Showing 42001 words to 45000 words out of 104433 words
Chapter 15 - DANGI DAYA COMPLETE by Amnah El Yaqoub .pdf
kalleshi tace "to Abba"
Bayan yashiga daki ya Usman yace "Momy ran Abba fa yabaci, Kamar kishi yake"
Aliyu shi dama Babu wasa, kai tsaye yace "basai yayi ba, shiyasa ko sallama baiyi manaba yayi
daki"
Farouq yayi dariya ya dauki wayarsa yace "anayi ina daga gefe ina smiling"
Momy tace "a a shide Abba baice hakaba, ni farin ciki ma naga yanayi"
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Dawowar sa kenan daga yawonsa, yashigo falon da sallama, yaji shiru, kai tsaye dakinta
yashiga, a lokacin tana kwance tana bacci, daga ita sai d'an qaramin siket under wear shitaja
har sama, hakan yasa cinyoyinta suka baiyana, hankalin ta kwance tana bacci bataji shigowar
sa ba, yadade a tsaye yana Kallanta, shi sai yau nema ya qarewa yarinyar kallo san ransa, tana
yanayi da Diyana sosai, ahankali yataka yaje gaban gadon ya tsugunna yaja qarewa fuskarta
kallo, saida yagama ganinta tsaf, sannan yakai hannunsa ya shafa kanta Ahankali, Allah ya
temakeshi bata farkaba,Inda tafarka ta kamashi da yaya zaiyi? Shida yake cewa itace take liqe
masa
Ahankali yatashi yafuto yayi cikin dakinsa
Zama yayi agefen gadon tareda yin tagumi hannu bibbiyu, babu abinda yake masifar son yasha
irin qwaya, gashi ya cewa wannan yarinyar yadena sha, amma a yanda yakeji yanzu idan bai
shaba gaskiya akwai matsala, hannu yasa a aljihunsa yadauko su har guda biyu, yasha abinsa
sosai yayi watsi da kwalaben anan, sannan ya kwanta yafara kokarin bacci, yasan cewa kafin
ma tatashi daga bacci yatashi yayi wanka yafice
Dida kuwa ta dade tana bacci sannan tatashi tashige toilet tayi wanka, shaf ta shirya cikin
atamfa dinkin riga da siket, tasan ya Fawaz bai dawoba Dan haka ta nufi kitchen domin dora
musu abinda zasuci
Tafuto falon kenan zata shiga kitchen din taga kofar dakinsa abude, cikin mamaki tace "to
lafiya?"
Dakin ta nufa tashiga kanta tsaye, ranta ne yayi mugun baci ganinsa kwance shame-shame
yana bacci ga kwalaben kayan mayensa nan azube agefe, kenan sake sha yayi, haushi yaqara
kamata, cikin takaici ta qarasa wajansa tana dukansa yatashi amma Fawaz ko gizau beyiba,
awajan ta tsugunna ta dora kanta akan gadon setin kafafunsa tasaki wani irin kuka Mai cin rai,
kuka take sosai tana tunanin Rayuwar ta, duk cikin 'yan'uwanta da aka musu aure tare ko
wacce tana zaune gidan mijinta lafiya amma banda ita, ya Fawaz kullum shaye-shaye, ga duka,
dago idonta tayi ta harareshi Kamar yana ganinta,garama tatashi Tun kafin yatashi Yarufe ta
dawani dukan, shaye-shayen ma yace ya daina gashinan Akwance bai daina ba, to dukanma
tasan cewa bazai fasa ba
Ahankali tatashi tafice daga dakin nasa, ko kallan kitchen din batayi ba tashige nata dakin
tadauko mayafi da wayarta da jakar ta, tafuto daga gidan, saida ta kalli gidan hawaye yazubo
mata sannan tasamu me napep tahau tayi masa kwatancen Inda zai kaita
Yana ajiyeta directly part dinsu tanufa, tana Jan jaka tana share hawaye
Hajiya Farida da Alhaji Habib suna zaune afalo suna tattaunawa akan maganar Diyana, kwata
kwata Adam Yaqi zuwa gidanma bare ayi masa magana yadauketa su koma
Kawai sai ganin Dida sukai afalon tashigo tana kuka, gaban hajiya Farida yafadi, tace "nashiga
uku Alhaji, meyake faruwa ne yara sai dawowa gida suke daya bayan daya?"
Kafin yabata amsa Dida ta qaraso dakin tazauna akan kujera tareda dora kanta akan cinyar
uwar tana kuka sosai
Alhaji Habib yace "ke Dida, meyake faruwa? Kinshigo gida da jakar kayanki bakice mana komai
ba"
Cikin kuka tace "Allah ni nagaji bazan koma ba"
"me yafaru?" cewar hajiya Farida
Dida tace "Mom kullum ya Fawaz saiya dinga shan kayan maye, nace yadena Yaqi ji, rannan
yacemin yadena sha, shine yanzu ma naganshi yasha"
Alhaji Habib yayi ajiye zuciya, hajiya Farida tace "toke Dida waya fada miki ana kama maganar
Mashayi? Ai yanzu zai zauna yadinga yimiki rantsuwa da Allah yadena amma ana jimawa
zakiga yasha, waya kai Dan qwaya biyaiya? Idan gaisuwa ce har qasa zakiga yana gaida
babba Kamar mutumin kirki, kuma yadinga yimiki rantsuwa shifa yadena shaye-shaye, amma
hakan bazai sa anjima inde yaga qwaya yadauka yasha ba, kuma su masu shaye-shaye mace
bata gabansu, bare ayi tunanin zataja hankalinsu harsu daina, da wahala kiga Mashayi wai
yana kula yanmata, addu'ah daya zakiyi Dida Allah yasa Fawaz ya soki, to wannan kam idan
yafara sonki duk abinda kikace zaiyi, amma a yanzu kam saide kiyi hakuri"
Ta kalli Alhaji Habib tace "Alhaji ba zama zakai ba7, tashi zakai kamaidata dakin mijinta"
Dida najin haka ta qara volume din kuka tace "Mom Allah bazan koma ba, dukana fa yakeyi"
Hajiya Farida da Alhaji Habib suka hada baki wajan fadin "Duka!!"
Alhaji Habib yace "subhanallah"
Hajiya Farida tace "a a, to bazaki koma ba Dida, bazakije ya kashe minke ba, ina sonki, tashi ki
shiga daki"
Dida tatashi taja jakar kayan ta tashige dakinta, hajiya Farida tayi tagumi tace "yau naga ta
kaina, yarana har biyu agida,Allah ya hadani da sirikai biyu na arziki dana tsiya, shi na arzikin
ya koro min 'yar tana gida, shina tsiyar matar tagudo tabarshi, kaiiii Allah ka sayaya mana"
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Qaran da wayarsa takene yasa yaji baccin duk ya'isheshi, daqyar yabude idonsa ya kalli
Agogon hannunsa yaga magrib ta kusa, kaiii gaskiya yadau lokaci yana baccin nan, wani kiran
ne yasake shigowa yadauka yana magana daqyar "hello ummah yane"
Ajiya Abida ta Girgiza kanta, Allah ya shirya mata Fawaz, wai ita yake cewa yane tace "naje
Asibiti ne ganin mijin qanwar ka naga family kowa yana zuwa amma bangankaba"
Yace "Ummah meyasamu mijin Ilham din"
"wallahi Accident yayi, harya samu karayama, yakamata de kaje, narasa meyake damunka
Fawaz, gaba daya baka cikin nutsuwarka, anyi ma fada kadena shan qwayar nan amma kaqi ji,
tokaci gaba wataran saita haukatar dakai, yanzu ace mijin yar'uwarka ciki daya yayi rashin lafiya
kusan sati amma ace kai baka saniba, ai shikkenan idan Baqin cikin ka ya kasheni "dif ta kashe
wayarta
" kai ummah tanada damuwa wallahi, menene kuma na ambatar mutuwa? "cewar Fawaz, daga
nan yatashi yashige toilet yayi wanka, tsaf ya shirya cikin qananun kaya, yafuto falon, ganin
dakin Dida arufe yasa bai shigaba, yasan tana bacci itama
Kai tsaye Mota yashiga yakira wayar Ilham din tafada masa a asbitin dasuke, sannan ya kashe
wayar yaci gaba da driving
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Zaune take agefen gadon akan kujera dede setin Inda kansa yake, Dan qaramin handkerchief
ne a hanunta data jiqashi da ruwa tana goge masa kansa dashi, saboda taji kan nasa akwai zafi
Fawaz ne yashigo dakin shida wata nus datayi masa jagora, yana ganin halin da Aslam yake
ciki jikinsa yayi sanyi, wannan hannu duk an nad'e masa shi, ga qananun ciwuka, tashi Ilham
tayi tabashi kujerar Yazauna, anan yake tambayarta yamai jiki
Shiru sukayi na wani lokaci, Fawaz de jiki yayi sanyi, cikin ransa yake magana tabbas dan'adam
ba abakin komai yakeba, kaduba kaga de halinsa Aslam yake ciki rai ahannun Allah shida
bayama shan ko wacce irin qwaya, Allah ya jarabceshi da wannan qaddarar, to idan shine
dayake aikata wannan mugun halin yaya nasa abin zai kasance kenan? Tabbas dole ne yayiwa kansa fada ya shiryu Kamar sauran yan'uwansa, insha Allah yayi
alqawarin daga yau yaraba hanya da kayan maye.
Jiki a sanyaye yayi mata sallama yatafi gida
Shiru Ilham tayi tana kallan Aslam, ita sai yanzu ne take ganin mugun kyansa, ya Aslam ya
hadu ba qarya, amma da qiyaiya tahanata gani,Allah sarki, ko yaushe zai farka?.
Ahankali yafara bude idonsa, yasaukesu akanta, rufe idonsa yayi yana tunani nan take hatsarin
dayayi yadawo masa cikin qwaqwalwar sa, bude idon yayi yaga tabbas Ilham yake gani a
gefensa, meyasa tazo Inda yake? Ai yayi tunanin zatafi kowa murna
Farinciki ya rufe Ilham, cikin murna tace "Alhamdulillah, ya Aslam katashi? Sannu ya Aslam bari
nakira Doc."
Cikin sauri tafice daga dakin yabi bayanta da kallo, menene ya sauya yarinyar nan haka lokaci
daya?
Doc. ne yashigo dakin ya duddubashi tareda yimasa yan tambayoyi sannan yace yaci gaba da
shan magunguna zuwa jibi za'a warware masa hannun nasa, sannan yafita
Ilham kuwa sai murna take bakinta Yaqi rufuwa, kujerar datake kai takoma ta zauna, ta dora
hannunta akan goshinsa tace "ya Aslam sannu, ahadama Tea kasha ko?"
Dayan hannunsa da Babu ciwo yasa yakawar hannunta dake kansa yace "kidena tabani
banaso, ai shikkenan tunda hankalinki ya kwanta, ba haka kike so kiganni ba"
Wani irin kuka ne yazo mata maicin rai, batasan lokacin data fada kansa ta rungumeshi ba, tana
kuka, hawayenta yana d'isa agefen wuyansa, cikin kukan tace "ya Aslam Dan Allah kayi hakuri
Allah nadena"
Aslam kuwa baisan lokacin daya lumshe idonsa ba jin nashanunta masu laushi akan qirjinsa,
dama gwadat yake yaga tadena rashin kunyar kokuma de tarkonsa yakama shima tafara
sonsa
Adede lokacin Adam yashigo dakin, hannunsa dauke da ledojin fruits, murna yafara ganin idon
dan'uwansa biyu yaude yafarka, adaya bangaren kuma kunya ce ta kamashi ganin yanda Ilham
ta rungumeshi tana wani kuka qasa-qasa
Aslam yace "Adam sannu da zuwa"
Ya kalli Ilham dako niyyar tashi batayi yayi qasa da murya yace "qanina fa yashigo, zakisa ya
renani"
Ahankali tatashi tana goge hawayen idonta tace" ya Adam sannu da zuwa, ina wunin "
Adam yayi ajiyar zuciya yace" lafiya Ilham, ashe maigida ya miqe "
Murmushi tayi masa kawai, takama hannun Aslam din tariqe Kamar wani zai qwace mata shi.
Hajiya Na'ila ce tashigo dakin Diyana tana gefenta da abinci a hannunta
Da Adam tafara tozali acikin dakin, yana sanye da qananun kaya, saiyayi mata mugun kyau,
ahankali tasauke idonta kasa, shikuwa Kallanta yake yana magana cikin ransa, Wato maryam
dayace taje gida saiya nemeta wajansa mahaifiyarsa tatafi kenan , dama ai matsalar ka auri
wadda kuke DANGI 'DAYA da'ita kenan, yanzu Inda bare ya aura ko hanyar gidansu bazata
nemaba, Dan Allah kalli wannan shegen kayan data saka duk ya kamata hips dinta awaje,
kuma mama tana gani shine suka futo ahaka
Cikin nutsuwa Diyana tace "ya Aslam ya jiki?"
Yace "jiki Dasauqi Diyana"
Ta kalli Adam dinma tace "ya Adam ina wuni ya aiki"
Shiru Adam yayi be amsa mata ba, haushi yakamata, Hmm zata rama ne
Hajiya Na'ila tace "kema de dabata yawun bakinki kike, kina gaidashi yana wani hura hanci,
ajiye musu Abincin mutafi gida"
Diyana ta ajiye Abincin tafice daga dakin, hajiya ta kalli Adam tace "kasan abinda ka aikata ai,
shiyasa idan na nemeka baka dagaba, to kazo gida ka sameni ina nemanka" tana fadar haka
tafice daga dakin
Aslam yace "Adam kayi hakuri, kasan sha'anin mata sai Ahankali, dole sai kakai zuciyarka
nesa, da niyya ma zasu dinga qin yiwa mutum biyaiya kasan... Su"
Maganar sace ta katse saboda mintsininsa da Ilham tayi ahannu
Adam yayi Murmushi, shikam sun birgeshi, inama maryam zatazo ta koyi yanda ake kula da miji
anan, yace "to insha Allah, nizan tafi, sai gobe idan Allah yakaimu"
Aslam yace "to shikkenan kakira Abba kafada masa natashi please"
Yace "okey"
Daga nan yaja musu kofar, Ilham tayi masa hararar wasa cikin shagwaba tace "shine zakake
fada masa laifi na ko?"
Murmushi yayi yana Kallanta Kamar ba'itaba, Kamar an sauya masa qanwar budurwarsa
Yace "ya jikinki? Yanzu de Babu kuka kin warke sosai ko?"
Kunya takama Ilham, tasa hannu ta rufe idonta tace "dan Allah ya Aslam katashi Muje kayi
wanka"
Murmushi yayi, sannan yafara kokarin tashi, yana jin dayan hannun yana masa ciwon
kadan-kadan
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Jikinsa a sanyaye yadawo gida yana tunanin mutuwa, kai tsaye dakinsa yawuce yabude
kayansa duk wata qwaya datake ciki saida ya dauko ta, nacikin fridge ma yadauko su yazuba
acikin wani kwali yanufi dakin Dida dasu, yanaso ya tabbatar mata cewa yau yadena shan
komai, yanaso yafara tabbatar wa matar sa cewa daga yau Babu me sake kiransa da Mashayi Amma me, yana bude dakin yaga bata nan, qarasa shiga yayi yaga kofar toilet dinta abude, afili
yace "a a, to ina yarinyar nan tatafi ne? Nasan duk Inda zataje tana tambayata ai"
Cikin sauri yafuto yadawo kitchen bata nan, yaduba compound bata nan, kwalin dake hannunsa
yasaki yafadi qasa, yasake komawa cikin gidan da gudu, karon farko daya fara ambatar
sunanta "Dida! Dida!! Dida!!!, ina kike ne?"
Wasa-wasa saida Fawaz yagama duba gidan tas yaga bata nan, Kamar mahaukaci haka ya
koma dakinta ya kalli Inda akwatunanta suke yaga sunragu, anya kuwa Dida ba guduwa tayi
tabarshi ba? Kode taganshi ne dazu bayan yasha maganin mayen nan? Tabbas yarinyar nan
taganshi, awajan ya sulale yazube akan gwiwar sa tareda dafe kansa ♂️, ya zata masa haka?
Dasauri yatashi yafuto daga dakin yashige motarsa bai zarce ko'inaba sai gida
Kai tsaye part dinsu yatafi, hajiya Abida tana zaune tana kallo sai ganinsa tayi yashigo Kamar
mahaukaci
Tace "subhanallah Fawaz lafiya?"
Yana daga tsaye yace "umma Dida batazo nan ba?"
Tace "Dida kuma? Aini rabona da Dida Tun bikinku Fawaz, kai baka taba hankalin dauko ta ka
kawomin ita ko wuni ne muyi ba, itama batazo ba"
Gabansa ne yafadi, Yazauna aqasa kafet din falon jagwab, Idanunsa suka kada sukai jajir yace
"Innalillahi wa inna ilaihir raju'un , Umma Dida tagudu tabarni" sai kuka
Gaban hajiya Abida yafadi tace "kaini banason sakarci, yanzu Inda qannanka suna nanma haka
zaka zauna kanamin kuka, kayi min bayani dalla-dalla meyake faruwa?"
Cikin kuka yace "umma...gani...ganina..tayi nasha wani magani shine... Shine...tagudu"
Tace "ahaf, ni nasan da walakin goro amiya, haba Fawaz, yarinyar nanfa tana kokari, aure
kusan shekara biyu amma bata taba kawomin kararka ba, lokacin da akace anhadaka da'ita
yarinyar nan ko uhm batace ba, duk family dinnan kowa yasan anfi qwararta akan sauran
'yan'uwanta, ai kai kamata yayi ma ace kayiwa yarinyar nan gata samada kowa acikin gidannan,
kayi mata abinda takeso ka fifitata saboda ta rufama Asiri ta zauna dakai, yanzu ma dakace
akan kasha wani magani tagudu bawani magani dazaka sha Fawaz bayan na maye "
Cikin kuka Fawaz yace" to umma kuma saita gudu tabarni "
Tace" a a, bamu bincikaba ba zamuce tagudu ba, tashi Muje wajan maigadi muji ko yaga
shigowar ta gidan "
Tashi yayi yana goge hawaye yabi bayanta, suna zuwa wajan maigadi ya tabbatar musu da
cewa tabbas yaga Dida Tun rana tashigo gidan, shine ma yabude mata get
Hajiya Abida tayi masa godia takoma part dinta, ta nemi kujera zata zauna kenan Fawaz yasa
hannu yariqe rigarta yace "Ummah matata"
Qwace rigarta tayi tazauna tace "tome Zan maka Fawaz? Bakaji da bakinka ance tazo gidaba?
Ai kasan hanyar part dinsu"
Zama yayi agefen qafafunta yana kuka Kamar mace yace "Ummah Allah nide adawomin da
matata, ya za'ai naje part dinsu bayan nasan mamanta bata sona"
Hajiya Abida tace "kaga Fawaz karufe min baki, ya zakazo kasani agaba kanamin kuka?
Lokacin daka mata laifin kayi shawara Dani? To bari kaji, tunda akai auren ku har yau Babu
Wanda yace uffan akan zaman aurenku, Dan haka ba zanje part din hajiya Farida tafadamin
magana inqyale taba, wallahi saide kaje"
Bece da'ita komai ba, yatashi yafice daga part din, yayi nasu Dida, hankalin sa kwance yatura
kofar falon, a lokacin kuwa Dida tana zaune itada Hajiya Farida suna kallo, kallo daya tayi masa
tadauke kanta, cikin ransa yace tana nan kenan
Hajiya Farida tace "a a Fawaz kaine atafe, sannu da zuwa, shigo ka zauna"
Fawaz yanemi waje Yazauna yana mamakin yanda ta karbe shi hannu biyu, sai sunkuyarda
kansa yake qasa dan karsu gano yasha kuka
Hajiya Farida ta miqe tsaye tace "Dida kawo masa ruwa mana" daga nan tayi cikin dakinta
tabarsu su biyu, cikin ranta tace tasan bazai wuce biko Fawaz yazo ba, ita kuwa bada itaba,
yaje su qarata atsakaninsu, tunda taga Dida tadawo gida tasan cewa qarshe yakai yarinyar
shiyasa tayi fishi tataho gida, to ba zatayi mata dole akan takoma gidansa ba, Dan daga nanma
zata iyayin wani gidan su nemeta su rasa, gara yanda tazo da qafarta, takoma da qafarta,
amma bazata bakinta a sabgar yara ba
Daga kan kujerar yasauko yadawo kusa da ita har tanajin yanda numfashinshi yake sauka akan
fuskarta yace "Dida"
Kallansa tayi, yaune karon farko data tabaji yakira sunanta, harara ta sakar masa tatashi ta nufi
hanyar dakinsu, shima yatashi yabita, tana shiga dakin tarufo kofar, shikuma yakawo kansa zai
shiga sai qumm tabige masa fuska
Kadan yarage Fawaz yayi hauka agidan surukai , haka yafuto jikinsa duk yayi sanya, ko
kallan part dinsu baiyi ba yaja motarsa ya koma gida
❣️❣️❣️ ❣️❣️❣️
Yau Tun safe hajiya Na'ila bataga futowar Diyana ba, Dan futowar datake ta yataya aiki ma yau
shiru
Tace "to wannan yarinya ko lafiya?" tashi tayi ta nufi dakin nata, tana zuwa ta risketa tana kuka
adaki, hajiya tace "subhanallah Diyana menene kuma yafaru?"
Cikin kuka tace "Hajiya niso nake natafi gidanmu"
Hajiya tanemi waje tazauna agefen Diyana tace "ai dole kice zaki tafi gida Diyana, tunda shi
yazo ya ajiye ki baya tunanin zuwa ya dauke ki, bansan yaushe Adam yakoyi taurin kaiba, nace
yazo gida ya sameni Yaqi zuwa, nakira wayarsa kuma yadena dauka ma yanzu, inde baso yake
na yiwa babansu maganar ba bansan yaya zanyi ba, hada kayanki ina zuwa "
Gyada kanta tayi, sannan tadauke komai nata na dakin itama ta shirya, hajiya ce tadawo dauke
da cup ahannun ta da zuma aciki, tace "ki kalli abinda Zan hada