Showing 18001 words to 21000 words out of 72369 words

Chapter 7 - Ni Da Ke Book Complete Document by Amnah El Yaqoub --.txt

28 Dec 2024

8913

uba hakuri, Allah ya hore miki hakuri


kasancewar yana mura sai Jan hanci yake🤦🏻‍♀gashi babu tissue ahannunsa, kasan kana mura kuma zaka je wajan budurwa zance saikazo da tissue kodan handkerchief, 🤣🤣


yaci gaba da cewa saikuma Breast, Allah ya hore miki su nidama kuma inason na auri mace Kamar hak... Bai qarasaba majina tataho ta hancinsa🙆🏻🤦🏻‍♀🙈😩🤣


Tana gani tafara yamutsa fuska😣, zuciyarta tafara tashi, Nuhu wanne irin qazami ne, amai taji yataho mata, cikin sauri ta daakatar dashi tace "Nuhu Zan shiga Gida, aiki nake ka katseni," daga nan tayi wuf ta shige cikin Gida😂


Tana shiga Gida mus'ab Dan autan Mama Mariya yashigo yaje wajan ta yace "yaya Baby"


Tayi zatan abin arziqi zai fada mata tace "na'am mus'ab"


Yace "naga hancin Nuhu da majina 🤣"


Haushi yasa ta dafe kanta da hannunta🤦🏻‍♀tace "Mus'ab wuce kaban waje"


Sum Sum yaron yafice daga falon🤣
Tayaya ma zata auri Nuhu bayan qannanka ma sunsan halin qazantarsa


Da daddare taje wajan umma tace "umma kinada dari biyu kibani nasai kati Zan kira yan school dinmu 😱?


"kiduba gefen waccan kujerar kidauka"


Tace "to" sannan tadauka tafice daga gidan, kasancewar akwai shago akusa da gidansu nan danan tasiyo tadawo, yau umma a dakin Abba take, shiyasa ta bari saida tazo bacci sannan ta kirashi, amma abu daya ake fada mata shine layin bayakan waya🤦🏻‍♀


Tashin hankali ne ya bayyana afuskarta qarara, duk wannan murnar datake zata kirashi hakan yatashi abanza kenan? 🤔


Number Nasrin takira, bugu uku tadauka tace "Beauty ya kike yagida?"


"lafiya lau Nas zaki shiga school ne gobe?"


"eh Zan shiga insha Allah, meyafaru?"


"inaso ne zamuyi magana Mai muhinmanci, saimun hadu goben kawai"


"toba damuwa Beauty saimun hadu"


Kashewa tayi taci gaba da kiran number, saide takira yakai sau talatin, amma amsar de guda dayace, haka ta hakura tayi addu'ah ta kwanta bacci cikeda damuwa😖


Washe gari karfe tara ta shirya tsaf cikin hijabi dogo har qasa, fuskarta fayau babu kwalliya, sai powder kawai Data shafa, ta lakuci Vaseline tashafa a lebenta, sai pink lips dinta yayi mutuqar kyau sai sheqi yake
Wajan umma taje tace "umma natafi school"


Kallanta tayi, Kamar de tahanata amma sai tayi shiru ganin ta qwallafa ranta akan karatun "to saikin dawo"


Tana fita ta tsaya a kofar Gida har saida Allah yakawo Mai adedeta sannan tahau, sunzo dede Inda tahadu dasu Anwar tacewa Mai adedetan "bawan Allah yisauri Dan Allah," saboda jitake Gabanta yana faduwa sosai, Kamar zasu sake tareta




(in banda abinki suda basusan ki bama kullum fuska cikin niqab tayaya zasu ganeki🤔)


Cikin qaramin lokaci ta isa makaranta, Nasrin na jiran ta agaban hall din tana zuwa tace" Beauty yazuwa haka babu niqab?


"Hmm wallahi Malam ya hanani sakawa, Tun lokacin da abinnan yafaru"


"gaskiya ne Allah de yaqara kiyaayewa,"


Basufi minti ashirin da shiga hall dinba malami yashigo, aikuwa kowa sai Kallanta yake saboda basusan fuskar ba
Ita kuwa da tasan kowa ko a jikinta, har malamin yagama karatu yafara tambayoyi amma cikin maza ne kawai suke amsawa, mata sunyi shiru🙆🏻😳


Malami ya kalli wajan mata yayi musu wata tambayar nanma shiru 😳, aifa karkaso kaga ido wajan maza,Nasrin tayi qasa da murya tace "nikam babu abinda nafahimta wallahi, bazan daga hannu nabada amsa ba daidai ba, ke Beauty inkin sani kifada masa


" nasani Nas, amma wallahi tsoro nakeji, gabana faduwa yake, banaso ayita kallo nah


"lalle Beauty aikuwa yin shirunki shine zaisa adauka mata jakai ne wallahi"


Malami yaji shiru yasake cewa babu amsa?


Cikin faduwar gaba tadaga hannu, aikuwa sai ido yadawo kanta


Malamin yace "inajin ki"


Maimakon ta bashi amsa saita tata shi taje wajan sa ta karbi makar hannunsa tariqe shide yanata ganin ikon Allah, bayani tafara yi da baki, amma kokadan taqi kallan bangaren maza🤣


Hall yayi tsit, kowa ita yakeji, sosai tayi bayani sannan tafara rubuta example, tana sake yin bayani, dukda muryar ta tana danyin rawa haka de tadaure tayi
Tabawa malamin makarsa, aikuwa me za'ayi inba ihu da tafi ba, sosai ta birge kowa, saboda ba kasafai ake samun mata masu irin wannan jajircewar ba


Tana zama wata dake bancin bayaansu tatabota tace "Nawal ga wani abokina yaturomin text yanzu wai yana sonki 😳"


Kai ana budiri a jami'ah🤣🤣Ga malami a aji amma wasu saqon soyaiya suke turawa




Murmushi kawai tayi mata batare datace komai ba, suna fita daga lacture Nasrin tace" Beauty yau kinyi kokari, kin bawa kowa mamaki, inajin ki wacce magana kikeso muyi? "


Cikin nutsuwa tace" Nas nakasa cireshi araina "


Zaro ido Nasrin tayi cikin murna tace" wow, yau Beauty anfada soyaiya, fadamin waye shi? "


"MK"


Mamaki yakama Nasrin, "wai kina nufin mutumin daya biya kudin aikin ki?"


Daga mata kai tayi, idonta na kawo ruwa 🥺


"to dama kin hadu dashi ne Acan qasar da aka miki aikin idon?"


" ban hadu dashi ba, Tun lokacin danaji yana magana da baba nake tunanin sa, naji kawai yana birgeni duk da banganshi ba, nafada wa Najma tacemin wai qilama yanada aure, yafi karfina, narabu dashi, wai ko a 'yar aiki bazai daukeniba 😭, nasamu number sa awajan baba danaji yace zai kirashi yayi masa godia, shine nasaka number a wayata nadinga kira jiya taqi shiga, karshema layin bayakan waya haka aka nunamin, Nas ina sonsa wallahi, koda ace yanada mata wallahi Zan iya zama dashi, koda shi bayasona ni ina sonsa, ki temaka kiban shawara, Yaya zanyi? "


Ajiyar zuciya tasauke, ta saka hannu ta goge mata hawayen idonta" kiyi hakuri Beauty insha Allah, Allah zai kawo mana mafita, kinsan garin dayake ne?


"A a Nas bansaniba"


"Ok kinde san likitan dakuka je Albania tare dashi ko?"


"eh nasan shi Nas"


"yaya sunansa?"


Nawal tace "doctor babangida"


"shikkenan kiyi hakuri, yanzu tunda bamuda wata lacture tashi Muje"


Kallanta tayi "ina zamuje Nas?"


Kai tsaye tace mata "Asbitin Malam Aminu"




*** ***** ***


Kasancewar Abba yana gidan Malam shiyasa kwata kwata bai nemi Nawal ba, kuma yasan cewa safiyya bazata barta taje ko'inaba harsai yayanke hukunci akanta.


Malam ya kalleshi yace "muhammadu ya ake ciki dangane da karatun su Nura? Yaya kukai da mutumin?"


Abba yace "Malam nakira wani abokina dayake koyarwa a A.B.U zaria, nayi masa magana akan yarana maza guda biyu dasukai candy bana, inaso ya temaka ya nema musu admission, yakumace insha Allah zaiyi kokari yaga sun samu gurbin karatun, sannan yafadamin kudin registration dinsu,saboda haka naqara dubu talatin akan nakowaccee shekara incase ko zasu iya qarawa, na turawa Sultan kudin registration din Nura da Saif gaba daya na shekara hudu, nikuma zanci gaba da daukan nauyin kudin Mota dana abinci da sauran abubuwan buqata, amma maganar kudin registration de idan lokaci yayi sai suje wajan Sultan, saikuma Najma idan anfara yin jamb saita sake rubutawa itama idan Allah yasa taci jamb din saita shiga B.U.K
Ita kuma zan turawa Salisu nata kudin registration din, itama idan lokaci yayi sai taje wajan sa ta karba


Malam ya jinjina kai yace "muhammadu kayi tunani Mai kyau, amma ita kuma Nawal dinfa? Banji kayi maganar nata karatun ba"


"Malam ina sane da ita, akwai abinda nake tunani akanta tukunna"


Malam yace "to alhmdlh,wasu mutanan suna dauka haihuwar 'ya mace wahala ce, amma basusan ta Sanadin ta zaka iya samun alkhaairi ba, kagade abinda yafaru Ga Nawal, gashi Sanadin ta yanuwanta ma zasu tafi makaranta, yanzu de abinda Zan fadama shine, kaje kasa afara gyarama gidanka, sannan filinka daka siyar kanemi wani kasiya kamaida abinka, sauran kudin kuma saikaci gaba da amfanin yauda gobe dashi"


"to Malam insha Allah, daga nanma Zan wuce wajan masu saida kayan gyaran asiya akai gidan inyaso sai afara gyaran dawuri, sannan kaima Zan turo maka wani kudin, Zan qara dubu Hamsin akai asayi abin sadaka ayiwa wannan bawan Allah, Dan yaron nan daga ganinsa yana buqatar addu'ah "🤔🤣


Murmushi Malam yayi,cikin ransa yace" kome yagani a tattare da yaron yake cewa yana buqatar addu'ah?


Afili sai yace "to muhammadu, Allah ya shige mana gaba, nagode"


Daganan sukai sallama Abba yatafi




*** ***** ***




Cikin Murmushi yace "A a Nawal yanmata yau kece a office din namu"


"eh wallahi doctor nice ya ayyuka"


"aiki da godia, ya wajan Abbanki? “


" yana nan kalau, "daga nan tayi shiru
Nasrin sai zungurinta take amma takasa magana sai shine yace" meke tafe daku ne, ko zuwa kukai mugaisa "


Tace" am likita dama... Dama.. Munaso kafada mana garin... Ganin taana neman yimusu 'baran' 'barama ta zubda ajin mata 🤣🤣yasa Nasrin tace "doctor jiya wai Abbanta yazo yakarbi number wannan mutumin awajan ka, to shine suka dinga kira taqi shiga, shine tacewa abban nata zatazo da kanta wajan ka idan kanada wata number kabamu". (kai kai zuri😱🙈)


Murmushi yayi yakalli Nawal "kinaso ku gaisa ne kema?"


Murmushi tayi batace masa komai ba, yasake cewa "ai hakan yanada kyau kinsan manyan mutane may be baya qasar ne shiyasa baku sameshi ba (fada matade🤔)
Yaci gaba da fadin" Amma gaskiya banida number sa, wannan dinma awajan shugaban asbitin nan nasamu, "


Nas tace" ikon Allah, toshknn doctor mungode, amma shikam awanne garin yakene? "


Yace" wallahi bansaniba, amma akwai abokin aikina dasuka fita germany gyaran kafar wani yaro Wanda shi wannan yaron qanin abokin shi mk dinne saide na tuntubeshi naji ko yasan Dan inane"


Cikin murna tace "to Doc. Mungode"


Wayarsa ya janyo yakira dayan likitan yasaka ta a handsfree yanda zasuji komai, ana dagawa yace "abokina ya ayyuka?"


"aiki alhmdlh wallahi gashi muna ta fama"


"masha Allah, dama akwai wasu bayin Allah ne sun kira number mk basu sameshiba shine suke tambaya wai shi din Dan wanne gari ne? Shine nace saide na tambayeka tunda kunyi tafiya zuwa germany kaida abokinsa, ko zakasan wani abu daya danganceshi?"


"eto gaskiya abinda nasani shine naji abokin nasa yana fadawa qaninsa cewa shi mk din Dan Adamawa state ne, cikin garin yola, amma yana zaune a Abuja, saide mafi yawan harkokinsa yana gudanar dasu ne a qasar Dubai, amma baya cikakken sati biyu baizo Nigeria ba, maganar waya kuwa naaji yana cewa sai ranakun aiki yake amsa waya 😳🙆🏻, idan ba week day neba baya amsa waya saide in shine ya nemeka "


Yace" to shknn mungode, sai anjima "


Yana kashe wayar yadubesu yace" to kunji,"


Murmushin yaqe Nawal tayi" tace toshknn likita mungode, insha Allah zamu fadawa abban, ngd "


Yace" toki gaishe shi nagode sosai "




Fitowa sukai daga office din jikinsu a sanyaye, ta dubi Nas tace" Nasrin mutumin nan yafi qarfina, sai hawaye sharrr "


" haba Nawal, ya zaki karaya Tun yanzu? "


" Nas kinajifa abinda akace akansa, yana wata qasa, idan yazo Nigeria ma sai Abuja, nida ko hanyar Abuja ban taba biba" 🤣


"ki kwantar da hankalin ki nace, akwai bikin wata yar'uwarmu da za'ayi a Abuja, zamuje bikin, kawai ina ganin ki shirya mutafi tare, insha Allah zamu hadu da shi"


Hawayen idonta tashare, "Nas kina ganin babu damuwa kuma agida za'a barni?"


"mezai hana, zanzo gobe da kaina nayiwa umma da Abba lissafin karya kawai saimu wuce🙊🤣"


"to shikkenan Nas saikinzo"


Haka suka futo daga asbitin tana qara kwantar mata da hankali




*** ***** ***




Tana zuwa kofar gidansu taga yashi dasu siminti dayawa an jibge, Data shiga gidanma duk suna nan atsakar gida tayi sallama tareda cewa"umma nadawo, ta kalli mama mariya tace mama nadawo "


Atare sukace to sannu


Hijaabin jikinta tacire taja kujera ta zauna tana cewa wash Allah, Saif daya futo daga daki yaja ribom din kanta, kasancewar babu kitso sai gashin nata yazubo agadon bayanta yace" yaya Baby yalasha "


" Saif banaso, inba idaan aljannu na suka tashi ba zakaji dadiba "


Yace" yasin su tashi, muda muke da Malam "


ta kalleshi tace "ina Najma?"


"tana daki tana Zumba"


Cikin sauri ta tashi tace"a a nima natafi "ta shige dakin mama mariya


Wata tsohuwar computer Salisu ce agabanta ta qure wakar zumba tana gani tana rawa
Itama kuwa ta shige sukaci gaba


(zumba wata rawace da masu qiba sukeyi domin motsa jiki, idan kana yawaita yi qibarka zata ragu, idan bakada qiba kuma tana qara futowa da mutum shape dinsa musanman mata)


Har wajan azahar suna abu daya, sannan sukaje sukai wanka saboda gumi dasuka hada




*** ***** ***


Washe gari kuwa Nasrin tazo gidan, da Abba tafara haduwa a kofar Gida shi da masu aiki suna kwaba siminti, ta gaishe shi ya amsa mata, tace Abba dama wajan ka nazo kaida umma "


Cikin mamaki yace" to inajin ki me yafaru, Allah yasa de lafiya, "


" Abba dama biki zamuje Abuja nidasu mamata, shine mama tace nazo na tambayeku tanaso mutafi tareda Nawal "


(😃🙊Nasrin Allah ya hore miki)


Abba yayi jim yana tunani sannan yadubeta" to kwana nawa zakuyi? "


" kwana biyar "


Yace" to shknn Babu damuwa, idan tafiyar ta tashi saiki zo kutafi "


Cikin murna tace" to Abba mungode, daga nan ta shige gidan, tana bawa Nawal labari tahau murna tana kuma fata Allah yahadata dashi


Saida Nasrin tawuni sannan tatafi Gida


Cikin satin kuwa tafiya ta kankama🤣, Umma tace nide Baby ki nutsu karkije ki dinga yimusu sakarci agida, sannan kuma kidinga saka kayan mutunci banda zama da qananun kayan nan"


"to umma insha Allah, Abba yazo har dakin yabata dubu sha biyar, ta karba tana godia shikuma yafice umma ma tabi bayansa, Najma ce tashigo dakin tace" Baby mutanan Abuja, 🤣🤣yau kuma sai Abuja "


Tace" wallahi kuwa, Abuja Kamar munje "


Najma ta kwashe da daria," to yaushe ita Nas din zatazo? "


" tacemin tana hanya, zatazo mutafi, amma sai munje gidansu, da yamma kuma zamu dauki hanya "


Najma tace" to mude tunda munbaki shawara kinqi dauka bamace komai ba "


" Najma kekike nufi? "


" A a Babu abinda nake nufi Baby, kuda zakuje kusha biki, amma inaso kisani Tun muna yara tare muka taso dake, banda umma Babu Wanda yasan halin ki sama Dani, haka kema kinsanni kinsan abinda Zan iya da Wanda bazan iyaba, saboda haka Babu abinda zaki boyemin nakasa sani, "


" aikuwa wannan karon tunaninki bai baki daidai ba "


Cikin daria tace" to Baby, adawo lafiya, Wanda baiji bari ba yaji hoho🤣🤣, idan kin hadu dashi kice yayarki tana gaishe shi "


Daga haka tafice daga dakin, ita kuwa ko a jikinta kayan ta ma taci gaba da shirya wa cikin jakar da zata tafi da ita


Da yamma suka dauki hanyar Abuja itada Nasrin dakuma wani qanin Nasrin din, sunata firarsu amota
Har Allah yasauqesu lafiya


Gidan yan'uwan su Nasrin din suka sauka Inda ake hidimar bikin, matar tanada faram faram Babu ruwanta, daga nanfa aka fada harkar biki, koda batada niyyar kwalliya Nasrin ce take sakata dole taayi, aikuwa sosai suke zuba kyau abinsu duk Inda suka wuce sai ankallesu musanman Nawal


Kwanansu biyu a Abuja Babu wani labari, nanfa tadaga hankalin ta, ta shiga damuwa, Nas tace "kiyi hakuri beauty insha Allah zamu ganshi kafin mubar garin nan"


Tace "toshknn Nas Allah yasa"




Washe gari za'ai dinner haka sukaci kwalliya, matar Data yiwa amarya itace tayi musu daidai misali


Aikuwa sunyi masifar yin kyau


Suna zuwa wajan dinner aka farayi cikin kwanciyar hankali


tadubi Nasrin tace "Nas nagaji da zaman nan wallahi, bari nadan fita nadawo,"


Tace mata" to beauty "




Tana fita wajan kuwa ga motoci nan birjik, ta jingina ajikin wata Mota
gawasu maza nan agefenta kusan su hudu suna firar su


Wani bawan Allah ne yaqaraso wajan ta yace mata " hi"
Kallansa tayi kawai batace komai ba


Yasake cemata "Baby girl mekike jira ne anan wajan ke kadai? Be kamata mata kyawawa irinku sudinga zama su kadai ba"


Tace masa "ko?"


Yace "sosai ma kuwa, ga motata can, mezai hana kishiga Muje ko shisha ne musha mudawo kafin agama dinner" 🙆🏻


Zaro ido tayi😳, cikin ranta tace"nashiga uku shisha? Gabanta yafara faduwa, gatada tsoro


Amma afili sai tace "A a nagode"


Yace"fine, to nide nagani inaso "


" kayi hakuri bawan Allah ansamin rana, wani watanne ma bikina "


Cikin rashin damuwa yace" to shikkenan, Babu damuwa, bye "


Bayansa tabi da kallo, oh akwai tantirai aduniya, Allah kaqara tsare mana imaninmu"


Wasu motoci ne guda uku baqaqe sukazo wucewa ta wajan, ba wani gudu suke sosai ba, mazan nan na gefenta ne taji wani daga cikin su yace " kace akwai harka, MK Yashigo gari kenan"


Gabanta ne yafara faduwa, tabi motocin da kallo bakinta yafara rawa wajan furta m.m...mk


Wani daga cikin su yasake cewa "ai mk yayi a rayuwa, kana ganifa duk samarin nan na unguwar su daya bayan daya ya nema musu aikin yi"


Wani kuma yace "nifa naji ance wallahi ba qaramin Dan shaye shaye bane"


Na hudun kuma yace "dalla Malam ware, kawai hassadar mutane ce, inde anga kanada shi yanzu za'a fara cemaka manemin mata, Dan giya, Dan ta'adda"


Kanta ne ya kulle, tarasa abinyi, kawai saita doru abayan motocin tana binsu cikin sauri, wayar ta tad'auka takira Nas tace "Nas futo futo, futo Nas ga mk can, futo futo Dasauri Dan Allah"


Ai afujajan Nas ta futo 🤣🤣tana waigawa damanta sai hango Nawal tayi tanabin wasu motoci Dasauri, itama kawai saita fara binta da Dan gudu harta tarota


Adede lokacin saiga wani me adedeta, Nasrin ce ta tsaida shi, yana tsayawa kuwa Babu neman excuse suka fada ciki, Nawal tace "Muje Muje Dasauri kabi bayan wadancen motocin pls "


Hajiya kuyi hakuri, doka tahana adedeta haya agarin nan, nima yanzu satar hanya nayi nafuto, amma idan aka kamani kulleni za'ayi"


Nasrin tace "Dan darajar Allah karufa mana Asiri, Muje Dan Allah, Babu abinda zai faru "


Cikin faduwar gaba yaja adedeta suka fara tafiya, Nawal kira take "kaqara sauri mu tarosu pls Malam"


Hajiya saide kuyi hakuri ina hawa Babban titi kamani za'ayi, saide mubi ta qasa


Nasrin tace "koma ta inane Muje, mude fatanmu mutaro motocin kawai"


Aikuwa saiya qara gudu sosai , kasancewar hanyar akwai gargada ana sabunta titin ne, me adedeta yaci karo da wani rami sai kiyaaaaa adedeta tafadi 🙆🏻😳


Agefen da Nawal take zaune Agefenta adedetan yafadi, Nasrin tafad'o kanta 🤣🙆🏻🙆🏻


Aikuwa sai suka dauki ihu da kururuwa Nasrin tace "Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, jama'ah akawo dauki 🤣


Ita kuwa Nawal sai ihu take tana" cewa wayyo nashiga uku hannu na, na mutu na lalace 😂😂


Mutanan dasuke gefen titi ne suka taho aguje aka kawo musu dauki, aka samu aka dago adedetan, Nasrin tafuto, ita kuwa Nawal sai ihu take saida aka zarota


Sannan shima me adedetan aka bashi temako


Gaba dayansu sunyi tsumu tsumu agefe Nasrin na kuka Nawal na kuka🤣Babu Mai rarrashin wani


Maganar Najma ce tafado mata, gaskiya ne Wanda baiji bari ba yaji hoho 🤣🤣


Wani yace "yakamata kuje

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login