Showing 24001 words to 27000 words out of 44890 words

Chapter 9 - DR AHMAD BOOK COMPLETE BY Maman Khadija .pdf

16 Mar 2025

7229

wankan ka tunda kace fita zaka yi, ka gani banjima da
dawowa daga makaranta ba kai kuma ina shigowa ka taramin wata gajiyar, yanzu barci na keji
amma idan na tashi to zan kintsa kamin ayi la'asar sai ka dawo."

Cike da kauna ya sunbaci kuncinanta sannan yabar d'akin.

******

Daga masallaci suka dawo tare shida malam Mamuda suna tafe suna hira har suka iso gidan,
azauren gidan suka zauna kamar yadda Ahmad d'in ya bukata.

Sunjima zaune shiru babu wanda ya tanka domin sai yanzu Ahmad d'in yake jin wani irin nauyi
daya dabaibaye shi.

"Ahmad nifa babanka ne idan baka gayamin abunda ke tafe dakai ba wa zaka gaya mawa?
karka damu zan fahim ceka insha Allah fad'i ina jinka."

Cikin nutsuwa Ahmad d'in yayi mishi bayanin komai, sunjima babu wanda ya kuma tankawa
domin shikan shi malam Mamuda saida yaji babu dad'i domin har saida ya gaza hakuri ya
tambaye shi, kodai akwai abinda khadijan kemishi amma yace babu komai kawai dai yanaso ya
k'ara auren ne idan sunyi mishi izini.
Ajiyar zuciya malam Mamuda ya sauke kamin yace,

"Toh ai be kamata ai ita Maman taku ta hanaka yiba tunda har kana so, amma dai sai inga
kamar daka bari aikin naka ya kankama kadda ka takura kanka kaji?"

Cikin jin nauyi da kunya Ahmad d'in yace,

"Baba dama ba yanzu ba ina so Maman ta amince ne tukunna, itakuma yarinyar agana da
iyayenta sabida kadda tayi tunanin ko yaudarar ta zanyi, kuma ranar litinin zanfara zuwa aiki a
babban asbt har ofis d'ina naje nagani kuma akwai albashi me tsoka sannan kuma ko yanzu
akwai kud'i awajena Mama ce dama dai abin jin."
"Toh shike nan karka damu insha Allah da anyi sallar isha'i' zanzo gidan kaji ko?"

Cewar malam Mamuda.

****

kamar yadda ya gaya mishi kuwa haka aka yi domin daga masallacin ma kai tsaye gidan su
Ahmad d'in ya nufa.

Khadija da murna ta d'a ne mahaifinta, shiko dariya kawai yake tare da furta

"zaki kayar da nifa khadija ke har yanzu baki san kin girma ba ne..?!"

kallonta yayi yana jin tausayinta kamin yace,

"Ina Maman taku take ne wajanta nazo."

"To baba kashiga tana ciki."

"Yauwa toh kiramin mijinki idan yana nan ya taddani wajan Maman taku."

Sam babu sakin fuska haka suka gaisa domin tasan dalilin zuwan shi wajanta. shi kanshi

Ahmad d'in saida yasha jinin jikin shi balle da yaga sam babu walwala atare da ita hasalima ko
kallon inda yake bata yi..

Hakuri sosai malam Mamuda yayi ma Maman tare da nasiha san nan ya d'ora da fad'in ta
amince da auren domin babu wanda yasan me gobe zata yi.

"Haba malam yaushe ne zaka daina biyema shirman yaron nan?
toh nidai gaskiya ban amince ba sabida Allah duk irin kokarin da yarinyar nan take yi dashi shi
begani shinema zai saka mata da kishiya? kishiyarma gogagga 'yar duniya tunda har waje tatafi
karatu wama yasani ko iskancin su sukai tayi shida ita shine abin be ishe shiba zai aurenta, toni
ban yadda ba in kuma yace dole sai yayi to sai dai ya saki khadijan domin bazan yadda ya tozar
ta taba wallahi."

Cikin tashin hankali Ahmad d'in ya fara bata hakuri tare da gayamata cewar bazai iya rabuwa
da khadijan ba kuma yana sonta.

Wata uwar tsawa ta daka mishi wadda ta tsoratashi da malam Mamuda kamin tace,

"Maza ka tashi ka ficemin a d'aki na kamin na illataka wallahi sakarai kawai shasha sha."

Jiyayi kamar yayi ta kurma ihu lokacin daya fita kuma sai yayi karo da khadija bakin kofa tanata
zubar hawaye domin tajima da jin duk wata magana da suka yi.

Da sauri ya nufeta sai dai kamin ya k'arasa jikinta tayi waje sabida wani mugun takaicin shi
takeji, tunaninta shine duk irin yanda take kyautata mishi amma shi tunanin shi naga wata
kenan, kuka take yi sosai yana lallashinta, bayan shigarsu cikin d'akinsu sai dai ko sauraran shi
ta kasa yi balle ta fahimci me yake cewa ma.
A bangaren Maman kuwa ba k'aramin aikin lallashi da nasiha malam Mamuda yayi ba kamin ya
shawo kanta wanda har kuka sai da tayi sabida tsabar takaici, bata tab'a tunanin Ahmad d'in zai
iya haka ba ta kunya ba, domin wannan abun kunya ne sosai sannan tasan yaja mata zagi
wajan mutane kai ba itabama harta iyayen khadijan sai abin ya shafesu. koda ta amince sam
kin yadda tayi ayi maganar yanda za agyra komai sai dai daga karshema cewa tayi sam babu
ruwanta da hidimarshi yayi duk abinda yaga dama aishi ne ya d'aure mishi k'ugun yin auren.

Daga karshe dai dole malam Mamuda yabar gidan tare da tunanin yanda zai fara tsara hidimar
fatan shi Allah ya bawa khadijan shi hakuri da juriya kodan tallafama maraya da yayi shima....

*MANAN KHADIJA*🙇🏻�♀
[2/27, 7:06 PM] ⓠʊ¥ґѦ℮м℮¥: *💗DR.AHMAD💗*

31

*NA MAMAN KHADIJA*🙇🏻�♀

Edit by *Hajja ce*👈

*HASKE WRITER'S ASSO...*💡



*S*am k'in yarda tayi ya rabi jikinta, dole ya koma gefenta ya kwanta batare da tunanin bacci
zai d'auke shiba. sosai ya kejin tausayinta musamman yanzu da baccin wahala ya d'auketa
amma ajiyar zuciya kawai take saukewa, gawani zazzabi-zazzabi daya keji kamar zai rufeta.

Tun asuba yaso ko magana ta hadasu amma ina kalma daya ce ta iya d'aurewa ta furta mishi,
itace ina kwana daga ita bata k'ara ba.

kayan jikinta kawai ta canza tabar mishi d'akin gaba d'aya, wajan Mama taje suka gaisa sannan
tace,

"Me za a d'ora Mama?"

Wani tausayin tane ya kama Maman dan haka ta rungumota jikinta kamin tace,

"kiyi hakuri kinji, insha Allah babu komai kibarshi yayi auren tunda ya nace muzuba mishi ido
kawai, dama saida nace ban yadda da karatun sa a k'asar wajeba amma malam yazo ya matsa
gashinan tun kamin aje ko ina ya fara zuwa mana da sabbin abubuwa kiyi hakuri dan Allah
kidaina damun kanki kinji d'iyata..."
Hawaye tashare kamin tafara magana cikin kuka-kuka,

"Mama ya Ahmad be kyauta minba duk irin abinda nake mishi amma shine zaimin kishiya
Mama kofa haihuwa banyiba?"

"Nace kiyi hakuri kirabu dashi tunda yanzu babu yanda zanyi mahaifinki yazo ya kasa ya
tsare bani da wani abun yi domin ina jin nauyin mahafinki kiyi hakuri kawai."

Lallashinta taci gaba dayi har garin Allah ya waye kamin su shiga kitchen tare suka yi kunun
tsayima da alalen leda.

Babu wanda ya kulashi ko wajan yin breakfast d'in dan haka sai yaji duk ya kasa sakewa
ballema ya karya din dole ya tashi yabar gidan batare da sanin inda za shiba.

Dariya Maman tayi tare da mik'ama khadijan hannu suka kashe kamar wasu kawaye, ko
abokanan wasa.

"Mama bari naje nayi shirin makaranta kinsan munata shirye-shiryen jarabawar fita."

"Toh madallah a dawo lafiya."

****

Cikin sati d'aya Ahmad ya fara fita hayyacin shi domin sam cikin gidan yadaina mishi dad'i
sannan ga aiki daya fara zuwa duk zuciyar shi babu dad'i ga kuma shirye-shiryen biki domin tuni
malam Mamuda yayi jagora zuwa funtuwa sungana da iyayen zainab kuma komai ya dai-daita
ansa biki nan da wata biyu masu zuwa.
Tsakanin shi da khadija kuwa sai gaisuwa babu ruwanta da fitinar shi yanzu shi yasa harwani
kumari tayi jikinta ya murje, sai dai tayi wanka ta shirya ta fice wajan Mama. to shima da yake
yanzu be zaman gidan idan yafita takwas na safe sai biyar da rabi na yamma yake dawowa,
burinshi yanzu ya sai mota kozai huta da wannan zirga-zirgar da yake fama da ita.
*****

A b'agaren amarya zainab kuwa burinta ya cika zata auri gwarzon namiji kamar Ahmad sam
bata da damuwa, duk da cewa iyayenta sun raina arzikin shi Ahmad d'in da kuma kankantar
shekarunsa da nata amma da yake diyar gatace shi yasa suka amince dashi domin suna sonta
shi yasa suka amsa kuma suka bashi. shirye-shirye suke yi sosai na bikin.


*****

Cikin ikon Allah su khadija suka fara jarabawa tafi daga secondary sosai tamanta da duk wata
damuwa da take ciki, kuma dama shima Ahmad d'in ya samusu ido ita da Maman ta hidimar
ginin shi kawai ya keyi domin gefen d'akin khadijan yasa ginin wani d'akin ciki da falo da toilet
kamar dai na khadijan. Ana saura sati biyu biki suka gama jarabawan dan haka ana saura sati
d'aya bikin Maman tace khadijan ta shirya zasu unguwa kuma ta d'ibi kaya, haka shima Aminu.

Charanci suka nufa batare da sanin shi Ahmad din ba sai dai kawai ya dawo gidan ya tadda
babu kowa ga key din dakin khadija nan amma babu na kitchen balle na d'akin Maman.

Jiyai ranshi yayi mummunan b'aci musamman daya duba kayan khadijan yaga an d'iba da
yawa, dama yana takaicin hanashi hakkinshi da take yi tun lokacin da taji batun auran shi wai
yajira na amarya shine yanzu kuma zata fice bada saninshi ba.


*****

Komai da ake bukata na dangin amarya iyayen khadijane suka yishi duk da cewa ita mahaifiyar
khadijan ba akan son ranta takeyin komaiba kawai dai tanabin umarnin shi mahaifin khadijan
ne.


Ranar da aka d'aura auren, khadija kwana tayi kuka wanda daga karshe haddasu zazzabi da
amaye-amaye ta dinga yi.

A bangaren amarya da ango kuwa burinsu ya cika dankuwa an d'aure aure lafiya kuma amarya
ta tare a cikin d'akinta sai dai kamin danginta subar gidan saida rayukan su Ahmad din yayi
mummunan b'aci dankuwa habaici da korafe korafe babu kalar wanda basu zubarba, atunanin
su zainab ta wuce da ajin wannan gidan balle mutanen ciki.....









*MAMAN KHADIJA*🙇🏻�♀

[3/14, 2:41 PM] ⓠʊ¥ґѦ℮м℮¥: *💗DR.AHMAD💗*

33

*NA MAMAN KHADIJA*🙇🏻�♀

Edit by *Hajja ce*👈

*HASKE WRITER'S ASSO...*💡
(Home of expert & perfect writer's)

*K*allon-kallo sukai tsakanin Mama da ita khadijan domin dukan su sunji abunda Ahmad d'in
yace, tsora ya kama khadija sosai dan haka nan da nan tafara hawaye.

"To maye nayin kuka kuma? kitashi ki shirya mutafi yau zai hadu da fishina wallahi tunda shi
mugune tashi ki kintsa bari nima in gyara jikina idan munje gidan lafiya nayi wanka, bari
ingayama baba maganar tafiyar tamu."

Sai wajan bayan la'asar sannan suka sami motar da zata yi malumfashi, Aminu sai murna ya
keyi da tsallen yau za akoma gida domin dama ya gaji da tuwon da akeci kullum agidan sai dai
idan khadija na sha'awar wani abu sannan ayi mata shima ya samu yaci.

Har wani tsallen dadi yayi tayi cikin d'akin domin yasan duk wuya yau zasu dawo fad'an Mama
kuwa tayi zai bata hakuri, dakanshi ya tashi ya fara gyaran d'akin khadijan saida yaga komai
yayi mai yanda ya keso sannan yafita masallaci, saida ya fara lekawa d'akin zainab tana
kwance har lokacin tana barcin wahala, dariya yayi kamin yace,
"Raguwa kawai zumata ta kusa dawowa ai nima na huta da dambe dake."

Da cefanen shi me kyau ya shigo yace gashi zainabuna tashi ki gyarama su Mama suna hanya
insha Allah, aiko da saurinta ta tashi hadda dariyar farin ciki,.

Girki me rai da lafiya ta shirya, shi kuma ya share gidan tsaf da wankin bayin tsakar gidan haka
domin Ahmad gwanin tsaftane kuma har yanzu bashi da kiwar taya iyalinshi aikin gida. kamin
magriba sun gama komai ta shige dakinta domin wanka da sallah shiko d'akin khadija ya shige
domin shiryawa shima.

Sai bayan sallar isha'i' sannan suka shigo gidan sosai suka sauka da gajiya musannan khadija
me yaron ciki domin mararta har wani k'ullewa tayi.Jin sallarmar su yasa zainab fitowa domin
tararsu, shi kuma Ahmad be dawo daga masallaciba lokacin. daga Maman har khadijan babu
wanda ya nuna mata wani abu domin ta taresu da murna da farinciki wanda daga karshema
tace,

"Mama idan kun huta ga ruwan wanka can akan wuta sannanunku da hanya. Aminu babu
maganako?"

Shi dai kallon rashin sani kawai yake binta dashi domin be santaba duk cikin danginsu, shiya
sama ko magana ya kasa yi mata. Afakaice zainab ke kallon khadijan, lallai babu abinda zata
iya nunama khadija sai zallar wayewa amma kyan jiki dana sura kam sai dai tabiyo bayanta,.

Khadija ce ta kalli Mama tace,

"Mama bari naje nayi wanka da sallah kila jikina ya saki ko ina ciwo ya kemin wallahi."

"To inkin gama ki fito sai muci abinci gaba d'aya anan kinji?"

cewar zainab wadda tabi khadijan da kallo tana yaba zallar kyawun surar da Allah yayi mata
gashi kamar ciki ne a jikinta domin ya fito.

Kai tsaye d'akin khadijan ya nufa, nufinshi ya leka ya gani ko sun shigo, aikam yana shiga d'akin
yaji motsin ruwa dadi kamar zai kasheshi ya nufi d'akin Maman zaman dirshan yayi gaban
Maman yana gaisheta yayin da ita kuma ta amsa tana wani basar dashi d'innan, jiyayi jikin shi
yayi sanyi ashe har yanzu bata gama hucewaba to balle kuma khadija.
Kallonshi tayi kamin tace,

"Naji sakonka wajan khadija ai shi yasa muka dawo kadda Allah ya tsine mana muduka tunda
dai nice na d'auketa nasan tsinuwar haddani kayita ko?"

Bakinshi har rawa yake wajan bata hakuri tare da furta shiba nufinshi kenan ba amma dai tayi
hakuri. Tattara shi tayi ta watsar taci gaba da lazuminta shi kuma ya fara hira da Aminu a haka
zainab ta gabatar da kayan abincin kamin taje ta kira khadija wadda ke zaune akan kujera cikin
falonta tana kallo acikin wayarta, da sallama ta shiga cikin d'akin kamin tace,
"kizo muci abinci."

khadija bata kalletaba tace,

"OK kije ganinan fitowa."

Ta jima sosai sannan tafi ta sai bula kamshi take yi.

KO kallon inda yake bata yiba tafara cin abincinta, yayin da shi kuma mamaki yaka mashi ganin
yanda ta canza gaba d'aya kamar ba ita ba, kallonta yake yi kallo irinna kurillah. dukkansu saida
suka farga da irin mayen kallon da yake bin khadijan dashi domin ko abincin sai dai kawai ya
tsakura ya bari.
Maman ce tayi gyaran murya aiko ya d'ago ya kalleta wata uwar harara ta wurga mishi dan
haka da sauri ya tashi ya nufi waje yana sosa sumar kanshi.

Kayan jikin shi kawai ya canza ya haye gadon zainab tare da kwanciya ya lumshe idanun shi
khadija kawai ke gitta mishi gaskiya yayi kewarta ba karama ba sosai yake jinta ako,ina na jikin
shi koda yake matace ta rufin asiri domin arayuwar shi bazai tab'a mance khadija da iyayen
taba domin mutane ne da suka cancanci ya bawa a dai wannan zamanin da ake wanda kowa
nashi ya sani.

"Mama zanje na kwanta saida safe.."

"To khadija Allah ya bamu alkhari sai da safe."

Ita ko zainab saida ta gyara inda akaci abincin sannan itama tayi mata sallama.

****

kirjinta ne yayi wata irin bugawa lokacin da ta hangeshi akan gadonta, turo bakinta tayi gaba
kamin tace toh kuma kai Ahmad me kazoyi d'akina baga matar kaba can ta dawo ba?"

Dama dan yaji me zata ce ne dan haka da dariya ya bar d'akin.

Cikin b'arcin daya fara d'ibarta taji ana lalubarta dole tabud'e idanunta, ido biyu suka yi dashi
wani mugun kallo tabi shi dashi kamin tace,

"lafiya..?!"

Wani marairai cewa yayi kamin yace,

"Haba mana babyna yaza kimin haka kin dai san nayi hakuri dame ko?"

Cikin jin wani haushin shi tace,

"Amma dai ya Ahmad idan kace haka kusan kaima Allah butulci ne kaida kai sabuwar
amarya me zaka yi da tsohon abu kuma ma ni wallahi banso dan haka ka koma wajanta, naya
femaka domin nasan gundurarka nayi tunda har ka k'ara aure alhalin babu ta inda nagaza
maka..."
"A'a khady kadda kice haka wallahi baki tab'a gundura taba kuma bana fatan hakan har
abada sabida nasami haihuwa yasa nayi auren nan badan bani sonki ba."

Kuka me sauti ta saki jin abinda yace wato sabida bata haihuwa zai mata kishiya kenan, jin
sautin kukanta yasa shi tuna abinda yace innalillahi ya fara nanatawa cikin ranshi hartafara
fitowa.

Cikin sanyin murya tace,

"Ya Ahmad kenan ba zaka iya hakuri da duk yadda kaddara ta zata zo mana nan gaba ba ko?
niko inda nice nasan koda kaine baka haihuwar bazan iya guje maka ba domin nasan koda nayi
niyyar aikata hakanma iyayena bazasu amince minba sai dai in dawwama dakai a haka to koma
dai menene babu komai kuma na godema Allah tunda yanzu nasan irin zaman da kake yi dani

dan haka dan Allah kata shi ka koma wajan matarka me haihuwa ni kuma ka barni inji da jikina
domin banjin dadin jikin kuma nagaji babu wani abu dazan iya yi maka."

Rungumeta yayi sosai ajikin shi yana sauke numfashi jiyake ayanzu babu wanda zai iya
hanashi kusantarta a yanda dai ya kejin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login