Showing 42001 words to 44890 words out of 44890 words

Chapter 15 - DR AHMAD BOOK COMPLETE BY Maman Khadija .pdf

16 Mar 2025

7241

zauna dan jiranshi yayinda take tuno mijin nata wai kewa sai kace da safe
be taketaba amma yanzu biyu na rana harya fara maganar neman k'ari Allah ya rangwanta mai.

Har ya tsaya gefenta hankalinta baya wajen shi saida taji yana k'okarin d'aukarta sannan ta
farga, gaishe shi tayi sannan ta zagaya ta shiga motar, madarar Hollandia me sanyi ya mik'a
mata saida ta shanyeta tas! sannan tayi hamdala tana kallonshi,

Girarshi ya d'aga mata kamin yace,

"Kin dawo dai-dai ko?!"

"Sosai ma wallahi yunwa ba tayi ba."

"Ina fa tayi ai shi yasa zakiji almajiri d'an malam yana cewa iya yinwa zata kasheni."

Duk suka yi dariya koda suka koma gida kallo Mama tabisu dashi kamin tace,

"Ikon Allah daga ina haka ku kuma?"

Shigewa d'aki khadija tayi tana dariya yayin da shi kuma Ahmad d'in yayi tsaye gabanta yana
sosar kanshi kamin yace,

"Mama ina abba ne banji motsin shiba?!"

"Hummmm Allah-Allah ya shiryaka babana amma dai ka dinga kula da aikinka kaji ko? ga abba
can yau barcin rana ya keji."

"Toh Mama insha Allahu a ci gaba da yi mana addu'a."

"Muna kan yinta ai banana."

Da haka ya sulale zuwa b'angaran su,

"Baby na babu kara shine zaki gudo ki barni da Mama ko?"

Dariya tayi kamin tace,

"To ai tasan halin 'yan kayanta tsayawar me zanyi ni kuma..?!"

Tare suka watso ruwa sannan ta kula dashi saida ya sami nutsuwa sannan ya shirya yabar
gidan itako nan yabarta tana barcin gajiya.

****

Bayan wata hudu:-

Rarrafe yaron keyi yanata zagaye gidan yana wasanninshi shi kadai kyakykyawa ne na gaske
gashi lafiyayye yasan kowa na cikin gidan ga d'an karan b'arna kamar sun had'a kawance da
b'era. da yake weekend ne sam kiriniyar shi ta hana uban barci wanda tuni ya keso yayi barcin
amma wasannin da yaron keyi shi kawai ya keji akunnuwan shi.
Jikin shi ya zare daga na khadijan kamin ya tashi dogon wando ya saka sannan ya nufi tsakar
gidan inda ya kejin hayaniyar yaron, nan ya ganshi ya fara tsallen a d'aukeshi, Mama dake gefe
tana dariya tace,

"Ya hanaka barci ko? ai abba badai kiriniya ba."

Sama ya dinga cab'e yaron suna dariya kamin yace,

"Wallahi Mama motsinshi kawai nakeji ko barcin ranar ma ya kiyi, amma bari na kama
Mamanshi kila in tabashi nono yayi bacci."

Yana farashan nonon yayi barci sai gashi su duka sunyi barcin har Mama wadda dama itama
motsinshi ya sata zama tsakar gidan dan kadda yai wajen ruwa.

Cikin ikon Allah komai na tafiya tsaf yanda suke bukata basu da wata matsala kullum arzikinsu
karuwa yake kamar yanda temakonsu ga mabukata yake karuwa lokaci zuwa lokaci suna zuwa
malumfashi tare da charanci domin ziyarar 'yan uwan su.

****

"Wai kai dr. bazaka iya k'ara aure bane kaduba kaga yadda yarinyar nan take ta binka kaiko
tausayinta ba kaji ne?!"

Cewar dr. Hassan wanda ke zaune cikin office d'in DR.AHMAD din suna hira, wani.......








*MAMAN KHADIJA*🙇🏻�♀
[3/14, 2:43 PM] ⓠʊ¥ґѦ℮м℮¥: *💗DR.AHMAD💗*

45

*NA MAMAN KHADIJA*🙇🏻�♀

Edit by *HAJJA CE*👈

*HASKE WRITER'S ASSO.....*💡
(Home of expert & perfect writer's)

*KARSHE*💃🏻

*W*ani murmushin gefen baki yayi kamin yace,

"Dr. Hassan kenan, kana tunanin idanuna zasu iya kallan wata mace alhalin ina da khadija
agida? To wallahi bari kaji wani abu da baka sani ba khadija ta zama wani b'angare na rayuwata
na tabbata shigarta damuwa zai iya saka ni haukacewa, kowa ne bil adama daka sani yana son
me kyauta ta mishi, khadija bata tab'a barina cikin halin damuwa ba kullum burinta ta gani cikin
farin ciki to kana ganin nayi mata adalci idan nace zanyi mata kishiya?

Kin yi mata shine kawai sakayyar da zan mata a duniya, yanzu alhalin wahalata babu kalar
wacce bata shaba, kuma kadda ka manta na baka labarin aurena da Zainab babu kalar
soyayyar da bata nuna minba amma takasa iya zama dani balle wannan dana san dan wasu
abubuwa kawai take sona.
Dr Hassan da khadija na saba ta zamani nazama ita na tabbata yanda muka koyama juna ba
zamu iya rabuwa da junan muba domin khadija rainonace ninenan na raineta na kuma koya
mata jurema bukatata tun tana kuka hartazo ta saba, tun ana zagin iyayenta yanzu har anbari,
nikam bazan iya kara aure ba kai kodana cema zan kara na tabbata Mama bazata yadda ba
ballema ni kaina bani da sha'awar yi my Dijama ta isheni rayuwar duniya."

Ajiyar zuciya me k'arfi dr. Hassan ya sauke kamin yace,

"Gaskiya ne dr. Ahmad kuma na fahimceka, Allah yabar kaunar tsakaninku ya kuma kore
sharrin shaid'an azaman ku kuma dama gaskiya ya kamata khadija taji dad'i a wajanka kodan
iyaye su sami kwarin guiwar kuma bawa yaro kamarka aure, sabida duk wanda yaga ka
wulakantata tofa zaiga kayi butulci kamar yadda su sukai maka halacci domin maganar gaskiya
mahaifinta babban mutum ne kuma ya rike amanarku sai dai muyi mishi fatan Alkhairi Allah ya
kai lada mizani."

"Amin ai shi yasa nama fidda wani kwad'ayin aure araina domin babu wani abu dana rasa daga
gareta wallahi duk jarabata bata tab'a guduna ba kullum cikin temakamin take koda bataso
domin ni kaina nasan wani lokacin ina takurata amma sam bata nunawa ita dai burinta kadda
inje innemi na waje, nasan ko aurena da Zainab kaddara ce kawai wallahi."

KHADIJA kenan wayayyar matashiya me matukar kyawun gani kusan yanzu ne take tashen
balagarta ta cika ta batse idan ka ganta bazaka tab'a cewa wai tasan wani abu shi aure ba balle
ai maganar yaro, tana da jiki me kyau sannan ga gyara da take samu kusan koda yaushe daga
mahaifiyarta da surukarta boko ta fara ratsata shi yasa yanzu sai abun yayi matukar da cewa da
ita.

Zaune suke fitowar su kenan daga dakin lecture ida ta k'awarta konace aminiyarta domin ita
kadaice kawarta acikin makarantar sai dai wa inda ake gaisuwar mutunci dasu.

khadija ta kalli Fatima bayan sun zauna tace,

"Kai Fatee kin rame da yawa wallahi ki daure kidinga cin abinci sosai ke kanki zaki fijin dad'in
jikinki kinga nima haka nai laulayin Abba har kuka nakema ya Ahmad idan zai bani amma kuma
danaci sai inji dad'in jikina."

Yamutsa fuska fatima tayi tace,

"Wallahi lamarin ne da takura khadija sam banijin dad'in jikina ga fitinar Usman sam be son
zaman lafiya be San yadda nakeji ba Sam.."

Dariya khadijan tayi kamin tace,

"Anzo wajan, ai in dai wannan matsalarce hakuri kawai zaki yi da addu'a amma wallahi akwai
mata da yawa da suke fuskantar wannan damuwar, to amma kuma wani lokacin sai naga
bawata damuwa bace indai zaki iya daurewa domin zaki kuma daraja a idanun shi sannan idan
kin matsa kin rabu dashi bakisan wanda zaki fad'ama mawaba, kumafa akwai wa inda sukafi
mazajen mu bukata ma kuma suna zaune da matayen su lafiya. kinga ni anyimin aure tunban
san komai ba na rayuwa amma a haka naima iyayena biyayya lokacin da na fahimci manufarsu
gareni domin temako ne, duk wanda ya temaki wani hakika kaima Allah zai temakeka, da
babana be kai zuciyarshi ne saba yabawa ya Ahmad aurena ba na tabbata da Allah ne kadai
yasan iyakar adadin yaran da zai lalata sabida yanada matukar karfin sha'awa kuma kila ciki
harda ni domin yadda muke dasu babu abinda bamayi kinga da nai hakuri kuma na jure baga
shiba yanzu hadda yaron mu na halak malak kuma sai dai in bada labari."

"Haka ne khadija shi yasa nima na ke son yin koyi dake wallahi sai dai nakasa wani lokacin
jinake wajan ya koma kamar banawaba, sai naji duk na tsane shi musamman dana sami cikin
nan ga laulayi ga lalurarshi da wanne zanji?!"

Dariya khadijan tayi kamin tace,

"Zan baki shawara guda d'aya kacal fatima, shawarar itace kimaida kayan marmari abincinki
sannan ki dirfafi dafa zuma da mazarkwaila da kanunfari kinasha insha Allah zakiji wani lokacin
da kankima kinaso, nikam bana huld'a da duk wani abu mesunan maganin mata amma nasan
nafi karfin wulakanci ga mijina wallahi dan haka kikama mijinki tunkamin ya fara gajiya da
gardamar da kike mishi yafara hango na waje inbe auroba ya bisu watarana. kinga ni yanzu
bani da wata damuwa kullum cikin godema Allah nake da iyayena domin sunyi min babban
gata..."

"Hakane wallahi nagode sosai khadija insha Allahu ni kuma zanyi amfani da duk shawararki na
gode da tarayyarmu Allah ya raya mana Abba ya barmu tare da aminci."

"Kai ga mayen mijinki nan yazo khadija.."

Cewar fatima wadda ke nuna mata Ahmad daya faka motarshi daga nesa dasu.

Rungumarta yayi jikin shi tare da sunbatar goshinta sannan ya d'aga ma fatima hannu, tana like
jikin shi ya bud'e mata motar saida ya zaunar da ita sannan yaza gaya ya shiga shima sukai
gida babu ruwanshi da yawan mutanan dake kallonsu.

Bayan shekara biyu

Rayuwa tayi mawa in nan bayin Allah dad'i hankalin su kwace masu dana sani sunyi
danasanin su damma Allah ya temake su sunyi kamin kasa ta rufe idanunsu, Abba ya girma
sosai ga surutu kamar redio haka ga wayo sannan ga khadija da wani cikin, kullum cikin
godema Allah suke domin babu abinda suka rasa ya rufamusu asiri lokacin da mutane suka so
tona musu shi yasa ake son ka zab'i rufin asirin Allah bana mutum ba.

Dama dai ita rayuwa haka take yanda ka dauketa haka take zuwar maka inka kyautata niyyarka
sai Allah ya cika maka inko kayi sabinin haka sai Allah ya barka da shaid'an ya taya ka jan
ragamar zuciyarka Allah ya karemu daga sharrin zuciya amin.


_Duka-duka anan na kawo karshen wannan labari nawa me suna *DR.AHMAD*, Ina fatan inda
nayi dai-dai Allah ya bani lada inda kuma nayi kuskure Allah ya gafarta min domin d'an Adam
munsan kullun cikin aikata zunubi muke sai dai Allah ya ya femana Albarkar soyayyar shi da
ANNABIN RAHMA (s.a,w)._
*SHARHI*

JIGON LABARIN DR. AHMAD SHINE.
Babban dalilina na kawo wannan labari shine, domin yiwa iyayen mu tuni akan amanar da
Allah ya bamu, domin awannan zamanin ana yawan samun wannan matsalar, zaka ga k'aramin
yaro da matsanciyar sha'awa amma babu kula daga iyayenshi har shi, shi yasa yanzu fyade da
zinace-zinace suka yawaita.
Yaro zai nuna yana son aure amma iyaye su hana sai suce wai wani duka nawa yake da zaice
aure zai yi? Kunsan dalilinshi na cewa aure zai yi? Idan baki saniba ke uwa kai uba kuna damar
zaunar dashi ya sanar muku kuji sai ku magance mishi idan ba haka ba zakuji kunyar duniya
kuje lahira ma kuma ku karb'i sakamako.
An yi a kusa dani nagani ganin idona inda iyaye suka hana yaronsu aure yanada shekaru 27
suka ce sai ya gama karatu yazo yayi suka ce sai ya sami aiki ya gina gida, kundai san yanzu
samun aiki a Nigeria yanda yake be samu ba tsawon lokaci, 'yan mata biyu yayi ma ciki sannan
ya gudu yabar iyayen kunga wa gari ya waya sunyi dana sani lokacin da babu amfani. Toh

akwai iyaye da yawa masu wannan burin dan haka gara mu gyara tunkamin lokaci ya kure
mana domin bako wane yaro bane zai yi tunanin tsare kanshi daga halaka ba kamar Ahmad,
suna ganin da suyi azumi gara suyi zina da hannuwansu ko subi wata hanyar mummuna
kanacan kana cewa wane yaron kirki babu ruwan shi kaza-kaza baki san me yake aikatawa a
waje ko a d'aki ba, Allah ka shirya mana zuria ka tsare manasu.

Sannan sai ZAINAB,
Ta shigo gidan Ahmad amatsayin kishiyar khadija, to wannan wata kaddara ce da zata iya
fad'awa akanki a kaina, mata da yawa bama san kishiya sam sai dai muna mantawa da
rubutaccen Al'amari daga Allah wanda idan mijinki aure goma zai yi toh fa sai fa yayi shi ko kina
raye ko kina mace duk kwalliyarki duk kyawunki duk dirinki duk nutsuwarki duk biyayyarki idan
Allah yayi toh sai kin samu abokiyar zama.

Sannan wani shirme domin wannan dole akira shi da shirme da yawan mu zamu taso gidan mu
muga mahaifinmu da mata biyu uku hudu, kilama da wayanki ya saki wata ya auro wata kintaso
a irin wannan gidan sannan kizo kice waike bakisan kishiya kuma bazaki yarda da ita ba,
wannan wane irin tunani ne? BABU kalar surutun da banjiba daga mutane lokacin da Ahmad ya
auri zainab nayi mamaki sosai wallahi domin na san akwai babban aiki a gaban mu matukar
haka tafiyar zata kasance, akwai ma wadda naji tace ita book in dai da kishiya bata karan tashi
to me yayi zafi haka? zaman duniya ne bawai na kiya maba shekaru kalilan kike jira k'asa ta
rufe idanun kifa A haka zamuje ma Allah da mummunan k'uduri ga 'yan uwan mu? Kuma wata
kilama mahaifiyarka a ta biyu tazo ku itace ma ta hudu kuma ta shiga har aka haifeki amma ke
kin hana wata ta shigo kuma idan 'ya'yanki duk mata ne kuma duk masu zuwa gurinsu suna da
aure gashi suma na gidan sunce baza'ayi musu kishiya ba ki gyamin ya zakiyi da yaranki kuma
suna son aure? Muyi tunani muyi ma kanmu adalci da hallaci dan Allah.


SANNAN SURUKAI:-
Da yawan mu yanzu bamu son auren wanda iyayen shi ke a raye musamman uwa mace,
menene ya jawo haka?

Amsar itace mugun hali na zalinci sa ido da kuma wulakanci da wasu surukai suke gwadawa
matan 'ya'yan su, kada mu manta daga lokacin da yaronki yayi aure tofa duk wani hakkin
wannan mata tashi ya bar wajan iyayenta ya koma kanshi kinga hana warki yayi mata wani abu
ko kyautatawa kamar kin sashi sab'ama Allah ne dan haka ki saurari hukuncinki wajan Allah
domin shine ya tsara komai tun kamin zuwanki.

kudu ba kuga yanda Maman Ahmad ta rike khadija wanda daga karshe saida khadijan ta koma
bata son Maman taje konan da can sabida son da take mata. kowace uwa tagari nasan baza
taso akunta tama na taba tofa tunda bakiso kema kadda kifara yima d'an wani.

MALAM MAMUDA:-
Malam Mamuda yayi halacci kuma yarike amanar makota sannan ya fara ganin saka mako

tun a duniya.

Eh mana tunda gashi Ahmad ya d'auke mishi dawainiyar komai sabida halaccin dayayi mishi
kamin yaje wajan Allah yasamu saka mako me kyau domin yayi aiki me kyau na toshe wata
kafa ta b'arna, sannan matar shi taba shi goyan baya inda ta toshe kunnuwanta daga dukkan
wani gulmace-gulmace da mutane suka yita jifanta dashi.
GA KHADIJ KUMA:-
Khadija itace tauraruwar labarin dan Allah banda cigaba akwai wani na kasu data samu a
rayuwarta? amsar itace babu taga ranar biyyayya dan kuwa gashinan tana karatunta tana da
mijinta na nunawa sa'a sannan ga albarkar aure da Allah yaba su, kaddafa mu manta da yawa
akwai iyayen mu da akaima aure tun basu da wayan kirki kuma suka zauna qalau, amma yanzu
sai yarinya tayi shekaru akalla 20 kuma kuji iyayenta na maganar bata isa aureba toma idan
zina batai yawaba meye zai yi yawa? abarshi a kunaso tayi karatu! karatu bawani illa bane dan
tayi amma me ku aurar da ita sannan taje makarantar shifa aure daraja ne dashi wa innan
igiyoyin da suka hau kanta sai kuga sanadin ta tasamu nutsuwar yin komai.

*DR.AHMAD*
Gaba d'aya labarin na shine mutane nata maganar jarabarshi tacika yawa, to wallahi kunji na
rantse akwai mazan da suka fishi tsananin buk'ata kuma sunada yawa sosai acikin maza.
sabida haka ni banga wani abun mamakiba dajin labarin Ahmad ke dai kawai amatsayin ki na
mace kiyi addu'ar Allah ya baki miji dai-dai da yanayin bukatarki harda masu cewa wallahi babu
masu irin wannan yawan buk'atar toh kuje da rantsuwarku amma mudena saurin rantsuwa akan
abinda bamuda sani akai.

*ANAN NI MAMAN KHADIJA nake muku fatan Alkhairi ina fatan zaku tayani da addu'ar Allah
yasa na haihuwa lafiya na gode sosai.*


*TO YOU HAJJA CE my hajja, Dota hajja nagode sosai da temakonki gareni domin kece me
gyaran kusan dukkan kurakuran da ake samu a ciki da kuma rubutun, toh kundai san mace me
ciki😃sai a slow na gode sosai may God bless you and jikata ihsan.*

_Sai kuma ke! Na gode da kulawarki da adduarki gareni Mamana ta kaina Maijidda musa
Allah ya barmu tare._

*KUNGIYATA ABIN ALFAHARINA HASKE WRITER'S ASSO*
Allah ya kareku ya k'ara muku basira da hangen nesa Maman Khady na yinku Allah yabarmu
tare

_Ummi Aisha, phatymah Zarah, Hajja ce, khaleesat hydar, miss Xoxo, billy galadanci, Aisha
d/sabo, safiyya Huguma, Asmy b Aliyu, Afrah bhai, Faxyfation, Nana diso, Feedohm,
Nuceeyluv, Ayusher Muhd Allah ya kara had'e kanmu_�

*MAMAN KHADIJA*🙇🏻�♀

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login