Showing 15001 words to 18000 words out of 72369 words
Chapter 6 - Ni Da Ke Book Complete Document by Amnah El Yaqoub --.txt
munkai qara wajan yan sanda, amma wani daga cikinsu yabamu shawara akan mujanye case din, saboda Mai unguwa sale zai iyayin komai akan hakan, kuma idan mukaje kotu za'a iyayin watsi da qarar, shine nakeso na kamashi itama ta lalata nashi idon kaga anyi 50 50 kenan 🤣yayinda ubansa yakaimu kotu kaaga anan dole a saurari qarar, tunda mu yanzu idan muka kaishi babu abinda za'a yi masa
Amma kaji usy wai ahaka Abba yake cewa narabu dashi "
" kata'i, shine abinda yafuto daga bakin usy🤣🤣sannan yace "Sultan wannan ai ba abin yafiya bane, idan ku kunyi shiru ai anbashi damar dazai sake yiwa yar wani haka"
Sultan yace "kaima de kafada"
"Amma Sultan baka kyauta minba dabaka kirani munje tare daku gidanba, narantse da Allah dakunje Dani inba saina wankawa Mai unguwa sale mari ba 😳🙊saide yasa adaureni,"
Sultan yace "abinda nasoyi kenan Abba ya katseni"
Usy yace "wallahi Anwar bayanan, yaje Uganda, amma inde yadawo Zanzo har Gida nafadama"
"Usman lagos zankoma, Abba yace natafi, sannan itama yarinyar yanzu suna Albania anayi mata aikin idon Acan, sai sundawo sannan zanzo naganta, ina fatan a lokacin Data dawo shima Anwar yadawo, zanzo naganta kaga a lokacin saina ritsa shege🤣"
"good hakan yayi, Allah yasa lokacin dazaka zodin shima yadawo"
"usy koda baidawo ba Zan jinkirta zuwan nawa har sai lokacin daya dawo, nide abinda nakeso dakai shine daka ganshi kamin waya"
"to shikkenan Sultan saika jini,"
Daga haka sukai sallama
*** ***** ***
Washe gari tunda asuba Abba dayai sallah a dakin nasu yafara karatun qur'ani Ahankali, karatun dayake ne yatashi Nawal daga baccin datake
Ahankali ta yunqura ta tashi, Dasauri Abba yaqaraso ya riqeta "Nawal kina buqatar wani abu ne?"
"Abba fitsari nakeji, kuma da yunwa ma🤣"
Yace"to bari akira likita", yana fita yadawo da wata mace, itace takamata har zuwa toilet tayi fitsari tareda wanke baki, suka futo "
Gadon tamaidata ta kwantar, itade mamaki yagama kasheta cikin sauri tace" Abba bata barni nayi alwala bafa "
Adede lokacin likitan dasukazo dashi yashigo dakin tareda bata amsa" ai saide kiyi hakuri har acire miki wannan abun na idonki sannan ki rama sallolin dake kanki, keda ba'aso ko abu ne kidauka aqasa saboda idonki "
Abba yayi Murmushi yace" to kinji "
Sannan suka gaisa, itama ta gaishe su tayi shiru, Abba yace" kidinga addu'ah fa, anjima zasuzo su cire miki wannan abun na idonki, idan anyi nasarar aikin idonki zai bude"
Murmushi tasaki tace "to Abba zanyi" cikin zuciyarta kuwa murna ce fal, idonta zai bude zataci gaba da ganin su ummanta
Wata zuciyar tace mata toshi kumafa?mutumin daya ceci Rayuwar ki daga fadawa makanta ta din-din-din? Murmushi tasake saki ita kadai, to kodan tasake jin muryar sa ai dole ma ta nemeshi, bare kuma yayi mata wannan kirkin ai dole ma ta nemeshi a duk Inda yake (tofa😳🤔)
Shide Abba yaga tana ta faman Murmushi, amma bai kawo komai aransa ba, yadanganta hakan da murna akan maganar dayayi mata
Sai wajan sha daya saura sannan likitoci suka shigo dakin nasu kusan su uku
Ba ita da akaiwa aikiba hatta su kansu likitocin idan kadubi fuskar su zaka tabbatar suna cikin shakku, kowa fatansa asamu nasara akan aikin nata
Gabanta kawai luguden faduwa yake, yanzu idan aka kunce mata tace bata gani shikkenan fa tariga tazama makauniyar karfi da yaji
Wanda zai cire mata ne cikin sigar rarrashi yace "ki kwantar da hankalin ki kinji?sannan yafara warware mata bandejin Ahankali
Mutanan dakin duk sunyi shiru 😱kowa jiki yayi sanyi, musanman Abba, Wanda mutanan Nigeria suke jiran kiran wayarsa🤔
Cikin nutsuwa yake warware mata bandejin harya cireshi gaba daya,idanunta alumshe, yace "Open your Eyes"
Ahankali tafara bude idonta harta bude shi gaba daya, cikin sauri ta maida idonta tarufe ganin wani irin haske daya ziyarci idonta
Gaba dayansu hankalinsu yana kanta, kowa jira yake yaji abinda zatace
Likitan yace, "bude mana "
Sake budewa tayi ta kalleshi, sannan ta kalli Abba, tasake kallan likitan dasukazo tare amatsayin Wanda yayi musu jagora 🤣
Abba de atsorace yake, 🤣
Likitan yace "kina ganina?"
Ahankali ta daga masa kanta, sai hawayen farinciki tace "ina gani, amma dishi-dishi nake gani"
Gaba dayansu likitocin suka fara murna ganin anyi nasarar aikin, yadubi su Abba yace, "aiki yayi kyau, dama dole ranar da'akai mata aikin bazata gani karkar ba, dole sai Ahankali idonta zai washe taci gaba da gani sosai, zuwa gobe za'a iya sallamarku"
Abba yadaga hannu sama yace "Alhamdulillah, Alhamdulillah, Allah nagode ma"
Fita likitocin sukai daaga dakin kowa na farinciki
Suna fita likitan dasukazo tare yadubeta "to yanzu de kuka yaqare ko? Tunda kinga abbanki, shikkenan kuma idanu sun bude"
Hawayen idonta tashare tace "Abba ashe Zan sake ganinka? Abba Dan Allah kiramin umma tah"
Shima kansa dadin yakeji yace "to bari akira su, yana kira baiyi magaanaba yabata wayar, cikin sanyin jiki umma tadaga tace" Alhaji yaya ake ciki? Idanun nata sun bude?
Hawayen farin ciki suka sake zubo mata tace "umma nice, Umma idona yabude, ina ganin komai, Ga Abba ma ina ganinsa da idona"
Ai cikin murna umma tafuto daga falonta tanufi dakin mama mariya tace "maman mus'ab idon Baby yabude" sai hawaye, nan danan umma tafara shashshekar kuka, duk abinda sukeyi Nawal tana jiyosu, itama anata bangaren hawaye take, Abba kuwa yazuba mata ido yana Kallanta wani irin farinciki yaana ratsashi
Shi kansa likitan dasukazo tare jiyake Kamar yayi kuka saboda tsabar farin ciki
Mama mariya tace "Aiyiriri 🤣jama'ar Gida Baby de tawarke"
Aifa lokaci daya suka kaure da ihun murna, har hakan ya janyo hankalin maqota, aka fara tambayar ba'asi
Najma Data futo daga wanka daga ita sai daurin Zani 🤣takarbe wayar tace "shegiya Baby ido kuma yabude, fadamin ya kikaga jirgi?"
Dukda tana kuka hakan bai hanata darawa ba tace "Najma taya zanga jirgi nida nataho a makance?"
Tace "ke wallahi namanta,😃 idan zaku dawo ki karbi wayar Abba kidauko mana photon cikin jirgin mugani"
"to Najma Zan dauko, ina wayata?"
Najma tace "tana nan naboye miki ita adaki,"
"to kisa min ita achrge, kuma kikira Nas kifada mata Dan Allah"
"to Zan fada mata, Ga yaya Sultan ma da yaya Salisu sun shigo"
Suma karbar wayar sukai kowa yana taya ta murna, daga nan sukai sallama da yaya Sultan akan idan sun dawo zaisa lokaci yadawo yaganta 🤔
Saida aka bawa kowa wayar yayi magana da ita sannan takashe wayar tana share hawaye, nanfa yan'uwanta kowa ita yake tayawa murna, gaskiya tayi sa'ar yan'uwa, kowa soyaiya yake nuna mata
Ta bawa Abba wayar shikuma yakira Malam yanayi masa bayanin komai, aka ba tashi suka gaisa yanata tsokanarta
Saida tagama waya da Malam tashare guntun hawayen idonta, cikin ranta tace "ita kuwa dame zata sakawa wannan mutumin? Bai santaba, babu wata alaqa tsakanin su amma har ya iya bata wannan gudunmawar, "MK" sunan yafado mata cikin qwaqwalwar ta, waye mk? Yaya zatai tasake ganinsa Taji muryar sa?wacce irin godia zata masa? Dame zata saka masa? Tunani tasake yi sannan taci gaba da zance cikin zuciyarta tabbas babu abinda zatayi masa ta nuna godiyarta agareshi face tayi masa tayin auren ta 😳🙆🏻
(aradu kin taro december Nawal 😱to inba mk sai baqa ba😂)
Ganin tana ta tunani tayi shiru yasa Abba yafara janta da fira harta sake tanada daria, daga qarshe ma ta tashi tana ganin tsarin dakin nasu, sannan tawuce toilet domin yin alwala
*** ***** ***
Kamar yanda doctor's suka fada hakace ta kasance, washe gari aka sallamesu dasafe
Saida suka gama had'a komai nasu sannan suka nemi ticket sukayo gida, Nawal kam tasha kallo, domin kuwa abinda bata ganiba atahowarsu yanzu ta ganshi
Sai bayan azahar suka sauka akano, gida kowa yanata murna, Salisu yaje yasiyo kaji guda uku akayi musu hadaddan abinci
Taxi suka tara ta kawosu Gida, yayinda shima Doc. Yawuce Gida, Tun kafin su futo daga cikin motar yan gidan suka mamaye jikin motar, tana futowa dukansu suka fara rungumeta saida suka kaita qasa🤣
Daga nan suka shiga Gida aka fara baje kolin fira, maqota sunata shigowa suna taya umma murna, Najma kuwa taqi tafiya nan da can hannunta yana cikin na Nawal, saida sukaci abinci sannan tafara bawa su nura da saif da Najma labarin abubuwan Data gani
Har dare suka kai sunata fira abin sha'awa
Da daddare suna kwance da umma adaki, Umma ta dubeta"Nikam baby abbanku yayi miki magana ne akan abinda yafaru? "
" A a ummah, baimin magana ba, tunde fad'an da Malam yamin a asbiti, amma shide baicemin komaiba "
Umma tasaki ajiyar zuciya" to Allah yarufa Asiri "
Fira sukaci gaba dayi sama samah daga nan bacci ya daukesu Ga kanta Gana mahaifiyarta
Washe gari Abba ya shirya tsaf, kasancewar ba ummah ce adakinsa ba mama mariya ce, Dan haka yaleqo dakin nata, anan yagansu suna bacci Kamar zata maida Nawal cikinta🤣
Murmushi yayi yafara kiran sunanta harta farka "cikin yanayin bacci tace Alhaji zaka fita ne?"
Yace "eh zanje asbiti likitan da mukai tafiyar nan dashi yace yanaso naje, sannan kuma nima dama inaso naje wajansa na tambayeshi number wannan bawan Allah daya temaka mana, inaso na kirashi nasake yimasa godia, inso samu nema saimu shirya nida Malam Muje har Gida muyiwa iyayen sa godia, saboda naduba jikin katin daya bamu babu number wayarsa ajiki
"
Tun lokacin dayayi maganar zuwa asbiti tafarka daga baccin datake, amma sai tayi shiru tana saurarensu 🤣tanajin maganar number waya tayi hamdala ciki ranta
Umma tace" to Alhaji saika dawo "
Abba yana fita kofar Gida yahadu da Nasrin tazo gidan itama, kasancewar yasan ta kuma yasan tsakanin ta da yaransa yasa ya tsaya suka gaisa sosai, harda tambayarta mutanan gida, sannan ta shige gidan, shikuma yayi asbiti
Yana zuwa asbiti likitan yace "Alhaji dama akan maganar sauran kudin ku ne, inaso kubani account number natura muku abinku"
Abba yace "to likita mungode, amma karaba mana, kaima ka dauki sauran"
"A a Alhaji, idan ban temaka mukuba ai bazan karbe muku ba, dama million goma yaturo, munyi amfani da million biyar da rabi, saura hudu da rabi "
"to likita Dan Allah ka dauki wani abu aciki, nima idan ka dauka din zanji dadi ai"
Yace "to shknn Alhaji, zan dauki Rabin, saina turo muku million hudun , nagode sosai, Allah yabar zumunci"
"amin likita, amma Dan Allah ina zamu samu number wannan yaron ? Inaso na kirashi naqara gode masa,"
"gaskiya Alhaji nide banida number sa, asali ma ni bansan shiba ranar nafara ganinsa, kasan number manyan mutane Kamarsu, wahalar samu take, mutum saiya rasa wajan wama zaije yanema, amma kajirani, zanje wajan director nasan bazai rasaba"
Abba yace "to alhmdlh, nagode sosai saika dawo"
Likita nafita bai dadeba yadawo da number arubuce a takarda, yabawa Abba tareda karbar account number din nasa, daga nan sukai sallama Abba yayo gida
Abba yana zuwa gida mama mariya takawo masa abin kari, yace taje takira masa Nawal
Mama mariya na futowa ta duba daki bata ganta ba, tajuya zata koma dakin abban taganta tashigo da hijabi a jikinta, tace "kekuma daga ina kike?"😏
"mama Nasrin naraka soro, babu Inda naje"
"to kije abbanku yana nemanki"
Dakin abban tanufa, a lokacin takardar tana hannunsa yana kokarin saka number aciki
Tashigo ta zauna agefensa, idonta kar akan takardar hannunsa😉
Tace "Abba gani"
Takardar ya ajiye agabansa sannan ya fuskanceta yace "babu Inda yake miki ciwo deko?"
Kanta aqasa tace "babu ko'ina Abba, lafiya kalau nake," magana take masa, amma gaba daya hankalin ta yana kan takardar dataga anrubuta number ajiki
Kasancewar layin nasu na manya ne number special ce nan da nan ta haddaceta akanta💃🏻
Abba yace "shikkenan zaki iya tafiya"
Kallansa tayi tace"abba harka karbo number mutumin ne? Naji umma tace zaka je kasamo number sa😱🤣
Yace "eh nasamo, gatama har nasaka acikin wayata, yaqarasa zancen yanayi mata nuni da takardar dake gabansa
Nan da nan fuskar ta tanuna farin cikin datake ciki, tace to Abba atashi lafiya, tamiqe tafice daga dakin
Bayanta yabi da kallo cikeda mamaki, cikin ransa yace ita kuma menene take tawani Fara'ah? 🤔🤔
Tana zuwa daki ta dauki wayarta tayi saving number aciki da sunan 'my Choice' (tab😳)
Dole ma tasa kati awayarta ta kirashi da daddare, sai Murmushi take ita kadai Kamar sabon kamu 😒
Najma ce tashigo dakin ta zauna agefenta tace"ke Baby kin dawoma amma kin wani liqe adaki Kamar Anwar din zai shigo Gida yakamaki? Haba yakamata ki futo tsakar Gida asha fira "
Ajiyar zuciya tayi ta dubi Najma, tace" ina nan ina tunanin za'bina "
Najma ta juya idanunta tace" zabinki? Waye kuma zabinki? Kode kin fara son Nuhu bansaniba? "
Lokaci daya tabata ranta tace" waye kuma Nuhu? Kinga ni MK nake nufi "
Kallanta tayi dakyau tace" Baby kinada hankali kuwa?kyautar million goma fa ba dubu goma bace, cikin yan siyasa ma bakowa ne zai dauki zunzurutun kudi har million goma yabaka ba, to banqiba gwamnoni haka, kinsan kuwa tunda yayi wannan kyautar ba qaramin mutum bane, shine zakice kina tunanin sa, nasan qarshan maganar dai shine kice kina sonsa, kinsan matansa nawa? Kinsan halinsa? Mutumin kirki ne kona tsiya? Sufa irin wannan manyan mutanan ba kasafai suke zama da mace guda d'ayaba "
Itama Kallanta tayi tace" Najma, kinata maganar wani kudi million million, ni waye yace miki Dan kudinsa nake sansa? Kawai nima haka naji ina sansa, sannan ni koda yanada wata matar hakan ba zai dameni ba tunda shi nakeso dole naso abinda yakeso, koda matansa uku ni Zan roqeshi ya aureni amatsayin ta hudu 😳🙆🏻
Najma tace "to wallahi bari kiji, Dan baki ganshi bane ranar daya biya miki kudin aikin idonki a asbiti, mutane ne suke take masa baya Kamar wani Dan siyasa, yasin wannan mutumin duk da banganshi ba ko a 'yar aikinsa ba zai daukeki ba Baby 🤣🤣
Nusaiba Muhammad
saqonki ya iso gareni, sau dayawa zakaga ana karanta littafi amma ba' asan ma'anar sunayen taurarin littafin ba, abinda sunan NAWAL yake nufi shine (kyauta) NAJMA kuma (tauraruwa) NAJMATY ( tauraruwata)
Naci karo da Comment din wani bawan Allah dayake tambayata wai Wacece Baby din da MK yakesan yasake gani? 🤔
Idan kana bibiyata daaga farko naayi bayani cewa yarinyar sunanta Nawal, kasancewar adakinsu babu mace sai maza shiyasa yayunta suke kiranta da Baby, Beauty kuma qawarta ce take fada mata hakan,shikam mk ai bai santa da Nawal ba, da Baby yaji ankirata, kaga kuwa aishi Baby zaice, Allah yasa Wanda basu ganeba sun fahimta yanzu
Banajin dadin yanda wasu basasan yin Comments bayan kuma sun krnta, inasan sharhi sosai
(yaya makomar alwashin da Nawal ta dauka akan mk?)
(shin waye mk?)
Mutara zuwa gobe insha Allah
Amnah El Yaqoub ✍🏻
[1/28, 11:26 AM] Amnahelyaqoob: 🌺NI DAKE...🌺
(Hot luv story)
Writing by Amnah El Yaqoub
*Gaskiya Babu abinda zance tsakanina da 'yan group din Khaleesat Haidar sai godia akan yanda suke zuba sharhi, ban taba tunanin book din zai samu karbuwa hakaba shiyasa na sadaukar da wannan shafi agareku* 💃🏻💃🏻💃🏻
13&14
To yanzu waya fadamiki su masu aikin basuda qima? Ai idan nasamu ya dauke ni aiki shikkenan zance yaqare yagama sona, Kamar baki karanta labarin shalelan baba ba? "
Najma tace" kada kiyi kuskuren hada Rayuwar novel da Rayuwar ki Baby, marubuta suna saka abubuwan da bazai taba faruwaba agaske acikin novel,misali :ya rungumota, yakama hannun ta, yayi kissing dinta wannan duk tatsuniyace, kawai maggi ne suke qarawa miyar littafin su Dan yayi dadi, amma agaske cikin al'ummar hausawa yarinya Mai tarbiya ai bazata taba yarda hakan tafaru a gareta ba
Sannan itama shalelan da tayi aikin aka sota aiba haka kawai yaso taba, da temakon yar'uwarsa, ke kuwafa? Wakika sani nasa dazai soki harya temaka miki kisamu shi mk yasoki? Kamar fa kiwayi gari ne kice ke Mai kamfanin mtn kikeso, Dan Allah Baby awacce duniyar zaki sameshi? 😂🤔Saiki hadu dashi ahanya ma yawuce kiwuce bakisan shine ba, nide shawara ta agareki kicire wannan al'amarin daga cikin zuciyarki, wahala kawai zakisha "
Budar bakin Nawal sai tace" ai dama ita soyaiyar gaskiya sai ansha wahala ake samunta, 🤔kawai Najma kifadi alkhaairi ko ki shiru "
Miqewa tayi tace" nayi shiru, kisha tunani lafiya Baby "daga haka tafice daga d'akin
*** ***** ***
Har zuwa yamma tana d'aki tana tunanin mafita, ta saqa wannan ta kunce wancen nazari tayi akan kalaman Najma, kuma fa aduk cikin maganganunta babu na yarwa🤔gaskiya ce abaiyane, yanzu idan nemansa zata fara ta wacce hanya zata bi? Hanyar farko de itace number sa kuma tasamu, hanya ta biyu kuwa itace nemansa, ta ganshi yaganta, Dan haka dole zata nemi shawarar Nas, tasan cewa bazata bata shawarar banza ba
Umma ce ta leqo cikin dakin tace "kije Nuhu yazo inji Saif,"tareda juyawa
Wani haushi ne yakamata, ace za'azo wajan ka amma akasa sanar dakai? Ai aqalla ko awaya ne akiraka aji kana Gida ko bakanan, kanada lokaci ko bakada shi? Amma kawai shi kullum babu tunani babu komai saide ya wanke qafa yazo 🤦🏻♀yanzu Inda girki take haka zata katse kenan taje wajansa
Tsaki tasaki tadauki dogon hijabinta tasaka tafice daga dakin
Umma tana zaune afalo ta kalleta "ahaka zaki fita idanunki fari qal ko kwalli babu?"
Murya ciki-ciki tace "umma bansan zaizo ba, bai fadamin ba shiyasa ban shirya ba, kuma likita ma ya hanani saka kwalli (🙆🏻🙊😳kai)
" ke kika sani, idan bakya sansa meyahana kifada masa gaskiya Tun tuni, Tun magana bataje ko'inaba "
Itade batace komaiba tafice, ta iskeshi a kofar gidansu azaune akan wani banci, tasan aikinsu Saif ne wannan, a tsaye ta tsaya masa aka tareda sallama 🤣
Ya amsa mata cikin sakin fuska," My heart Rabin raina ya hanya? "
Tace" lafiya "😖
" to Alhmdlh ido kuma sun bude Allah yaqara kiyayewa gaba, "
" amin ya Allah, wai Dan Allah Nuhu na tambayeka "
" inajin ki malama Nawal "
Tace" meyasa kake sona ne? "
Murmushi yayi ya gyara zama" abu na farko shine kinada kyau, zaki dinga haifamin yara masu kyau kamarki, amma nafiso suyi kamarki kawai, jikin kuma saisu iyo nawa, kinga Ga kyau Ga tsawo kuma Ga qiba 😳😱, kuma masha Allah kinga nidin dama gentleman ne, saikiga ana layi a kofar gidana"🤣
Cikin takaici tace" Nuhu saikace samudawa? 😂😃Kasan tsawonka kuwa? Tsawo ne dakai Kamar daran mutuwa, ahakan za'ayi layi a kofar gidanka?
Dariyar yaqe yayi, shi yana ganinsa da tsawo gad'an haskensa amma shine take masa haka
Yace "to ai inde sunyi kyanki to banida damuwa, sai abu na biyu shine tarbiya, kinada tarbiya, Ga kuma uwa