Showing 30001 words to 33000 words out of 72369 words

Chapter 11 - Ni Da Ke Book Complete Document by Amnah El Yaqoub --.txt

28 Dec 2024

8934

tundaga lokacin harkokin uban yadawo hannunsa, ta bangaren siyasa ma dashi ake komai, yanda mahaifinsa zai kira meeting aje haka shima yakeyi, taronsu na qarshe shine Wanda suka gudanar dashi a qasar kuwait tareda mahaifin Anwar da kuma sauran yan jam'iya


Kasancewar sa matashi yasa yake shiga motar dayaso, yasa kayan dayaso, yayi kwalliya irin yanda yakeso, sauran kasuwancin mahaifinsa dakuma kamfanunnuka Ummi ce take kula dashi, wasu daga cikin harkar kasuwancin nasu kuma shine yake gudanar dashi a Dubai


Ita kuma Ummi take gudanar dana cikin gida Nigeria


Arayuwarsa bayaso a kirashi da muhammadu, saide MK,Wato Muhammad Kabeer, amma dangin su na yola kowa muhammadu yake cewa Babu ruwansu da wani mk, shima kuma haka yake amsawa Babu yanda ya iya😖


Amma sunan Baffah, Ummi ce kawai take kiransa dashi, bayan ita Babu mai fada masa sunan


Abokin sa daya, yarima Nasir, daan sarkin gombe ne, amma yana kiransa da Nas


Yanzu haka shekararsa 34 amma ba aure, kuma Babu wadda yake kulawa, sai zuwansa kano da Allah yahada shi da Baby🤣




Yana mutuqar son mahaifiyarsa, idan ka naso yasoka toka Mutunta mahaifiyarsa, tausayi da temakon mutane Babu abinda yabari na mahaifinsa, har kama, inde kasan mahaifin sa to kana ganin mk zaka gane shi




Wannan shine labarin MK🤗




*** ***** ***


Cikin satin su Abba suka gama bincike akan Ummi, amma basuji dadin labarin dasuka samu akan danta ba, Dan haka Abba da kansa ya kirata yafara yimata maganar awaya, kai tsaye tace masa zata biyo jirgi tazo, sai su qarasa maganar azahiri, tunda wannan ba qaramar magana bace


Washe gari Nuhu yaturo wani dan'uwansu Abba, Kamar yaya yake awajan Abba


mutumin
Yace Nuhu ne yaturo shi yanaso abashi dama yakawo wa Nawal kayan gaisuwa saboda kar wani
Yarigashi
Abba yadubi mutumin yace bawai Yaqi Nuhu bane, wallahi tallahi yanason Nuhu, amma Nuhu yanada gajen hakuri, ita yarinyar ma tace bataso, yanzu haka kokarin janyo hankalin ta sukeyi
Daga nan mutumin yatafi, Abba yace yau nagamu da Nuhu, ni wannan yarinya yaya Zan mata ne? 🤣🤣


Acikin satin Ummi tazo kano, Umma tana ganin ta ta karbeta a mutunce
Abba yakira Malam awaya, ba'a dauki lokaci ba Malam yaqaraso


Nawal tana dakin mama mariya itada Najma, tunda taji baquwar rannan tazo takasa fita saboda gani take kowa haushin ta yakeji, bayan batada laifin komai


Malam yadubi Ummi bayan sunyi gaishe gaishe yace"baiwar Allah kinzo garemu da Babban al'amari, gashi kuma mu munyi bincike mungano cewa yaron wajan ki har neman mata ma yanayi,😳 ga kuma shigar dabata daceba, kinsan kuma ba kowanne ubane zai iya daukar yarsa yabawa irin wannan yaron ba "


Ummi ta jinjina kai tace" Baba nasan d'ana, shi yasa Tun farko ban boye muku ba nafada muku cewa bayaji, nasan cewa yana saka kayaiyakin dabasu daceba, amma neman mata kaam bayayi, Inda yanayi Tun farko bazan boye muku ba, akwai qanwata uwa daya uba daya, itace tabani shawara namasa aure zai daina irin wannan shigar da temakon matarsa, nikuma nayaba da hankalin 'yarku, uwa uba tanada hakuri, shikuma d'ana yanada tausayi, nasan cewa da temakon ta zansamu Allah ya shiryamin shi, yana fita wasu qasashen yana ayyuka yanzu hakama bayanan,kuma banaso yasan da maganar auren, nafiso kafin yadawo ayi musu auren,


to kaga baba bazai iyu duk Inda yaro zaije nadinga binsa ina ganin me yakeba, amma itaa matarsa dole duk Inda zaije tana tare dashi, kuma idan taga yayi ba daidai ba zata tsawatar masa🙊, bayan neman aure harda neman alfarma nazo akan kuban 'yarnan taku Dan Allah, saboda inasonta har cikin raina Kamar d'ana, sunan yaron nawa Muhammad Kabeer ammma ina kiransa da Baffah, saboda sunan babana yaci "


Malam yayi ajiyar zuciya yacemin" to munji baya nanki, kuma insha Allah duk abinda muka yanke zamu sake tuntubarki "


Tace" to nagode baba, bayan kunyi nazarin, idan kun amince inaso adaura musu auren ad'an qanqanin lokaci ,banaso ayi wasu bidi'a saboda albarkar auren kawai muke buqata, idan kuma baku amince ba daan Allah karku boyemin kawai ku sanar Dani, ina nan ina jiran wayar taku "


Daga nan sukai sallama da ita tatafi, Malam yadubi Abba yace" akira masa Nawal," Umma taje da kanta ta kirata


Malam yadubeta yace"Nawal, kwanaki anzauna dake akan zaki kawomin Wanda kikeso, kin samo wani? "


Jijjiga kanta tayi, gaabanta na faduwa


Malam yasake cewa" to yanzu Nuhun za'a baki? "


Hawaye ne suka zubo mata,zancen zuci tafara, karfa naje ahad'ani da mutumin da ban saniba daga qarshe nazo ina DANA SANI, bayan kuma BURINAH a rayuwa shine mk, to shikuma mk ya gujeni bare inyi tunani tsakanin shida Nuhu WAZAN ZABA?
inama ace zan zamo SHALELAN MK wata rana? Haqiqa danaji dadi arayuwata


Ahankali ta girgiza kai alamar a a


Yace" to shikkenan tashi kije sai abaki wannan bawan Allah da matar nan tazo da maganar sa "


Kuka tasa musu tace" Malam wallahi bana sonsa, banfa sanshi ba,
Dan haka karku bani shi "
Malam yace" Nawal auren wannan yaron Kamar jihadi ne zakiyi, ni kaina abin alfahrina ne ace jikata ta shiryar da wani, tashi kije Allah yamiki albarka"


Daki tashige take kuka tuquru, yanzu shikkenan Babu mk, wacce irin qaddara ce wannan? Ita tana haukanta ashe bama mk din zata aura ba, wanine daban, tayaya zata soshi? Inaa bazai iyuba, bazata iya sonshi ba


Acikin satin Abba da Malam suka fadawa Ummi cewa sun amince, kai tsaye tatafi yola tasamu danginsu maza ta turasu akayi komai aka gama Kamar yanda al'ada ta nuna, aka saka ranar biki kwana kusa, haka gida suka fara shirye shirye aka sanarwa da dangi na kusa bikin Nawal ya matso, anty maryam batayi qasa a gwiwa ba tataho, Umma ko kallan Nawal batayi, anty maryam ce take mata komai, amma cikin ranta tausayi ne fal na 'yar tata


Najma tayi rarrashi harta gaji, abubuwan tsumin da anty maryam take bata batasha, zuwa take tazubar dashi, Data gano haka sai take tsayawa akanta sai taga tasha komai
Abubuwan datake sha yasa jikinta yayi kyau,ko'ina yaciko yayi bulbul musanman Kirjinta, Kamar zai tsolewa mutum ido


Jiki kaam yayi kyau har ya gaji amma zuciyarta Babu dadi


Cikin satin mutanan yola sukazo da sadakinsu ahannu, aka daura auren Muhammad Kabeer, tareda matarsa Nawal Muhammad lawan akan sadaki nera dubu hamsin Kamar yanda Ummi takeso


Sannan suka sake bawa iyayen amarya hakuri kan rashin zuwan Ango, baya qasar idan yadawo zaizo tareda amaryarsa tanuna masa yan'uwanta, amma yanzu yarinya kawai suke buqata, basa buqatar akaita da Komai




Duk yan unguwa kowa saijin labarin auren Nawal yayi, saboda bakowa ne yajiba
Aranar kuma suka dauki amarya, a lokacin da zasu tafi ta qanqame ummah, ita kanta umman kuka take sosai, Najma kuwa daki tashige ta dinga rasgar kuka


Malam ne da kansa yayi mata nasiha Mai shiga jiki akan biyaiyar aure, kuma yanemi tayi masa alqawarin zatayiwa mijinta biyaiya, atake ta dauki alqawari


Yan'uwan umma da Abba mutum biyar ne sukabi amarya, sai anty maryam da Salisu, Sultan yace zaije daga baya


Sunkai amarya lafiya, sun samu tarba Mai kyau, tunda su kaga gidan suka tabbatar ba qaramin gida Nawal tajeba


Kai tsaye Ummi tace akai mata Nawal cikin Dakinta su zauna tare kafin mijinta yadawo, duk lokacin da yadawo qasar saisu shirya d'akinsu dakansu irin yanda sukeso🤣🤣


Washe gari tasa aka musu komai suka dawo gida ta jirgi


Sauran yan'uwanta da sukazo daga yola suma duk sun koma, tunda ba wani event da za'ayi


*** ***** ***


Da yamma Nawal na dakin Ummi tana sallah, bayan ta idar tayi addu'ointa tashafa, tafada duniyar tunani, Allah sarki ummah, kome Najma takeyi yanzu? Hawaye suka zubo mata, tashare
Turo dakin Ummi tayi tashigo Tace"Nawal tashi mukoma falo mana, banaso kina yawan tunani fa, kid'aukeni Kamar ummanki kinji?


Ahankali tace "to Ummi"


Futowa sukai falon, Nawal de tanata ganin tsarin gidan wannan uwar tv din kadai ma ta isa kagane cewa ba qananun mutane bane


Zazzabi yanaso ya rufeta saboda bata saba da esi ba, gara gara de fanka🤣🤣
Ummi na lura da ita tace "meyake damunki?"


Ahankali tace "zazzabi nakeji kad'an"


"subhanallah, bari narage wannan esin saikici abinci kisha magani ki kwanta, Baffah baya nan dasai yamiki allura ya iya sosai"🤣
Amma bari na kirashi nafada masa yana da patient
Wayarta tadau ta kirashi bugu daya yadauka"Baffa yaushe zaka dawone? Kanada maraar lafiya "


Gabansa ne yafadi yayi zatan itace batada lafiya" Innalillahi Ummi meyasameki? "


Tace" kaga nide kawai kataho inason ganinka "
Daga haka takashe wayar


Nawal dake gefe Cikin ranta tace "tofa nikuma nashiga uku, banzo bama ana ban labarin baffa inaga nazo kuma 🤦🏻‍♀🙆🏻


Abinci taci tasha magani, ta kwanta, har dare de bata wani sake da Ummi ba, har washe gari, taji zazzabin nata yasauka


Harma ta gyarawa Ummi 'Dakinta, wdrb d'in da Ummi tace tabude akwai kaya aciki tasaka, shita bude tasaka wata doguwar riga ready made, rigar tamata kyau, sannan tafitar mata da shape dinta, shafaffan cikinta ya kwanta, hips dinta yasake futowa aciki, amma batayi batayi kwalliya ba, sannan tafara goge mata dakin






Ummi na falo kawai sai ganinsa tayi yashigo hankali tashe
Cikin murna tace "oyoyo Baffah nah, sannu da zuwa,"


Zama yayi akan kujera jagwab yadafe kansa 🤦🏻‍♂yace "yanzu Ummi fisabilillah , kinsan qalau kike shine kika tasoni?"


Cikin Murmushi tace"to yanzu bagashi naganka ba, dama akwai maganar danakeso muyi dakai "


Kafin yayi magana ta d'aga murya tafara kiranta "Nawal! Nawal!
'yata Nawal


Cikin ransa yake fadin Ummi da kwashe kwashe take wallahi,kowa ta kwaso harta bata iznin shiga cikin dakinta? 🤔


"ya kalleta yace" Ummi kinyi Sabuwar mai aiki ne? "😳🙆🏻😱


Kallansa tayi tace" A a, ba Mai aiki bace, Matarka ce Baffah, aure namaka ai "🤣


Cikin sauri yazabura yamiqe tsaye yace" wai wanne Baffan kike nufi ne? "


































Mutara zuwa gobe




(kullum de maganar guda daya itace hakuri, mudinga hakuri da junanmu yan'uwa, sai kaga Allah ya azurtaka ta Inda baka taba zatoba, idan kukai dogon tunani zaku gane cewa Shifa Anwar Kamar alkhaairi ga Rayuwar Nawal, yayi mata cin mutunci tayi hakuri ta dauki qaddara daga qarshe ga abinda hakurin yajamata, Sanadin ta yan'uwan ta zasu shiga makaranta, still sunyi karo gashi de shine da laifin amma itace ta bashi hakuri, Sanadin hakurin gashi Allah yahadata da mahaifiyar mk cikin Ruwan sanyi, itafa duniyar nan idan kayi hakuri ka dauketa asannu wallahi zakaga daidai arayuwarka, abinda nakeso mutane su gane har nake wannan haqilon typing din wallahi shine fa'ida da amfanin hakuri)




Masu cewa nayi 2pages kuyi hakuri, duk Wanda kukaga anyi muku posting dinsa to aranar na zauna na rubuta, bazai iyu nayi sau biyu ba, mu lallaba ahakan de🤣






































Sharhi sharhi pls🙏🏻




Sorry Nuhu kaban tausayi wlhy😭


Yaya zaman mk, Baby, da Ummi zai kasance? kubiyoni🤗












































Amnah El ✍🏻
[2/2, 1:47 AM] Amnahelyaqoob: 🌺NI DAKE🌺


(Hot luv story)




Writing by Amnah El Yaqoub


Dedicated to Itz sadeek




23&24






Cikin ransa yafara cewa "wallahi sak irinna Baby, to kode sunada wata alaqa ne?"


Wata zuciyar tace masa Babu wata alaqa, yawancin fararen fata haka bakinsu yake, Ahankali yatashi, still bai daina Kallanta ba harya fice daga dakin


(nikam nace da sannu🤔)




Yana zuwa falo Ummi tace" dafatan kayi mata addu'ah? "


" eh nayi mata saida safe "bai jira amsartaba yafice daga falon, sai mita yake, ga jaririya mezai hana yayi mata addu'ah


Ummi ma kawai bayansa tabi da kallo badan ta yarda da maganar tasaba




*** ***** ***


Washe gari kiran sallar farko acikin kunnanta akayi, tana juyi tareda addu'ar tashi daga bacci kawai saita ganta akan gado, tajuya gefenta taga Ummi tana bacci
Tambayar Data fara zuwa ranta itace waye yakawo ta? Itade tasan cewa a kujera bacci yadauketa, bade wannan Baffan ne yadaukota ba?cikin sauri tafara dudduba jikinta, Allah yasa de bashi bane


Saukowa tayi tashige toilet tadauro alwala tafara gabatar da sallah, bayan ta idar tafara karatun qur'ani har aka shiga sallar asuba, saida ta idar sannan ta tashi Ummi itama tayi, harsaida gari yayi haske sannan ta gaida Ummi, fita zatayi waje, Ummi tace tadawo ta kwanta tahuta, komawa sukai suka kwanta, amma bakwai da rabi tafarka, ta tashi Ahankali tashige kitchen, tana zuwa taga wata yarinya tana aiki, tace mata "sannu da aiki, kema anan gidan kike?"


Kallanta tayi cikin ladabi tace"ina kwana? "


Nawal tace" lafiya, Yaya sunanki? "


Ranki yadade sunana" Sabira, nice me aikin gidan nan, naje ganin gida ne kwana biyu, bana nan akai bikin yallabai "


Tace" Allah sarki, kawo nataimaka miki da wani aikin "
" A a ranki yadade kibarshi, yallabai bazaiji dadiba idan ya ganki kina aiki "🤣


" kinga Karki damu, kawo muyi tare "


Badan tasoba tabata suka fara gabatar da break fast din tare, har falo suka kai komai, sannan ta koma daki taga Ummi bata nan da alama tana toilet, gadon tafara gyarawa sannan tafara gyara dakin, ta nemo wayarta acikin jaka ta kunnata, tareda ficewa daga dakin takoma falo


Layin umma tafara kira, bugu uku umma ta dauka, "Baby yagidan"


Muryarta ce tafara rawa Kamar zatai kuka tace "umma ina kwana"


"lafiya, menene kuma abin kukan? Bakya rabo da sakarci"


"umma inasu Najma?"


"Najma gata can adaki a kwance, batajin dadi ba amma yau jikin nata da sauqi, bari nakai mata wayar"
Tashi tayi tashige daki tabawa Najma wayar tareda futowa, sai yanzu hankalin ta yadan kwanta dataji muryar 'yar tata


Najma tace "Baby yagari, ina angon namu?"


"lafiya kalau Najma, Umma tace bakida lafiya ya jikin naaki?"
"wallahi bana danjin dadi, zazzabi ne yarufeni, amma yau da sauqi"


"nima haka shekaran jiya nayi wannan zazzabin wallahi, amma yanzu da sauqi"


"to Allah yasawaqe, ina in law dinki me kirki?"


"Ummi wallahi taana daki tana shirya wa, ni ina falo"


"falo kuma? Me kike nufi ne Baby? Keda yakamata kicemin kina kirjin mijinki, amma wai wani falo" 🤔


😳Zaro ido tayi dukda Najma bata ganin ta, sannan tace "ke baya nan yafita" 🤣


Najma tace"owk yanzu naji batu, ai naso ace yana nan kibani shi nayi masa gargadi akanki, kada yabari ko quda yatabamin qanwata, amma yanzu tunda bayanan idan yadawo ki gaishe shi "


Murmushi tayi tace" Najma kenan, to zaiji, bawa ummah wayar takaiwa mama mugaisa "


Tashi Najma tayi takaiwa ummah wayar, suka gaisa da mama mariya dasu mus'ab, suna sallama da umma awayar a lokacin Ummi tafuto tace" Nawal dawa ake waya ne?"


Kallanta tayi tace" su ummah ne "


Hannu tabata tace" bani su nima mugaisa, kije kiyi wanka ki shirya muyi break "


Wayar tabata, tashige cikin daki


Sosai suka gaisa dasu ummah tana kuma qara bata tabbacin insha Allah zata kula da Nawal Kamar yanda zata kula da Baffah, daga nan sukai sallama
Tana kashe wayar aka nuno mata adadin kudin da akaja dakuma sauran blance dinta, katsewa tayi ta ajiye wayar agefe


Wajan goma da rabi yashigo falon, da takardu ahannun sa, ya rissina yace "Ummi barka da safiya"


"yawwa Baffah barka, yanaga idonka yayi ja,? Ko bakai bacci bane daren jiya?"


Ahankali yace "nayi" share shi tayi, tasan cewa baiyi baccin ba, Yaya zata masa, yarinya ma tayi hakuri bare shi?


Tsintar maganar ta yayi tana cewa"Yakamata kaje kayiwa layin Nawal register basai tasa kati ba, su dinga cirewa a account dinka Kamar yanda kayiwa naka sim crd din, sannan kasaka mata Data saboda ganin labarai a yanar gizo"


Cikin rashin walwala ysce"yanzu Ummi wannan yarinyar wanne labarai zata gani? Me labarai zasu qara mata? "


" kacemin kawai baza'ayi ba"


Ahankali batare daya kalleta ba yace"za'ayi"
Cikin ransa kuwa tunanin barin qasar yake inba hakaba wannan yarinyar zata dinga hadashi da Ummi 😱


Sake kallanshi tayi tace"ga wayar tata nan kaduba kadauki number, idan kafita yanzu sai kayi mata abinda yakamata, kaga saikaga number tata ma koda zaka dinga kiranta kaji lafiyarta,🤣 itama sai kayi mata saving taka number, sannan ba number ka ta gama gari zaka saka mataba, number ka zaka saka mata wadda koda baka qasar idan ta nemeka zata sameka "


Wayar yadauka yasaka number sa aciki yayi kira, kiran yana shiga cikin wayarsa yakatse, sannan yayi mata saving number tasa da Muhammadu 🤣🤣😃


Amma shi baiyi saving number taba, kai tsaye wajan massage yaje yaturawa wani abokin sa number, yasa yayi mata register tareda turo datar


Futowa tayi falon, tayi kyau cikin doguwar riga Mai fadi Kamar ta 'yan mali tareda mayafin rigar, mayafin sosai yabawa sumar kanta damar futowa, tana zuwa ta tsugunna har qasa tace masa "ina kwana?"


Kamar anmasa dole yace"lafiya" atakaice


Ahankali tatashi ta zauna daga gefen Ummi 🤣🤣Sabira ta gabatar musu da abinci, shikam kawai tea yasha, shima yadade yana juya tea spoon din sannan yagama
Saida yabari suka gama sannan yadubi Ummi "Ummi Zan fita, akwai aikin dazanyi"


Tace"to Baffah adawo lafiya "


Kallanta yasake yi, baiyi magana ba, tasan nufinsa sarai, jira yake taje tarakashi, Dan haka tasa hannu ta dauki takardun gefensa


Yana gani ta dauki takardun yamiqe, yayi zatan zata rakashi ne, kawai sai gani yayi tabawa Nawal takardun tareda cewa" tashi ki rakashi bakin gate"🤣


Yana jin abinda tace yayi gaba, baima tsaya jiran taba, itama kuwa ta doru abayansa 🤣🤣


Sai sauri yake fiya-fiya, har yazo harabar gidan, yajuyo yaga Nawal tana wata irin tafiya Kamar bataso, cikin bacin rai yadawo baya, yamiqa mata hannu batare dayayi magana ba


Tayi zuruu tana kallansa tarasa gane meyake nufi


Cikin tsawa yace "kibani takarduna nace"


Cikin sauri ta miqa masa, ya warce yayi gaba




*** ***** ***


"Nuhu abinda nakeso dakai shine kayi hakuri Nuhu, haka Allah yatsara, dama can Allah ya qaddara ba matar ka bace"


Hawaye ne suka zubo masa, yasa hannu ya share "hakane Abba, kukam kun soni, Babu abinda zance daku sai godia, Allah yabata zaman lafiya"


Mama mariya tazo wuce tadawo daga unguwa taga Nuhu a tsugunne gaban Abba yana share hawaye tace"a a Nuhu ashe kaine 🤣"


Cikin sauri ya gaishe ta yace" yasu Najma?"


Tace" lafiya kalau Nuhu, ai Najma ma batanan tayi tafiya,🙈🙆🏻 🤣yaya qarin hakuri kuma na Baby? "


Kansa aqasa yace" Hakuri da godia"


Tace"Allah sarki, sai hakuri Nuhu, Baby antafi Birnin tarayya, saide ka musu addu'ar samun zuri'ah tagari "🙊😂


Abba ne yawatsa mata wani kallo, tasake cewa" to Nuhu kagaida mutanan gida "daga nan tashige cikin gidan, shikuma Abba yaci gaba da bawa Nuhu baki




*** ***** ***


Da yamma suna zaune itada Ummi, Ummi tace"kinga ameerah har yanzu bata zoba, Tun jiya naketa faman kiran wayarta bata shiga "


Cikin sanyin murya tace" Ummi baquwa zamuyi? "


" A a Nawal ba baquwa bace, zuwatake kawai tanamin karatu, akwai littattafan datake qaramin "


Tace" To Ummi kawo nayi miki mana "
" kin iyane Nawal? "eh Ummi na'iya"


Littafin tabata tace to gashi 'yata
Nan suka fara

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login