Showing 39001 words to 42000 words out of 72369 words
Chapter 14 - Ni Da Ke Book Complete Document by Amnah El Yaqoub --.txt
jikinsa ta runtse idonta, gashi batada karfin hanawa
Tanajinsa yaja blanket din datake ciki shima yashige ciki, tareda mannata a Kirjinsa, Ahankali tafara kwace jikinta, amma haka yasa hannu yadawo da ita cikin jikinsa yarungumeta sosai, dumin da yaji a jikinta yasa yaqara matseta ajikinsa
Kansa yadora a wuyanta yana goga mata jikinsa ako'ina na jikinta
Hawaye ne yake silalowa daga idonta, babu damar qwacewa, body contact aka samu sosai atsakaninsu
Saiji yayi tayi shiru alamar bacci ya dauketa, memakon yasaketa saiya sake maida ta cikin jikinsa tareda lumshe idonsa
Tunaninsa ne yake neman barin jikinsa, Ahankali yatashi idonsa yayi jajir
Yafice daga dakin
Daakinsa ya koma yazauna yadafe kansa, yayi tunanin idan yasakejinsa acikin wannan yanayin zaiji sauqin abinda yakeji, ashe ba haka bane wata masifar zai sake ballowa kansa
Shide ba mazinaci bane, bazai so ya aikata yanzu dayake da aure ba, Dan haka dole zaiyi tunanin mafita, dole zai nemawa kansa mafita akan neman Baby, yazama dole yafara neman yarinyar ta kowacce hanya
Daga haka yatashi yashige toilet
Zuwa yamma jikinta ya warware, tana jiyo motsinsa afalo taqi fita, toda wanne ido zata kalleshi? Bayan yanda taganshi dazu Babu maraba da rashin kaya, wannan gajeren wandon Babu abinda baya nunawa, amma kuma ya akai taji jikinta da Dan sauqi? Bade wannan abin daya mata ne yasa hakaba? Tunani tafara inama ace daga wajan mk ne tasamu hakan? Da Babu abinda zai hana ta sallama masa komai, istighfari tayi tareda lumshe idonta takoma cikin bargo
*** ***** ***
Ummi ta kirashi awaya ta sanar dashi cewa zataje saudia umara, tanaso sutafi da Nawal
Haka kawai yaji aransa cewa bayaso yarinyar tayi nesa dashi, Dan haka yace wa Ummi ba zataje ba
Ummi tace yayi hakuri sati biyu zasuyi kawai, shima saiya tafi Dubai idan sun dawo saiya dawo
Badan ransa yasoba ya amince, cikin satin yatafi, suma kuma asatin suka tafi umara
Tunda suka je datage da addu'ah akan Allah ya nuna mata mk koda a tv ne sau daya arayuwarta, sannan tayi addu'ah akan Allah ya cire mata sonsa daga cikon zuciyar ta, saboda tasamu dama da qwarin gwiwar yiwa mijinta biyyaiya
Daga qarshe tayiwa Baffah addu'ah akan Allah ya shiryeshi idan mai shiryuwa ne 🙊🤣🤣😂
Amma Ummi kam maqasudin zuwan nata da Nawal shine akan tayiwa Baffah addu'ah Allah ya shiryeshi, domin kuwa ita addu'ar mata akan mijinta, batada hijabi awajan ubangiji
Sunyi siyaiya sosai, Ummi ta kashe mata kudi baana wasaba, duk wani kayan ado na yanmata tasiya mata
Har suka dawo Nigeria lafiya, takira su ummah ta dinga basu labari, Inda tace ta ajiye musu tsarabar su duk lokacin dazasuzo da Baffah zata kawo musu 🤣
Kwananta biyu da dawowa amma Baffah bai dawoba
Tunani tafara, ko yaushe ne zaman aurensu zai daidai ta? Gaskya yakamata tafara kawowa gidan nan nasu gyara
Tsamm tamiqe tashige cikin d'akinsa, komai neat Babu wani datti, dakin ya birgeta, haka kuma Babu abinda Babu sirkin baqi aciki
Afili ta furta "wannan mutumin yana son abu baqi da alama"
Bedside drower tajawo taga wata hadaddiyar akwati aciki
Jikin akwatin kadai ma antsarashi sosai, ciki sauri ta bude taga wasuma zobuna guda biyu na azurfa,qarami da Babba, irinsu daya sak, anyi musu ado da Baqin stones, acikin stones din anyi harafin 'B' da farin kala
Kalla tayi tasake kallah, B da B tome yake nufi? Shide nasa B din tasan cewa Baffah take nufi to amma dayar fa? Wata zuciyar tace da ita Budurwarsa yake nufi mana, wadda yake kuka akanta, yake kiran mutum takanas azana masa ita
Baqin ciki yakamata, duk hakuri da biyaiyar datake baya gani shi watama yake yiwa hidima, zoben hannun ta takalla, ita kuwa saida Ummi tasashi yasiya mata
Rufewa tayi tamayar masa tafice daga dakin zuwa falon, tadauki waya takira Nas
"Nas yakike ya garin?"
"lafiya Beauty, yagida yame gida?"
Adede lokacin yashigo cikin falon, dawowar sa kenan daga Dubai
Itama sarai taganshi, taci gaba da waya Nasrin tace"qawata maigida bayanan yatafi cirani "🤣🤣
Harya wuce yajuyo ya kalleta, shine yake tafiya cirani?
Shareta yayi yashige daki, itama bayan sa tabi da kallo ranta na quna idan tatuna da zobunaan data gani
Tashi tayi tashige cikin daki tace" Nas kiban shawara, inaso nakawo qarshan matsalar gidan nan "
Nas tace" to yanzu kuwa Zan baki shawara, menene yake miki Wanda bakyaso?"
" Nas bayacin abinci na, babu magana Mai dad'i, kullum acikin aikin doka nake, karfe bakwai dede nafita nafara aiki, sannan kayanda Ummi takeso yadena sawa ta zubamin ido tana jira taga result amma har yanzu nagagara yin komai"
"Beauty maganar gaskiya itace kinada tsoro, kuma dole saikin dena jin tsoron sa sannan ne zaki gyara gidanki"
Tace "Nas haka Ummi ma tace"
"ato kingani, dole saikin dena tsoron sa, sannan tunda kinyi biyyaiya ai kin fita haqqinsa, tunda haka yakeso kema ki zama mahaukaciya, zaku fi dedetawa"
Nawal tace"a a fa Nas, Karki bani shawarar dazanzo ina kuka daga baya, kinga shawarar zuwa Abuja ga yanda ta qare mana 🤣🤣sannan shawarar zuwa makaranta haka kikasa nazo qarshe nahadu da Ummi nanma Abba yahauni da fada🤣🤣🤣"
Nas tace" Karki damu, ki gwada wallahi "
Daga nan sukai sallama
Tana kashe waya tace" goben wasan zai fara
Washe gari ta dinga jira yafita, bai fitaba, sai yamma yafita, yaje gidan Ummi
Tana ganin fitarsa tashige cikin d'akinsa, kayansa qananu Wanda suke crazy da riguna Wanda taganta da yaga ko kadan ce, tadinga debowa tana zubasu akan gado😳😳
Saida ta kwashe duk kayansa crezy sannan taje harabar gidan ta zubasu waje daya
Kitchen takoma tadauka fetir 🙆🏻😳
tadaga bakin jarkar ta kwara musu😳😳🙆🏻
Sannan ta qyasta ashana ta banka musu wuta
Nan da nan wuta takama kaya taanaci
Adede lokacin yadanno hancin motarsa cikin gidan yaga hayaqi yana tashi, ga Nawal a tsaye a gefe
cikin sauri yabude motar yafuto yaqaraso wajan
Kayansa yagani yanaci da wuta 😳yace"kai kai kai kayana kika qonamin? "
Tace" to menene amfanin su? Banaso naga kana sakawa, sannan amatsayina na matarka, inada haqqin hanaka sakawa "
" nikike na fadawa wannan maaganr saboda rashin kunya? Kewai mekike taqama dashi ne? Bafa sanki nakeba inada wadda nakeso, bazakizo har gidana ki nemi ki dagamin hankali ba"
Dama ga haushin wannan zobunan daga gani adakinsa yana cin ranta, cikin bacin rai tace"to ni din cemaka akai inasonka?inada Wanda nake sosai nima mutum Mai tausayi da hangen nesa "
" Karki sake ambatar sunan wani a cikin gidannan, sannan abu na qarshe, yafara tafa hannunsa yace"nagaji da halin ki, ki tattara kayanki kitafi gida, saina nemeki "
Maganarsa tabata tsoro, amma data tuni shawarar Ummi data Nas saita dake tace" wallahi Babu Inda zanje, "
" Ok haka kikace? "
Ta kalleshi tace" qwarai kuwa BAFFAH haka nace "
Yace" nikike kira da Baffah,? "ya iyo kanta gadan gadan
Tana ganin haka ta kwasa aguje, shima yadoru a bayanta
Kasancewar da hijabi a jikinta sai hijabin yake ta tashin iska🤣🤣
🙆🏻😱Ko'a'ina wannan gudu zai tsaya?
Wani lokacin zakuna ganin posting kadan, saboda mkrnt danake zuwa, wataran kuma zaku iya jina shiru, amma insha Allah zanyi kokari naga ina turo muku ko yaya ne
pls sharhi Dan Allah 🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻
Mrs Usman ce ✍🏻
[2/4, 10:18 PM] Amnahelyaqoob: 🌺NI DAKE🌺
(Hot luv story)
Writing by Amnah El Yaqoub
Dedicated to Itz sadeek
29&30
Cak yatsaya daga gudun dayake tareda juyawa gida, yana haki yana cewa saide ki nemi wani gidan amma ba nanba
Ita kuwa tsabar tsorata ko Juyowa batayi taga yana binta ko baya binta
Saiji tayi tayi karo da Mota, Allah yarufa Asiri motar bata gudu,shiyasa bataji ciwoba, sai haki take, takasa daidaita numfashinta, Dasauri tafuto daga cikin motar cikin mamaki ta kalleta"Nawal, keda waye kike gudu haka Kamar kinyi gamo? "🤣
Dago kanta tayi Dasauri jin muryar Ummi
Cikin haki tace" Ummi mutafi gida, zai dakeni "
Ummi tasa hannu ta dagota tace" Babu abinda zai miki, tashi mukoma gidan "
Bayanta takoma tabuya Kamar yana wajan tace" A a Ummi, mutafi gida Dan Allah "
Ummi de cikeda mamaki tajata tasata amota, suka juya zuwa gidan Ummin
*** ***** ***
Yana dawo wa gidan yasa dayyabu ya gyara wajan data bata, sannan yawuce d'akinsa tareda dafe kansa da hannunsa duka biyu, duk Ummi ce ta janyo masa wannan rainin awajan yarinyar nan, amma banda haka kisa hannu ki dauki sutura ki qona? Wardrob dinsa yaduba yaga Babu komai takwashe qananun kayan sai manya 😭wani kayanma rabonsa daya waiwaicesu ya Manta
Yasan bazata wuce gidan Ummi ba, Dan haka bazai damuba
Dole yatashi ya nemawa kansa mafita, wannan zaman Babu Inda zai kaishi, yanada abubuwa dayawa dasuka tsaya masa arai, kuma yarasa dawa zai tattaunasu, yakamata ya nemi wani mutumin Mai ilmi sosai
daga nan yatashi yayi masallaci domin sallar magrib
*** ***** ***
Zaune suke afalo, Ummi nakan kujera Nawal na zaune aqasanta
Ummi ta kalleta "Nawal ki fadamin gaskiya, menene yahadaki dashi har kike wannan gudun?"
"Ummi nice nayi masa laifi, kayansa na qone masa, saboda banaso yana yawo acikin kayan, kuma banida qwarin gwiwar dazan iya hanashi, shiyasa nayi tunanin qonesu"tana qarasa fadar haka hawaye suka zubo mata
Ummi tace" to menene abin kukan kuma? Ko akwai wani abu bayan haka?"
" Ummi cewa yayi natafi gida saiya nemeni "
Ummi tayi tagumi tama kasa magana 😱, Kallanta tasake yi tace" Nawal Baffah yataba biya miki haqqinki na aure? "
Tambayar tayi mutuqar yimata nauyi, cikin sauri ta sunkuyarda kanta qasa
Nan take Ummi ta gane Babu abinda yafaru, sannan tace" Nawal ina wayonki yake?keda kike yar zamani, keya kamata kiyiwa mijin ki shiga Mai kyau ta daukan hankali harki jawo hankalinsa gareki, aishi ba dutse bane, dakinja hankalin sa cikin Ruwan sanyi zaki bashi umarni yabi, ciki harda hanashi saka kayan, ni kaina banaso yadinga wannan shigar Nawal, abin yana mutuqar damuna, yan'uwan mu dasuke yola dayawa daga cikin su gani suke zuba masa ido nayi kawai naqyaleshi, namiji Kamar yaro ne awajan matarsa Nawal, keda kanki zaki iya sarrafa abinki ayayinda yashigo hannun ki, to amma Babu damuwa, zanyi maganin abun, zansa sabira taje tadauko min wayarki, sannan kishiga daki Karki kuskura naqara ganin koda kafarki ne afalo, zansa agyara miki wani dakin kikoma can gaba daya, kada kifuto harsai nabaki umarni "
Cikin nutsuwa tace" to Ummi, mungode "🤣🤣
Sannan tatashi tashige dakin ummin
*** ***** ***
Yana zuwa gidan, Ummi taganshi fuska atamke, da alama akusa yake
Tea takesha yayinda take aiki a computer, yana zuwa yafada kan kujera tareda dora kansa akan cinyarta
Fuskarta Babu alamun Fara'ah tace"ina cinyar taka matar"
Kallanta yayi "yanzu Ummi laifi ne danna Dan kwanta?"
"Babba ma kuwa, kakoma wajan matarka, inkuma ciki kakesan komawa to 🤣"
Ahankali yatashi yafara leqe leqe ko zaiga Nawal, ta kalleshi, sarai tasan ita yake nema, sai tace masa "yaya Nawal din take?"
Cikin ransa yace tofa 😳kenan batazo nanba?
Sumar kansa ya shafa yace"tana nan lafiya Ummi "
Kamar an tsikareshi yatashi yace" Ummi bari inje masallaci, saida safe"
Tace"toshikkenan ka gaishe ta, saida safenku "
Yana fita yatsaya ahabar gidan, to ina yarinyar nan tatafi? Karfa ace gidan tatafi, to amma tayaya zatayi gangancin hawa motar haya bayan da aurensa akanta? 🤔
(waannn aure😂)
Direct masallaci yaje yayi sallar isha'i, bayan an idar bai tashiba, saida yabari kowa yafice daga masallacin sannan ya qarasa wajan limamin suka gaisa, liman yace"muhammadu mungode sosai da kokari, ana yawan aiko mana da sadaka, mungode sosai, Allah yajiqan mahaifa
Cikin yanayi na damuwa yace"amin Malam, dama akwai abinda yake tafe Dani "
Liman yace" to inajin ka muhammadu "
" Wato Malam, wasu 'yan watanni dasuka wuce naje ta'aziyya kano, saina hadu da wata yarinya, tundaga lokacin nake mafarkin ta, kuma Allah da ikonsa banga fuskar ita wannan yarinyar ba, saide wani sashi na fuskarta,naji wasu yara daga bayanta sun kirata da Baby, wallahi Malam ina cikin halin damuwa, ina buqatar kyakykyawar shawara, saboda yarinyar tana yawan zuwamin cikin mafarki
Kwatsam rana daya sai mahaifiyata tahadani aure da wata, bana sonta, itama yarinyar bata sona, to tunda akai auren, Allah yasaakamin kishinta acikin raina, ina mutuqar kishinta, bansan dalili ba, yanzu hakama de maganar danake ma mun samu sabani da ita nace taje gida saina nemeta "
Liman yace" subhanallah, subhanallah, muhammadu akwai matsaloli Wanda dole kaine zaka gyara su da kanka, na farko muhammadu ba'a taba samun kishi saida soyaiya, muhammadu Allah yasaka maka qaunar matarka acikin ranka batare daka shirya ba, kana sonta, yakamata kajata ajikinka ka koya mata yanda itama zata soka, idan ka kwantar da hankalin ka ka rungumi abinda mahaifiyarka tamaka Zabi dashi sai kaga ta Sanadin haka Allah yabaiyana ma ita waccen yarinyar dakake mafarki, sannan kai namiji ne kanada damar dazaka iya auren mace hudu, bare guda biyu, saboda haka ka tsananta bincike akan yarinyar harka sameta, kahada su su biyu, zakafi samun nutsuwa acikin zuciyrka, kuma muma anan zamu dage dayima wasu 'yan addu'o'in "
Yace" Wato Malam, ba auren ne matsala ba, matsalar shine adalci, bazan iya musu adalci ba, ni kaina nasan cewa bazan iyaba, idan nace zanyi to haqiqa na yaudari kaina "
Murmushi liman yayi yace" karka damu, wanaan duk wani abu ne dayake hannun Allah, insha Allah ubangiji yana sane dakai, idan kayi addu'ah zai duba lamarin"
Shiru yayi, jikinsa yayi mutuqar sanyi, yace"to Malam nagode "
Liman yace" Babu komai muhammadu, ai Zan iya yima komai karka damu "
Daga nan yafuto daga masallacin jikinsa a mutuqar sanyaye
Direct gidansa yawuce, afalo ya zauna yadafe kansa da hannunsa🤦🏻♂ tareda lumshe ido, afili ya furta" tayaya? Iname hakan tafaru Dani? Me zance da Baby idan naganta? Tayaya zanso wannan yarinyar bayan nariga dana mallaka wa Baby zuciyata da gangar jikina?
Fillon dake gefensa na kujera ya dauka yayi jifa dashi, da karfi yadaga murya yace "Baby!!!!"
🤣🤣🤣
Gaskiya dole nanemawa kaina mafita, wayarsa ya dauka yakira Yasir
"hello Yas"
"na'am mk yahutu"
"to alhmdlh za'ace" 🤣
Yasir yace"aikin daka turonifa yadade da qarewa, dama inaso kasamin lokaci nazo akwai maganganun danake so mu tattauna akai"
Yace"Ok Babu damuwa, but kafin nan inaso ka bincika min wata yarinya agaba da layinku take"
Yas yace"yarinya kuma mk? Yaushe kayi aure? Sannan....
Cikin sauri yace "Yas" ya Dakatar dashi
Sannan yaci gaba da cewa "sunanta BABY, yarinya ce qarama, tana saka wannan Baqin abun a fuskarta, inaso ka tattaromin baya nanta cikin one week"
Yana gama magana yakashe wayar, sannan yafara tunanin ina ita kuma wannan yarinyar tayi?
My fan's kuyi manage da wannan, da ace Babu posting aganina gara asamu ko kadanne💃🏻
Dan Allah masu labe kufuto kuyi sharhi pls 🙏🏻
Amnah El Yaqoub ✍🏻
[2/6, 10:44 PM] Amnahelyaqoob: 🌺NI DAKE🌺
(Hot luv story)
Writing by Amnah El Yaqoub
Dedicated to Itz sadeek
31&32
Yaci gaba da tunanin
To yanzu idan bataje gidan Ummi ba gidan uwar wa zata tafi?
To kode gidan tatafi da gaske? 😳, gata yarinya ce shi yaro baya qarya tsaf zataje ta zayyanewa iyayen ta komai tace yace saiya nemeta, sukuma su zagi Ummi suce Tun aure baije ko'inaba har ansamu matsala 😂
Shikuma Ummi tasakoshi agaba 😱
To yaya zaiyi tunda liman yace yakamu dason matarsa 😒dole hakuri zaiyi ya rungumi qaddara, inyaso saiya hadata da Babyn, amma ba haka yasoba, domin kuwa bai tsarawa kansa cewa zai hada Babynsa da wataba
Tsam yatashi ya yi daki ya kwanta, yana tunanin yanda zai shawo kan lamarin zuwa gobe
*** ***** ***
Washe gari dasafe tsaf ya shirya cikin qananun kaya, riga green wadda ta kamashi saiya dora milk din suit asama, saikuma wando jeans
Kai tsaye gidan Ummi yanufa, a lokacin tana zaune afalo tana break fast ita kadai
Kusa da ita yaje ya zauna jikinsa yana gogar nata, Yace"Ummi walijam "(ina kwana)
Ahankali ta ajiye cup din dake hannunta, tashafa kansa tace" sejam kalau Baffah nah, where is your wife? "
Gabansa ne yafadi, kansa yasara, da gasken de bata nan din kenan, hannunsa yasa yadafe kansa🤦🏻♂yace" Ummi wai yarinyar nan batazo nan gidan ba kenan? "
Yi tayi Kamar batasan komai ba tace" tacema zatazo ne? "
" no bata fadamin ba, Ummi yarinyar ce batajin magana wallahi, laifi tayimin shine nace tatafi gida saina nemeta "
Ummi tace" ikon Allah, to kaga kenan kai da kanka kabawa kanka amsa, tunda cewa kayi tatafi gida, may be tatafi gidan ne, "
Cikin shagwaba yace" to Ummi meyasa ba zatazo nanba saita kama hanya taje ta shiga wata motar tana hada jikinta dana wani"
"ikon Allah, Baffah nanfa ba gidansu bane, tayaya miji zai sallami yarinya ita kuma takama hanya tatafi gidansu?"
"to Ummi ba 'yarki ceba, zata iya zuwa mana"
Ummi tace"to batazo ba, da menene yahadaku har abin yakai haka? "🤣
" Ummi yarinyar nan takama kayana ta qonesu duka, batasan kudin dana kashe akan kayanba, takama ta babbakesu, 😂sannan naayi mata magana waini yarinyar nan zata kalli tsabar idona tace Dani BAFFAH "
" to menene aciki danta qona kayan? Ka fadamin sau nawa ina karbe irin wannan kayan awajan ka amma kabada oder wasu? Kaga yanzu ma kanada right din dazaka sake wasu, may be tunanin ta bazai iya daukar ganin mijinta kullum yana yawo ana kalle mata jikinsa ba, shiyasa ta qona 🤣
Sannan yarinyar nan tunda akai aure baka zaunar da ita kafada mata cewa bakasan a kiraka da Baffah ba, kamata yayi Tun farko kafada mata cewa ni sunana Muhammad, Ummi na tana kirana da Baffah, amma gayu yasa namaida sunana zuwa MK
Saboda haaka kaga ni anan ma banga laifin yarinya ba, Dan tace Baffah, koda cewa tayi me sunan baban Ummi, 🤣🤣ba zanga laifin ta ba
Baffah ka kiyayi kanka da Rayuwar nan, ada de nasanka da tausayi amma zuwa yanzu nasan cewa d'ana ya sauya, ya koma marar tausayi, Baffah ina sane da cewa Babu abinda yashiga tsakanin ka da yarinyar nan na auratayya, idan kai bakada lafiya ita yarinyar haka take?
Shiru yayi Kamar ruwa ya shanyeshi 🤣
Kuna zaune gida daya bazaka saukewa yarinya haqqinta ba? To yanzu ai shikkenan komai yazo qarshe, tunda ka sallameta zuwa gida kaga ai saitaji dadin auren wani, tunda batada iddar kowa akanta, yamaka kyau "
Ahankali yace" Ummi kiyi hakuri, nima bayin kaina bane, amma insha Allah zangyara, za'a bata haqqinta "🙊🙈😳
Tace" zancen yaushe kuma?ai magana ta qare "
" kiyi hakuri Ummi, yanzu ni zanje saudia, akwai binciken danasa yasir yayi min, inaso nayi addu'ah akan Allah yasa adace, ita kuma nasan zata dawo ai"
Ummi ta kalleshi galala 🤣🤣sannan tace"shi aikin har yakai ka tsaya ka nemi matarka muhinmanci? "
" Ummi nace miki zata dawo "
Tace" to shikkenan, tunda batada zuciya Allah yadawo da ita lafiya "😂😂
Shima Babu kunya yace " Amin " 🤣🤣
Sannan yaja abincin datakeci Gabansa shima yaci kadan,