Showing 27001 words to 30000 words out of 72369 words
Chapter 10 - Ni Da Ke Book Complete Document by Amnah El Yaqoub --.txt
mata "to Muje"
Tafiya suka fara yi, matar ta dubeta tace" kinga ga Mota can Muje saiki masa kwatancen gidan "
Tace" to, amma cikin ranta mamaki take, wacce irin macece wannan, dole sai a gidansu zatayi sallar? Yanzu idan takoma gida Abba yace ina suka hadu matar tace makaranta yaya zasu qare dashi? Shknnn ita kuma tasan kawai yau asirinta yagama tonuwa 🙆🏻🙆🏻
Direban ne yazo da sauri yabude musu motar gidan baya, matar ta dubeta tace "shiga "
Ahankali ta shiga, tana shiga qamshi yaratsa hancinta, ga sanyin esi daya cika motar
Itama ta shiga dreba yaja suka fara tafiya
Suna kan hanya matar ta kalleta tace "sainaga Kamar wayar taki zata iya samin matsala,"
Murmushi tayi kanta na qasa tace "a a hajiya, Babu komai wallahi"
Cikin sigar wasa tace "lala ba sunana hajiya ba, sunana Halima, amma d'ana Baffah yana kirana da Ummi, kema zanso ki fadamin hakan, Yaya sunan kine?
Ahankali tace" Ummi sunana Nawal "
Murmushi Ummi tayi tace" Nawal daurin dankwalin naki yamin kyau, duk lokacin dazan fita unguwa idan Zan daura dankwali d'ana Baffah qwacewa yakeyi yace shizai daura min, yanaso yadinga min kwalliya "
Cikin ranta tace yau nagamu da uwa Mai jarabar son danta 🤔😂😂
Zance daya biyu sai ta saka shi ciki?
Amma kawai sai tayi Murmushi tace" Allah sarki "
Ummi tasake cewa" muga wayar taki? "
Nawal ta miqa mata wayar, tana karba tace" gashi kuwa har screen yafashe "
Jakarta ta zuge tadauko wata waya qirar iphone tabata tace" ga wannan wayar Babu komai acikin ta, zaki iya cigaba da amfani da ita kibada sadakar wannan dayar, nima Baffah ne yakawomin lokacin da zaizo "🤣🤣
Dasauri tace" a a wlhy kibarshi nagode, wallahi Babu damuwa Zan iya amfani da tawama ahaka,"
Ummi tace" a a, Nawal, Inda tare nake da Baffah to zai iya marinki, saboda bayaso kokadan yaga ana ja'inja dani" 🤣🤣🤣
Ahankali tace "to ngd sosai, Allah yasaka da alkhaairi," cikin ranta kuwa cewa take gara na karba inba hakaba kafin mu sauka saita gama fadamin komai na Baffah 🤣🤣
Da kwatance da Komai suka qaraso gidansu, tareda ita suka shiga gidan , Umma da mama mariya na ganin ta tareda baquwa suka karbeta hannu bibiyu,amma umma kam tambaya ce fal ranta, jira kawai take matar tatafi 🤣🤣
bayan tayi sallah tace" zata tafi amma tanason ganin maigidan
Aka tura Saif yaje yakira Abba amajallisa, har falon umma Abba yaqaraso yaga baquwar fuska, cikin Murmushi tace "Alhaji dama inaso ne zamuyi wata magana"
Abba yanemi waje ya zauna yace "to baiwar Allah gashi kuma bansan kiba"
Murmushi tayi tace "Sunana Halima Jamal Baba, ni mutuniyar Adamawa State ce, naga 'yarka Nawal ne amakaranta yanzu, Wato Alhaji gaskiya kayi kokari kuma ka jajirce akan tarbiyar yarka, nima hakan ne yad' au hankalina akanta harna biyota gida inaso kabawa d'ana Baffah auren ta idan Babu damuwa, bazan boye maba dana bayaji, amma inaso sanadiyar yarka yazama abin alfahri agareni, "
Ta ajiye masa number wayarta taci gaba da cewa" wannan itace number ta, kuma na baka dama kayi bincike akaina Kamar yanda shari' ah ta fada, zaku iya tuntubata daga baya domin naji duk abinda kuka yanke "
Tana gama magana taayi musu sallama tatafi
Ina fatan zakumin uzuri duk lokacin dakuka jini shiru kunsan jiki da jini😉
Sharhi Dan Allah 🙏🏻
Mrs Usman ce ✍🏻
[2/2, 1:47 AM] Amnahelyaqoob: 🌺NI DAKE🌺
(Hot luv story)
Writing by Amnah El Yaqoub
Dedicated to Itz sadeek
21&22
"To Baffah nawa nake dashi inba kaiba?"
Kansa dake masa barazanar rabewa biyu yadafe🤦🏻♂, jiri-jiri yafara daukan sa yatafi luuu zai fadi tayi saurin tashi ta riqoshi tareda zaunar dashi akan kujera
Idanunsa sun kad'a sunyi jajir, yafara furta kalmar "Innalillahi wa inna ilaihir raju'un" sai kuka 😭
Kuka yafara Kamar qaramin yaro
Ita kanta Ummi jikinta ne yayi mutuqar sanyi, al'amarinsa yayi masifa tsoratata, rabon dataga kuka a'idon Baffah ita kanta ta manta
Kuka yake sosai yadafe kansa da hannayensa duka biyun, cikin hawaye ga idanu yayi jajir yajuyo ya kalleta "why Ummi? Ummi meyasa? Meyasa zakimin haka? Ummi akwai yarinyar danake so, akwai yarinyar da d'anki abin sonki yake mutuwar so Ummi, ina cikin tashin hankali kullum sai nayi mafarkin ta, naqi sanar dakene saboda inaso saina nemota, haba Ummi, meyasa Dan Allah?" yasa tafukan hannunsa Yarufe idonsa dasu Idanunsa naci gaba da tsiyayar hawaye
Adede wannan lokacin tafuto daga cikin dakin Ummi, Gabanta ne yafara faduwa ganin wani hadadden gaye yana kuka tuquru, ko shine Baffan? Ta tambayi kanta
Tsananin mamaki yakamata Babba Kamar wannan yana kuka
Ummi ce tadago taganta, cikin sanyin jiki tace"zoki zauna Nawal "
Jin ankira sunanta akusa yasa yadago kansa yazuba mata wani kallo me kama da harara,still idanun nasa na zubar da hawaye, gabansa ne yafadi Wanda shi kansa baisan ma'ana da dalilin hakanba, kuma arasa waza'a aura masa sai wannan ficiciyar yarinyar dazai iya karyawa Tun adaren farko
Adarare taje kusa da Ummi ta zauna tareda sunkuyar da kanta
Ummi ta dubeshi "Baffah, naji bayaninka, kayi hakuri Umminka tamaka laifi, tayima aure batareda saninka ba, nayi tunanin Zan iya zartar maka da kowanne hukunci ne amatsayina na mahaifiyar ka, amma kayi hakuri"
Wani sabon hawayen ne yazubo masa, yasaka hannu ya share, "A a Ummi, kiyi hakuri ba haka nake nufi ba, kin kalli zancena ta wata fuskar ne, kiyi hakuri"
Quri Nawal tayi da ido tana kallansa harya gama maganar, Gabanta yana faduwa da sauri
Tausayinsa ne yakama Ummi, tace"shikkenan, Allah yayima albarka, bansan cewa akwai yarinyar da kakeso ba,amma yanzu ma lokaci bai qureba, duk lokacin daka sameta, zaka iya auren ta, amma yanzu de, ga yata Nawal nan, Baffah ka riqemin ita amana, "
Wani irin qullutun Baqin ciki ne yazo wuyan Nawal, kowa yanada Wanda yakeso amma antashi anwani hadasu da juna, jin cewa yanada wadda yakeso yasa mk yafado mata arai, batasan lokacin da hawaye suke silalowa daga idanuwanta ba
Jin bece komai ba yasa Ummi tasake cewa "Kayi alqawari?"
Still baiyi mata maganaba yadaga kansa
Hannunta ta miqa masa tace "bani"
Ahankali ga idanu jajir yace "ban siyoba"
"baka tabaamin qaryaba, banaso kafara, qaryar bata dace dakai ba kwata kwata," tasake miqa masa hannu batare datace komai ba
Ahankali yasa hannu cikin cikin wandon jeans din jikinsa yadauko wata akwati yar qanqanuwa irin wadda zobe yake zuwa aciki, yadora mata atafin hannunta
Budewa tayi taga zoben Dan qarami dashi yayi kyau, atsakiyarsa akai harafin 'n' din, saika zuba ido sosai zaka gani
Ta kalleshi tace yayi kyau sosai, gashi ka karba kasaka mata, hakan zai nunamin cewa alqawarin daka daukamin nacewa zaka kula da ita yana nan "
Zuciyarsa Kamar zata fashe saboda haushi, ya karbi zoben yariqe baiko kalli Inda takeba
Ummi ta dubi Nawal tace" 'yata share hawayen ki, kiyi hakuri kinji, tashi kije yasaka miki zobenki "
Hawaye ne yazubo daga idonta Ahankali ta tashi taje gabansa ya tsugunna, amma ta kasa kallansa, wani irin kwarjini yaamata, yanzu wannan Babban ne mijinta?take tambayar kanta
Ummi ta kallesu tace" menene haka Kamar wani me laifi dame neman yafiya?please kutashi tsaye mana"
Ahankali ta miqe tsaye, shi kuwa saida yadebi wasu seconds sannan yatashi tsaye shima
Ummi tace "Nawal bashi hannu"
Ahankali tadaga farin hannunta dayaji zanen fulawa tamiqa masa
Ganin Ummi tana wajan yasa yakai hannunsa yakama nata hannun, wani irinsa zirrrr yaji tundaga kansa har tafin qafarsa, duk rungume rungumen mata da yakeyi bai tabajin hakan akan kowaba sai akanta
Tafin hannun nata laushi, Ahankali yafara tura zoben harya gama saka mata, yana gamawa yasaki hannun nata, yakama hanyar fita daga falon
Ummi tace "ina zakaje?"
Cak ya tsaya a Inda yake, bai juyo ya kalleta ba yace "Ummi Zan fita ne"
"kadawo ka zauna, koka Manta kai Ango ne?, sannan idaan zaka fita matarka yakamata ka fadawa"
Baqin ciki ne yakama shi, Kamar zai fashe da kuka haka yadawo ya zauna yakawar da kansa can gefe, kwata kwata Yaqi kallan Inda take ma
Har azahar haka suke wannan zaman kuramen, Ummi tana lura dasu kuma ba tayi musu maganaba ta qyalesu, tasan cewa rashin sabo ne kawai, zuwa Dan wani lokacin zasu saba
Ummi ta kalleta tace" Nawal tashi kizuba mana abinci, Karki zubawa Baffah da yawa, bayasan cin abinci "
Cikin nutsuwa tace "to" ta tashi tanufi kitchen din
Kamar yanda Ummi tace haka tayi, amma tana tsugunnawa agabansa da abinci yamiqe tsaye
Ummi tace"ina zakaje? "
" masallaci zanje Ummi" abinda yace kenan
Tace" idan ka'idar kadawo gida "
Bece da ita komaiba yafice, haka kuma yana idarwa yadawo ya zauna yayi tagumi 😱🙉yana kallan tv
Shide wannan zama kawai Dan dole yake yinsa🤣🤣
*** ***** ***
"umma ashe Najma batada lafiya, saida nazo yanzu naga jikin nata"
"Nasrin wallahi kinganta nan tunda Baby tatafi takwanta jinya, zazzabi yarufeta, datawo nan ta kwanta a'inda Baby take bacci"
"Allah sarki, Allah yabata lafiya, Umma yaya wajan Babyn kuwa? Inata kiran wayarta akashe"
"eh nima Tun dazu nake kiranta bata shiga, amma nasan idan tabude wayar zata kira mu"
Jinjina kai tayi tace"Allah sarki Baby, toshknn umma bari natafi gida, "
" to Nasrin ki gaida mamanku, ga wannan kikai mata "tabata wata leda
Tace" to umma sai anjima "
*** ***** ***
Har dare suna zaune kowa yayi shiru, yana zuwa sallah Ummi zatace yana idarwa yadawo
Har qarfe tara na dare suna zaune suna kallo
Amma shikam kawai yana kallan photon cikin ne, amma baya fahimtar komai, Baqin ciki ne cike da ransa fuskarsa Babu alamun annuri atamke
Ummi ta kalleshi "Baffah adakina nace Nawal ta zauna kafin kadawo, tunda kadawo gobe saikuje ka nuna mata dakin naka, saiku sake gyara shi zuwa yanda kukeso"
"No Ummi kawai kibarta anan din zaifi,"
"wai Baffah meyake damunka ne? Cemaka akai itama yarinyar tanaso ne?"
Cikin ransa yace"tanaso mana, idan bataso ai bazata yardaba, shi Dan bai saniba ne, aida bazai yarda ayi ba, ciki ciki yace mata "Ummi bansaba kwana da kowa bane ad'akina, bayan hakama d'akin yamana kad'an"
"duk wannan uban dakinne zakace yamuku kadan? Saikace wata giwa?" 😂
Shiru yayi baice komaiba
Sai cika yake yana batsewa
Ummi ta kalli gefen da Nawal take zaune, sai taga har tayi bacci
Ta maida Kallanta gareshi tace "laa Baffah kaga yarinyar nan har tayi bacci, d'an meqamin ita daki"
Dasauri ya kalleta saboda jin furucinta
Tace"yi sauri mana yarinya tana bacci a kujera kar wuyanta yayi ciwo"
Takaici ne yakamashi, wai Ummi daga ganin yarinya duk tabi ta rikice
Tashi yayi sai qunci yake yaje kanta ya tsaya, amma bashi da niyyar tabata
Ummi tace "mekake jirane?"
Kallanta yayi yaga hankalin ta ma yana kan tashar datake kallo
Hannun rigar jikinsa yafara tattarewa Kamar Wanda zaiyi wanki 🤣
Sannan yakai hannu zai dauketa, hannun nasa bai sauka ko'inaba sai akan hips dinta, cikin sauri yajanye hannunsa daga wajan
Sannan yadauketa cimak yayi dakin Ummi da ita, Kamar yanda ya zata haka yaji, batada wani nauyi, to dama wannan ficiciyar yarinyar ina zataga wani nauyi
Saida yakai ta har kan gadon Ummi sannan ya kwantar da ita, garin d'ora kanta akan fillo hular datasa akanta tafadi gefe, dogon gashinta yazubo akan hannunsa, gashin nata yabi da kallo yaga sai sheqi yake kuma da alama zaiyi santsi
Cikin sauri yajanye dayan hannunsa daga jikinta, Wanda gashin yazubo mata ma yawatsar dashi Kamar yaga wani abin qyama
Tambayar Data fara zuwa kansa itace, meyasa gashinta yake haka kode ba bahaushiya bace? Domin ya tabbatar bahaushiyar ce ko akasin haka yakai dubansa gareta
Tsura mata ido yayi yana kallan tsabar kyanda Allah ya mata, afatar bakinsa yafurta "tanada kyau, but na tabbatar Baby zata fita kyau" Wanda shi kadai ne zai iyajin furucin nasa
Lips dinta yakallah, yasake kallah, sak irinna Baby, meyasa dazu tashin hankali ya hanashi lura da hakan ne?
Ahankali yatako yadawo gefen kanta ya tsugunnah tareda zuwaba lips dinta ido
Wash yau nasha typing, 🙈🙈🙈nasan Zanga Ruwan Comments da sharhi Kamar yanda nadage nayi wannan uban typing 🙈🙈
pls sharhi 🙏🏻
Amnah El Yaqoub ✍🏻
[2/2, 1:47 AM] Amnahelyaqoob: 🌺NI DAKE🌺
(Hot luv story)
Writing by Amnah El Yaqoub
Dedicated to Itz sadeek
19&20
Shide Abba jikinsa asanyaye yariqe wannan number, yadubi umma yace "waye yabawa wannan yarinyar iznin zuwa makaranta ne?
" Alhaji wallahi nima bansan cewa makaranta tatafi ba, tacemin de zataje gidansu Nasrin "
Mama mariya tace" nifa Alhaji hankalina bai kwanta da matar nanba, kadubi fa hannunta duk gwala gwalai ne, sannan wacce uwace zata fadi laifin danta? (niko nace uwa tagari 🤔)
Taci gaba da fadin,
Yanzu hakama yaron Dan shaye shaye ne ko manemin mata "
'Daga murya yayi yace" Nawal ! " asukwane ta futo daga cikin dakin dama jiran sammaci take 🤣
"Abba gani"
"Wacece wannan matar da kikaje kika yayimo?"
"Abba nima bansan taba"
"to naji d'aya, wayar waye wannan kuma ahannun ki?"
Wayar ta meqa masa tace "Abba itace tabani"
Batare daya karbi wayar ba yace "nahanaki zuwa makaranta shine kika take magana ta kika tafi, toshknn yamiki kyau kijirani ina nan dawowa kanki" yana fadar haka yafice daga gidan
Mama mariya tace"nikam tsoro ma matar tabani, daga gaanin ta irin matan nanne na birni Wanda idonsu yabude daga nan ta fice daga falon itama
Umma ta kalleta "ashe ni zaki yaudara kiyiwa qarya Baby ? 🤣, bakisan ramin qarya qurarre bane ko? Ai shknn, yanzu saiki san yanda zakiyi da matar da kika kawo, tunda kinji abinda tazo nema"
"umma Dan Allah kiyi hakuri, wallahi dana fita mukai waya da Nasrin din shi ne tacemin wai tana makaranta, shine naj...
" rufemin baki, maqaryaciya kawai, aina dena yarda da maganar ki Nawal, naga alama nema kike kifi karfina "
" umma Dan Allah kiyi hakuri insha Allah bazan...
Katseta tayi," tashi kiban waje ni"
Cikin damuwa ta shige daki, wayar hannunta takallah wadda maman Baffah tabata🤣🤣
*** ***** ***
"wallahi Malam matar tabani tausayi, da girman ta da Komai, sannan abinda yasa naqara tausaya mata shine, da bakinta tace ita tasan cewa danta bayajin magana, amma ta budi baki ta fadamin hakan, abinda yanzu yake wahala acikin neman aure kai tsaye afuto a fadama gaskiya, wasu 'yarsu tanada lalurar aljannu iyayen ta bazasu fad'aba, sai kaga sai anyi auren qarshe azo ana samun matsala, wasu kuma zakaga yaransu suna da wasu cututtukan amma akasa bayyana wa saboda nauyin abun dakuma tsoron cewa masu neman auren zasu iya fasawa
Amma ni bansan wanne irin rashin ji yaron nata yake dashi ba, amma ga number tabani tace ayi bincike akanta "
Malam yayi ajiyar zuciya sannan yace" Nawal kenan me jama'ah, ga Nuhu gakuma wani ta janyo🤣🤣
Wannan ba abin damuwa bane muhammadu, akwai mutane na a Adamawa, zansa ayi binciken insha Allah, duk abinda bincike yabamu saai akira yarinyar aji ta bakinta, mude Nuhu muka sani koba hakaba wannan bamu sanshi ba, da haka sai abata zabi acikinsu, "
Abba yace" to Malam nagode "
" Babu godia tsakanina dakai muhammadu, d'ana gari ai shine yake neman shawarar iyayensa"
*** ***** ***
Kemade Baby meya kaiki zuwa makaranta, yanzu gashi bayan kina cikin matsalar Nuhu kinsake danna kanki cikin wata matsalar "
" Najma nimafa matar nan kawai dagewa tayi akan saita biyoni, nayima tunanin kawai sallar zatayi tatafi, idan nasan zatazo da wannan maganar tayaya Zan barta tabiyoni, amma kowa sai laifi na yake gani, ya kukeso nayi ne "
" abinda zakiyi shine kizabi d'anta koki zabi Nuhu "
" Najma kinsan abinda kike fada kuwa? Bansan mutum ba, ban taba ganinsaba, kawai shikkenan saina amin ce "
" to Baby idan baki aminceba ai shikkenan saiki amincewa Nuhu "🤣🤣
*** ***** ***
Kallanta yayi yace
"to Ummi nizan wuce"
Ta kalleshi cikin jin dadi, ganin yasaka norml kaya qanana Wanda ba crezy ba tace"to Baffah, dawuri zaka koma kenan wannan karon, bazaka mana Dan kwana biyu ba "
" ai Ummi akwai ayyuka ne"
Cikin Murmushi tace "to Allah yadawo dakai lafiya, nayima alqawarin wannan dawowar da zakayi zanbaka wani kyakykyawan Surprice"
"Ummi naga sai farinciki kikeyi, meyake faruwa ne"
"A a Babu komai, kaide kawai saika dawo din"
"to Ummi Zan tafi"
Tace "Allah yakiyaye"
Yasake cewa "Ummi Zan tafi"
Tashi tayi tsaye tace Dan Allah naji, Muje, suka fice daga falon, har zuwa harabar gidan, Babban gida ne Mai mutuqar girma, wanda yatsaru da kyawawan motocin sa, har gaban motar dazai shiga tarakashi, tace "to Muhammadu adawo lafiya, Allah yakaika lafiya yadawo dakai lafiya, idan zaka dawo inada saqo"
"saqon me kikeso Ummi?"
"zobe nakeso kasa ayimin Mai harafin 'N' na gold sannan na yarinyar da bazata wuce 18 years ba"
Yayi mamakin maganar ta, amma saiya basar yace"to insha Allah "
" bakayi sallama da yafendo ba itama yau zata tafi "
" um ki gaishe ta kawai Ummi, taagaida mutanan gida "
" to shikkenan, sannan ta kai hannu takama kunnansa tace"yagaggun kaya "🤣
Dasauri yakai hannunsa kan kunnansa yace" Auch! Ummi bazan saba "
Badan ta yarda da maganar tasaba tacika shi, sannan aka jashi zuwa Airport
Wannan shine gidan Alhaji Kabeer Sule yola, ba qaramin me kudi bane, yataka matsayi na siyasa sosai da sosai, haka kuma yana daya daga cikin masu fada ajin 'yan siyasa, yana daya daga cikin mutanan dasuke tsaida d'an siyasa takara
Mutum ne Mai mutuqar tausayi, da temakon talakawa, yana kaiwa gidan marayu ziyara tareda temakon su, bayan aikin yi dayake temakon mutane dashi
Kowama nasane, yanada halin kirki, matar sa daya Hajiya Halima Jamal baba, itama yar adamawa ce sunyi aurensu tunna saurayi da Budurwa
Aikin dayake ne yasa suka tattara suka dawo Abuja da zama
'Dansu daya namiji suka saka masa sunan Baban Hajiya Halima, Wato muhammadu, kasancewar su fulani shiyasa suke kiransu da Baffah, saboda haka dabi'ar fulani take, idaan sun sakawa yaro sunan babansu sunayi masa inkiya da Baffah
Tun yana karami yataso shiru shiru marar son magana, babansa yadaukeshi yakai shi qasar waje karatu tundaga lokacin dabi'ar sa tasauya,yahana ace masa muhammadu saide mk, zama da abokai yasa yakoyi wasu daga cikin halin su marar kyau, Kamar shigar dabata daceba, haka kuma idan yaga mace ba komai bane awajan sa ya rungume ta, yayi kissing dinta, wannan abu yana yiwa iyayen sa ciwo, Dan haka suka dawo dashi gida aka maida shi makarantar mu tagida Nigeria, harya kammala secondry dinsa, tareda saukar alqur'ani da sauran littatafai
Daga baya suka maida shi qasar waje yayi degree da masters tareda phd, anan yahadu da Yasir sukai zama na mutunci har yake kiransa da Yas
A tunanin iyayen sa yadena wannan dabi'ar, ashe abin ba haka yakeba, cigaba ma aka samu akan da, domin kuwa har Dan kunne sakawa yake
Kwatsam rana daya Allah yayi wa mahaifinsa rasuwa,