Showing 33001 words to 36000 words out of 44890 words

Chapter 12 - DR AHMAD BOOK COMPLETE BY Maman Khadija .pdf

16 Mar 2025

7232

yayi wajan
kwana biyar sabida rashin lafiyar da tayi.
Kusan babu kalar shirmen da bemata ba sabida tsabar gigicewar da yayi, jiyayi kamar ranar ya
fara saninta sabida irin samun nutsuwar da yayi akanta jikinta yayi zam-zam ta k'ara armashi
har ya kasa gane farkon yinshi da na yanzu.

Cikin sanyin murya ya fara mata magana yayin da hannun shi ke cigaba da yawo ajikinta,

"Babyna kin gaji ko?"

"Uhumm..!"

Kawai ta iya cewa sabida gajiyar da tayi.

Ganin tayi shiru yasa shi cigaba da lalubarta da alama sake yi zai yi sabida ba karamin dad'i
yajiba yanzu saima ji yayi kamar ya tsokano ma kanshi buk'atarta.

Cigaba da murzarta yayi har saida yaji ta sakar mishi kukan ta gaji sannan ya saura mata tare
da rungumeta ajikin shi yana d'an jijjigata jikin shi saida yaga tayi lamo tana sauke nunfashi
sannan ya tashi a hankali yana cewa,

"Bari in had'a mana ruwan wanka kinji ko..?!"

Tare suka yo wankan su har lokacin bebar lakud'ar jikinta ba ita ko kasala sai dai kawai tabishi
da manyan idanuwan ta farare kal.

****

Sun jima tsaye kofar gidan suna jiran ganin yaron da zasu aika cikin gidan domin sam basu
yadda da cewa wai wannan gidan nasu Ahmad bane, domin cikin suma akwai wa in da basu
yarda da cewa Ahmad d'in likita bane.

Cikin ikon Allah saiga malam Mamuda zai shiga gidan domin tunda suka tare bezo yayi musu
Allah ya sanya alkhairi ba, shine yaga yau tunda asabar ce yasan duk suna gida bari yaje.

Saida sukai kallon-kallon tsakaninsu kamin malam Mamudan ya mika musu hannu sukai
musabaha domin shi yaga basu da niyyar bashi hannun da alama dai mamaki ne ya kusa
kashe su.

"Kushigo mana kuzo mushiga ai sunanan ciki yau hutun karshen mako har Dr d'in ma nasan
yana nan ciki."

Cikin sanyin jiki suka bi bayan shi, yayin da idanunsu keta yawo acikin gidan domin ba wata
k'arya aka tsaraba agidan ammafa bak'aramin kyau yayi ba musamman da har yanzu yake
kamshin sabon fenti.

Zaune suka taddasu d'akin Maman Ahmad na kusa da Maman shi yayin da khadija ke kwance
acinyar Maman Ahmad d'in na mata matsar kafafu ita kuma Maman nata shafar gashin kanta
tuni ita tayi barcinta sukuma hira kawai suke abunsu bazaka tab'a gane cewar suruka akewa
wannan gatan ba.
"Sannu da zuwa Ahmad d'in da Maman kema malam Mamuda kamin idanun su ya sauka akan

wa inda ke bayan shi.

Fuskar Maman babu wata damuwa sai dai tuni ta Ahmad ta canza dan haka komawa yayi
kawai ya zauna tare da gyarama khadijan kafafunta wa inda ya sauke daga jikin shi yanzu.

Malam salisu ne ya fara magana cikin alhini da karayar zuciya yace,

"Dama mun zone domin muyi zumunci tunda kun yaddar damu sai kace ba jinin kuba."

Wani mugun kallon takaici Ahmad yayi mishi kamin yace cikin gadara,

"Ahh zumuncifa kace malam? kanaso kuyi shari'a da zumunci a gaban Allah kenan tunda har
zaka iya zuwa wajan mu da sunan wai zumunci, koda yake kila ka manta irin korar dabbobin da
kukai mana tare da yanke duk wata alaka datake tsakanin mu? kamanta ranar da ka dinga
kiranmu da shegu karnuka kuma lalatattu dan kawai munje sada zumunci daku? ka manta ranar
da kace mu d'auka bamu da sauran dangi acikin garin charanci sabida kun ruga kun ya femu?
kun manta ranar da kuka tasani nida kanina kuka dinga tsine mana albarka da zagin cin
mutunci ga mahafiyar mu kuma a gaban idanun mu?

Kamanta ranar da kake furta cewa kune kuka kashe mana mahaifi kuma kani agareku sabida
kawai beyi muku d'in kunan daya saba mukuba?

Kun manta kace duk ranar da muka sake waiwayar charanci lallai sai kunyi sanadin ajalina
musamman ni danake babba?
a hakan kuke tunanin zamu kuma waiwayarku harmu sada zumuncin?"

Ckin matukar sanyin murya ya furta,

"Ina yawan zuwa charanci ba tare da sanin kuba haka ma Mama sabida inaso inga ko zuciyarku
ta sauya kunfara son mu, sai dai kash! kullum baku da aiki saina binmu da mugun kalaima na
b'atanci da lalacewa, idan ban manta ba ko wata hudu da suka shige ankama yaronku musa
yayima wata yarinya ciki, me kace a ranar? cewa kayi inama me sunan babane aka samu da
laifin nan.
sabida haka kunga wannan ya nuna musu malam Mamuda wanda ya zabga tagumin mamaki
da tsoran halin mutanen ya hanashi ko motsin kirki, Ahmad yaci gaba, to wannan shine uba
agaremu nida k'anina bamu da kowa saishi shine ya tsaya mana haihuwar mune kawai beyi ba
sannan daga karshe kun san gatan da yayi min wanda Ku kuka kekashe kuka kasa yimin?
nasan baku saniba to wannan d'iyarshi ce ya aura min kamar yadda kukemin fatan inyima yaran
mutane ciki to hakan be faruba sabida ya bani d'iyar shi tun kamin ta mallaki hankalin kanta,
yanzu haka cikina ne na halal a cikin jikinta kuma ban tab'a shaye-shaye ba kamar yadda kuke
min fata, ni _AHMAD BANI DA SAURAN WATA ALAKA DAKU_, dan haka kuyi gaggawar barin
gidan nan kamin in had'aku da hukuma."

"Kai Ahmad gidan ku, nace kajiko gidan ku, nace iyayen naka zaka kai ga hukuma dan iya
shege to inji kafara kaga yanda zanyi dakai..."

Cewar malam Mamuda da yayi karfin halin yin maganar, itako Mama ai kuka kawai take yi
sabida jitai komai ya dawo mata sabo sannan bata tab'a tunanin shi Ahmad d'in ya rike
abubuwan da suka faruba a baya ba.

Ahmad da takaici ya kusa kashewa share kwallar idanunshi yayi kamin d'auki khadija cak!
daketa barcinta yasab'ata akafad'a yabar d'akin, gaba d"aya suka bishi da idanu domin har
yanzu anrasa wanda zai kuma tankawa cikin su, saima sheshshekar kukan Maman dake tashi
kadan-kadan cikin dakin.
Sunjima cikin shiru kamin sufara bata hakuri daya-bayan daya, tare da neman gafararta data
yaranta duk da cewa sunga rashin sauki dagashi gurin *DR.AHMAD* d'in amma dai suna so ta
yafe musu.

Malam salisu ne ya d'ora da cewa,

"Tabbas muncika azzalumai Habiba domin tun tasowar iro muke cutar dashi sai gashi duk da
abinda muke mushi hakan besa Allah ya tabar da shiba sai ma yayi mishi d'aukaka sama
damu, muna cikin wani hali munsan cewa alhakin kune yake bibiyarmu kuduba irin gidan da
kuke ciki babu abunda kuka rasa, muko kullum cikin tashin hankali muke sabida yanzu tun a
duniya Allah kefara sakayya dan Allah kuya femana kuyi mana afuwa tabbas masu hali irin
namu nanan sunada yawa a duniya, munafatan Allah ya shirya su tunkamin lokaci ya kuremusu
kamar yadda muka sami kanmu aciki kuyi hakuri Habiba muntub'a wallahi harga Allah kuma
bazamu kuma aikata wani abuba makamancin wannan domin munga ishara."

Saida malam Mamuda yasa baki sannan tace ta yafe, aiko sukai ta godiya tare da cewa zasu
kawo iyalansu domin suka waje.


MALAM Mamuda ne ya fara magana cikin farin ciki domin tabbas yajima yana fatan zuwan
wannan ranar yacce,

"Tabbas mun godewa Allah daya nuna mana wannan lokaci munafatan Allah ya kuma kare
zumuncin shi, gaskiya nayi farin ciki sosai wallahi na tabbata malam ibrahim shima zai yi farin
ciki duk da yake kwance cikin k'abari Allah yaji kanshi yayi mai rahma."

Gaba d'aya suka amsa amin cikin jimami.

Malam Mamuda ya d'ora da cewa,

"Tabbas mutane da dama sukan aikata kuskure batare da tunanin kuskurene ba misali zaka

sami yaron wani kaita zagi tare da aibatashi da munanan kalamai sai-dai sani ne da ba muyi ba
amma a duk lokacin da kai hakan to tabbas mala'iku sukan maido da wa'innan muyagun
kalaman ne akan iyalinka, shi yasa sai kaga kaima acikin iyalinka kasami me irin wannan halin
koma fiye,
Haka kuma idan kayima iyalan wani kyakykyawan addu'a to tabbas saita sami naka iyalin
sabida haka yaka mata mu kula sannan mudaina kullatar marayu domin dayawansu Allah baya
tabar dasu kuma tabbas wataran sai kaci arzikinsu Allah yasa mugane.

Sannan ina iyaye masu tsatstsauran ra'ayi akan yaran su? kanada yaro namiji kuma baligi
cikakken mabukaci amma ku hanashi aure harsai ya gama karatu ya sami aiki kuma ya gina
gida yasai mota tsawon wannan lokacin kasan iyakar zunubin daya kwasarma kanshi? to karka
manta kuma iyayenshi akwai naku kason na zunubin domin laifin kune duk wani abu da zai
aikata
.
Yima yara k'ana nu fyad'e ya yawaita sabida haka aure da iyaye suke yi sabida wani buri nasu
nada ban, yarinya zata nuna tana son aure amma iyaye suk'i yi mata sai tasami me kud'i ko
kuma sai tayi zurfin karatu wannan kuskureni domin sha'awa babu abinda baza tasa mutun ya
aika taba, misali yanzu shi Ahmad me yarasa? Babu, itace amsar anyi mishi aure alokacin da ya bukata kuma gashi yayi karatun shi hankali
kwance, yanzu inda ba ayi mishi ba mun san iyakar yaran da zai lalata? bamu saniba dan haka
yaka mata mu iyaye mu kula tunkamin ranar da Allah zai tirkemu da tambayar yaya muka tafiyar
da amanar daya bamu.
Bari muje sallah Habiba a sama musu abinda za suci kamin mu dawo zan shawo kan shi
Ahmad d'in insha Allah."

Godiya suka yima malam Mamuda kamar zasu yi mai sujjada sabida farin ciki, a haka duk suka
yi alwala suka fice, itako Maman kitchen ta shige domin ganin ta dafa abu me sauki wanda zasu
ci......










*MAMAN KHADIJA*🙇🏻�♀
[3/14, 2:43 PM] ⓠʊ¥ґѦ℮м℮¥: *💗DR.AHMAD💗*

40

*NA MAMAN KHADIJA*🙇🏻�♀

Edit by *HAJJA CE*👈

*HASKE WRITER'S ASSO...*💡
(Home of expert & perfect writer's)



*D*uk iyakar lallashin malam Mamuda gurin Ahmad daya yiyafiyar amma ta gagara domin,
bayan dawowar su daga masallaci sunci sun koshi kowan ne baki awashe Ahmad ya yunkura
zai tashi malam Mamuda ya hanashi tare da bashi hakurin da suketa fama dashi, idanun shi
sunyi jawur sosai yake kallon yayyen mahaifin nashi da kannenshi d'aya bayan d'aya kamin
yace da kyar.

"Na yafe musu duk abinda sukai min ammafa babu ruwana da huld'a dasu domin ina jin tsoran
in sake dasu su cutar damu kamar yadda sukai sanadin d'an uwansu."

Ganin ya bar d'akin yasa malam Mamuda kallonsu tare da cewa,

"Kuyi hakuri insh Allah zai sakko kunsan yaro da rikon abu dole sai a hankali zai manta."

Itama matma hakurin dai ta basu tare da musu alkawarin zuwa su su duka garin domin sada
zumunci.

***

"Ya Ahmad gaskiya be kamata kai musu haka ba naji baba nata fad'a dan Allah kai musu hakuri
su duka ka yafe musu, kaga sun tuba zaka sami ladan yafiya kaji kaji..?!"

Murmishi yayi tare da rungumota jikin shi ya fara shafar cikinta wanda yake ashafe kamin yace,

"Nima na yafe musu baby kawai dai haushin su na keji wallahi na kasa manta abinda suka yi
mana, oya haa bakin ki amshi abincin idan kinci da yawa to zan fita yawo dake anjima da
yamma."

Baki ta bud'e da sauri a hankali ya dinga bata yana janta da hira hartaci da yawa ba tare da
tasani ba, sai da ta kammala sannan ya kwashe kayan ya mayar kitchen ya dawo kusa da ita ya
zauna.

"Sannu kaji mijin Khadija, Allah yabar mu tare ya k'ara mana hakurin juna.."

"Amin Dijama ta 'yar albarka ke kad'ai kike iyawa dani Allah yayi miki albarka."

"Amin my Dr ai kaine duk ka koya min ka raineni akan duk yadda kake so na kasan ce Khadija
love you so much."

Da sauri ya kankameta a jikinshi tare da furta,

"Ahmad love's you so so very much..."

***

Ahmad da kanshi yayi tunanin fara azumi domin samun sauk'in rayuwar shi data khadijan shi,
sai dai lokuta da dama adaddafe yake kai azumin sabida dama yunwa takan kwantar da
sha'awa ammafa da kaci ka koshi zata iya tasowa.

Hakan yasa idan yana yi baya zuwa gida sai gaf da magriba sabida ko kwalliyarta ya gani sai
taji abu ya fito mai amma idan gaf da magriba be zai koma yayi sallah a masallacin kofar gida
sannan ta shiga ciki da haka yake samu ya saurarawa Khadija dama Zainab tunda ta tafi ba'a
biyo sahuba shima bebiba tunda ta nuna mai bazata iya maiba.
*Bayan wata bakwai*
Cikin ikon Allah rayuwa ke juyawa wataran da dad'i wataran asami aka sin hakan. a bangaren
su Ahmad sun cigaba da zumunci da 'yan uwansu suna matukar girmama Ahmad d'in domin
yana kokarin ganin ya manta da komai daya faru abaya dan ya kyautata musu, sannan sukan
ziyar ce su akai-akai domin temakon su shi yasa suke mishi kallon babban mutun ballantana da
Allah yayi mishi arziki dai-dai bakin gwargwado.

A bangarenshi da khadija kuwa sai dai ace alhamdulillah domin cikinta harya shiga watan na
haihuwa tana matukar samun kulawa fiye da duk yanda zan misalta muku musamman wajan
mijinta ya d'auketa da matukar muhimmanci arayuwar shi ko washh ta furta to yanzu hankalin
shi zai tashi, kullum cikin lallashi da bata labarin kaunar shi gareta ya keyi abinda ranta keso shi
suke mata, domin samun surkai irinsu Mama zai yi wahala bata tab'a cewa babana meyasa
kaima khadija abu kazaba ni bakai min ba? A'a sai dai kullun cikin tuna mishi take khadija
taimaka halacci babana kadda kai mata butulci tayima iyayenta biyayyar zama dakai tunbaka
da hankali sabida haka kadda ka cutar da ita, sannan ka dinga saurara mata da bukatarka
sabida cikin jikinta kadda ka yadda ka koya mata gudunka kadinga tausaya mata domin tana
bukatar hakan. kullun Mama bata barcin kirki kusan kwana take yi akan sallaya tana rokama
khadija saukin haihuwa da zuri'a d'ayyaba.

Shin iyaye mata surukai munayin hakan kuwa?
nasan da yawa amsar itace a'a sabida haka kadda mu manta duk abinda kaima d'an wani to
tabbas yananan zuwa kan naka. in kai me kyau zaka gani haka in kai sab'anin hakan shima

zaka gani Allah yasa Mu dace, idan mun dace Mu dafe abunmu....

****

"Babyna zan fita babu abinda kike bukata?"

Tulelen cikinta ta shafa kamin tace,

"Honey yayana kadan d'ebe min kewa mana kota minti talatin ce ina bukace da kai naga kwana
biyu baka san yi kuma ni wallahi ina..ina so."

Zama yayi gefenta tare da damke hannayenta cikin nashi yanajin wani irin mugun sonta na
ratsa sassan jikinshi murya can k'asa kamin yace,

"Ayy sorry babyna ina jin tausayin kine shi yasa nake hakura amma tunda kinaso bari muyi
sannan na tafi asibiti but babu inda kemiki ciwo yanzu ko..?!"

"Ni dai babu sai ciwon buk'atar mijina itace kawai take damuna."

Yana jin haka yayi saurin zame takalmin k'afarshi dama me neman yin kuka ne sai aka jefeshi
da kashin awaki kunga kuwa sai yi.

Kusan da dabara ya samu biyan bukata sabida girman cikin yau kwana uku kenan ta lura ko
bacci baya yi sosai kuma abinda ke damun shi kenan shi yasa tayi mishi wannan dabarar dan
yasamu sakewa koda kuwa ita da babyn zasu takura.

Saida ya temaka mata tayi wanka sannan shima yayi ya sake kintsa jikin shi yayi mata sallama
yana ta faman sa mata albarka zuciyar shi wasai a haka ya fita.

****

"Wayyo Allah na...!"

Cewa khadija wadda taji mararta ta isheta da tsinkulawa. da kyar ta kai hannu kan wayarta ta
kira Maman kamin ta ajiye wayar Maman ta shigo.

"Sannu..sannu khadija oh ikon Allah kamar ana jiran babana ya bar gidan? kodai shine ya
dameki?"

Banza tayiwa Manan ita dai hannu kawai take yarfewa ganin haihuwar tariga tazone yasa
Maman gyara mata wajan zama cikin yardar Allah ko minti arba'in ba tayi ba saiga yaronta
d'irkeke gundumeme kato tabarkalla Masha Allah, kuma daga ganin shi lafiyayye ne ko dan
ihun daya cika musu kunne dashi.

Nan da nan jikin Mama ko ina rawa yake sabida murna ta rungume jaririn da jinin shi a jikinta da
komai tana addu'a kamin tafara gyara shi ta na d'eshi ta koma kan khadija wacce tuni barcin
dad'i ya fara d'ibarta.

Goge mata jikinta tayi sannan ta kamata ta maida ita gado sabida tasamu isasshen hutu sabida
anaso idan kika haihu akalla kisami awa hud'u a kwance kamin wanka ya biyo baya sabida yin
wankan da wuri shine ya kan kawo bugun jini da sauran su.

Zama tayi ta goge yaron nan tas! sannan tasa ka mishi kayan sanyi ta zuba mishi ido babu inda
yaron ya baro uban shi sai bud'e idanun shi yake yi yana rufewa jitayi wasu hawaye sun zubo
mata tace,

"Oh yanzu da basu yi mishi aure ba kila can za'a tsiyayar da yaron nan kila ma a kawo mata shi
ya zamto itace zata raini d'an da bana halak ba da hannunta, amma yanzu murna take ji take
tamkar ta suma danjin dad'i.

Godiya ta dinga jerama lillahi kamin ta rab'ashi gefen Maman shi wacce tuni tai barci, tashi tayi
tafara gyaran wurin cikin kanknin lokaci d'akin ya d'auki kamshi kamin tayi waje da kanta ta
d'auraye kayan ta shanya sannan ta d'orama khadijan ruwan tea wanda yaji kayan yaji saida ta
had'a komai har kunun waken soya tayi mata sabida ruwan nono yazo sannan ta d'ora musu
ruwan wanka domin daga mejego har jaririn ba aso daga haihuwa asamusu ruwan zafi ajiki
hutunsu akafi bukata bawai wankan ba.

*****

kiranshi na hud'u kenan sannan yaji an d'aga sallama tayi mishi kamin tace,

"Honey yayana ya aikin naka?"

"Lafiya lau babyna ya kike ya ajiyata?ina fatan duk lafiya kuke ko?!"

"Lafiya lau muke wallahi ga Mama zaku yi waya."

Maman

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login