Showing 21001 words to 24000 words out of 104433 words

Chapter 8 - DANGI DAYA COMPLETE by Amnah El Yaqoub .pdf


daga motar wani qato

Shikuwa Fawaz tunani yafara wai A'ina yakejin Dida ne? Wacece Dida ne acikin yaran?

Daddy yayi shiru yana kallan kowa, matan sai hayaniya suke, Alhaji Baqir ne yatashi yadaka
musu tsawa sannan suka nutsu kowa takoma wajan zamanta tazauna

Cikin ransa yafara magana, mata biyu!! amma wad'annan tsofaffin sunfi kowa cimasa mutunci,
to aishi guda d'ayanma bayajin zai iya zama da ita, Dan haka yadago kansa Ahankali ya kalli
Daddy yace

" I'am sorry Daddy, amma i can't marry her, Daddy bazan iya auren taba, inada wadda nakeso"

Gaban Nihla yayanke yafadi, ita yaya Abba yake cewa bazai aura ba agaban jama'a?
Lokaci daya hawaye suka wanke mata fuska, babu wanda yafado mata sai Diddi, tabbas sai
kayi rashin uwa zakasan wani bangaren na rayuwa

Momy ta kalli Abba da sauri tanaso ta gaskata abinda kunnanta sukaji, ba ita kadai ba hatta
Usman, Aliyu, farouq, shi suke kallo cikin tsananin mamaki

Daddy kansa maganar Abba tadaki ransa, amma saiya basar bai nuna ba ya kalli Abban yace
"Amma kasan cewa yanda 'ya'yan wasu sukabi umarni bazai iyu d'anda nahaifa acikina
yaqibiba ko? Tunda kace baka sonta tokaje kanemo son aduk inda yake, idan kuma kanakan
bakanka har yanzu to kasa aranka cewa, qin auren Nihla dede yake da fitarka daga cikin
Mazawaje family,sannan ni kaina nacireka acikin 'ya'yana, Zabi na gareka, koka amince
kokuma daga nan katashi kafita baka cikin Mazawaje family "

Hall yasakeyin tsit, maganar Daddy ta daki kowa, tabbas yanda yayanke wannan hukunci akan
d'ansa nacikin sa tofa bazaiji kunyar yankewa Dan wani ba

Babu musu Abba yamiqe, yafuto daga cikin Hall din

Momy tafara kuka wiwi, tace" Innalillahi wa inna ilaihir raju'un, meyake shirin faruwa damune?"

Ta kalli Abba dayake dab dabarin cikin hall din ta qwala masa kira tace "Abba!!!"

Amma ko juyowa baiyiba







(wai ina labarin yusif ne,?Yaje China ya maqale)

(tab bari na fece kar masu dukan Abba sudawo kaina }

Mutara zuwa gobe






Kada ku Manta da sharhi, Comments, dakuma share, please

Amnah El Yaqoub ✍️
[6/19, 10:55 PM] El Yaqoub: ❣️DANGI 'DAYA❣️

{Romance & Friendship luv}

Writing by Amnah El Yaqoub

Like my page On facebook
https://m.facebook.com/Amnah-El-Yaqoub-Novel-105487771101493



15&16


Baqin ciki yakama Momy, batasan lokacin data rungume Nihla ba suna kuka tare, Nihla kukan
abu uku takeyi, na farko yanda ta dauki Abba aranta, take jinsa na daban acikin zuciyarta Tun
tana qarama, amma karshe ga irin abinda yamata, na biyu Diddi, ta tabbatar da ace tana raye,
zataji Dan sauqi acikin zuciyarta, na uku mafi munin yanda yafadi kalmar baya sonta acikin
bainar jama'ah

Momy kam Baqin ciki yahanata magana tama kasa Dagowa ta kalli idon kowa saboda abin
kunyar da d'ansu ya aikata

Hajiya Farida bataji dadin abinda akaiwa Nihla ba, yanda take shiri da Mai Hakuri bataso
wannan abu yafaru akan yarsa ba, kowa yasan cewa yaran Babu Wanda yakeso, amma dukda
haka ai basuyi magana ba

Hajiya Abida mahaifiyar Ilham tayi shiru abun duniya yayi mata yawa, wannan abin takaici da
yanzu harda Ayshanta za'ace baza'a iya aura ba


Ran Daddy yayi mutuqar baci akan abinda Abba yayi, haqiqa ya kunya tasu agaban mutane, ya
nuna musu cewa ba'a isa dashi ba

Ahankali yadago kansa ya kalli al'umar dake gabansa yace "amatsayina na babba acikin
wannan family daga ranar yau, na yankewa wannan yara ranar aure, nanda wata daya Mai
zuwa"

Ahankali Momy tatashi taja hannun Nihla suka futo daga cikon hall din, qafar Nihla sai hard'ewa
take saboda yanda ake Kallanta
Suna fita shima Usman yatashi yayi gaba ransa abace, Aliyu ma ya biyo bayansa, yayinda
farouq shima yaga to zaman me zaiyi? Yatashi yabiyo bayan 'yan uwansa

Sai ajiyar zuciya Nihla take ja saboda yanda taci kuka, ta kalli Momy tace "Anty inajin zazzabi"
daga haka tashige cikin dakinta tafada kan gado tana sakin sabon kuka

Momy ma ta doru abayanta,tana zuwa taganta tana kuka, tasa hannu tadagota ta rungumeta
tana bubbuga bayanta alamar rarrashi, saida taji ta rage kukan sannan tadagota tana kallan
idonta tace "Nihla, zaki iya rabuwa da Abba? Ki cireshi gaba daya daga cikin zuciyarki?"

Hawaye ne yazubo mata tace "Anty inason ya Abba sosai, bazan iyaba Anty"

Momy tace "zaki iya Nihla"

Girgizakai tayi alamun a a, sannan ta koma kan gado tarufe idonta da fillo tana kuka
Jikin Momy yayi sanyi, taso ace Nihla zata iya rabuwa da Abba, dasai ta nunawa Abba Dan
hakin daka raina Shike tsone maka ido, to amma yaya zatayi tunda yarinyar ta dage akan tana
sonshi? Dole shi zatayi wa dole akan saiya amince da wannan auren
Tana gama wannan tunanin tafuto daga dakin domin zuwa wajan Abba, dasu Usman tafara cin
karo afalon azaune, kowa ransa Babu dadi

Batace dasu komai ba tashige dakin Abba, suma sukabi bayanta dukansu

Suna shiga dakin suka sameshi yana zuba kayansa acikin jaka, Momy ta kalleshi tace "ina
zakaje?"

Fuskarsa atamke yace "Momy already hutu na yaqare Zan koma bakin aikina"

Usman yace "Abba kanada hankali kuwa? Kasan abinda ka aikata zakayi dana sanin sa agaba
ko?"

"bana tunanin haka yaya Usman, wai meyasa kuka kasa fahimta tane? Saboda me Zan boye
mata gaskiyar abinda yake raina?"

Cikin zafi Aliyu yace "to Dan uwarka baka isaba, wacce yarinya kakeso dazaka Wulaqanta
Nihla akanta? Wacece?"

Kai tsaye yace "sunanta Nadiya, tana Abuja, tare mukai karatu da ita a germany"

Momy tace "Abba,yarinyar nanfa marainiya ce, agabanka mahaifiyar ta tace idan ka girma da
kanta zata samo maka matar aure, kana tunanin tanada wadda zata samo makane bayan

Nihla? Ashe yanzu da ace Aisha tana raye a gabanta zaka watsawa yarta barkono a'ido?
Banasan abinda zakazo kana dana Dani akansa nan gaba "

Shiru yayi Bece komai ba, farouq kam me raguwar zuciya hawaye yake sharewa yakasa cewa
komai tunda suka shigo dakin, sai yanzu yadago kansa cikin hawaye yace " Momy nizan aure
ta"

Kallansa Abba yayi jin irin furucin dayayi, yarasa meyasa duk suka damu kansu akan Nihla,
shima yanaso yaga ya faranta ransu ta hanyar amince wa to amma Nadiya fa?

Aliyu yace "farouq bazaka aure taba, shidin shine dai zai auri yarinyar, da yanaso da bayaso"

Momy ta kallesu tace "ya'isa haka,"

Taci gaba da cewa "Abba idan na isa dakai, amatsayina na mahaifiyar ka to inama umarni akan
ka auri Nihla, nide amatsayina na wadda tayi renon cikin ka Nihla tafi kwanta min a raina, idan
kuma nima zaka nunamin ban'isa dakai bane shikkenan katafi kabar Mazawaje family din
Kamar yanda mahaifin ka yace, su Usman ma sun isheni " Dasauri tafice daga cikin dakin saboda wani sabon kuka daya Taho mata

Farouq ya kalleshi yace " danma kasamu yarinyar tana sonka, duk tarasa wazata so acikin mu
saikai, kaje kayi tayi, kada Allah yasa ka amince, bazata rasa masoya ba"
Yatashi yafice daga dakin, su Aliyu suka mara masa baya suka Barshi shi kadai a dakin

Ahankali Yazauna yadafe kansa ‍♂️
Meyasa kowa yakasa fahimtar sane?

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Daddy tunda yadawo daga wajan taro Yazauna afalon nasa yayi shiru yana tunani, yanda Aisha
tatafi tabarshi ai dole ya kyautatawa yarta, yanajin Nihla aransa sosai, duk lokacin daya bude
ido yaganta yanajin dadi, bayasan abinda zai rabashi da yarinyar kokadan,
Su Usman suna zaune afalon suma, ya kallesu fuskarsa Kamar Babu damuwa yace "kume
kuke jira anan ne? Tunda angama ai yakamata kutafi gida ko?"

Babu musu suka tashi, amma farouq kansa har ciwo yake saboda yanda yayi kuka
Momy ce tafuto tafon taga Daddy azaune shi kadai, tazauna kusa dashi tace "Sannu da zuwa
Alhaji"

"yawwa Rahma sannu, ina wannan yarinyar take?"

"tana daki, zazzabi ne yadan rufeta, amma na bata magani tasha, nabarta tahuta"

Jinjina kansa yayi batare dayace komai ba, itace tasake kallansa tace "Alhaji nasamu Abba
munyi magana dashi, ya amince da auren, yana cikin dakinsa baitafi ko'inaba, kayi hakuri akan
abinda yafaru"

Ajiyar zuciya yayi "ai nayi tunanin yatafi wajan wadda yakeso din, da saide yanemi wani uban,
amma baniba"

Itama Jinjina kanta tayi, tace "yana ciki, kayi hakuri Allah yahuci zuciyarka"

Batare dayace mata komaiba yatashi yayi cikin dakinsa

Awannan rana haka Nihla tawuni adaki ko falon bata futoba, gaba daya family din Babu mejin
dadi aransa

Acikin yammatan ma Babu wadda taje wajan kowa, ko wacce tana part dinsu tanaji da abinda
yadameta

Bayan sati biyu tana zaune a dakinta, yammatan suka zo wajan ta, kullum tana zaune adaki,
abincima saide Momy takawo mata, kunyar ma hada ido take da Abba saboda yanda take
shishishige masa amma yayi watsi da'ita

Ilham ta kalleta tace "Nihla har yanzu kinqi sakin ranki, yakamata ki Manta da abinda yafaru fa,
duk kin rame"

Dida tace "wallahi kuwa, ni bazan d'orawa kaina ba, muma nan dukanmu hakuri mukayi, dama
yaya Adam naso, kuma yanzu anbawa Diyana shi"

Tsaki Diyana tayi tace "ni wallahi Dida kina qara ba tamin raina idan kina hadani da wannan
mutumin, arasa Wanda za'a bani sai malami, ni kunyar fita ma nake wallahi, adinga nunaka ana
ga matar Malam" ‍♀️

Ilham tace "nide bansan yaya Zan zauna da yaya Aslam ba, agabana Anty aysha take wayar
soyaiya dashi amma wai ace shi Zan aura, haba aida kunya, amma Zan bashi girman sa yanda
yakamata, renin hankali ne bazan daukaba, idan ya min wallahi ramawa zanyi, Dan dagashi har
Hajiya Na'ila bazan dauki renin wayonsu ba "
Ta kalli Dida tace" kekuma Dida wannan shiru shirun naki wallahi saikin Barshi, bar ganin yaya
Fawaz yaya nane wallahi idan yamiki kicire kunya kirama "

Ahankali tace" inani ina shi Ilham, bazan iya bama, kowa yayi sabgar gabansa "

Diyana ta kalli Nihla tace" ke ya batun yaya Abba kuwa?"

Tace" bansani ba Diyana, Tun lokacin da abin yafaru ban qara haduwa dashiba, banyi tunanin
zaimin hakaba, abin takaicin ma shine yanda nakasa cireshi a raina, har yanzu ina nan ina jinsa
acikin raina, abinda yake bani tsoro Diyana shine idan na kwanta bacci kullum sainayi mafarkin
sa, dana kwanta dashi a raina daban kwanta dashi a raina ba "
Gaba dayansu sun tausaya mata, Dida tace" kiyi hakuri Nihla, lokaci ne "

❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Tsaye suke a compound din gidan shida Abba, Aslam ya dubeshi yace "Abba biki yanata
matsowa bamu gayyaci kowaba"

"nifa Aslam mantawa nake da wannan auren, babu wanda Zan gayyata, tunda sundage saina
aure ta, ayi bikin kawai, naji haushin wasiyyar nan, akan wannan qullin nasu suka hana wannan
family yin taron komai, wai saboda sun tanadar mana Babban taro agaba, mutsw "
ya qarasa maganar dajan tsaki

Aslam yace" to aikai Dasauqi Abba tunda Nihla zaka aura, amma nifa, qanwar budurwa ta fa,
gata da rashin kunya yarinyar "

" idan tayi maka rashin kunya ka zaneta kawai ka wullota waje karufe gidanka "
Cewar Abba

Ajiyar zuciya Aslam yayi" Abba duk cikin mu kaida Fawaz ne kukai sa'ah, Nihla tana sonka
sosai "

" So, so, so, maganar kenan dai, Aslam narasa gane meyasa qananun yara suke daukar
kulawa amatsayin soyaiya, kaga mubar wannan maganar dai, na turawa wajan aikina takarda
inaso su yimin transfer nadawo gida "

" hakanma yayi Abba, kaga zamufi samun damar kammala abubuwan damuke buqata na
company "



❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

"my son, kacika rigima dayawa, idan kazo gidan me zakayi? Mami d'inka tana nan lafiya, saini
nikuma kana ganina idan nazo"

Shiru yayi yana sauraron yaron nasa, saida yagama jin abinda yace sannan yace "to shikkenan
naji, idan kazo ma bazan barka ka kadede ba zaka koma, Allah yakaimu next week din, Yaya
batun kayaiyakin da nace katuro? Katuro kuwa?"

Cikin muryarsa Mai cikeda Aji yace "anturo su, zuwa jibi zasu qaraso"

"Ok to, to, ba laifi, zan fadawa mami dinnaka zuwan ka"
daga haka suka yanke wayar, yana juyowa bayansa yaga Ibrahim Mai hakuri, nan take ya
fadada fara'arsa yace "a a mai hakuri, kace kana tafe"

Baba yace "ina nan wallahi Alhaji, ai nazo na tarar kana waya, shine nace bari naqyaleka
kagama tukunna"

Cikin murmushi yace "eh wallahi ina waya da yusif ne Dan wajena, yadage yanaso nabarshi
yazo gida yaga maminsa"

Baba yayi Murmushi yace "to Alhaji abarshi mana, aiya dade yayi kokari ma, daga karatu
anzarce harkar canji ai yaro yayi hankali saide muce Allah yaraya mana"

Yace "hakane kam, Mai hakuri abinda yasa nakiraka shine dama nayanke shawara zamu koma
Abuja da zama nida Mai dakina, saboda harkokin nawa sunfi yawa Acan, shine nakeso kaima
ka shirya akwai wani aiki na canji danake so na doraka akai, idan Babu damuwa inason mutafi
gaba dayanmu harkai, mu koma can gaba daya "
Cikin tsananin murna baba yafara yiwa alhaji isma'eeil godia, Alhaji yace" Babu damuwa, sai ka
fara shiri, wani satin idan Yarona yadawo, zamu wuce insha Allah "

Cikin tsananin murna baba yace zai shirya, haka suka rabu da maqocinnasa cikin farin ciki

Yana shiga gida yafara hada kayaiyakin gidan yanata farin-ciki, wayarsa ce tayi qara, yana
dubawa yaga hajiya Farida ce mutuniyar tasa, cikin farin ciki yadaga wayar "Barka da wannan
lokaci hajiya Farida"

Itama anata bangaren "tace yawwa Mai hakuri, mu munata shirye shirye, amma banga yan
yalleman sunzo ba"

"shirin me kuke hajiya?"

Tace "Ah Mai hakuri karka cemin bakasan ansawa yaranmu ranar aure ba? Kuma danaga
harda Nihla shiyasa nace bari nakiraka naji yaushe zakuzo"

Cikin mamaki yace "ranar aure kuma hajiya Farida?"

"qwarai kuwa, wani satin ma aure idan Allah yakaimu"

Yace "subhanallah wallahi bansaniba hajiya, banida labari, waye ne Nihla zata aura?"

Tace "Abba aka bata, saboda anbi tsarin wasiyya ne da iyayen mu suka bari, shine sukace
ahadata da Abba, abin takaicin ma shine yaron baya sonta, acikin bainan Nasi yafuto qarara
yace bayaso"

"subhanallah, subhnllh, banida labari hajiya, Allah yakiyaye gaba,"

Tace "amin Ibrahim to sai anjima"

Shima yace mata "to hajiya Farida nagode sosai"

Wayarta takashe tana tunani aranta, anya kuwa Mai hakuri Babu abinda yake damunsa? Afada
maka wannan maganar amma kace Allah yakiyaye gaba,? lalle kuwa in hakane ya tabbata Mai
hakuri

Shiru yayi yariqe wayar a hannunsa, me Alhaji Abubakar yakeji da shine? Za'ayi bikin yarsa ta
cikin sa amma bashida ikon da za'a kirashi Afada masa amatsayin sa na ubanta? Wannan
wanne irin iko ne?


❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

Zaune suke a part dinsu, shida Momy, yasaka qananun kaya, farin wandon jeans, sai riga marar
hannu, yana zaune afalon suna kallo shida Momy, gaba daya tamanta dashi awajan, harkar
gabanta kawai takeyi, Dan wani irin haushi takeji aqasan ranta, yana Kallanta Tun dazu take ta
hada wani abu da madara, daga gani zai yi dadi sosai Nihla ce tafuto, jikinta sanye da kayan bacci amma ta dora Babban hijabi akai,dogo ne sosai
Tsawon sa har qasa, daqyar kake gano qarshan wandon jikinta saboda tsayin hijabin
Tana ganinsa afalo tayi turus, nan da nan gabanta yafara faduwa, ahankali ta qaraso cikin falon
itama tazauna, tunda akai meeting dinnan sai yau taganshi

Tunda tafuto yake Kallanta, cikin ransa yake cewa kullum tana cikin hijabi, yarasa metake boye
wa, yarinya qarama ta d'orawa kanta wahala �, kullum ka takura kanka acikin hijabi kome zata
boye masa bayan yagama yimata wanka?

Ahankali ta dago kanta, karaf suka hada ido, cikin sauri yakawar da kansa gefe, Kamar ba
shiba
Ajiyar zuciya tayi tace "Ya Abba ina kwana?"

Ataiqaice yace "lafiya"

Haushi yakama Momy, taso ace Nihla tayi banza dashi wallahi, domin kawar da bacin ranta
yasa tadau cup din maganin tsumin data hada mata tace "Nihla ungo wannan kisha"

Dasauri ya kallesu, yayi tunanin shi zata bawa yasha ashe wannan yarinyar take hadawa?
Kona menene oho musu

Dauka tayi tafara sha, abin yanada dadi Dan haka Babu musu ta shanye shi tsaf

Yana ganin ta shanye cikin ransa yace gaskiya ne, yanzu Momy bata sonsa , kowa dakowa
Nihla Nihla Kamar abin sihiri ‍♂️

Kallanta yayi Babu ko d'ar yace mata "Am Zan'iya samun coffee?"

Ba Nihla kadai ba, hatta Momy saida tayi mamakin qarfin halin Abba
Batare da tace komai ba tatashi taje kitchen tahado takawo masa, daga nan tawuce daki, bata
qara dawowa falon ba, Dan ganinsa ma zai iya qara mata wata soyaiyar tasa acikin zuciyarta


❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️

"umma Tun safe gashi har yamma tayi amma yaya Fawaz yana dakinsa yana bacci, saikace me
baccin mutuwa"

Hajiya Abida tace "Ilham kenan, zai wuce qwaya yasha ne? Jiya idona biyu har karfe biyu
Fawaz bai dawo gidaba, sai wajan biyu da kwata yadawo shima ina Tambayar sa daga ina yake
yafara min magana cikin maye alamun wajan abokansa yaje suka sha tare, nasan shine yasa
har yanzu bai tashi ba"
"to amma ummah meyasa yaya Fawaz bazai daina halinsa ba? Kayi ta bankawa cikinka kayan
maye baka tsoro suma illa? Gashi ko sallah baiyi ba"

"Hmm Ilham ni kaina al'amarin Fawaz yana bani mamaki, kinga babanku yayi masa maganar
aiki yafara zuwa office amma Fawaz yayi biris, inajin haushin yanda ake kiran dana Mashayi,
Allah ya shirya minshi kawai"

"Ilham tace" amin ummah, gabana yana faduwa idan natuna da ranar bikin nan ummah "

" kiyi hakuri, insha Allah komai zaizo da sauqi, kitashi kije gidan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login