Showing 51001 words to 54000 words out of 104433 words

Chapter 18 - DANGI DAYA COMPLETE by Amnah El Yaqoub .pdf

cikin dakin Diyanan, a lokacin su kuma suka futo
daga toilet shida ita, Allah yaso su sun dauro towel ajikinsa, hajiya Na'ila ta kallesu cikeda
mamaki, tace "a a, ashe ku kuna ciki sai rafka sallama nake naji shiru"

Diyana tayi shiru ta qyaleta,
Hawaye suka silalo daga idonta, Adam kuwa kansa ya sosa, cikin kunya yace "Sannu da zuwa
mama" daga nan yafuto daga dakin dagashi sai towel iya qugu

Hajiya takai kanta Kallanta kan Diyana tace "a a subhanallah, me aka miki kike kuka? Shiyasa
fa hankali na Yaqi kwanciya nace sainazo naga halin dakuke ciki,"

Nanma Diyana shiru tayi ta qyale hajiya, cikin ranta ma haushinta takeji, ai duk itace taja mata,
tabata magani tasha gashinan danta zai kasheta

Tafiya tafara da qyar, tana dingisa kafa, gashi sai bubbude kafa take tana runtse idonta, ko
kayan sakawa bata nemaba takoma kan gadon nasu da Babu ko bedsheet saboda Adam ya
cireshi, ta kwanta tana hawaye

Hajiya Na'ila tayi mutuwar tsaye, Innalillah kawai take maimaita wa acikin ranta, abinda idonta
yagani kadai ya'isa ya tabbatar mata da cewa maryam takawo budurcinta dakin mijinta, gaskiya
sun dauki alhakin Diyana, tatuna lokacin da'aka ce Adam zai aure ta sai fada take anhada danta
da Diyana yarinyar datake yawo club club
Cikin tasauyawa ta kalleta tace "kiyi hakuri mana Diyana, kowa da kike gani da haka yafara,
bari nayi masa magana yazo yakaiki Asbiti"

Fita tayi daga dakin tana magana cikin zuciyarta, wai meyake damun wannan yaran ne? Duk
sai yanzu suke mu'amular aure, ita kuma Allah yake nuna mata wannan abun kunya , Allah
sarki ashe shiyasa Adam Yaqi bin bayan matar sa, har take fada tana cewa Diyana batasan
gyara ashe ita yarinyar batasan komai bama na aure bare aje ga maganar gyara, aikuwa ta
dena zuwa gidansu kar gaba kuma taga abinda yafi haka , har gara Adam ma yaji kunyar ta
yagudu dakinsa, amma shi Aslam kiranta yayi awaya ma taje gidan nasa


Bakin dakin nasa ta tsaya tayi nocking, sannan tadaga murya tace "ka futo ka dauki yar'mutane
kuje asbiti"

Daga nan tafuto daga falon gaba daya ko dakin Diyana bata sake shiga ba, Mota tashige driver
yaja suka tafi



❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Tunda tagama school ta karbi result dinta second Class upper, taje tayi registration din Service,
tana jira ayi posting dinsu ne kawai, da wannan damar tayi amfani tashiga Catering school tana
koyar Birthday Cak, kullum zata shirya tayiwa mamy sallama tatafi, bazata dawoba sai yamma,
wani lokacin kuma ya Yusif ne yake kaita da kansa, zuwa wannan lokacin kam ita kanta tasan
cewa tagama mallaka masa zuciyarta, saboda yanda take samun kulawa sosai awajan sa,
kuma har zuwa wannan lokacin Bata sake kiran Momy ba, dama wancen dinma dokar
mahaifinta takarya takirata

Wayarta tace tayi qara tana dubawa taga Abokinta ne yake kira Wato Abdallah qanin Anty

Nadiya, tanayin picking ya sanar da'ita cewa Posting dinsu fa yafuto, taje taduba nata, shi
anduba masa nasa yaga sun turashi yola

Tace "toooo yola!, tabdi nikam ko'ina suka kaini? Sai Allah"

Yace "kije kiduba naki kema, sai munyi waya"

Bata jira komai ba, ta shirya tsaf, taje kafe aka duba mata, Wanda yaduba nata yaciro posting
latter din yabata, tana dubawa taga anyi posting dinta kano, cikeda mamaki tace "kano kuma?"
Kudinsa tabashi tadawo gida, a compound taga su Baba da ya Yusif da Alhaji Isma'iel Abban ya
Yusif, tana gaishe su ta miqa musu takardar, kowa yagani, duk sunyi mata murna da aka turata
jihar musulmai, Alhaji Isma'iel ya kalli Yusif yace "to Yusif ai sai kuje tasiyo abubuwan dazata
buqata gobe tabi jirgi tatafi ko?"
Yace "to Abba insha Allah"

Sannan ya kalleta yanayi mata wani kallan luv yace "kishirya anjima sai Muje shopping din"


Da yamma kuwa sukaje shopping, tasiyo komai na buqata, tagama shirya kayan ta tsaf, tunda
aka ambaci service akano taji tanayin murna badan komaiba, tasan zataga Ilham da Momy

Da daddare baba yazo har dakinta, tayi mamakin ganinsa a dakin Dan ba shigowa yake ba,
Kallanta yayi yace "Nihlan Diddi, gobe kuma sai kano ko?"

Murmushi tayi tace "hakane Baba"

Yace "to banda shirme de, ki tsaya kiyi abinda yakaiki, idan kun gama zaman camp din idan
kinga zaki iya cigaba dayin service din Acan saiki zauna, idan kuma bakyaso saiki nemi
relacation kidawo nan"

Tace "to Baba, amma Baba ai gara na dawo nan din yafi, saboda nanne gida"

Yace "a a, can dinma ai gida ne, ga yayun mahaifiyar ki duk suna can, sai kije can kiyi zaman
ki"

Tace "to Baba kakira su awaya kafada musu zanzo"

Yace "saboda ga gwamna ko shugaban qasa ko? Sai an sanar dasu zuwan ki, kema ai
iyayen ki ne, kikirasu da kanki kifada musu, ni bazan saka baki akan zaman ki agidanba, kawai
de bazan dauki abinda za'aci zarafin 'yataba"

Murmushi tayi tace "to Baba insha Allah, zankirasu"

Kallanta yayi yaga tanata murna, yasan kuma bazai wuce ace murnar ganin Momy bace, Dan
zuwa yanzu kam yasan ai ta cire Abba aranta, daga nan yatashi yayi mata sallama yatafi


Washe gari saida tayi sallar azahar sannan ta shirya cikin doguwar riga Mai adon stones ajiki,
sannan tayi rollinga tasaka wani shegen glass a'idonta, sai zuba qamshi take, idan ka kalleta
saika sake waigawa, tayi masifar yin kyau, farar fatarta yaqara futowa sosai sai shining jikinta
yake
Ya Yusif ne yakai ta Airport sai firar soyaiya suke abinsu gwanin sha'awa, har lokacin tashinsu
yayi, sukai sallama yace zai kawo mata ziyara idan yasamu dama, da haka tashige cikin jirgin
akaro na farko atarihin Rayuwar ta, wayarta tadauko zata kira Momy, kawai saita fasa, gara tayi
mata surprice kawai
Ko awa daya basuyi ba, jirginsu yayi landing, tana futowa daga Airport din mutane suke ta
Kallanta, daga ita sai yar qaramar truly dinta tanaja, tayi mutuqar birge kowa, Mai taxi ta tare
tashiga tafada masa Inda zai kaita, acikin motar ma kafa daya ta dora kan daya, tana daddana
waya, har sukazo bakin get din family house din Mazawaje
Sallamarsa tayi, ta tsaya ta qarewa Babban get din gidan kallo, duk an sassauya abubuwa
dayawa, yau gata a Mazawaje family akaro na biyu

Tura get din tayi tashiga, iliya Maigadi yana zaune yanajin radio, taga ya kalleta yayi shiru
Kamar besanta ba, cikin mamaki tace "iliya d'anmai qarfi baka ganeni bane?"

Kallanta yasake yi, yaji sunansa radau abakinta yace "Wacece? Bangane kiba wallahi, baquwa
mukayi ne?"

Murmushi tayi ta cire glass din idonta tace "iliya nice Nihla fa"

Cikin sauri yatashi tsaye yace "kai kai kai, wai Nihla kece? Aini jinake wata balarabiyar ce
wallahi, a a a a, masha Allah, sannu da zuwa, sannu sannu, kice yau munada manyan baqi
agidan namu, kawo jakar taki, kawo, kawo"

Nihla tayi Murmushi tace "iliya kenan,"

Sannan tabashi jakar, suka nufi part din Momy, saida yakai mata jakar har cikin falo sannan
yajuyo yana qara yimata sannu da zuwa, Nihla ta zube akan sabun kujerun falon da aka sake
tace "wash Allah nah, gajiya"

Sannan tadaga murya tace "Momy!!! To futo 'yarki tazo"

Kamar almara Momy Tajuyo Kamar muryar Nihla, amma sai taqi gaskatawa, mezai kawo Nihla
kano yanzu? Kawai de kunnanta ne

Nihla tasake cewa "Momy!, koba kowane agidan?"


Dasauri Momy tafuto falon, taga Nihla kwance akan kujera ga jakar tanan agefe, qaraso wa tayi
cikeda tsananin mamaki, Nihla na ganinta tatashi ta gudu taje ta rungumeta cikeda murna

Momy tadagota daga jikinta tana Kallanta tace " Nihla 'yata, yanzu Allah kece kika qara girma
haka? Gaba daya kin sauya kamar ba Nihla ta tadaba"

Dariya tayi tace "Momy nice mana, wai meyasa kowa yake cewa na sauya ne? Momy girma
naqara ne?"

"girman ma Nihla, kin qara kyau, Kamar balarabiya, mezakici adafa miki yanzu?"

Saida tayi farrrr da idonta sannan tace "Momy yanzu banajin yunwa, saide da daddare, but idan
akwai cornflakes zansha kadan"

Momy ta lakace mata hanci, tace "Wato bakyason cin abinci Kamar da ko? Ni narasa ya'akayi
ma kikai bul-bul dake masha Allah Babu wata rama Kamar da"

Dariya tayi, cikin ranta tace Anty Nadiya ce sirrin, afili kuwa sai tace "Momy bari nakai kayana
daki"

Momy tace "a a Barshi, Adala zatazo takai miki, tashi Muje ki gaisa da sauran yan gidan"

Hannunta Nihla ta riqe Kamar wasu qawaye suka futo, kowanne part saida sukaje ta gaida
kowa, kuma kowa sai nan-nan yake da'ita, kowa yayi murna da dawowar Nihla, saita zama wata
abar sha'awa kowa Kallanta yake yanda ta sauya,Hajiya Farida maman su Diyana kuwa tana
ganin Nihla taji tausayin Abba ya kamata
Haka suka dawo part din Momy, Nihla ta dora kanta akan cinyar Momy tana bata labarin
makaranta dakuma service din da aka turota

Suna wannan firar har la'asar tayi, Tatashi taje tayi wanka, tasaka riga da wando na jesy, (kayan
ball) na mata, amma nata dogon wando ne Mai launin dark blue, Momy ce da kanta tahado
mata cornflakes din, tace "to yata taso kisha, yauda kaina Zan baki"

Murmushi tayi tatashi, suka zauna a kafet din, Momy tafara bata, ita kuwa sai surutu take mata,
Momy cikin ranta sai mamakin yanda Nihla ta sauya takeyi, kanta Babu dankwali hakan yasa

dogon gashinta dayasha gyara kwanciya a bayanta

Adede lokacin yaturo falon nasu yashigo, yau kwanansa takwas baya qasar ma baki daya,
saukarsa kenan

da dogon gashinta yafara tozali, kasancewar tabashi baya baiga fuskar ko Wacece ba,
mamakin hakan yasa yaqame a tsaye abakin kofa, Wacece wannan Kamar ba 'yar hausawa ba
kuma Momy tana feeding dinta?

Momy ce ta lura dashi takalleshi cikin murmushi tace "a a Abba, shigo mana"

Jin an ambaci sunansa yasa bugun zuciyarta ya sauya, ahankali tajuya ta kalli bakin kofar
itama, lokaci d'aya Idanunsu yahade dana juna, cikin abinda baifi second ashirin ba tagama
qare masa kallo, yau ne karon farko daga taba ganinsa azahiri sanye cikin kakinsu na Pilot Mai
launin fari da baqi banda pic dinsa data gani awayar Anty Nadiya sanye da kayan , sosai kayan
sukayi bala'in karbar jikinsa, yaqara girma, yaqara yin kyau Kamar ba shiba yasake zama
babba tamkar wani cikakken magidanci, kawarda idonta tayi,ta karbi spoon din hannun Momy ta
cigaba dashan cornflakes din ta, shikuwa kasa dauke idonsa yayi akanta, shin anya kuwa ita
dince de agabansa? Inda ace baiyi mata kyakykyawan saniba Babu abinda zai hana yakasa
ganeta, but ya'akai takoma haka? Dogon gashinta yasake kalla Kamar ba gashin bahaushiya
ba, ahankali yaqaraso cikin falon cikin takun izza

Momy tace "Nihla ga yayanki yashigo fa, shima baya qasar yanzu yanzu yadawo, yaude ina
cikin farin-ciki yarana duk sun dawo gabana"

Hankalin Nihla yana kan cup din gabanta, ko dago kanta batayi ba, bare yasaka ran zata
kalleshi, kanta aqasa Kamar anyi mata dole tace "ina yini"

Ataqaice yace "lafiya"

Sannan yayi gaba, yajuyo yasake kallanta waiko zaiga ta kalleshi amma yaga gaba daya
hankalinta ma baya kansa, shi wannan yarinyar zata gaisar asheqe Kamar ta samu sa'anta?

Momy kuwa tayi mamaki guda daya, mamakin daya kamata shine yanda Nihla taqi ambatar ko
sunan Abba, da tasaba tanaji yarinyar tana ya Abba kaza, ya Abba kaza, duk da yana shareta
bata fasa fadar sunansa ba, Kamar a bakinta aka rada mata sunan ya Abba, amma yau taga
gaisuwar ma daqyar tayi

Dakinsa yashige yafada kan gado yana tunani, inaaa! Bazai iyuba, Sam bayason raini, Dan
haka bazai dauki wannan ba, lumshe Idanunsa yayi, meyasa yake jin farin-ciki ne awani
bangare na zuciyarsa?

(ko a film fad'an boss shine qarshe dafatan za'a min Comments )










Amnah El Yaqoub ✍️
[7/3, 12:43 AM] El Yaqoub: ❣️DANGI DAYA❣️
{Romance&Friendship luv}

Writing by Amnah El Yaqoub



Like my page On facebook
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493




33&34


Nihla ta kalli Momy "Momy kibani wayarki nakira su Ilham, banda number kowa acikinsu"

Momy tace "wayarki tada tana nan a dakin naki, ki kunna saiki dauka, ai Babu wadda ta sauya
number acikinsu, nima Bari nakira Daddynku dasu Usman nafada musu zuwanki"

Tace "to Momy" sannan tashige dakinta


Da daddare kuwa su ya Usman sukazo dukansu, dama Momy tasa Adala ta shirya musu abinci
Mai kyau

Alokacin Nihla tasake wanka tasaka riga da siket na atamfa Mai launin Jan duhu, dinkin yayi
mutuqar yimata kyau, siket din kuwa hips dinta yacikashi dam, daurin dankwali nede tayishi
simple amma gashinta awaje yake daga baya

Babu Wanda bai rude ba, lokacin dasuka ganta, gaba dayansu suna zaune acikin qayatattun
kujerun dakin, Adala kuma tana dauko abinci daga kitchen zuwa kan dining, firarsu suke cikeda
farin-ciki but Abba kam baya saka musu baki, baya cewa um bare um um, asali ma waya ce
ahannun sa yana danne-danne, yayinda yadora kafa daya kan daya
Farouq yace "Momy, yarki fa tagama rikicewa, gaba daya ta sauya kamar ba ita ba, ni sai yanzu
nema nakejin naqara matowa, inba itaba sai rijiya"

Ahankali yadago kansa ya kalli farouq, amma Bece masa komai ba

Murmushi Nihla tayi, har dimple dinta yana lotsawa, tace "ya farouq bakada dama, aina fadama
dakai za'ayi, tunda kaji sharadin"

Wannan karon ma tana fara magana Abba yadauke idonsa daga kan farouq yadawo dashi
kanta, har yanzu de wannan dimple din nata yana nan, yayi tunanin zata kalleshi amma kwata
kwata saiyaga ko kujerar dayake kai bata kalla ba

Aliyu yace "ai farouq, bazan baka qanwata ba, mijinda Nihla zata aura ai sai Wanda duniya
tasan dashi"

Usman yace "Kamar ni kenan"

Gaba dayansu sukasa daria, Momy tace "Dinner is ready kutashi Muje kowa yaci abinci"

Usman da farouq da Aliyu gaba dayansu ajere suka zauna, Momy ma tazauna akusa da
Usman, kujeru biyun dasukai saura kuwa na Abba ne da Nihla, hankalin ta kwance taja kujerar
tazauna sannan tafara cin Abincin ta, shima Abba daya qaraso wajan yaga saura kujera daya ta
kusa da Nihla, haka yaja Yazauna, idonsa akan wayarta data ajiye a gabanta, yana zama wani
irin sihirtaccen qamshi yabugeshi, baisan lokacin daya lumshe idonsa ba yabude, kowa shiru
yayi yana cin abinci, wayar Nihla tafara qara, kowa yazuba mata ido yana Kallanta, Abba yakai
dubansa kan screen din wayar yaga ansa
❤my Yusif❤ harda alamar hert ajikin sunan, Nihla tasa hannu tasaka wayar a silent, idonsa ne
yasauka akan kyawawan yatsun hannunta, dogaye gwanin sha'awa, janye idonsa yayi, Nihla
kuwa ko a jikinta taci gaba dacin Abincin ta, ana jimawa ya Yusif yasake kira, tasake sakata a
silent, akaro na uku ma yasake kira, ahankali ta miqe tsaye tace "Excuse me, zan amsa waya"
Tana fadar haka ta nufi hanyar dakinta, Hips dinta Abba yabi da kallo, anya kuwa yarinyar nan
itace bawani abu take sakawa a jikinta ba? gashi sai yawo take tana fitarda gashinta waje kowa
yana kallo, amma Momy tana gani ko magana bata taba yiba

Har suka gama cin Abincin Nihla tanacan tana waya, da dade tana shan wayarta dashi sannan
tafuto sukai sallama dasu ya Aliyu



❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

"ku shikkenan idan akace anyi muku aure, ankai muku amarya daki saiku rasa control dinku
gaba daya, tayaya za'ayi daren farko kace zaka shigi mace gaba daya, shiyasa mutanan da
sukafi mazan yanzu iya zama da mata, da kanku kukesa matanku suna tsoron ku, yanzu
saboda Allah wannan dame yayi kama? Kaja anyiwa yarinya dinki, tayaya kake tunanin zata
sake yarda dakai akaro na biyu? "

Adam yayi shiru kansa aqasa, ko yayiwa doctor bayani bazata ganeba, gara yayi shiru tagama
fadanta kawai, ahankali yadago kansa ya kalleta, matar kam babba ce zata iya haifansa,
shiyasa Babu kunya baro baro take masa fada, yace" insha Allah Zan kiyaye gaba likita "

Fuska a cukune tace" to dade yafi muku, narubuta muku magunguna kasata agaba tadinga sha,
sannan karka sake zuwa wajanta sai nanda yan kwanaki "

Kansa aqasa yace" to insha Allah "

Daga nan yafuto daga office din nata yaje wajan Diyana daya tarar tana bacci, baiyi kokarin
tashinta ba, yabarta tagama baccinta sannan tatashi Dan kanta, yakamo hannunta da kafadarta
suka futo daga asbitin, saida yasai magungunan da aka rubuta musu sannan suka wuce gida

Dakinta tashige ta kwanta tana tunani, dama haka daren farko yake? Ahakan wasu suke cewa
sunason daren farko? Wannan aiba abin dadi bane abin wahala ne kawai, har akan wannan
abun wasu matan suke fada? Har wasu sukai kansu ga aikata zina, tabdi, ita kam, itada ya
Adam danba qara

Dakin yaturo yashigo yakalli fuskarta tayi fayau, zama yayi agefenta yace "maryam kiyi hakuri,
insha Allah hakan bazata sake faruwa ba"

Shiru tayi masa batare datayi magana ba, ahankali ya miqe yafara cire kayan jikinsa, gaban
Diyana yafadi, me kuma zai sake yi?

Tsaf ya cire komai dagashi da boxer yahau kan gadon, cikin faduwa gaba tace "dan Allah kayi
hakuri ya Adam,"hawaye ya silalo daga idonta

" ohhh Diyana, niba wani abu Zan miki ba, kawai inaso najiki ajikina ne "
Yana fadar haka yasa hannu yadaga mata hannayenta ya cire rigar jikinta, daga ita sai breziya
ya janyo ta jikinsa ya rungumeta tsam, sannan cikin rarrashi yace "muyi bacci ko?"



❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Tunda suka dawo normal shida ita yakasa yimata komai, yasan cewa Dida mace ce Mai
matuqar kunya bazata taba kawo kanta gareshi ba, to shi kuma kunya yakeji da girman sa yaje
gun yarinyar mutane da sunan neman haqqin sa, amma azahiri yana matuqar buqatar matar sa,
saide zaici gaba da haquri kawai har Allah ya yaye masa abinda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login