Showing 33001 words to 36000 words out of 72369 words

Chapter 12 - Ni Da Ke Book Complete Document by Amnah El Yaqoub --.txt

28 Dec 2024

8922

karatun tana koya mata littafin ishmawi babin dayake magana akan abubuwan dasuke warware alwala


Har wajan karfe biyar suna karatun su, wata mata tayi sallama tashigo, Ummi tace"a a Hajiya Karima mutanan cairo, ashe kindawo? "


Qarasowa tayi cikin falon ta zauna akan kujera tareda cewa, Hajiya Halima wallahi nadawo jiya, kawai wai saiji nayi Muhammad yayi aure"


Ummi tace "wallahi Baffah yayi aure hajiya"


Nawal ce ta gaida matar tareda shigewa kitchen domin kawo mata ruwa


Matar ta dubi Ummi tace" Hajiya Halima ina kika samo 'yar kyakykyawar yarinya haka? "


Murmushi Ummi tayi tace"laa matar Baffah ce"


Tace "kai amma yaron namu yayi sa'ar mace, gaskiya Baffah yasamu mace"


Cikin jin dadi Ummi tace "wallahi"


Nawal tadawo takawo wa matar ruwa da lemo, tace "gashi"tareda juyawa daki


Tace"to nagode amarya"


Bayan tasha Ruwan ta kalli Ummi tace "Ziyara tazo miki ne?"


"A a Hajiya, anan suke, tare nake zaune dasu saboda kinsan halin Dan naki, auren ba sonsa yakeba, shiyasa kawai nabarsu agidana"


"ai hajiya Halima inde kinsan basason junansu, toki tarkatasu sukoma gidansu, suje suyi fad'a awajan shara suyi fad'a awajan wanke wanke, ke sujiwa kansu ciwoma suyi 50 50 zasu so junansu, amma ahaka kam, hajiya bana tunanin zasu samu daidaito"


Ummi tayi jimm tace"kuma fa hakane hajiya, kinyi gaskiya, to kawai abinda yafi shine akwai wani gida anan kusa, kawai gobe Zan tarkatasu sukoma can, tunda nan din ina tareda sabira, yanzu fa ko magana ba sayi, tunda akai auren basu zauna sunyi magana ba, ina hankalce dasu "


Hajiya tace" yawwa kinga abinda nake fada miki ko, amma idan gidansu daya, dole wani abu zai tashi dazaisa suyiwa junansu magana, amma ahaka kam, akwai gyara "


Ummi tace" wannan gaskiya, ai kuwa gobe zasu tafiπŸ˜‚"


Daga nan sukaci gaba da firarsu




*** ***** ***


Zuwa dare kam Nawal tasake da Ummi, dad'i da qari ma idan tatuna Baffah yafita saitaji wani sanyi, haka ta ware sunata fira sosai, har Ummi tana mamakinta


Sai wajan goma da rabi yashigo gida,bema lura da Nawal dake kusa da Ummi ba yafad'a cikin kujera cikin sigar shagwaba yace"Ummi wallahi nagaji dayawa yau "


Dadi Nawal taji,maganar tasa tana mata yanayi Data mk, cikin sauri tayi istighfari, domin tuno da cewa yanxu tanada aure


Ummi takalleshi" Baffah sarkin shagwaba, to ai yanzu bani zakayi wa ba, "ta nuna masa Nawal, kaga wadda zakacigaba dayiwa shagwaba"


Gaba daya yamanta da yarinyar, jin antuno masa da ita yasa nan da nan annurin fuskarsa ya dauke 😠
Ummi tana gani, tasake tabbatar da maganar qawarta, bata sake yimasa magana ba, tadubi Nawal tace "tashi kikawowa mijinki abinci"


Cikin nutsuwa tatashi tayi hanyar kitchen,by mistek yad'ago idonsa, bai tsaya ko'inaba sai a tudun hips dinta, nan take yakawar dakai yasaki tsaki, wannan yarinyar har tasan tasaka irin abinda turawa suke sakawa na cikon hips


Ummi dataji yana tsaki tace"kode yunwar ce Baffah? "


Batare daya kalletaba yace" A a "


Tasake cewa" Baffah Nawal fa tana zuwa makaranta, shine nace mezai hana itama kamaidata, tunda kaima wajan aiki kake zuwa, kaga ba dadi ta zauna ita kadai agida "


" Ummi ni yanzu banda time, amma zanyi magana sai akaita, a JSS nawa za'a sata? πŸ€”πŸ™†πŸ»πŸ˜‚


"Baffah jss kuma? Yarinyar datake university?"


"ki qyaleta"


Tace "aqyaleta haka ta zauna Babu makaranta?"


Babu kunya yasake cewa "eh"


Ummi bata sake yimasa magana ba, Nawal takawo masa abincin, ta ajiye masa batare datace komaiba
Shima baice da ita uffan ba, Ummi duk tana kallansu, anan tasake tabbatar wa gara tamaidasu wani gidan su kadai
Ko 5 spoon baiyiba ya ajiye yatashi yace "Ummi gudnight"


Tace "to Baffah saida safe"


Baifi minti talatin datafiyaba, Ummi tasata tayi wanka, tabata humra Mai qamshi tashafa, sannan tasaka kaya madaidaici, dede bacci, takama hannun ta sukayi part dinsa
Saida suka je har falo sannan ta nuna mata d'akinsa tace "ga dakin naku can, 🀣kije ki kwanta saida safe


Jikinta ne yayi sanyi, haka tafara tafiya salalo salalo, har taje bakin kofar dakin tajuyo taga Ummi tana tsaye, Ahankali ta tura kofar dakin tashiga, Ummi kuwa tana ganin shigarta dakin tajuya part dinta ranta fess


Tana shiga dakin taga duhu ya gauraye, gashi ya qure esi bayan sanyin da ake na duniya,maida kofar tayi tarufe, duk abinda ake yana jinta domin kuwa ba bacci yakeba, Tun daren shekaran jiya rabonsa da bacci Mai dad'i daya fara zai farka


"ke me yakawo ki cikin dakina?" ta tsinci maganar sa


Tsorone yakamata, cikin sanyin jiki tace "Ummi ce takawoni"


"kijuya kificemin daga daki"


Zuwa yanzu kam muryarta tafara rawa tace"dan Allah kayi hakuri, "


Tashi yayi zaune, yakunna wutar dakin, haske ya wanzu adakin taganshi muraran Babu kaya da gashi sai gajeren wando, murdaddan jikinsa takalla, ga qirjinsa duk gashi tayi saurin kawar da idonta


Cikin bacin rai yace" zaki fice ko saina taso? "


Hawaye suka zubo mata tace" to ina zanje? "


" kifice kibarmin dakina, ke bayan d'akinama kifice daga part dinnan Gaba daya "


Tsugunnawa tayi awajan, tafara rusa kuka," wayyo Allah na yaya Sultan nashiga uku kazo ka ceceni"


( Sultan ga ranarkaπŸ˜ƒπŸ€£)


Baqin ciki da taqaici suka kamashi, saikace Wanda yadaketa take kira masa wani qato yazo ya ceceta yace"ke bari kiji, ba Sultan ba,ko Sarki zaki kira saikin barmin dakina " ya yunqura zai sakko daga gadon, tana ganin haka tatashi tana goge hawaye tafice daga dakin tareda jawo masa kofarsa


Yace" fine"tareda kashe wutar dakin ya kwanta


Tana zuwa falo tayi kwanciyar ta akan kujera, saide daqyar baccin ya dauketa saboda tsoro, tasaba kullum gata ga ummanta take bacci


Ana kiran sallar asuba tafice daga part din tatafi dakin Ummi, a lokacin Ummi tana kan sallaya kawai sai ganin Nawal tayi, tace "Nawal yanaganki Tun yanzu? Lafiya kuwa?"


"Ummi lafiya kalau, yatafi masallaci ne, shine nataho nan"


Ummi tayi Murmushi tareda girgiza kanta kawai


Gari nayin haske bayan sunyi break Ummi ta kalleshi tace "Baffah jeka hado kayanka zaku komai gidanku"


Cikin sauri Nawal ta kalleta


Shima cikin mamaki yace "Ummi gida kuma? Menene laifin nan din?"


"to idan kagama Tambayar tawa bari ni naje nadeboma kayan naaka, tunda ban isa nafadama ba"


Miqewa yayi batare dayayi magana ba, daga hado kaya yaje ya zauna har Ummi tafara tunanin binsa sannan yashigo falon dauke da troly guda daya ya tsaya akansu batare daya zauna ba, hannunsa daya dauke da jaka, dayan kuma ya turashi cikin aljihun wandonsa


Ummi ta kalleshi tace "kayan Nawal suna cikin motar ka, kaje kakai gidan dakake ajiye baqi, nan zaku koma da zama, muma gamunan zuwa"


Fita yayi daga falon ransa duk ba dadi


Ummi ta kalli Nawal " 'yata kiyi hakuri da halin Baffah, watarana zai sauya, temako daya nakeso kimin shine kitayani daidaita Baffah, duk abinda kikaga Babu agidan kiyi masa magana, Karkiji shakkarsa mijinki ne, tundaga ranar da' aka daura muku aure kun zama daya, zaisan sirrin ki zakisan nasa, ki temakamin Baffah yadena wasu halaiyar tasa "


Zancen zuci tafara, wai tayaya kowa yake cewa nasashi yadena wasu abubuwan, tayaya zan iya?meyasa suke son doramin abinda ni nasan ba lalle na iyaba? Domin tabawa ummi qwarin gwiwa sai tace"to Ummi insha Allah"


Daganan Ummi tabata magungunan tsimi, dana infection tace ta dinga amfani dashi, itade kawai takarba ne, amma idan tasha ma amfanin mezai mata bayan d'aki ma ana korarka bakada ikon kwana aciki


Har gidan Ummi tarakata, a lokacin dasukaje baya gidan, sannan tasake yimata fada akan tayi wa mijinta biyaiya, daga nan tayi mata sallama tatafi gida


Ummi na tafiya taga duk gidan yamata fadi, wayarta tadauka takira Najma sukaita fira, har taji ranta yadan saki,suna sallama taga ba'aja mata ko sisi ba πŸ€”
Inbox dinta taduba tagani ko wanine yayi mata transfer amma bataga komaiba saika data dataga wata number ta turo mata


Alokacin takira number akaqi dauka
Afili tace to may be bonus aka bani 🀣🀣


annan ta fita harabar gidan tana kallan tsari da kuma yanayin gidan


Gidan yayi kyau, kuma ya birgeta sosaai, harabar gidan tanada girma sosai, bakin gate ta kallah tahango maigadi yanajin redio, ta qarasa suka gaisa, sannan tadawo ciki, can wajan gefe wajan bayan dakunansu ta duba taga wani Dan qaramin swimming pool, cikin murna tace "laaaaa tareda qarasa wa wajan da gudu, tana zuwa tafara wasa da Ruwan, kafarta ta tsoma aciki cikin sauri tajanye saboda sanyin dataji


Awannan wajan anan ta wuni, sai wajan yamma lis sannan ta koma daki


Da daddare batayi girki ba, saboda tagaji, kawai lemukan da tagani a fridge su tasha ta qoshi, ta kunna kallo tayi kadan sannan taje dakin da aka saka mata kayan ta tayi wanka ta kwanta


data fara jin tsoro zata leqo ta window ta kalli dakin maigadi, idan tahango hasken fitilarsa saita koma ta kwanta, haka taitayi har bacci ya dauketa


Shikuwa bai dawo gida da wuri ba, sai dare, daya dawoma ko dakin datake bai nemaba yawuce d'akinsa ya kwanta


Da asuba tana idar da sallah tafara karatun qur'ani har gari yayi haske, qur'anin ta dauka tafita waje tanata zagayawa tana tilawa


Cikin baccinsa yaji qira'ah kai dad'i tana rera karatun qur'ani adede satin window dinsa
Idanunsa cike da bacci yajawo wayarsa yaduba time 7:41


Ahankali yatashi zaune, shibe koma bacci ba shikuma baitashi ba


πŸ€¦πŸ»β€β™‚Kansa yadafe da hannunsa, Tun shekaran jiya yakeso yayi bacci amma damuwa ta hanashi, yanzu yau yasamu baccin yafara daukar sa amma ita kuma wannan ta hanashi πŸ€”shide bashi da damar hanata karatun qur'ani 🀣🀣
Dole sai hakura yayi da baccin yatashi yashige toilet, daga nan yayi wanka yafice daga gidan gaba daya


Da yamma tana zaune tafara tunani, ta wacce hanya zata shirya Baffah? Tasan de masu irin wannan halin hanya ta farko itace kadinga tunatar dasu, to amma tayaya? Shida baya zama agidan?
dole bari zatai sai ranar dayake zaune agida saita fara gabatar da makaman yaqinta πŸ˜‚


Washe gari dasafe ma karatunta ne yatadashi daga bacci, gashi idan yatashi daga bacci zaiyi wahala ya koma a lokacin, Already yayi sallar sa tun asuba Dan haka kawai yatashi yayi wanka yafara duba wasu document, a cumputer


Yanajinta har zuwa lokacin data gama karatun


Itama anata bangaren bayan tayi wanka taci abinci, sha biyu saura a lokacin, ta duba waje taga duka motocin gidan suna nan, alamun yana nan yau bai fita ko inaba, browsing tayi tadauko wa'azin da ake magana akan kule-kulen yanmata


Shikuwa yana d'akinsa a lokacin yagama aikin dayake zai kwanta yayi bacci zuwa azahar




A lokacin takunna tv tajona wayarta tayi connecting sannan takunna wannan wa'azin ta qure volume yanda zai iya jiyota


Bacci yafara daukar sa yaji gida Kamar zai fashe da qaran wa'azi 🀣🀣


Yadauki fillo yatoshe kunnuwansa dashi, amma still bai daina jiba, cikin sauri yatashi zaune yace"yau nashiga ukuna πŸ˜‚πŸ˜‚, yarinyar nan ita kadai ma ciwon kai ce, yau bazata taba bari na na rintsa ba πŸ˜–πŸ˜–
Da asuba karatun qur'ani,yanzu kusan sha biyun rana ta kunna wa'azi, πŸ€¦πŸ»β€β™‚πŸ€¦πŸ»β€β™‚ko kasheni takesonyi ne?🀣🀣


Cikin bacin rai yafuto daga d'akinsa da gashi three quater Mai laushi,Babu riga ajikinsa sai vest, murdaddan jikinsa yafuto fili


Adede lokacin daya qaraso Mai wa'azin yake cewa Kuma maza kuji tsoron Allah, kudena damuqar matayan daba naku ba, ko hannun mace ka riqe hakan haramun ne, bare kuma ka rungumeta kasata a qirjinka batare da aure ba🀣🀣, sannan kuma yanmata kuriqe mutuncin kan...


Yana qaraso wa wajan yadauketa cimak yadora ta akafadarsa yayi bayan dakin su da ita


Harbe Harbe tafara tana cewa "kasaukeni, wallahi nadena, Dan Allah kasaukeni, kayi hakuri"


Amma ko Saurarar ta baiyi ba, saida yaje bayan dakin su kawai ya wullata cikin swimming pool dinnan yajuya, ga sanyin da akeyi agari, shi kansa Ruwan yadau sanyi, tanajin ta cikin Ruwan ta shid'e


Tafara karkarwar sanyi, tana kira "ka temaka min,zan mutu"
Tana kokarin futowa santsi yajata takoma ciki can qasan Ruwan, aikuwa sai ruwa yafara shiga hancinta da bakinta bul-bul-bul, daga nan tasume


Shikuwa yakusa shiga falo yaji shiru, yadena jiyo ihunta, Kamar wasa yajuya ya kalli wajan kawai sai yaga Babu yarinya Babu dalilinta πŸ™†πŸ»πŸ™†πŸ»


Gabansa yayi mummunar faduwa, cikin sauri ya furta Innalillahi... Aguje ya koma wajan, yana zuwa yaganta a kwance aqasan ruwan


😳Zaro idonsa yayi Gabansa na faduwa , baiyi wata wataba yafada cikin Ruwan yadaukota Kamar jaririya,ya tsaya acikin Ruwan tana dauke ahannun sa yana Kallanta, dogon gashinta Mai santsi yaji ruwa saiya qara kwanciya akanta,jelar gashin tana yawo acikin Ruwan, madedetan breast dinta sai suka sake futowa saboda rigarta data liqe a jikinta
aqasan wajan ya kwantar da ita sannan yafuto yafara jijjigata yana cewa "ke, ke ki tashi mana,"


Amma shiru kakeji baabu ko motsi, Gabansa yafara tsananta faduwa duk ya rikice yarasa abinyi, sake jijjigata yayi yace"ke Nawal ki tashi mana, wasa nake miki fa, πŸ™ŠπŸ€£πŸ˜‚
Karki mutu ki tashi "


Nanma shiru Babu alamar motsi awajan ta, yarasa ya zaiyi, yadebo Ruwan wajan ya kwara mata amma bata farka ba


Shafaffan cikinta ya kallah yadora hannunsa ya danna Ahankali, ruwa yafuto daga bakinta d'an kadan
Yajira ko zata farka amma kwata kwata bata motsi


Kalle Kalle yafara Kamar yana tsoron wani ya ganshi sannan
Ahankali yakai hannunsa kan dogon hancinta yatoshe hancin, sannan yafara kai fuskar sa dab da tata fuskar, yadora bakinsa akan nata, yafara hura mata iska abakin ta


Lokaci daya tafara tari, sai a lokacin ya dauke bakinsa daga kan nata, cikin wahala take bude idonta harta bude shi gaba daya afuskar sa, yayinda shima yazuba mata ido yana Kallanta




































Mutara zuwa gobe


















Sharhi please πŸ™πŸ»






















Amnah El Yaqoub ✍🏻
[2/3, 12:15 AM] Amnahelyaqoob: 🌺NI DAKE🌺


(Hot luv story)


Writing by Amnah El Yaqoub


Dedicated to Itz sadeek




25&26




Kallanta takai zuwa jikinta taganshi d'ame d'ame akan qirjinta


Shima ganin tana kallan jikinta yasa ya kalli wajan, cikin sauri yatashi daga jikinta, gaba daya kunya ta rufeshi, sai kawar da fuskarsa yake bai yarda sun hada idoba yayi hanyar dazata sa dashi da cikin falon nasu


Sararin samaniya ta kallah tana maida numfashi Ahankali, sannan ta yunqura ta tashi zaune, afili ta furta "marar imani kawai"


Tashi tayi tanufi hanyar falon nasu, sai karkarwar sanyi take
daki tashige tasauya kaya
sannan ta busar da gashin kanta takulle kofar ta tareda shigewa cikin bargo




*** ***** ***


Yana shiga d'akinsa ya zauna abakin gado tareda dafe kansa hannu bibiyu
Yanzu dataa mutu mezai cewa Ummi? Shikkenan fa shima yabi sahun masu kisan kai, amma itama tanada laifi yaga alama batajin magana, bayasan hayaniya amma ta qure masa volume qara Kamar zai fasa masa kai
koda yake batada laifi, tunda bai fada mata dokokin saba, amma yakamata yafara yi kenan
Tashi yayi ya shige toilet yasake wanka sannan ya kwanta


Baby ce tafado masa arai, nan da nan yafara zancen zuci, Inda ace ita aura yasan cewa bazata qyamaci halinsaba, zata zauna dashi ako yaya ma yake, bazata kunna masa wa'azi ba, zaunar dashi zatai tafada masa abinda yakamata ayi, tanada hakuri duk abinda yamata zatayi hakuri dashi
Huci yayi, basahida photon ta, baisan yaya zaiyi yasamu ba domin yadinga gani yadebe masa kewarta
Tokode yasa Yas ya bincika masa ita ne? Ya tambayi kansa, wata zuciyar tace inaaa, Yas bazai santaba, hamdala yayi wa Allah dawani tunani yafado masa Wanda idan yayi hakan zai taimaka masa wajan debe masa kewar Baby


Da yamma ya shirya cikin qananun kaya, Baqin wando jeans yasaka saide crazy ne, kasancewar sa fari sai farar fatarsa tafuto sosai acikin Baqin wandon


Saide riga itama baqa Mai laushi, yadauki jacket Mai laushi yadora asama, Saukowa yayi kasancewar d'akinsa yana samah
Yana zuwa falo bai tsaya ko'inaba sai abakin qofar dakinta


bai tsaya wani qwanqwasa ba yatura kansa cikin dakin
Adede lokacin tafuto daga wanka tanaso tayi sauri ta shirya domin yin sallar la'asar


Cak idonsa ya tsaya akan fararen cinyoyinta, tana ganinsa tayi sauri ta tsugunna aqasa
Fuskarsa Babu alamun Fara'ah yace mata "biyoni"


Cikin rawar jiki, ta dora rigarta doguwa hadeda hula ta futo, afalo taganshi yana sauya chanel yadora qafa d'aya kan d'aya ranta ne yabaci ganinsa da irin wannan shigar, Kamar ba Babban mutum ba
Gabansa taje ta tsugunna tace "gani"


Remote din hannunsa ya ajiye ya dubeta"Am Nawal kike kowa, naga alama kanki yana miki rawa, nikuma bana jurar haka, a lokacin nake saitawa mutum zamansa, inada qa'idoji da dokoki Wanda idan kika bisu zamu zauna lafiya, Karki shiga harkata agidan nan, nima bazan shiga takiba, kiyi abinda kikaga dama ni bazan hanaki ba saboda bakya gabana,inada wadda nakeso, kuma kisa aranki taana nan zuwa, yazama dole karfe bakwai ki tashi ki gyara gida, banason qazanta,idan ba hakaba toki dauka ankawomin kene kawai nadinga faffalla miki mari"
Yadora hannunsa akan kunnansa yace"kinji abinda nace?


Cikin rawar murya tace "naji"


"Ok tashi kibar gabana"


Ahankali ta tashi tashige cikin daki, hawaye suka zubo mata, tashare tatada kabbarar sallah


Wayarsa ya dauka yakira Nasir "Nas ina zaka samomin mutumin daya iya zanene?"


"mk wanne irin zane kuma? Ko akwai gidan da kakeso azana maka?"


"no Nas, inaso azanamin photon yarinyar nan ne, zan ajiye shi a d'akina"


Nasir yace"aikuwa akwai wani mutum dana sani ya'iya zane, ya qware wajan zana mutum "


" yawwa Nas, toka turomin shi gobe pls "


Nasir yace" to Babu damuwa "
daganan yatashi yafice daga gidan




*** ***** ***


Bai dawo gidaba sai bayan sallar magrib, yana doso cikin falon da shashshekar kukanta yafara cin karo, meyasa ne yarinyar nan kuka baya mata wahala, komai kuka, cak yaja ya tsaya abayanta batare daya qaraso cikin falon ba


Cikin kuka tace "ni wallahi umma nagaji, dazu dasafe kusan mutuwa nayi,"


Umma tace"to Nawal menene auren ne? sokike koda yaushe kijiki cikin jin dadi da kwanciyar hankali Kamar kina gida?ai bazai iyuba, ki yi hakuri watarana sai labari "


Wahaye ne suka zubo mata tace" Ummah wallahi DANA SANI tun farko Nuhu na aura 🀣🀣, nasan bazai taba wulakanta niba "


Ummah tace" Nawal, kina gidan wani amma kina maganar Nuhu, kiyi hakuri kede kiyi masa biyaiya, Karki kuskura kirageshi da haqqi d'aya kinji abinda nafada miki, sannan Zan yiwa Sultan waya idan yasamu lokaci yazo yaganki tunda kuna kusa "


Jin yaya Sultan zaizo yasa tasaki ranta, tace" to shknn sai yazo "


"Nuhu" ya maimaita sunan cikin zuciyarsa


Bai kalletaba yazo yawuce tagabanta yayi d'akinsa, amma ransa idan yayi dubu toya baci, kan gado yafada, sannan yafara magana a bayyane "wannan yarinyar yaudarar Ummi kawai take,rannan takira masa sunan Sultan, yau kuma Nuhu, Wato data sani shita aura, gani dan'iska yarinya tana zaune agidana amma tana kiramin sunayen qarti, Allah yakawo shi lafiya, ai naji tace Allah yakawo shi lafiya, to Allah yakawo shi lafiyarπŸ™ŠπŸ˜³πŸ˜‚Zan yi maganin abun "


Yaanaji aka kira sallar isha'i yamiqe yafita, a lokacin bata falon, yaana zuwa masallaci bayan yayi sallah yadawo gida, awajan maigadi ya tsaya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login