Showing 3001 words to 6000 words out of 72369 words
Chapter 2 - Ni Da Ke Book Complete Document by Amnah El Yaqoub --.txt
datake gabanta, umma datake zaune tana wanke kwanuka tace "kanki daya kuwa Baby?"
Umma wallahi banganiba , bnda nutsuwa ne, ka'deni akai da mashin
Kallanta tayi dakyau tace "kina ta shegen tunanin naki har aka bigeki ko, yamiki kyau, saikije kicire kayan kuje _chemist_ abaki magani"
Awajan tacire niqab din nata, tacire dankwalin abayar datayi _rolling_ sannan tazare abayar ma gaaba dayanta
Qananan kayane a jikinta, wandon _three_ _quater_ ne yawuce gwiwarta da kadan, amma ya kamata, saida riga marar hannu Kamar _vest_
Surar jikinta ce ta bayyana, fara ce sosai, me matuqar kyau, _long_ _face_ gareta, tanada madedetan _breast_ yayinda _hips_ dinta yacika wondon jikinta taf, cikin ta ashafe Kamar batacin komai
Harara umma tasaki tace "amma yau kinyi gamo ko?"
Cikin sigar shagwaba tace "umma Allah nagaji, kuma jikina ciwo yake" 😔
Cikin tsawa tace "Baby wallahi zanci ubanki kinji ko, kwashe kayanki kibar kaina, kin wani baza gashi saikace mahaukaciya"
Tsugunnawa tayi tadora kanta akan cinyar uwar tace to umma dauremin "
Girgiza kai tayi sannan ta kama dogon gashinta tadaure mata, tace jeki abincinki yana daki, karna qara Ga kin zauna haka atsakar gidannan nafada miki"
Batace komai ba ta wuce dakinsu
Tana shiga tahada Ruwan zafi tayi wanka, tarama sallolin dake kanta sannan taci abinci ta kwanta, saida tajira akai sallar isha'i sannan ta kwanta,batare dataje chemist din da umma tace tajeba
Wani yaro ne yashigo dakin yace "yaya Baby kince zakibaan wayarki idan kindawo daga school"
Tace "mus'ab banda chargi, jeka Dan Allah kabarni nahuta kaji ko"
Yaron nafita, bacci yadauketa
Washe gari karfe takwas daidai tabar Gida, sunada lacture takwas da rabi, bayan sun gaisa da babanta yabata kudin Mota tatafi, lafiya kalau yau ta wuce babu su Anwar a hanyar, hartaje school lafiya
Sosai ta fahimci karatun nasu nayau saboda hankalin ta akwance yake, basu tashi da wuri ba yau sai karfe biyar na yamma, minti goma sha biyar ta dauka ahanya aka sauketa adede layin unguwarsu, cikin nutsuwa take tafiya Kamar yanda tasaba
Ruf taji anrufe mata ido, andagata sama
Ihu tafara tana nemaan temako amma babu Wanda yaji, asalima daga fuskar ta har hancinta zuwa bakinta arufe suke
Harbe Harbe take da qafafunta tanaso takwace amma takasa, saida suka koma can gefe sannan suka direta
Yaye mata fuska sukai, anan ta ganshi, gabanta ne yafadi, lokaci daya jikinta yafara rawa, tace "Dan Allah kuyi hakuri, karku cutar Dani, Dan Allah Dan annabi karku lalatamin rayuwa"
Daria sukasa gaba dayansu
Yace "ke har kin isa ki mareni ki zauna kalau?" kina tunanin kinci banza ne? To yau Zan nuna miki niba tsaranki bane, zan takaki inga uban daya tsaya miki
Wata kwalba ya nuna mata yace "kinga wannan? To _acid_ ne aciki, zan lalata miki fuskar dakike taqama da ita har kike marin maza akanta,"
Gabanta ne yayi mugun faduwa " _acid_ "
Tace "na shiga uku, Dan Allah kayi hakuri, wallahi tallahi natuba bazan sake ba,"
"bakince zaki iya yin komai saboda ki kare mutuncin kanki ba? To ai Ga wajan nan kiyi nagani _NI DAKE...d'an halak kafasa_
Yadubi abokansa biyu yace "nabeel ku riqemin ita"
Lokaci daya suka kamata tana fiffizgewa, haka suka riqeta kowa yakama hannunta daya, shikuma yabude murfin kwalbar yanufota dashi
Ganin zai lalata mata fuska tanaji tana gani yasa tasaka kafarta tabige kwalbar
Ruwan ciki yazube aqasa, take qasar wajan tafara kumfa
Yace "iyeeeee nizaki yiwa iskanci? Tass ya wanka mata mari, yajuya zuwa wajan motar sa Dasauri, yadawo da Shaltos a hannunsa
Cikin tsawa yace" kuriqemin ita nace "
Sake riqeta sukai, tanata kawar da fuskar ta, amma haka ya matso ya gwale mata cikin idonta
Haqorinta tasa tana kawo masa cizo amma haka yacire murfin Shaltos din yafesa mata a idonta, lokaci daya ganinta ganinta ya dauke
Yayinda tasaki wata irin qara tafadi awajan
Cikin tsoro jazy yace "gaye karfa Muje tamutu, yasaka hannunsa aka 🙆🏻♂na shiga uku idan akaji agidan mu"
Anwar yace "to Dan matsoraciya, dalla kuzo mu ware"
Cikin sauri suka shiga Mota sukabar wajan
Acan Gida kuwa umma takasa zaune takasa tsaye, har ana kiran sallar magrib amma shiru Baby bata dawo Gida ba
"ke kuma lafiya Tun dazu nashigo inata sallama kinyi shiru"
Kamar da ita yake magana ta yi burum tafuto daga Dakinta tace "rashin kawaici ne kawai irinna yaya, Tun dazu Baby bata dawo daga makaranta ba shine ta daga hankalin ta, ita Babyn yarinyar goye ce daza'a tsaya ana d'aga hankali akanta"
Abba yace"badake nakeba Mariya, kidenamin katsalandan "yajuya ya kalli umma yace" ke Safiya karfe nawa take dawowa yau? "
" Karfe biyar, wani lokacin biyar da kwata, kuma tabar wayarta agida saboda batada chaji
Jinjina kansa yayi yace" to bari Muje dasu salisu abi sawunta, "
Mayafinta tazara tace" maigida hankalina bazai kwanta ba Muje "
Fita sukai gaba dayansu, Mariya tatabe baki takoma daki
Da salisu da qannanta maza guda biyu dakuma umma suka tafi hanyar domin dubata
Kasancewar duhu yafara yasa suka fara haskawa, shiru basu gantaba, saida suka duba layin duka basu gantaba
Kamar wasa umma ta haska gefenta, taga baqi awajan Kamar abayar jikinta, sake haskawa tayi, gabanta yana faduwa, cikin sauri tayi wajan taga 'yarta ayashe aqasa
Salati tasaki cikin kururuwa tace "Innalillahi wa inna ilaihir raju'un Alhaji gata anan, ai suna jin haka sukai wajanta gaba dayansu
Jijjigata umma tafarayi amma shiru bata numfashi, lokaci daya umma tasaki kuka" alhaji munshiga uku bata motsi, Jijjigata tasake yi da karfi tace "Innalillahi..."NAWAL"
(sharhi da Comments dinku shine zaisa nagane cewa labarin yayi muku, harma nasamu qwarin gwiwar cigaba da turo muku, duk Wanda yakeso naci gaba da turo musu Dan Allah yayimin sharhi ko Comments 🙏🏻
Wanan karon kai tsaye muka dannu cikin labarin mu😇, labarin *Nidake* yanada yawa, mutum zai gane hakanne ta page din farko da mukai yau😘
Wacece _NAWAL_ ?
Yaya makomar su _Anwar_ ?
Mutara zuwa gobe
Amnah El Yaqoub ✍🏻
[1/25, 9:42 AM] Amnahelyaqoob: 🌺NI DAKE...🌺
(Hot luv story)
Writing by Amnah El Yaqoub
Deducated to *Itz* *sadeek*
5&6
"A a baba, ba za'ayi hakaba,kakawo ko rabi ne sauran saika biya daga baya"
"nace kuje kuyanke"
"to shikkenan baba, mude akan aikinmu Muke" haka sukaje suka yanke wutar yana kallansu
Daga qarshe ma tsaki yasaki yana tunani, da kudin da ake nema awajansa zaiji koda wata kudin wuta, su wutar ta dama, a wannan yanayin dayake ciki wutar nan bata gabansa🤣🤣
"Salamu alaikum barka da hutawa Abba, dafatan mun sameku lafiya"
Juyowa yayi ya kalli maiyi masa maganar yace "A a sultan, kaine akan hanya"
"eh Abba nine wallahi, Yaya jikin na Baby?"
"to sultan jiki da sauqi za'a ce, sunacan asbitin de, bamu samu munje bama, muna nan munata fafutukar yanda za'ayi"
Sunkuyar da kansa yayi, zuciyarsa nayi masa rad'ad'i, yace "Allah yabata lafiya"
"amin ya Allah, tashi mu qarasa gidan" Sultan yatashi sukayi cikin gidan
Da ummansa yafara tozali tayi tagumi hannu bibiyu atsakar gidan, mama mariya tanajin sallamarsu tafuto daga d'aki tace "Alhaji ansamu miliyan d'in? (🤣)
Abba yace" eh ansamu mariya, ai kinsan su kudin zuwa ake adebosu a'inda aka ajiye
"Alhaji daga magana sai baqar magana?
Kafin Abba yasake magana Sultan yayi Murmushi, cikin ransa yace wannan Gida de yana nan yanda yake bazai sauyaba
Ya tsugunna qasa yace" umma tah ina kwana? Yaya jikin Baby? Ajiyar zuciya tasauke "Baby jiki da sauqi Sultan"
sannan yamaida kallansa ga mama yace" mama mariya yaya muka sameku?
Cikin baqin ciki tace "gashi kuwa kaganmu, gashi kagani da idonka yanda kasamemun, aiba saika tambaya ba, tunda ni banida matsayin da zakace Dani ina kwana"
Shide baice mata komai ba yayi Murmushi kawai, yasaka hannu a aljihun wandon jeans din dake jikinsa yazaro kudi yamiqawa Abba yace "Abba Ga wannan basuda yawa, dubu dari da ashirin ne, ahada dasu akai asbitin"
Tun kafin Abba yace wani abu mama mariya tace "yanzu kaida Sultan kana da dubu darin kabarmu mukecin fara da mai🤣
Yace" to mama kuyi hakuri "
Yakalli Abba yace" Abba ina yaya Salisu ne Muje asbitin naga jikin nata?
"Salisu Tun safe suka fita shida Malam neman gidansu shi yaron da Nawal tafada mana"
"Ok bari na kirashi, daga can saimu wuce"
Abba yace "to Sultan Allah yayi maka albarka, Allah yaqara horewa
Yace" amin Abba "yayi qasa da muryarsa yanda babu Wanda yakejin meyake fada sai ita, yace" umma kiyi hakuri, insha Allah zamusan yanda za'ayi, Baby zataji sauqi insha Allah, ki kwantar da hankalin ki kinji "
Umma batace komai ba, kawai de ta daga masa kai alamar to
Yana fita yakira Salisu awaya yasanar dashi cewa su hadu agida, ba'a dade bakuwa saigasu akan _keke napep_ sun qaraso
Bayan sun gaisa da Malam yace" ya ake ciki? Kunsami yaron kuwa?
Salisu yace "inaaaa wallahi har yanzu de shiru,"
Yace "nifa yaya akwai abinda nake tunani amma _first_ mufara zuwa naga Babyn tukunna
Malam yace" to shknn Sultan Muje, dama yau bamu jeba, Tun safe Muketa abu daya "
Gaba dayansu suka dunguma sukai asbitin, suna zuwa suka tarar dasu nura, saif, da Najma azaune kowa yayi shiru, Salisu yace" A a yakukai shiru, ai zakusa tadinga tunani"
Saif yace "yaya idan munyi magana ma kyalemu takeyi tana kuka, Tun yaya Najma na bata hakuri harta dawo tayi shiru
Idananun Sultan sukai jajir, Ahankali ya furta Baby nah"
Aitanajin muryarsa tatashi zaune, tace "yaya Sultan,kaine kazo? ina kake?yaya yanzu fa shikkenan bazan iya ganinkaba ko?
Qwalla tacika idon Sultan, qiris yake jira yayi kuka, Ahankali yataka yaje har Inda take zaune agadon, tanajinsa kusa da ita tarungume shi tasaki kuka
Bubbuga bayanta yafara yi Ahankali yace" kiyi shiru kinji, insha Allah zaki warke, zaki warke kidinga ganin kowa, kiga umma da Abba da mama
Kinji ko Baby na?
Daga masa kai tayi, yace "to _smiling_ "
Murmushi tayi, yayinda hawaye yasake zubo mata
Yace "fadamin wanne Anwar ne yayi miki haka? Yaya kamanninsa suke?"
Tiryan Tiryan take zayyano masa kamanninsa, har abinda yahad'asu bata boye masa komaiba
Tana kai aya yace "shine wallahi, aikuwa zaici ubansa🙊🤣
Malam yace" Sultan kasan shine? "
" nasan shi Malam, Anwar ne yaron _Honorable_ Mai unguwa Saleh dogo "
Malam yace" Dan gidan Dan majalissa ne kenan "
Salisu yace" aiba Mai unguwa ba, ko megari ne, wallahi sai yasan yataba Baby,kawai kai tsaye mutafi _police_ _station_"
Malam yace "A a Salisu, Muje Zan yi magana da mahaifin yaron, ba zamuyi gaggawar kai maganar wajan yansanda ba, yakamata mufara yimusu bayani tukunna"
Sultan yace "hakan yakamata Malam, nasan gidan, kuzo mutafi, cikin ransa kuwa fata yake yaga Anwar,"
Basu bata lokaci ba wajan zuwa gidan,
Maigadi sukaiwa bayanin cewa sunzo ne wajan __Honorable_ yace wallahi baya qasar, yaje _Kuwait_ , amma zata iya yiyuwa yadawo yau
Sultan yace" Matar gidan fa, zamu iya ganin ta?
Maigadin yace "wallahi hajiya taje Abuja dazu, sai jibi zata dawo"
Malam yace "to zamu iya samun number wayarsa?"
Yace "mezai hana baba"
Yafada musu suka saka, sannan suka tafi, ahanya sukaita kira wayar akashe, saboda baya qasar
Har yamma suna gwadawa amma basu sameshi ba, dole Salisu da Sultan suka sake komawa suga ko yazo amma Maigadi yace musu baidawo ba, daga qarshe ma sai number Sultan suka bayar akan idan maigidan yazo saiya kirasu yasanar dasu
Gida suka wuce suka huta sannan suka koma asbiti gaba dayansu, dukansu azaune suke ad'akin datake, kowa yana janta da fira, suna kokarin ganin tasaki ranta tadena damuwa
Sai wajan karfe biyar Maigadi yasanar dasu zuwan _Honorable_, basu bata lokaci ba sukaje Gida suka dauki Malam, wannan karon harda Abba, suka tafi susu hudu
Suna zuwa kuwa Maigadi yamusu iso, har zuwa wani falo Dan madaidaici, sunkusa awa daya azaune kafin yafuto yagansu, Sultan kuwa sai sakin tsaki yake shi kadai, Abba yajuya ya kalleshi, shide aransa yana cewa baiso aka taho da Sultan ba🤣saboda yasan hali
Babban mutum ne, yaci manyan kaya harda Babbar riga, idan kaganshi saika dauka mutumin qwarai ne
Yana qarasowa garesu, yanemi waje ya zauna, Malam yatashi ya bashi hannu suka gaisa Abba ma haka
Yace "sannunku fa, kuyi hakuri nabarku kuna jirana, kunsan yanayin sai Ahankali, shi talaka dayaji kazo gari tofa babu zaman lafiya, andinga yin dandanzo kenan agidan ka"
Murmushi Malam yayi yace "gaskiya ne, muma akwai abinda yake tafe damu, shiyasa kaganmu, munzo munsake zuwa akace baka nan, to kuma yanzu Allah da ikonsa sai gashi mun sameka"
Yace "gaskiya ne, ina jinku meke tafe daku?"
Malam yace "akwai yaron wajanka waishi Anwar, sun samu sabani shida yarinyar wajan mu, hartakaita Ga marinsa, shikuma yaro daga baya maimakon yayi mata hukunci dede da irin abinda ta masa, saiya dauki shaltos ya fesa mata a idanunta, har hakan yakawowa yarinyar makanta, yanzu haka tana asbiti, bata gani kokadan, sannan likitan dayake kula da ita yace...
"Dan Allah dakata tsoho ✋🏻" _Honorable_ yakatse Malam cikin sauri.
Sannan yaci gaba da fadin "wai wanne yaro kuke magana akansa ne? Kuna nufin Dan wajena Anwar? To ni nasan waye d'ana, na kuma san irin tarbiyar dana bawa d'ana, nasan bazai aikata hakanba, kai kodama ace yayi mata hakan waye yaja? Kukukace ta mareshi, to Dan haka hukuncinta takarba dede da irin laifin data aikata, koma meyayi mata ai itace sila, wacce yarinya ce me tarbiya zata dauki hannu ta shararawa namiji mari, kai ni banma yarda cewa d'ana zaiyi hakaba, yaron dako zagi bai iyaba🤣😱
Nariga da nasan cewa maula ce kawai take tafe daku, "
Yasaka hannu acikin Babbar rigarsa yadauko kudi dami biyu yan dari biyar biyar ya watso musu
Sannan yatashi tsaye yace Dan Allah kufice kubarmin gidana, abinda kukazo nema gashi nan kunsamu
" amma kaikam badan arziqi bane, nika kalla ka watsowa kudi? "cewar Malam
Kafafunsa yadaga 🤷🏻♂yace" _And so?_ "
" aidama shi jahilin mutum basai anfada maka bama kana ganinsa zaka gane hakan, dame kake taqama? Siyasar? Da bazarmu fa kuke rawa, Inda bamu zabekuba babu Inda zakuje, "yanunashi da hannu👉🏻yaci gaba da cewa wallahi wallahi kaji na rantse kafadawa Anwar cewa yakiyayi haduwarsa da Sultan, shi yasanni nasanshi"
Cikin bacin rai _Honorable_ yace"nikake nunawa hannu saboda gidanku babu tarbiya? "
Sultan yana zaune yatashi tsaye, yasake nunashi da hannun👉🏻 yace" an nuna maka, kayi...
" Sultan"
Abba ya kirashi
Juyowa yayi ya kalli mahaifin nasa, baiso yakatse shiba , idanun Abba sunyi jajir, tunda aka fara maganar shida Salisu basuce komai ba, Abba Yakalli Sultan yace
"wuce mutafi Gida"
Share🙏🏻
Comments 🙏🏻
Sharhi Dan Allah 🙏🏻😢
Me kuke ganin zai faru zuwa nan gaba?
Anya kuwa _Honorable_ Saleh dogo baiyi kuskure ba?
Muhadu zuwa gobe insha Allah
Mrs Usman ce ✍🏻
[1/25, 9:42 AM] Amnahelyaqoob: 🌺NI DAKE...🌺
(Hot luv story)
Writing by Amnah El Yaqoub
Deducated to *Abubakar* *Abdulbasir* Wanda akafi sani da *Itz* *sadeek* ,wannan shafin nakane, halalinka ne katurashi duk Inda kakeso😃🤗, Allah yabar zumunci
3&4
Cikin kuka umma taci gaba da fadin, "Alhaji shikkenan an lalatawa Nawal rayuwa, anyi mata pyade, Innalillahi ni safiya mezancewa ubangiji na akan amanar daya bamu akan 'ya'yanmu"
Lokaci daya kan abba yasara, yace "Innalillahi wa inna ilaihir raju'un,"
'yarsa dayakeji da ita, kuma yake sonta fiye da kowa acikin 'ya'yansa itace yau aka lalatawa rayuwa
jiri-jiri yafara ji, kafafunsa suka fara rawa nan danan yatafi zai fad'i aqasa, daqyar Salisu yataroshi yafadi ajikinsa
Yace" subhanallah sannu Abba "
Shi kansa salisun jikinsa rawa yake, wannan wacce irin masifa ce tasamesu yau?
Saida abba yadauki minti biyu azaune sannan nutsuwa tafara dawo masa, amma bai daina maimaita kalmar Innalillahi ba acikin ransa
Su kuwa sauran mazan guda biyu shiru sukai sun kasa magana kowa yana ganin ikon Allah
Umma tashare hawayenta idonta tafara janye abayar jikin Nawal zata duba wajan🙈😳
Ganin akwai qannanta awajan yasa yadubi Salisu yace "Salisu dauketa Muje Gida"
Cimak yadauketa yasata a qirjinsa Kamar yadauki jariri yayi gaba duk jikinsa babu laka, sannan suma suka biyoshi abaya, umma sai share hawaye take da gefen mayafinta
Najma ce tafuto daga Gida sanye da hijabi a jikinta dogo,zata tafi makarantar dare, tana ganinsu fuskarta tasauya alamar tashin hankali qarara
Tanufi Salisu tace "yaya Salisu, meyasameta?"
Kasa bata amsa yayi, yawuceta yashiga Gida, suma su umma sukabi bayansa
Daya daga cikin qannansu tayiwa magana "Nura meyasami Baby naga yaya yadaukota ahannu?"
Cikin sanyin jiki yace "wallahi acan layin muka tsinceta ayashe aqasa, amma naji umma tana cewa wai anyi _Raping_ dinta"
Hannu tasa abakinta tareda zaro ido waje🙊😳
Bata sake saurarensa ba tafasa zuwa makarantar tayi cikin Gidan
Mariya najin shigowarsu tafuto tana daura zani duk sukai falon umma, abba yadubi umma "safiya jeki dubata kigani, Allah yasa ba abinda muke tunani bane"
"Alhaji me za'aje aduba ni Mariya, karde garin karatun nan Baby taje tadauko mana abin fad'a acikin unguwa"
Babu Wanda baiji ciwon maganar taba, haka sukai shiru suka qyaleta
Umma ta shiga daki tafara dubata, saida ta cajeta ciki da bai sannan tasaki sanyaiyar ajiyar zuciya, tafuto falon nata tace "Alhaji babu komai, lafiyarta kalau, banga wata alama ta nuna cewa any mata pyade ba"
Gaba dayansu suka Dan saki ransu, kowa sai cewaa yake Alhmdlh
Abba yace "Nura dauko ruwa ashafa mata, da alama tayi doguwar suma ne"
Nura nakawo ruwa dukansu sukayi cikin dakin umma, abba ne da kansa yashafa mata Ruwan, yaji shiru batai motsi ba, yasake tsiyayowa medan yawa yashafa mata
Sai a sannan taja dogon numfashi tasaki ajiyar zuciya "nace kuyi hakuri, hakuri fa nake baku, Dan Allah Karku cutar da rayuwata,"
Abba yace "Nawal bude idonki, nine abbanki, kiyi nutsu kidena kuka, babu abinda za'a miki, bude idonki 'yata"
Bude idanunta tayi,tafara kalle kalle Kamar me neman wani abu, saide bata ganin komai, asalima duhu take gani qirim, hannu tafara meqawa tana tattaba jikinsa tace "Abba bana gani, bana ganinku Abba, Abba ina ummata take... Sai hawaye zirrr
Abba yace" Innalillahi wa inna ilaihir raju'un "
Najma ce ta matso tafara jijjigata tace" Baby meyake faruwa? Meyasami idonki?kibude idonki dakyau, munefa agabanki, Ga mama Ga umma Ga yaya Salisu gasu Nura da Saif"
"nashiga ukuna ni Nawal, Najma bana ganinku, duhu kawai nake gani, shikkenan Anwar yacuceni, tsakanina dashi saide Allah yayi mana sakayya"
Ta kifa kanta agwiwarta tana kuka, dogon gashinta me santsi tuni yayi bankwana da ribom din jikinsa, sai gashin nata yasamu damar barbajewa agadon bayanta
Tunda tafara magana umma takasa cewa komai, kawai hawaye ne yake zirara daga idonta
Abba yadubeta "Safiya Dan Allah kidena wannan kukan,"
"ke Nawal fadamin wayene Anwar? Menene yahadaki dashi?
" Abba shine yafesamin shaltos a'idona, shida abokansa, "
Salisu yace" Innalillahi shaltos... Ki fadamin Dan gidan uban wayeshi, wannan wanne irin rashin imani ne?
Abba yadubeshi yace "kai Salisu dauketa Muje asbiti, daga baya maji abinda yafaru, mu gaggauta kaita asbiti yanzun"
Cimak Salisu yadauketa suka futo daga dakin, jikin kowa asanyaye, Najma tuni tafara kuka, yau yar'uwarta ce babu idanu,waye wannan Anwar din datake magana akansa?
Abba yace "saif kaje gidan Malam kafada masa abinda yake faruwa, mu zamu wuce asbiti, saiku samemu Acan"