Showing 51001 words to 54000 words out of 72369 words
Chapter 18 - Ni Da Ke Book Complete Document by Amnah El Yaqoub --.txt
Dan Allah kiyi hakuri, ummi itama na bata hakuri, kuma tace tayafemin "
" A a ni Al'amarin Nawal ai nasan ba kalau kabarta ba🤔"
Murmushi yayi, baice mata komai ba
Takalleshi taga har yanzu Yaqi hada ido da ita, ciki ranta tace "um su Baffah yau yaushe 🤣, waishi ma nan ya girma
Dagowa yayi ya kalleta suka hada ido, yayi saurin sunkuyarda kansa 🤣🤣
Murmushi tayi tatashi tsaye tace" to inka gama jin kunyar Umminka sai anjima nina tafi nahuta "
Saida yayi Murmushi sannan yace" Ummi idan kin futo Zan baki wani labari "
"labari kuma?"
Miqewa yayi tsaye shima yace "yes, dangane da Baby"
Murmushi tayi tace "to masu Baby, harka saka mata suna kenan"
"Ummi ai shiyasa nace Zan baki labarin, kede saikina futo" yana fadar haka ya yi dakin da Nawal take ciki
Ummi tayi sauri tace "Baffah dawo, babu Inda zakaje🤣🤣kai likita ma yace abarta tahuta, inso samu nema surutu ma kar amata🙊🤣
Murmushi yayi ganin yanda Ummi take kaffa kaffa da Nawal yace" Ummi sallama zanyi mata kawai zanfita unguwa ne "
Tace" to yanzu naji zance, yi sauri kafuto minti biyar "
Yace" to Ummi sannan ya shige dakin"yana shiga yahaye gadon shima ya kwanta, ya janye Bargon daya rufa mata, Ahankali ya janyo ta jikinsa tareda dora kansa agefen wuyanta
Bude idonta tayi ta kalleshi, cikin sauri ta sunkuyarda kanta qasa, gaba daya yasaka ta a Kirjinsa yahanata motsi
Cikin rada yace"natasheki ko? "
Shiru tayi masa, gaba daya ya yi mata kwarjini, gashi ya qaqumeta yahanata katabus
Ahankali yadora bakinsa akan kunnenta yafara lasa
Wani iri yarrr taji a jikinta, cikin kunnanta yace" please fadamin yaushe kika fara son mk?, ya maida idonsa kan kirjinta yazuba musu ido yace "bani nasha"
Kallansa tayi yace abashi labari yasha amma kuma idonsa yanakan nono
Ahankali tadanyi baya kadan, yasake janyo ta jikinsa yace "inajin ki"
Ahankali tace masa "saika fadamin yaushe kasan sunan Baby"
Murmushi yayi, yadora hannunsa akan gashin idonta yafara shafawa, Ahankali ta lumshe idon, yaci gaba da shafa mata idonta, sannan cikin rad'a yace "inbaki labarin kinason ji?"
Ahankali ta d'aga masa kanta
(mk kode ya Manta Ummi tana jiransa ne😱)
Duk yanda kukaga nayi posting Dan Allah kuyi hakuri kuce sannu 🤣, ni kaina banso na tsaya anan ba wallahi, amma kuyi hakuri da ace banyi posting ba gara ku samu ko yaya ne, inajin dadin yanda mutane sukemin sharhi wallahi, babu abinda zance da masoyan ni dake sai godia, nagode mgode naagode sosai 🙏🏻🙏🏻
Mrs Usman ce ✍🏻
[2/11, 6:27 PM] Amnahelyaqoob: 🌺NI DAKE🌺
(Hot luv story)
Writing by Amnah El Yaqoub
Dedicated to Itz sadeek
39&40
Cikin nutsuwa yafara cewa "Tun lokacin dana ganki mai machine ya kad'eki
Sainaji Kamar ni aka kad'e, abinda yafi bani mamaki yakuma yad'auki hankali na shine yanda aka kad'ekin amma kuma kika tashi kika tafi batare dakin yi masa fad'aba kamar sauran mata, wannan ne yaja hankali na gareki naji kinbani tausayi, nafara tunanin dududu ma nawa kike dazaki d'orawa kanki wannan abubuwan, nafara tunanin anya za'a samu Mai hakuri Kamar ki kuwa a yanzu?
Naga Wanda ya bigekin yana kokarin tafiya batare daya kaiki asbiti andubaki ba, nafara yimasa magana amma inaa har yaja yatafi, nawaiga kozan ganki kema naga Babu ke kwata kwata, banji dadi ba a lokacin, mukaje wajan gaisuwa, har muka dawo ina waigen hanyar dana ganki
Yakalleta cikin ido yace"tundaga lokacin nafara tunanin ki, gashi ban ganki ba, saide lokacin da aka kad'eki kince wayyo kuma abinda kikasa a fuskarki yad'an yaye anan naga lips dinki, dakuma sunanki danaji wasu yara sun ambata, nafara qarya ta kaina cewa ina sonki, kawai tausayinki yasa nake tunanin ki, daga baya de abu yaci gaba harna fara mafarkin ki, still ban yarda ba nabarshi a tausayi, saida Ummi ta auramin Nawal,🤣 anan nashiga tashin hankali, kuma nasan cewa lalle inason Baby
Kullum saina tunaki, zuciyata bata samun nutsuwa idan banyi tunanin kiba, tunanin kine yasa nakasa kwantar da hankalina inkula dake, naje wajan limamin unguwar nan shima yabani shawara akan nayi hakuri naso mata ta kuma nabada bincike akan Baby
Tundaga lokacin nasa yasir Abokina yafara yimin bincike akan Baby, nikuma na shirya natafi saudia nayi addu'ah akaan Allah yabaiyana min ke, ashe bansaniba kece kike tare Dani, ashe dake nake tare harna bata lokacina wajan kiran Mai zane yazanamin ke, nasan cewa nashiga haqqinki amma pls kiyafemin, yayi qasa da muryar sa yace "kinji?"
Kai tsaye ta jefo masa tambaya a maimakon amsa "dama kana surutu haka?"
Murmushi yayi yace"ina yiwa Ummi, sannan Inayiwa Nawal lokacin da kishinta yakama ni nakira Mai sunan saurayinta nadinga zuba masa surutu akan ya wanke min motocina duk Dan taji haushi 🤣, saikuma Baby nah dazan zauna inyi ta miki zance idan kinaso"
Itama Murmushi tayi, tace "Sai yanzu nagane ma'anar zoben nan guda biyu Wanda aka sakawa kowanne harafin B ajikinsa"
Yace "yes Baffah & Baby, means BB, wato har bincike kikai adakina bayan qone kayan?"
Rufe idonta tayi, da hannunta 🙈tace"kayi hakuri, shawarar qawata nabi "
Yace" nadade dayafe miki Baby nah, yanzu bani labarin mk "
Kafin tafara bashi labarin suka jiyo alamun tafiya a kofar dakin, anqi ashigo amma kuma sai taku ake agaban dakin🤣🤣
Zaro ido yayi😳 yace" Ummi ce wallahi namanta, "yayi sauri yaduro daga gadon
Yanda yasakko din har daria yabata 🤣
Futowa yayi daga dakin aikuwa saiga Ummi a kofar daki tana safa da marwa ta kuma kasa shiga🤣🤣
Ta kalleshi tace" Baffah yadaga baka minti biyar ka shanyani awaje sama da Rabin awa😒"
Kansa ya sunkuyar yace" Ummi kiyi hakuri wallahi namanta 🤣"
Tace" Baffah, Baffah, Baffah nakiraka sau uku kabar yarinyar nan tahuta, likita yamin kashedi cewa abarta tahuta Baffah, karnaji karna gani Baffah 🤣"
Daria ta bashi, wai shine yazama haka awajan Ummi 😀, kansa aqasa yace" Ummi insha Allah bazakiji komai ba "
Tace" to shikkenan, nina tafi da kina, "
Dadi yaji har ransa, yace" to Ummi afuto lafiya" 🤣
Saida yaga tafiyar ta sannan ya koma cikin dakin, a lokacin har bacci yafara fizgarta, Ahankali ya janyo ta jikinsa yace"tashi yarinya ai baki isaba saikin bani labarin mk tukunna "
Ahankali ta bude idonta tace" mk, nikuwa nice Zan baka labarin mk 🤣🤔, in fadama a Sanadin neman mk Babu irin azabar daban shaba🤣"
Nide Tun a asbiti danaji kana magana da Abba nah lokacin daka biya mana kudin aikin idona, tundaga lokacin narasa gane kaina, nide fatana kawai naganka koda saudaya ne arayuwata, gashi baabu idon ganin ka, nasa Najma ta ganomin kai tacemin ai itama bayanku tagani, baabu yanda na iya haka na hakura, damuka dawo daga qasar waje nasamu number ka awajan Doc. Nakiraka a lokacin da aka sakoni agaba agida akan na auri Nuhu, narasa ya zanyi, dole tasa ta nemeka, da nufin in fadama cewa agida za'a bani wani amma inaso kazo kayi magana da Abba nah, akan yabar maganar Nuhu, tunda shi idan yaganka zai ganeka, kuma zaiji nauyin yimaka musu, amma ina kiranka kahauni da fada kace na yiwa iyayena biyaiya, daga qarshe ma kakashemin waya "
Dasauri ya kalleta yace" wai kece? "
Daga masa kanta tayi, yace" Innalillah... Ashe ni a lokacin abnda nadade ina nemane yazo har gida yasameni amma nayi watsi dashi? Kiyi hakuri Baby nah, a lokacin raina yabaci ne, bana amsa waya cikin week end, amma kuma ke kikai takira harkikasa na karya dokata 🤣"
Tace" Babu komai, sannan taci gaba da fadin, banida niyyar in fadawa d'a namiji cewa ina sonsa, amma saboda matsi dana samu agida kuma naga da gaske de za'a Auramin Nuhu, hakanne yasa nake nemanka ido rufe, amma narasa ka, har wataran qawata Nasrin zasuzo Abuja biki itada qanin ta nabiyo ta muka zo da nufin zamu nemo mk muyi masa bayani, har biki yakusa qarewa bamu samekaba
Qarshe de munje wajan dinner na futo waje naga wasu motoci suna wucewa sai naji wasu samari dake gefena suna cewa mk yashigo gari, daganan hankalina yatashi muka tare adedeta mukahau, yace mana bazai hau Babbar hanya ba, duk da haka muka ce mude yabi damu tako'inane, kawai fatanmu mutaro motocin dake gabanmu, wallahi ina fad'ama kawai sai adedeta tafadi aqasa😳🙆🏻daqyar aka ciromu daga ciki🤣
Wata irin daria ce tazo masa wadda bai shiryaba 🤣yadinga daria, ta zuba masa ido tana kallansa, itade tunda take dashi bata taba ganin dariyar saba, ya kalleta cikin daria yace "duk saboda neman mk din ?
Cikin shagwaba tace" shine kakemin daria ko? "
Tafara kokarin juya masa baya, Ahankali yasa hannunsa ya juyo da ita yace" kiyi hakuri nadena, shikkenan? "
Amma please ki fadamin waye yazuba miki shaltos a idonki? "
" wallahi wanine sunansa Anwar, amma ai komai ma yawuce, Tun a lokacin ma nace nayafe masa
Koba haka bama tunda shine yayi silar haduwata da mk ai kaga dole nayafe masa "
" Kamar yaya mekike nufi? "
" haduwa nayi dashi a makaranta, har mukai karo wayata ta fashe, anan nahadu da Ummi, ranar dana fara ganinta kenan, tadinga bani labarin Baffah ahanya, a raina nace gaskiya ta nasan wannan Baffan kowaye "
Jinjina kansa yayi yace" kin tabbatar kin hakuran komai yawuce? "
Tace" na hakura, nayafe masa "
" Baby anya kuwa bazan cutar dakeba? "
" mekake nufi? "
" Baby hakurinki yayi yawa, sainaga Kamar Zan shiga haqqinki azaman da zamuyi nan gaba "
Turo d'an qaramin bakin ta tayi gaba tace" nide Dan Allah kadena wannan maganar, to menene? "
Lips dinta ya kallah, yamatso da fuskarsa zuwa tata fuskar sajensa ya goga mata awuyanta yace" to shknn nadena, ina son lips dinki Baby, yana birgeni sosaai, arayuwata ina son baqar mace, amma zuwanki cikin rayuwa ta ya sauyamin komai, i luv u"
Tace"nagode "
" ba godia zakimin ba "
" tome zanma? "
" abinda mata takewa mijinta idan yace yana sonta "
Tace" menene abin? "
" in nuna miki? "
Daga masa kai tayi alamun eh,
Yace" to rufe idonki "
Babu musu tarufe idonta
Yana ganin haka yadora bakinsa akan nata
Dasauri ta bude idonta tareda qwace bakinta cikin shagwba tace" Allah nifa akwai zafi pls kabari "
Shagwabar tata tabirgeshi sosai, wai irin dadi yakeji aransa, daga qarshe de ga Baby Akwance a qirjinsa 🤣
Batare dayayi mata magana ba yayi Murmushi kawai tareda cigaba da abinda yafara
*** ***** ***
"haba bawan Allah, ya kana ganin mutane da kaya niqi-niqi ahannu amma katsaya akan hanya duk ka babbake wajan, idan baka temaka ka karba ba, aibaka tare hanya bako? 🤔
Tab to aishi Tun dazuma dayake Kallanta daga nesa baisan harta qaraso wajansa ba🤔🤣
Ajiyar zuciya yasaki yabata hannu yace"tokawo kayan "
Tace" A a, Barshi wallahi, dama kawai hanyar nake buqata"
Kai tsaye yace "to shikkenan, ga hanyar nan zoki wuce 🤣"
Cikin mamaki ta kalleshi,tace"wannan irinku ne bakwa yiwa mutum kara 🤣🤣
Inba hakaba daga cewa kabarshi saikace ga hanya nan? "
Yace" hanya kika nema, kuma nabaki, nace kikawo kaya na kince a a, danhaka ga hanya nan, kaya kuma idan kin gaji ki ajiye daya anan, idan kin kai guda dayan saiki dawoki dauki wannan din 🤣🤣"
Kafin tayi magana Nura yazo wucewa yace" yaya Najma wannan kayan kinfi minti talatin akansu🤣
Tace "to Nura ya zanyi?"
Nura yace"ke komai sai anmiki "🤣
Yakalli Yasir dake tsaye agefen ta ya bashi hannu suka gaisa
Daga nan yayi gaba yabarta anan, dama suna qarasa debe kayan gidan ne suna kai wasu maqota
Shima yasir ya kalleta yace" wallahi kuwa, injunin mutum san jiki ai saiyayi, nima kinga tafiyata nan🤣🤣"
Duk suka watse suka barta awajan, bayansa tabi da kallo ga mutum de har mutum amma ba zuciyar taimako, 🤣ta girgiza kanta taja kayan tayi waje
*** ***** ***
"Ummi Albishirinki"
Tace "goro Baffah"
"Ummi Nawal fa itace Baby nah"
"bangane ba Baffah me kake nufi, wacce Babyn taaka?"
"Ummi Baby nade danace miki ni ita nakeso, ita nake nema, ita nakeso nagani na aureta, kikace Idan naganta saina aureta daga baya"
"Baffah, kasan banasan qarya ko?"
Yace"Ummi da gaske nake wallahi, gatanan ki tambyeta "
Ummi ta kalli Nawal tace" yata wai hakane? Garin yaya hakan tafaru? "
Kafin Nawal tace wani abu yafara bata labarin komaai, har zuwa yanzu dakuma binciken dayasa yasir yayi masa akanta
Ummi tasaki ajiyar zuciya tace" ikon Allah, Baffah kaga amfanin biyaiyarka agareni ko? Amma Awannan ranar bana mantawa haka ka zauna kanata min kuka wiwi🤣
"haba Ummi Dan Allah, adinga tone tone dai 🤣
Tace" to alhmdlh, gaskiya nafi kowa murna wallahi, ubangiji Allah yaqara hademin kanku, yabaku zuria tagari nima naga yara agabana sunata wasa, har gidan namu yayi kyan gani, suzo suna cemin Ummi bamuda biro, Ummi book dina yacika asaimin sabo🤣"
Nawal najin haka tatashi Dasauri tayi cikin dakinta, cikeda kunya 🙈
Haka zaman su agidan Ummi ya kasance, koda yaushe tana samun kulawa awaajansu, Ummi bata sanya wajan gyarawa Baffah matarsa🤣, babu ruwanta da wata kunyar surukai, kawai jin Nawal din take Kamar 'yarta, kwananta uku ta warke ras, batajin ciwon komai, haka kuma har zuwa wannan lokacin Babu abinda yaqara shiga tsakanin ta da mk, domin kuwa Ummi takafa ta tsare
Akwana na hudun ne suna zaune a dakin Ummi dukansu, tace "Ummi inaso naje gida Dan Allah"
Ummi tace "haba Nawal, gaki ga mijinki, aishi zaki tambaya"
Juyawa tayi ta kalli Baffah tace "Dan Allah kaji?"
Cikin damuwa yace"yaushe ma akai auren dazaki fara fita? 🤣🙆🏻
Kawai kiyi hakuri next time sai Muje
Kamar zatai kuka tace "kaifa rannan kaje, Dan Allah kabarni naje kaji mai Babban suna"
Yace"naji, amma kwana biyu zakiyi kidawo, inba hakaba Zan biyoki "
Ummi ta kallesu a boye,taga alama sauda dama suna mantawa da ita awaje 🤣
cikin ranta tace oh ni Halima ina ganin duniya, aikuwa idan kuka dawo din saide ku wuce gidanku 🤣
Nawal kuwa cikin murna tace" yawwa Baffan Ummi nagode "
Yace" keko Hmm "
Murmushi tayi masa tareda hararar wasa, duk Ummi tana ganinsu, saide kawai yi tayi Kamar batasan mesuke ba🤣
Washe gari kuwa Ummi da kanta ta shirya mata tafiyar, tasiya mata kayaiyaki dayawa Kamar su yadi dasu shadda Wanda zata rabawa mutane, dakuma Wanda zata kaiwa yan gida, cikin sanyin jiki oga yarakata Airport da kansa tareda direba
Saida jirginsu yatashi zuwa kano sannan suka koma gida, ahanyarsu ta zuwa gida yakira yasir yace, atura mata motoci suje Airport su dauketa idan tasauka saisu kaita gida
Haka akayi kuwa, motoci hudu yasir yatura mata, Kamar wata matar Governor
Jirginsu nasauka kuwa suka dauki komai nata suka saka amotar, tana ganin haka tasan aikin Baffah ne
Kai tsaye gidansu suka nufa, amma suna zuwa layin gidan taga anrushe gidan anata aiki sosai, mamaki ya kamata, tacewa direba ya dakata daga nan kawai, basai sun qarasa kofar gidan ba, saboda Babu Inda Mota zata shiga
Umarninta yabi, ya dakata tasaauka, sannan suka biyo bayanta da kayaiyakin datazo dasu
Kamar wasa taganshi agaban ta, a yatsine ya kalleta yace "kaga yar Malam Shehu ansamu abinda akeso sai wani abu kike Kamar yar wani"
Murmushi tayi masa kawai tawuceshi batareda tace masa komai ba
Daya daga cikin direbobin da suka kawo ta yace, "Hajiya mekike buqata ayi masa?"
Tajuyo tace "ku rabu dashi Babu komai"
Shima cikin kuri yace "yoda meta isa tamin? ubana yana tsaya min akan komai, Mai unguwa saleh dogo"
Suma basu kulashi ba suka bita suka ajiye mata kayan ta, tareda Juyowa, su nura suna ganinta sukayo wajanta cikin murna
Su kuwa direbobi suka komawa wajan Mota, Wanda yadauko Nawal kai tsaye yakira mk awaya ya sanar dashi komai
Cikin bacin rai yace"shine yace muku shi yaron Mai unguwa ne? "
yace" yes Sir,namaji wani agefe ya kirashi da suna Anwar "
Ransa yaqara baci, matar tasa za'a ciwa mutunci? Kai tsaye yace" Am kanajina ko, ku dauko min shi kukawo shi Abuja yau "
Cikin ladabi yace" Angama Sir "tareda kashe wayar
(yau kam anyi typing 😇)
Amnah El Yaqoub ✍🏻
[2/12, 7:49 AM] Amnahelyaqoob: 🌺NI DAKE🌺
(Hot luv story)
Writing by Amnah El Yaqoub
Dedicated to Itz sadeek
41&42
Bayansa sukai tabi batare dasun kamashi ba, har saida sukaje layin gidansu,yana tsayawa maigadi yabude masa get zai shiga suma suka futo suka kamashi, dayake qarfafa ne nan da nan suka dagashi samah zuwa cikin motar su 🤣
Maigadi yace "Innalillahi, bayin Allah meyayi muku?" 🙆🏻♂Yakalli Anwar yace" kai Anwar mekayi musu? "
Cikin fada yafara cewa" dalla ni kusakeni, ku ajiye ni nace"!!
Basu kulashi ba kawai suka dannashi cikin Mota, driver ya kalli maigadi yace"Baba muma umarni aka bamu daga sama mutafi dashi "
Yana fadar haka ya shige motar, baba maigadi yabisu da gudu yace" Dan Allah ku tsaya, ku fadamin ina zaku kaishi? "
Wanda yariqe Anwar ya leqo yace" Wajan mk "
Baba maigadi yace" wanene kuma mk? Kunawa Allah ku sauko da yaron nan, "
Batare dasun saurareshi ba sukaja motar aguje sukabar wajan
Shima yadora hannu aka🙆🏻♂ yayi cikin gida yana qwalawa hajiya kira.
*** ***** ***
Ta kalli Saif tace"kai yanaga gidan duk ya haukace da gyara? Yaushe aka fara gyaran gida? "
Yace" au wai dama baki saniba? Naga mijinki ne yaturo ayi aikin "
" mijina kuma? To yaushe? Ni wallahi bansaniba kuma kaga shima bai fadamin ba "
" aikuwa Tun ranar dayazo washe gari akazo akaga gidan da irin gyaran da za'ayi masa "
Dakatawa tayi da tafiya tace" to yanzu ina zamu zauna? "🤔
Nura yace" kede kitaho mana, gashinan angama bangaren mama, anan muke kwana, amma Babu komai aciki, kawai sai kaya da katifu, sauran kayaiyakin suna maqota "
Tace" Ok yanzu naji batu"
Suna shiga gidan Najma tataho da gudu suka rungume juna, mama mariya tace"Baby mutanan Abuja sannu da zuwa "🤣
Tace" yauwa mama, ina wuni "
" lafiya kalau Nawal, saiki kazo kuma kika ganmu kaca kaca ana maida mana gidan namu na 'yan gayu "🤣
Murmushi tayi kawai, tafada jikin ummah
Ummah tace" to Allah yakawo mu kuma, shikkenan ke kullum bazaki girma ba Nawal"
Tace "Ummah na dade banganki ba, ina yaya Salisu? Yaya Sultan yaje rannan, har kaya yakawomin"
Ummah tace "to naji Baby, dagani kije kici abinci kihuta"
Najma tace"wallahi kuwa, tashi Muje "
takama hannunta suka wuce daki
Suna zuwa takawo musu abinci sukaci, Tun kafin su gama cin abincin takira Nas tace mata tazo, aikuwa nan da nan tace gatanan zuwa
Bayan sun gama cin abinci, tatashi tayi sallah
Bata dade da idar da sallah ba Nas tazo, anan suka baje kolin fira
Nas ta kalleta tace"Beauty gaskiya yanzu ne kike a Beauty, kin wani qara haske da cika, menene sirrin ne, me mk din yake baki? "
" Hmm mezai bani kuwa banda kulawa, ko daki natafi to shima saiya bini, wani lokacin har kunyar Ummi nakeji "
Najma tace" gaskiya dole kiji kunya kam, bazaka sakeba, amma