Showing 33001 words to 36000 words out of 104433 words

Chapter 12 - DANGI DAYA COMPLETE by Amnah El Yaqoub .pdf

yagama shafe shafensa yadawo zai saka kayan, gajeren
wando yadauko, ya cire towel din ya wulllashi kan gado, zai saka kenan sai gata taturo kofar
dakin tashigo ‍♀️
Tana ganinsa haka tasaki qara tafuto aguje, gabanta sai faduwa yake, Innalillahi..,meyakaita
dakin yaya Aslam?

Shikuwa Aslam yana jin qaranta ya tabbatar yarinyar taganshi, qarasa saka wandon yayi
Yazauna agefen gadon yadafe kansa ‍♂️, shikkenan girmansa yazube a'idon qanwar
budurwarsa, zance yaqare taga komai

Haka yatashi ransa abace yagama shirya wa yafuto, tana ganinsa futowarsa takwasa aguje tayi
dakinta, shikuwa Aslam ko Kallanta beyiba yawuce zai fice daga falon, ta kalli bayansa tasaka
dariya, tashige dakinta

Sarai yana jinta yayi fuska ya shareta, toba dole tayi masa dariya ba, duk yanda yake kare
mutuncinsa saida yarinyar nan taga komai, wallahi yanda yakeji aransa idan ta kuskura yadawo
tayi masa dariya wallahi sai jikinta yayi tsami �

Bayan sun gama ganawa da baqin harma suntafi, sun tsaida ranar dazasu shirya bude
campany, Aslam yayi shiru yana tunani, Abba ya kalleshi yace "meke damunka"

Ajiyar zuciya yayi yace "wallahi Abba akwai damuwa"

"wacce irin damuwa?"

"Abba kaga tunda akai auren nan, yarinyar nan ko abinci bata min, kullum ina wajan cin abinci,
idan na yi mata magana tafadamin ba dadi"

"Aslam wannan ne dalilin dayasa nake fada muku kudena kula qananun yara, amma bakwa
ganewa,"

Ajiyar zuciya yayi yace "yanzu de abinda nake fadama yarinyar nan fa taga komai, koda nayi
mata fada bama lalle taji ni ba"

Abba yace "Kamar ya, mekake nufi"

Cikin haushi Aslam yace "kagane mana, saina futo fili nama bayani ne"

Dariya takama Abba, sosai yake dariya yana kallan Aslam

Aslam yace "tomiye kuma abin dariya, miye hakan, wallahi Zan huce akanka"

Abba yace "maida wuqar abokina, kaima saika rama abinda tama, kaga shikkenan kunyi 50 50,
babu wanda zaiyi wa wani dariya"

Kallan Abba yayi yace "Kamar ya Abba? Ma kake nufi?"

Abba yakama Kunnan Aslam yayi masa rada
Lokaci daya sukasa dariya, Aslam yace "kai Abba wallahi bakada dama, natafi, yanzu yanzu
zanje nasiyo, sai munyi waya"

Daga nan kowa yayi gida


Aslam bai zarce ko'inaba sai wani super market da ake saida kayaiyakin wasan yara, daga nan
yayi gida, lokacin yamma liss, yana shiga falon yaji qamshin abinci yadaki hancinsa, ahankali
yaleqa kitchen yaganta tana girki tana waqa hankali kwance, cikin sand'a yadawo da baya
yashige cikin dakinta, yabude toilet dinta yadauko lizard cikin aljihunsa yasaka mata shi dede
Inda yaga tana shanya panties dinta, cikin sauri yafuto Yarufe dakin Ahankali ya koma falon
Yazauna yadora kafa daya kan daya yana jijjigata


Agabansa tafuto daga kitchen din, ta kalleshi tayi Murmushi, tazauna tazuba Abincin ta ita kadai
tanaci tana murmushi
Kallanta yayi yasan sarai dashi take, sotake yamata magana tafada masa marar dadi, Dan haka
yayi shiru yaqyaleta, suna zaune ana kallan kallo har dare yayi, bega tatashi ta shiga dakiba,
shikuwa sallah yake zuwa yadawo falon Yazauna, daga qarshe ma bayan sallar ishsha'i wanka
yayi yadawo falon Yazauna yana kallo, abin harya fara bata mamaki, yatsina fuska tayi tashige
daki, zuciyarta daya tazage ta shiga wanka, cikin nishadi tasha wankan ta tas, ta janyo towel
zata daura kenan tayi ido biyu da qadangare, tsaro ido tayi

Cikin faduwar gaba tace " Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, nashiga uku me yakawomin masifa
cikin toilet" dagudu tafuto towel ahannu

Shikuwa yana zaune yana kallo yana shan lemo, yana jin salati yace "lokaci yayi kenan"
Ahankali yatashi yayi hanyar dakin, yana zuwa bakin qofa sukai karo, jikinta yana karkarwa ta
kamashi ta riqe, cikin tsoro tace "yaya Aslam qadangare a toilet dina, wallahi yana ciki, Muje ka
ganshi"

Aslam kuwa gunki yazama a tsaye, magana take masa amma yadade da shagala yana kallan
surar jikinta, ashe haka yarinyar nan take?

Jijjigashi tayi tace "yaya Aslam!!!"

Firgigit yadawo cikin duniyar mu
Yanayin sa yadan sauya kadan, ya kwashe da dariya yace "to daura towel din"

Sai a lokacin talura da towel din dayake hannunta, kunya ta kamata, cikin sauri taja tarufe
jikinta, amma takasa kallan idonsa

Futowa yayi yabarmata dakin, tabiyo bayansa, yana dauke kafa tana maidawa, yajuyo ya
kalleta yace "wai menene?"

Cikin shagwaba tace "to Muje kacire min shi mana, haka kawai saika tafi kabarni"

Banza yayi da ita ya kashe kayan kallo yadauki wayarsa yayi hanyar dakinsa, itama ta doru
abayansa

Dakinsa yashiga, yafara cire kayansa,cikin sauri tajuya masa baya, Kallanta yayi yanda tajuya
bata kalleshi ba, ya zubawa cinyarta ido daga baya, yadauki jallabiya yasaka, yahau gadon ya
kwanta

Tanajin ya kwanta tataho kansa ta tsaya tana share hawaye, yanajinta ya qyaleta, ita kuwa
daga ta haka saita qara gunjin kuka, tsaki yayi yatashi yafuto yabar mata dakin, itama tasake
futowa, cikin ransa yace yau naga ta kaina
Hanyar fita daga falon yanufa tabiyoshi, yajuyo ya kalleta "ina zakije ahaka?"

Cikin kuka tace "Allah bazaka fita kabarni ba"

Yace "abinci nakeso naje nasiyo, banaso dare yamin"

Tace "to baga abinci can a kitchen ba, basai kaje kaciba"

Cikin sauri yace "ni? A a riqe abinki, Abincin da ba'abanishi Dan dadi ba saidon wuya?"

Yana fadin haka ya juya zai fice, tasa hannu ta riqe gefen jallabiyarsa
Yuyowa yayi ya kalleta ya girgiza kai sannan yadawo falon Yazauna, itama tadawo tazauna
akusa da qafafunsa


❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Computer datake gabansa Yarufe ya ajiye ta agefe, sannan yadauki coffee din da Adala
Sabuwar Mai aikin Momy takawo masa
Yana kai coffee din bakinsa ya runtse idonsa, zaqi yayi yawa, shikuma bayason zaqi, ga shi
kansa coffee din har wani d'aci-d'aci yakeyi

Tsaki yaja, yadauko cup din yafuto falo yana kwalawa Momy kira "Momy! Momy!!"

Momy dake kallo afalo tadago idonta ta kalleshi, tace "Abba nah menene?"

Cikin damuwa yace "Momy waye yahada wannan coffee din?"

Tace "waye zai hadama coffee Abba bayan Adalaiye? "

Tamkar qaramin yaro haka yafara yimata shagwaba "Momy wallahi Babu dadi, zaqi yayi yawa,
kuma ni kwata kwata ma bayamin dadi abakina Kamar yanda yarinyar nan take min, duk Babu
teste"

Momy tayi shiru tana kallansa, Wato Nihla ce bazai fad'aba saide yarinyar nan,ai already Nihla
tagama bata Abba da wannan shegen coffee Kamar qa'ida, Tun bayan barinta gidan komai yaci
yadinga mita kenan shi Babu dadi

ajiyar zuciya tayi afili tace "Abba Tun yanzu?"












Ko'ina masu lizard zasu kwana yau?

Oga me coffee ko yaya abin zaici gaba da kasancewa?

Amnah El Yaqoub ✍️
[6/23, 11:31 PM] El Yaqoub: ❣️DANGI 'DAYA❣️

{Romance&Friendship luv}

Writing by Amnah El Yaqoub


Like my page On facebook
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493


Wannan page din na'yan la'be ne
kawai sonake yau kuma ku futo kuce wani abu



23&24

Yace "Momy me kike nufi?"

"A a, babu komai Abba, zanyi mata magana saita gyara"

Ajiye cup din yayi "no kibarta Momy, kawai de daga yau karta sake min"

Haka ya juya cikin dakinsa ransa duk ajagule, zama yayi yadauki wayarsa yafara kiran number
Nadiya, but number busy, cikeda mamaki yakalli agogo "to Dawa take waya Awannan lokacin ?"

Babu me bashi amsa, Dan haka yayi wulli da wayar ya kwanta


❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Har sha biyu suna zaune jugum jugum afalo, Aslam sai hamma yake yanaso yaje ya kwanta,
gashi wannan yarinya ta hanashi sakat, tazo tasa shi agaba da wannan shegen towel din nata
Wanda dashi ma gara Babu
Ahankali yatashi yayi dakinsa, tatashi tabishi, Bece mata komai ba yahaye gadonsa ya kwanta,
kujerar datake dakin nasa tahau ta kwanta itama, saide atakure take
Yakalleta yace "kitashi kibarmin dakina"

Ilham kuwa tana jinsa tayi banza ta qyaleshi
Wai akan masifa ta sameta yake korarta, Hmm zata rama ne, da haka tayi addu'ah sannan tayi
bacci, shikuwa kasa baccin yayi yazuba mata ido yana Kallanta dukda ta juya masa baya,
daqyar yasamu yayi bacci bayan fama da juye juye dayake, idan Yarufe idonsa, surarta kawai
yake gani
Tun kafin tatashi daga bacci asubar fari yatashi yaje toilet dinta ya cire lizard din sannan yatafi
masallaci

❣️❣️❣️ ❣️ ❣️ ❣️

Yau daga makaranta gida yawuce, yadade agida sannan yakamo hanyar gidansa
Tun kafin yasako qafarsa cikin falon ya ganshi kaca-kaca, yariqe qugu ya tsaya yana qarewa
falon kallo, fillow's din dake kan kujera duk wasu aqasa, matsawa yayi yaje wajan kayan kallo
yasaka hannu yataba, yana duba hannunsa yaga qura

Daga murya yayi yafara qwala mata kira "maryam! Maryam!!"

Cikin sauri tafuto daga dakinta,fuskarta cikeda kwalliya, riga da wando ne a jikinta, rigar nan
takamata kyam ajiki, wandon kuwa tacika abin ta, Dan qaramin mayafi ne a hannunta tana
kokarin nad'ashi akanta tace "gani"

"yanzu maryam abinda kike acikin gidannan yadace kenan? Bakisan mukwana dake acikin
gidannan kibudi baki kice Dani ina kwana ba, idan zaki fita unguwa bankai matsayin dazaki
tambayeni ba,bakisan kidafawa mijinki abinci ba, now kalli gidannan, kina nema kibar min gida
ya lalace, kalli, kalli Dan Allah cikin falon nan "
Yaqarasa magana yana nuna mata cikin falon


Kallansa tayi " yanzu ya Adam duk kokarin danake dannaga na zauna dakai lafiya baka gani?
Auren nanfa baso nake ba, sannan kana maganar abinci aikai malami ne kasani, haqqinka ne
kaci Dani sannan kashayar Dani, ni bazan iyaba!, bazan iyaba!! Bazan takura kaina ba, in tashi
dasafe, inyi wanka, inyi kwalliya, inyi kokarin hadawa kaina abinci, sannan kuma inzo
ingyarama gida, na maka girki, saboda samu ma inyi mopping,inturara gida da turaren wuta,
saikace a novel? Aljanar inace nida Zan yi wannan aikin kullum?
To kaga ni gaskya ko agaban iyayena Babu me takuramin ehe! "

Tana fadar haka tajuya takoma cikin dakinta, jagwab Adam Yazauna akan kujera tareda dafe
kansa ‍♂️maryam zata haukatashi

Yadade azaune sannan yatashi yatattare hannun rigarsa yadauki tsintsiya yafara share gidan,
takan dakinsa yafara sannan kitchen, sai kuma falo, mopper yadauko ya goge falon tas, sannan

ya goge kayan kallan yadauko qur'ani adaki yadawo falon yana karantawa


❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Tunda taga ya Fawaz har gida yake shigowa da kayan maye yasaka acikin fridge ta shiga
damuwa, ya Fawaz koshi ba dan'uwanta bane yakamata tafara nuna masa abinda yake ba
daidai bane, balle ma shidin mijinta ne, haqqin kula dashi yana kanta
Jiya tatuno saida yagama qarewa fuskarta kallo sannan wai ta d'agashi tunda dama tasaba

Ahankali tatashi tashige cikin dakinsa, ta gyara masa dakin tas, ta lailaye masa gadon tsaf,
fridge din dakin tabude kwalaben maganin maye dana mura gasunan birjik, shiru tayi tana
tunani, tarasa mafita Dan haka tadau wayarta takira yayarta, bugu daya ta dauka tace "Diyana
kinga dakin ya Fawaz nake gyara wa bakiga kayan maye ba, nikuma banaso yanasha wallahi,
Yaya zanyi dasu ne?"

Diyana tace "um lalle Dida agaisheki, ke har gyaran dakinsa ma kike, tab!"

Dida tace "toya zanyi Diyana, mijina ne ko mahaukaci ne shi dole Zan kula dashi ahaka"

Batare da tunanin komai ba Diyana tace "kidebesu kizubar kawai"

Dida tace "to shikkenan nagode Diyana" daga haka takashe wayar, takwashe duka
magungunan tafitar dasu waje ta tsiyayar dasu sannan tayi watsi da kwalaben
Tadawo ta goge fridge din, ta dauko lemuka a kitchen da ruwa tazuba masa su sannan tafuto
daga dakin

Abinci taje tadafa musu bayan tagama tayi wanka tadawo falon tazauna tana game a wayarta
Ta dade azaune awajan sannan yashigo gidan, yau yayi mata sallama, cikin ladabi ta amsa
masa, tace "a kawo ma abinci ne?"

Yatsina fuska yayi "no kibarshi kawai, ke kidena dafa abinci Ma Dani, kiyi rayuwarki kawai"

Batare data ce masa komai ba ta kwanta taci gaba da abin datake

Yana shiga dakin ya ganshi yasha gyara sai qamshi yake, zama yayi agefen gadon afili yace
"wannan yarinyar da naci take wallahi"

Fridge dinsa yabude nan yaga Babu komai, cikin bacin rai yace "kan ubannan!!!"

Belt din jikinsa ya cire yafuto falon afusace, Dida tanayin game kawai sai Saukar belt din taji a
jikinta, cikin sauri tatashi tana sosa wajan, be tausaya mata ba yaci gaba da dukanta, tatashi
tana kuka sosai tana bashi hakuri, yana binta da duka tanayin baya har sukaje bangon falon ta

tsugunna aqasa tana kuka sosai, cikin hucin bacin rai yace "ke Dan uwarki nizaki renawa
hankali eh ? Okey wato saboda na sakar miki fuska acikin gidannan kina abinda kikaga dama
shine zaki nemi ki takurawa rayuwa ta ko?, to bari kiji duk lokacin dana sake ajiye kayana cikin
fridge tsautsayi yasa kika dauke min, saikin yabawa aya zaqin ta " Yayi wulli da belt din awajan ya koma dakinsa, Dida kuwa kanta yana cikin qafafunta tana kuka,
Dagowa tayi ta kalli jikinta, gefen hannunta harya shata



(Allah karabamu da mazaje masu dukan iyalinsu )

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Nihla karatu yayi nisa, alhmdlh tafara kwantar da hankalinta, saide damuwarta daya ya Abba,
yana nan daram acikin ranta, amma alqawarin data daukar wa kanta yana nan Babu shi Babu
ita,fatanta daya tasamu miji nagari Wanda zai nuna mata soyaiyar dazatasa ta Manta da Abba
kwata-kwata, tana fatan samun wannan mijin
Gefe daya kuma shaquwa Mai qarfi tashiga tsakaninta da abdallah, kullum suna tare, tana
karatun ta cikin kwanciyar hankali, abdallah yazame mata tamkar aboki, gashi yanada abin
dariya, idan suna tare dole nema saiya bata dariya, shiyasa take ganinsa Kamar qawanta, gashi
duk abinda bata ganeba yana temaka sosai harsai tagane, fatarta kadai zaka kalla a yanzu
kasan cewa lalle tasamu canji, Anty Nadiya tayi mata komai a rayuwa


❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️


Bayan tagama gasa jikinta tabawa megadi kudi yasiyo mata magani tasha sannan ta kwanta,
amma hawaye take sharewa, kanta har ciwo yake saboda kuka, yakamata tabarwa yaya Fawaz
gidansa, Tun ranar da aka kawota gidan nan tafara cin karo da mari, to tunda yafara duka bazai
dainaba gara tafara tunanin barin gidan Tun wuri,kuma yazo ya kwanta a jikinta yace itace,
bayan duka ga sharri, inaaaa! Da sake


❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Yau agajiye yadawo gida,gashi ya Manta bai siyo abinci ba awaje, tsaki yasaki yafara qwala
mata kira "Ilham"

Daga kitchen tafuto, ya kalleta daga ita sai wata qaramar riga da bata wuce gwiwarta ba
Ya Girgiza kai, yarinyar nan bazata dena halin ta ba, batada kunya, batasan shigar kamala
Yace "jeki kawomin abinci"

Babu musu tajuya takoma kitchen, Aslam yabita da kallan mamaki, yau shine yace wa Ilham
tabashi abinci Babu musu Babu rashin kunya tajuya zata kawo masa? Lalle yau za'ayi ruwa da
qanqara

Ilham kuwa tana shiga kitchen tazuba masa Abincin, sannan tad'ebo gishiri Mai uban yawa
tazuba masa aciki, tasa spoon ta jujjuya Sanna tadauko takawo masa, zuciyarsa daya yadebi
Abincin yakai bakinsa, lokaci daya ya yatsina fuska, gaba daya gishiri yahade masa baki,
daqyar ya iya hadiyewa, yadauko Abincin yakawo mata gabanta ya ajiye, tadago kai ta kalleshi
dariya ta nasan kamata, cikin fishi yace "Ashe ke zero ce bansaniba?"

Ran Ilham yabaci, ita ya Aslam zai kalla yace mata zero? Itama cikin bacin rai tace masa "To
sannu 1"

Tas kakeji yadauketa da mari, yace "Ilham idan kinaji da rashin kunyar ki kiyi abinki ke kadai,
tayaya Zan kashe kudi na kawo miki abinci gida na ajiye, banda damar dazaki dafamin, Sannan
yanzu nace kikawo min abinci zaki zuba min gishiri aciki?to gashinan zauna tas saikin cinye shi"

Hawaye ne yazubo mata, tasa hannu tashare tana magana cikin kuka "Allah bazanci Abincin
nanba"

Yace "nikuma kika sakamin naci namutu, baki damuba, zauna saikin cinye Abincin nan"

Haka Ilham tasa hannu acikin Abincin nan tanaci tana hawaye, fakar idonsa tayi tatafi dakinta
dagudu tana kuka, Kallanta yayi yafara fada cikin ransa, haba yarinya sai Jan magana da rashin
kunya, in banda yana mata kallan qanwar budurwarsa yau dasai ta cinye Abincin nan tas


❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️


Futowa tayi tatafi dakinsa kanta tsaye, shi kansa yayi mamakin ganinta a dakin, saboda ba
kulashi takeba, agefen gadon tazauna "yaya Adam inason kudi zanyi amfani dashi, banda kudi"

Kallanta yayi yace "banda shi"

"yanzu yaya Adam kaine zakace bakada kudi? Idan ban tambayeka kudi ba wazan tambaya?"

Yace "Allah masani"

Tace "Ok to sata zanje inyi insamu kenan?"

Yace "maryam koma menene kije kiyi, amma nide bazan dauki kudina nabaki kitafi yawon

banza ba, kokuma kisa kati ki kira samari, qarya haram!"

"Ok haka kace?"

"yes haka nace maryam, kije kiyi duk abinda kikaga dama"

Tashi tayi tafuto tabar masa dakinsa
Tunani tafara maranta ciwo yake, A'ina zata samu kudin dazata siyo pad, shikuma besiyo
mataba sannan yahanata kudin, haka takoma daki ta kwanta ga ciwo da takeji sosai, Tun tanaji
kadan-kadan harta faraji dayawa, daga qarshe ma zazzabi me zafi Yarufe ta


Washe gari dasafe ya shirya zai tafi makaranta saboda yanada lacture, yayi kyau sosai cikin
farin yadi sai qamshi yake
Har zai shiga Mota ya tuna yarinyar nanfa Tun jiya beji motsinta ba, Dan haka ya koma ciki kai
tsaye yashiga dakinta, tozali yayi da ita akan gado tana cikin blanket amma karkarwar sanyi
take


Cikin sauri ya qarasa wajanta yace "subhanallah... Maryam!"

Bargon ya janye saiga Diyana tana kuka sosai, yace "bakida lafiya ne?"

Bata iya bashi amsa ba sai kuka, dagota yayi yatasheta zaune sai riyamm tafada jikinsa, kanta
yana kan qirjinsa amma tana iya jiyo bugun zuciyarsa,wannan shine karo na farko da mace
tahada jiki dashi, sai yaji abin wani iri, goshinta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login