kayan marmarin,su Wauki ragowar, haka kajin na ce su Wauki Waya.

Cikin girmamawa da biyayya suka aikata yanda na faWa, tun daga lokacin kuwa sai na koma sama,a inda na umarci su Mansura da su Wauki daki Waya a ?asa su ?wanta,ni sai da safensu.

Ba?in ciki, takaici, suka saukar mini a daidai lokacin da na tuno da Anwar,na yi tunanin da shi na aura,muna can ya shigo Waki a sunanshi na ango, ina can yana tarairayata da nuna mini kulawa Wari bisa Wari, wannan tunanin yasa na sha kayan baccina, na buWe ?ofar da za ta fitar da kai barandar da take a gaban gidan.

Na dafa ?arfen barandar, wanda na mayar da idanuwana na lumshe,a daidai lokacin da wani ni'imtacciyar iska ta kaWa, iska ta dinga Waukar gashin kaina tana juya shi a hankali, hawaye masu sanyi suka tsiyayo mini a kumatuna, a lokacin da tunanin rayuwata ta raunana ya faWo mini,anya kuwa zan amince in dinga irin wannan zaman jakadancin? Komai ke tsakaninka da mijinka sai wata ta sani.

Na buWe idanuwana tare da ware hannayena tamkar ina jiran wani ya rungume ni, kamar an ce in kalli barandar sama wacce take kallon tawa barandar,sai kawai na hango mutum a tsaye, shi ma ya dafa ?arfen barandar ya sunkuyo yana kallona.

Da Wan nisa, shi ya hana ni in gane ko waye, kuma ga iska tana kaWawa, natsuwa na yi sosai na ?ura masa ido, ba abin da idanuwana suka karanta mini sai angona Faysal.

Tsanarshi na ji ta ?aru a zuciyata a take ban san lokacin da na juya na shige cikin Wakina ba, na mayar da ?ofa na kulle, na wuce na faWa gadona a inda na kasa tunano komai sai Dad wanda da ya san rayuwar da ya jefa ni ciki, na san da bai fara ba.

Ni ce har ?arfe biyun dare zaune a abin sallah ta, ina ro?on Allah ya kawo mini canjin rayuwar da ta fi alheri a gareni,ni kam na san ba zan iya wannan auran ba, na yi tunanin wai yau ne daren farko (first night) Wina,amma gani nan a zaune ko kalar ango ma ban gani ba.

?arfe shida na safe na farka, hakan yasa na yi saurin saukowa daga gadona, domin gabatar da sallar Asubahi Win da na makara ban samu yi ba. ?arfe tara na safe har na gama komai na sauka ?asa domin nemawa cikina abin da zan ci.

Wani abin mamaki da na gani, shi ne yanda har an gama gyara ko'ina na falon, sai ?amshi ke tashi, sannan kuma gaba Wayan gayyar ?an matan nan sun hallara waje Waya ni kawai ake jiran fitowata. Tausayinsu ya kama ni,a zuciyata na ce bayin Allah, insha Allahu sai na raba ku da wannan ?angin na bauta,a take na ji ina ?aunarsu, sannan ya zama dole ma in Wan saki jikina da su, saboda su ji daWi su ma.

A take na yi murmushin dariya, "A'a Mansura har kun tashi?"

Cikin sakan Waya har sun gama isowa bakin matattakalar benan da nake saukowa sun zube ?asa.

"Haba, abokaina, ya zaku dinga yi mini haka, tamkar wata wacce ku ke bautawa, na san dole ne ku ba ni girma, amma irin wanda nima zan ji daWinshi ba irin wannan ba.

Sai na ga wannan ya kalli waccan, waccan ta kalli ?ar uwarta, na sauko na dinga dafa kafaWar na kusa da ni.

"Ku zo muje." Suka biyo bayana. Ina zama gaba Waya suka zube ?asa.

"Gimbiya mun gaishe ki. Barka da ?wana?"

Na amsa masu da lafiya ?alau. A nan na dinga tambayarsu sunayensu, Waya bayan Waya, wani abun in yi ?o?arin ba su dariya, amma bayin Allah nan sai na ga sun kasa yin dariya, ga ta kuma suna son yi. Na waiga na kalli Mansura.

"Mansura, har yanzu ban fahimci waWanda ke kicin ba."

"Allah ya ja da ran Gimbiya ga mu nan."

A take na ga ?an mata masu ?yau suma.

"Yaya abinci?"

"An gama shirya shi a wajen cin abinci, na Yarima fa?"

"Ai can ake haWa masa shi ma."

"Su wa ke haWa masa?"

"Yana da masu yi masa."

*Maza ko mata?"

"Maza ne."

Na taSe baki, sannan na mi?e na bada umurnin a kai ni wajen cin abincin. Kai wata duniyar ma in ka shige ta, sai ka ga tamkar yau aka haife ka, saboda ganin sabon yanayi da sabon tsari.

Duk a cikin falon muke, amma da muka bi ta wata hanyar sai na ga tamkar mun fita ?asashen turawa, wani Wan rukuni ne mai kama da Wan ?aramin wajen sha?atawa an saka masa wasu labulaye masu kama da rumen kitso, da ka buWa sai ka ji sun yi kankacakau, madadin tebirin cin abinci da muka baro a falo.

Sai na samu shi kuma wajen shafe yake da kafet, mai ?yan gaske ga wani tsakiya mai zagayewa, sannan na ga an shinfiWa wani yanki mai ?yan gaske,fari mai zanen jajayen fulawoyi, shi ma zagayayye ne,saman shi aka jera kayan abincin,ga tuntayen alfarma guda uku gefunansa.

Ina zama jakadiya na isowa, ta zube gabana ta kai gaisuwa.

"Allah ya ja da ran kilishin Gimbiyoyi jakadiya na yi miki barka da Asuba."

Na yi murmushi, "Gimbiya na amsawa jakadiya,kin ?wana lafiya?" Sai na ga tana sussunne kai.

"Jakadiya ba a amsa mini."

"Lafiya lau, Kilishin Gimbiyoyi."

"Dama Yarima ne, ya aiko ni ya ce a gaya miki yana jiran gaisuwarki, sannan yana gayyatarki karya kumallon safiyar nan,zuwana na huWu kenan a lokacin dai baki fito ba."

"Ki gaya masa ina amsawa, amma ki ce kin same ni har na Zauna saman in da zan karya nawa kumallon,sai dai ya jira wata safiyar sai ya ?ara aikowa."

"An gaishe ki." Ta mi?e da hanzari ta yi gaba,ni kuwa na buWe kayan cin abincina, amma a cikin sauri ?an matan nan masu girki suka karSe ni. Farfesun naman kai ne da sinasir a gefe Waya, sai soyayyan dankali mai ?wai a ciki, ga kunun gyaWa a gefe Waya, ban da ruwan shayi da yake a gefe, da cinyoyin kaji zalla an soya su.

Bayan na gama ne na umarci su Mansura su zo su raka ni in zagaye gidan, har waje saboda sanin yanda yake duk da ?wanana biyar kenan a gidan, amma a tare nake da jama'a ?an biki.

Samana dai falo ne babban gaske, wanda ya sha kujerun alfarma har kala biyu, kowanne rukuni,kalar kujerun su daban, amma irin na gidan sarauta, sai Wakuna ?waya biyu kacal, wani gado ne ?waya Waya a tsakiyar Wakin zagayayye mai kama da ?wano (Circle), ?aton gaske,an zagaye shi da wasu labulaye farare, wanda sai dare ya yi ake danna wata na'ura wato remote sannan sai ya sauko.

Gaba Wayansa shinfiWe yake da zanin gadon da ya bazu ?asan shi, wanda kafet mai laushin gaske ne ?asan shi, shi ma a zagaye yake, sai daga can gefensa kujeru ne masu zagaye aka yi masu rukuninsu daban, har Wan tebirin tsakiyarsu (Centre table), sai daga kusurwa tebirin rubutu ne har da kujerunsa biyu.

Daga Wan nesa da gadon kuma kujerar kushin ce doguwa, ?waya Waya, wacce ta sha shinfiWar dardumar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login