Showing 75001 words to 78000 words out of 104433 words

Chapter 26 - DANGI DAYA COMPLETE by Amnah El Yaqoub .pdf



" amin, Allah yayi miki albarka ki gaida su hajiyan "

" to baba zasuji "

Tana kashewa ta kalli Momy tace" Momy nida baba ne, yana gaishe ki, maganar Auren ya yusif
yayi min, Momy nida nafiso saina gama service dina, amma shi baba yace wai basai nagama
ba kawai zasuyi magana da babansa, su tsaida magana daya "

Tun lokacin da al'amarin Nihla da Abba yafara wakana, Momy bata taba Jin faduwar gaba irinna
yauba, jikinta yayi sanyi, Nihla de da gaske take tarabu da Abba Yusif din takeso
Murmushi ta qaqaro tace" Alhamdulillah, to Nihla ai hakan yafi, menene amfanin jira yata,
abinda Mai hakuri yafada gaskya ne, aide kina sonsa ko? "

Momy tayi Tambayar tana zubawa Nihla ido ko zataga yanayin ta ya sauya amma saitaga Babu
damuwar komai akan fuskarta
Saima kanta data daga alamar eh tanaso

Murmushi tasakeyi, kafin tayi magana yaturo kofar dakinsa yafuto yayi mutuqar cikin suit kalar
ash, qaraso wa yayi Yazauna akan hannun kujerar da Nihla take zaune
Yasa hannu yadauki Ruwan da yagani ansha, yazuba a cup yafara sha Ahankali, Nihla sai
matsawa take gefe, tarasa wannan abu na ya Abba, duk kujerun falon sai akusa da'ita zai
zauna, wayarta tabude tashiga chatting tanayi

Shikuwa yana shan ruwa hankalinsa yana kan wayar tata, jikinta ne yabata ana kallonta,
danhaka tashiga cikin chat dinta itada ya Yusif tayi sallama daganan bata jira komai ba tafara
tura masa da kiss

Wani irin qullutun Baqin ciki ya tokarewa Abba wuya, ahankali yaji Ruwan dayake sha yafita
daga ransa

Yusif kuwa baya rufe datar sa, yana ganin saqon Nihla yadoko mata kira

Nanma akan idon Abba kiran yasake shigowa, murmushi tasaki sannan tayi cikin dakinta tana
amsawa wayar

Abba yabita da kallo ransa abace, Momy ta kalli yanayin sa, tace "Abba na sai ina?"

"Momy zamuje Abuja ne nida Aslam"

"Abuja kuma? Wajan wa? Me akeyi?"

"Momy wajan baba Ibrahim zamuje mugaidashi"

Tausayinsa yakama Momy, tasan duk saboda Nihla zaiyi hakan, taji dadi aranta tunda yau Abba
zai gyara kuskuren daya aikata, tace "to sai kundawo"

Daga nan tatashi, tsaye tayi hanyar dakinta, Abba ya kalleta dakyau yaga jikinta yayi sanyi,
Kamar akwai abinda yake damunta yace "Momy bakyajin dadi ne?"

Juyowa tayi "lafiya ta kalau Abba, kaina ne yake ciwo kadan"

"Momy ko mutafi asbiti?"

"A a Abba na, karka damu ai Nihla tana nan"

Yace"To shikkenan Momy, Allah yasawaqe "
Momy tashige dakinta tafada duniyar tunani, tunda Nihla tayi mata magana akan sunyi maganar
Yusif da babanta shikkenan ta saddaqar Nihla bazata auri Abba ba, bazata auri danta ba,
ahankali tatashi tasha magani, sannan ta kwanta


Abba kuwa dakinsa ya koma yadauko wayoyinsa, yana futowa daga dakin yaga wayar Nihla
akan kujera, mamaki ya kamashi, yaushe tadawo falon?

Hanyar kitchen yanufa yaleqa kansa yaganta a kitchen tana kokarin kunna gas
Bece da'ita komaiba, ya koma falon yadauki wayar tata batare da tunanin komai ba yahadata da
bangon falon ya doka, nan take wayar tafashe tayi raga-raga‍♀️

Yajuya yafice daga falon, yahau Mota yanufi gidan Aslam



❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️


"congratulation Adam, matarka tana dauke da juna biyu Tsawon wata uku"

Adam yasaki murmushi yace "Doc da gaske kake?"

"qwarai kuwa, haka bincikenmu ya nuna, sannan wannan zazzabin datake fama dashi da amai,
insha Allah zata denaji, karkuma kuyi wasa da bata magungunan da aka rubuta muku"

"insha Allah Doc. Nagode sosai"

Kallan Diyana yayi da aka yiwa qarin ruwa, tana bacci, saida Ruwan yaqare sannan yakira Doc
aka cire mata, sukayi shirin tafiya gida

Kamota yayi ya rirriqe yana ta mata sannu, ta kalleshi tace "ya Adam sai farin-ciki kake, bayan
kuma kasan banda lafiya"

"aidole nayi farin ciki maryam, kinsan me Doc yace kuwa?"

Shiru tayi masa, Dan a tunanin ta baidamu da rashin lafiyar tata bane, Motar tabude tashiga,
shima yashiga sannan tace "ina Zan sani saika fada"

Cikin murna yace "to cemin yayi matata maryam tana dauke da Baby na acikinta na wata uku"

Cikin sauri ta kalleshi tace "da gaske?"

"sosai ma kuwa, bari mu koma gida nakira su Aslam da mama nafada musu"

"yanzu ni ahakan ciki ne dani?"

"maryam kenan kina mamaki kenan, aike yanzu kin zama sarauniya maryama sai abinda
kikace"

Shiru tayi masa tazuba masa ido tana kallan yanda yake farin ciki, Allah sarki ya Adam, rayuwa
kenan



❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Kasancewar jirgi suka biyo ko awa daya basu yiba suka sauka,baba yayi mamakin zuwan su
Tun lokacin dasuka kirashi awaya

Afalon gidan aka saukesu, mamy takawo musu abin motsa baki suka gaisa dasu, sannan ta
basu waje

Sosai suka gaisa da baba, Inda suka sake bashi hakuri akan abinda yafaru abaya, baba ya
nuna musu Babu komai dama basune sukai masa laifin ba, amma komai yawuce insha Allah

Yusif ne yashigo falon yayi kyau cikin qananun kaya Baqin wando da farar riga an rubuta
handsome agaban rigar
Ido biyu sukai shida Abba, kowa ya kawar da kansa

Tunani Abba yafara, kenan gida daya take rayuwa da wannan gayen, shima Yusif din anasa
bangaren tunani yake menene yakawo wadannan gidansu


Ahankali yaqaraso wajansu yamiqa wa Aslam hannu suka gaisa
Sannan yabawa Abba hannu yana kawarda kansa gefe

Shima Abban kansa ya kawar gefe sukai musabaha ahaka

Baba yayi shiru yana kallon su, gaisawa suke amma kowa fuska adaure, kuma kowa ya kawar
da kansa basa kallan junansu

To tabbas da wani abu aqasa, duk yanda akai yarannan sunsan juna, sannan shi Yusif yayi
masa maganar Nihla, ga kuma Abba shima yazo domin gyara laifin dayayi abaya, da alama
shima da wani abu a tsakaninsa da yarinyar, to daga nanfa baba yafara tunanin akwai matsala

Suna gaisawa dasu yawuce dakinsa, suma su Abba basu jimaba suka dauki hanyar Airport
domin komawa kano



❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️


Azaune take aqasan kafet din dake malale acikin qayataccecn falon na Momy datafe kanta da
hannunta guda daya tana kuka, dayan hannun kuma ta riqe fashshiyar wayarta dashi, ba
fashewar wayar ce tasa ta kukaba, Information dinta dayake ciki takewa kuka, saboda idan
waya ce akwai Sabuwar da ya Yusif yakawo mata, kuma akwai tsohuwar wayarta ta farko duk
suna nan

Allah ne yakawo su Usman gidan gaba dayansu

Ya Aliyu ya kalleta yace "Momy me aka yiwa wannan yarinyar ne take kuka?"

"wallahi Aliyu futowa mukai falon nida ita shine mugaka wayarta afashe, shine take kuka"

Ya Usman yace "subhanallah... To garin yaya ta fashe Momy?"


"yaya ma za'ai kayimin wannan Tambayar Usman, Abba zai fasa mata wayar nina sani"

Farouq yace "haba Momy, ya za'ai yafasa mata waya, Abba bazai yi hakaba, da hankalin sa
dakomai yazaiyi yafasa mata waya"

Momy tace "a a Farouq rabu da shiru-shiru, rabu da shiru-shiru farouq, dukanku nice na haifeku
Babu Wanda bansan halinsa ba acikinku, nafada muku Abba ne yafasa wannan wayar"

Suna wannan zancen yashigo cikin falon, yayun nasa yagaisar sannan yace "Momy nadawo"

Momy tace "naganka ai Abba"

Ya Usman yace "Abba meyasa kafasa wa yarinyar nan wayarta, saboda me haka kawai zaka
fasa waya?"

Juyawa yayi ya kalli Nihla datake goge hawayen idonta, haushi ya kamashi, saboda yafasa
wayar da saurayinta yake kira shine take wannan uban kukan

Yamaida kallansa ga Usman yace "ya Usman ni ban fasa mata waya ba" yanemi waje Yazauna
yana cire jacket din saman suit din jikinsa

Momy tace "Abba, nasan halin ka sarai, idan bakaine ka fasa mata wayaba waye zai fasa?
Adala bata nan, dagani saikai sai ita dakuma Daddynku, mune zamu fasa wayar kenan?"

Cikin kishi dakuma wata irin murya Kamar zaiyi kuka yace "to Momy meyasa zata dinga waya
dawani can, bana fada mata banaso ba"


Hawaye suka zubowa Nihla ta kalli Momy tace "Momy ai kinji shi ko? Allah saiya biyamin
wayata"

Tashi yayi tsaye ya kalleta, ya girgiza kansa, sannan ya sunkuya yadauki wayarsa da jacket
dinsa daya cire yayi hanyar dakinsa











To,ko Alhaji Abubakar zaibawa Ibrahim hakuri akan abinda yafaru abaya?

Yaya labarin abdallah qanin Nadiya ne? Anya kuwa zai iyayin shiru akan abinda yagani

dangane da Abba da Nihla?






More Comments more typing....









Mrs Usman ce ✍️
[7/11, 12:19 AM] El Yaqoub: ❣️DANGI 'DAYA❣️
{Romance&Friendship luv}

Writing by Amnah El Yaqoub

Like my page On facebook
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493



47&48


Momy tayi zuru da ido tana Kallonsa, gaskiya ne karabu da miskilin mutum, ka kalleshi kawai,
kagama yiwa yarinya kuka ka matseta kayi kissing dinta amma kaduba kaga Kamar bashi ba,
kome yataka oho?

Usman yace "Nihla kiyi hakuri kidena kuka kinji, zanyi masa magana saiya nemo miki waya
wayar, kiyi shiru"

Ahankali yatashi yabi bayan Abba, zaune ya sameshi yayi tagumi hannu bibbiyu, zama yayi a
gefensa
"Abba!, meyasa zaka fasa mata waya, tayaya zata soka ahaka Abba?"

Kallan yayan nasa yayi, qwallah tacika idonsa, bai iya boye waba danhaka yabasu damar

zubowa, jikin ya Usman yafada, cikin hawaye yace "yaya ashe kowa yagane halinda nake ciki?
Yaya zanyi da soyaiyar ta yaya?"

Usman ya shafa kansa "kadena kuka mana"

"dama wannan shine abinda muke gujema tunda farko" Aliyu daya shigo dakin yafada

Gaba dayansu suka daga kansu suka kalleshi, farouq ma yashigo dakin sannan Yarufe

Zama sukai duk su hudun, Aliyu ya cigaba da cewa "yanzu wa gari ya waya? Kai taurin kai
gareka Abba, yarinyar nan kowa yasan tasoka, amma ka Qita, tayaya zata soka yanzu?"

Hawaye suka zubo daga idanun Abba, Usman yace "Abba na hanaka kukan nan, kuka bazai
kawo mafita ba"

Cikin hawaye yace "ya Usman kabarni nayi kukana, cewafa tayi batasona, kuma bata barni
hakaba saita dinga kula wasu"

Dariya takama farouq, bai boye ba yasaki dariyarsa �

Wani irin haushi yakama Abba, yazuba masa ido yana kallansa batare dayayi magana ba
Saida farouq yagama dariyarsa yace "wallahi banga laifin Nihla ba, gara ta gwaraka ka gwaru"

Cikin haushi yace "Aidama nadade da sanin sonta kakeyi, ai shikkenan"

Farouq yayi Murmushi yace "ahhh ina son Nihla,wayace ka Qita? Lokacin dakace baka sonta
nace Zan aure ta kaji haushi nane? Sai yanzu dakake sonta ne zakace ai dama kasan ina
sonta, a a ina auren ta"


"dan Allah kuyi mana shiru munemo kanmu mafita" cewar Aliyu

Gaba dayansu kuwa sukai shiru, ya Usman ya kalli Abba yace "Abba kishi banaka bane, ka
lallabata kagane? Kabata kulawa, kuma ka sameta kasake bata hakuri, kai Abba inta kama ma
saika tsugunna a gabanta ne, to kayi inde hakan zaisa tahuce"

"ya Usman har hakan fa nayi mata taqi yarda"

Aliyu da farouq suka saki murmushi, lalle Abba da gaske yake

Shima ya Usman din murmushin yayi yace "naji, kaci gaba da bata hakuri, insha Allah wani
lokacin zata hakura"

Aliyu ma yace "yawwa kuma naga Kamar Momy ma tanabin bayanta, yakamata kasamesu
itada Daddy kuyi magana, amma wannan fishin naka akan ankirata awaya Babu Inda zai kaika"

Haka yan'uwan nasa suka sakashi agaba sunayi masa huduba, dakuma shawara akan abinda
zai kawo musu mafita



❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️


Zaune yake agaban iyayen sa,acikin dakin Daddy, kansa aqasa, Momy tana zaune agefen
Daddy, yayinda hankalin Daddy yake kan news din da akeyi

Saida aka gama sannan ya kashe, yajuyo ya kalli Abba yace "Abubakar muna jinka, kazo kace
akwai maganar dakake so muyi, amma kayi shiru"

Gabansa ne yafara faduwa, yarasa ta Inda zaiyi wa iyayen nasa bayani

Momy tace "kayi shiru Abba"

Ahankali yadago kansa ya kallesu sannan yasauke idonsa cikin sauri,"Am.. Daddy dama....
dama inaso ne infada muku inason yin aure"


Murmushi ya baiyana a fuskar Daddy, amma Momy kuwa Kallonsa tace, tanaso taji yafadi
abinda ta dade dasani

Daddy yace "wacce Abba? Alhmdllh ashe de kaji fadan damukai ma"


Ahankali yadaga kansa alamar yaji

Momy tace "to Wacece? Ko wata yar Abujan kasamu?"


Kallanta yayi ya girgiza kansa alamun a a

Daddy yakalli Momy yace "ikon Allah, kinga yau Abba kunyar mu yakeji"

Momy tayi Murmushi batace komai ba

Daddy yace "to a wanne garin take? Saina tura su Alhaji Baqir suje su nema ma auren ta,

Wacece?"

Karon farko da Abba yaji tsoron mahaifin sa, gabansa sai faduwa yake, jikinsa yayi mugun
sanyi, har wata irin karkarwa yakeyi
Ahankali yadago kansa ya kalli Daddy yace "Nihla ce Daddy"

Lokaci daya, annurin fuskar Daddy ya dauke
Yamiqe tsaye yace "zancen banza, zancen wofi, Abubakar ashe bakada hankali bansani ba?"

Yasake maida kallansa wajan Momy yace "toke Rahma idan kin gama sauraren abinda yake
fada, saiku tattara kufita, nima zanje daki nahuta" yana fadar haka yafara takawa zai tafi
dakinsa
Caraf yasa hannu yariqe kafar mahaifin nasa, kansa aqasa, amma yakasa Dagowa, Daddy jin
anriqe masa kafa yasa ya tsaya cak, hawaye ne yake disowa daga Idanunsa, numfashin sa
yafara sama sama Kamar Mai Asma, yasaka hannunsa daya ya goge, yayinda dayan hannun
yake riqe da qafar Daddy Ahankali yadago kansa ya kalli Daddy yace "Daddy please, Dan girman Allah Daddy kayi hakuri
kuyafemin irin laifin danayi abaya, Daddy ka tausayamin wallahi ina sonta...." ya qarasa
maganar yana sakin wani irin kuka Mai cin rai

Daddy yajuyo ya kalleshi yace "Abba!, kalleni nan, niba mutumin banza bane, kuma niba
qaramin yaro bane dazaka raina wa hankali, saida kasa natara mutane agabansu ka nunamin
ban isa dakai ba, yarinyar nan akan ka aure ta kazabi karbar Mazawaje family, sai yanzu
zakazo min da wata irin magana, kaga da Allah, tashi kafice kabarmin dakin nan indena
ganinka "

Ahankali yamiqe yadafe kansa dayake masa muguwar sarawa, yakalli Momy da jikinta yayi
sanyi yace" Momy, Dan Allah Kibashi hakuri, kuyi hakuri Momy wallahi zuciyata zafi takemin,
Momy inason Nihla "

Momy tace" Abba ai lokaci yaqure ma, Nihla akwai wanda takeso, sannan mahaifin ta yayi
magana da ita akan hakan, kaine ka janyo koma menene, katashi kafice kawai, banason
maganar banza "

Hawaye yasake zubowa Abba, shikkenan Babu wani Mai goyon bayansa kuma, tunda Momy
ma tace haka to Babu Wanda bazai iya juya masa baya ba

Duhu duhu yafara gani, ahankali yafara takawa sai jiri ne yake dibansa, hannunsa yana dafe da
kansa, haka yatafi yabar falon na Daddy yana tafiya yana hada hanya

Hawaye ya zubowa Momy, tana tausayin Abba sosai amma dole zataso yagane dai dai da
abinda ba dai dai ba
Cikin sauri tatashi zatabi bayansa Daddy yace "Karki kuskura kije Inda yake, kinji nafada miki"

Yana fadar haka ya juya yashige dakinsa ransa duk abace

Momy ta zube akan kujera tana sakin wani irin kuka Mai ciwo



Jikin bango yakebi yana tafiya Kamar Mai koyon tafiya, sakamakon duhun dayake gani acikin
idonsa, da haka ya qarasa dakinsa yazube akan gado yana sakin kuka sosai abaiyane, nan
take wani irin zazzabi Mai zafi ya rufeshi



❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

"Abdallah yakirani awaya yafadamin komai, meyasa kika boyemin gaskiyar ke Wacece Nihla?"

"Anty Nadiya... Dan Allah kiyi hakuri, wallahi bansan ta yanda za'ai nayi miki bayani ba, Anty
Nadiya ya Abba ke yakeso, kuma a lokacin dana hadu dake kuna tare da juna, yana sonki kina
sonsa, meyasa Zan rusa muku soyaiyar ku, bazan iyaba, shiyasa nayi shiru ban fada miki alaqa
ta dashi ba, duk family dinmu kowa Abba yake cemasa, nahadu dake naji kince sadiq
Mazawaje, banyi tunanin shi bane saida kika nunamin pic dinsa, kuma daga lokacin nake
sporting dinsa awajan ki, harga Allah banso kikaqi auren saba, saboda banji dadi ba kokadan
Anty Nadiya, koma meyayi min shidin dan'uwana ne,nida shi munkance cikin DANGI DAYA, duk
da yayi min laifi wallahi banso kika Barshi ba, amma kiyi hakuri Anty Nadiya akan rashin sanar
dake dabanyi ba "

Ajiyar zuciya Nadiya tayi" nafahimceki Nihla, sai da abdallah yafadamin komai nasan cewa
bakida laifi, Sadiq yahadu Nihla Nikaina nasan da haka,ashe ba banza ba kika rikice, Nikaina
rashin kulawar sa ce tasa narabu dashi, amma Abdallah yacemin yaga soyaiyar ki sosai acikin
idonsa, hakane? "
" hakane Anty Nadiya, yafadamin ma, kawai de bazan iya sauraron sa bane, kuma nafada
masa "

" eto yakamata de yasan darajar ki gaskiya, sai kiyi addu'ah Allah yazaba miki mafi alkhaairi,
idan ansa ranar bikin saiki sanar Dani "

" munyi maganar ya Yusif da baba ma Anty Nadiya, insha Allah idan ansa Zan sanar dake "

" to shikkenan qanwata Mai yan samari, sai munyi waya, kicewa sadiq Nadiya tana gaishe shi
"

Murmushi Nihla tayi tace" Babu ruwana Anty Nadiya, kunfi kusa kedashi "

Da haka sukai sallama



❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️


Sanye take da atamfa Mai launin pink da brown, dinkin riga da siket ne amma Yazauna a jikinta
sosai, mayafi tayafa dan qarami iya gefen kafadarta daya, yayinda data riqe hand bag dinta
tafuto daga cikin dakinta, da alama unguwa zataje, adede lokacin shima yafuto idonsa yasauka
akanta, tayi mutuqar yimasa kyau sosai, kasa dauke idonsa yayi akanta harta qaraso ta
gabansa zata wuce shi batare data kalli Inda yakeba, hannu yasa ya fuzgota, lokaci daya tafada
jikinsa, bai jira komai ba yasaka ta cikin qirjinsa ya rungumeta sosai

Tudun nashanunta dayakejinsu akan qirjinsa ne yasa ya lumshe idonsa, sannan yaqara
matseta tsam ajikinsa, jijiyoyin jikinsa suka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login