Showing 12001 words to 15000 words out of 44890 words

Chapter 5 - DR AHMAD BOOK COMPLETE BY Maman Khadija .pdf

16 Mar 2025

5030


manta.


DA DARE:.......








*MAMAN KHADIJA*‍♀
[2/26, 9:27 PM] ⓠʊ¥ґѦ℮м℮¥: *DR.AHMAD*

17

*NA MAMAN KHADIJA*‍♀

Edit by *Hajja ce*

*HASKE WRITER'S ASSO....*
(Home of expert & perfect writer's)


*T*ana gama shirinta na barci ta d'auki wayarta ta rungume jira kawai ta keyi taji kiranshi
domin tunda asbah da sukai waya be kuma kiraba gashi har dare yayi har tama fara bacci, can
cikin bacci taji wayar nata ringing da sauri ta rarumi wayar ta latsa tana magagin barci tace.

"Hello..." ta furta kamar zata saka mishi kuka. gyara kwanciyar shi yayi tare da ture littattafan
dake jikin shi idanun shi alumshe yake yayi shiru yana sauraron zazzakar muryarta.

"Ya Ahmad ina yini ya karatu?"

"Alhamdulillah babyna sai dai kewarki data dameni jinake kamar na zama tsuntsu kawai in
ganni a k'irjinki, baby na kema kina kewata kuwa anya?"

Cikin shagwab"a tace mai

"Ina yi mana Yaya Ahmad."

"Kai anya zan yadda kuwa tunda gashinan har kinfara bacci niko ina tare da takardu a gabana
gashi dana runtse idanuna ke kawai nake hangowa."

Cikin tausayawa tace,

"Ayya! yayana to kayi hakuri, amma nima ina cikin kewarka wallahi ka saba minfa da zama a
jikin ka kasaba min da soyayyarka shi yasa yanzu nake wahala kwana biyu da tafiyarka ni bana
iya barci sai yanzu dana d'an fara sabawa, kuma kaga Hafsat bata kwana a wajena sai wajan
Mama take kwana ni kadai ke yin barci a gadon mu fa."
Yace "To ki kwantar da hankalinki kinji ko, dana samu lokaci zanzo in ganki koda kwana biyu ne
kinji?"

"Uuhum."

Ta furta tare da kuma matse wayar ajikinta. Yace mata "yauwa kun ga likitan d'azu?" Khadija
tace, "eh mana mun ganta wai kai shine kace akaini kuma ni lafiya ta lau gashi sai da ta
bud'emin abuna ta kallarmin."

Dariya yayi kad'an kamin yace "to ai shi yasa nace kuje wajanta sabida macece me matukar

k'ok'ari da jajir cewa akan aikinta, kuma kinga ita macece dole ita ya kamata ta duba kin, amma
dai bata tab'amin abuna ba ko?"

Dariya itama tayi kamin tace "Kaji yayan nan wai abunka, aiko ta tab'a hadda wani abu tasaka
ciki fa."

Wata muguwar kasalace ta sakko mishi lokacin da yaji abinda tace, kewar abun ta dabaibaye
shi, ya jima yana kokawa da numfashin sa sannan yace mata,

"To me tace muku???!"

"Tace babu wata matsala wajan zai bud'e a hankali kuma innaji zafi na daina yi maka kuka wata
rana zan daina jin zafin."

Murmushi yayi kamar wani babba shima kamin yace "aiko naji dad'in jin hakan bari na barki kiyi
bacci sabida makaranta banda wasa baby na, saida safe I love you."

Kashe wayar yayi tare da zuba ma wayar idanun shi, addu'a yake Allah yaba shi juriyar zaman
da zai yi sai dai yasan dole gobe ya tashi da azumi dan shi kadai ya san yanda ya keji ajikin shi.
Tunanin shine ya yanke jin yanda abokin shi Hamza keta zabga numfashi a cikin toilet kamar
me tarawa da mace, a tsorace ya fara kiran shi tare da komawa kusa da k'ofar band'akin dan
gasgatawa nan ya fara furta kalmar,

"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un, Hamza wai me kake yi haka da ba zaka fito ba?"

"Dallah malam Zan fito mana ka tsaya na gama mana karka samin ido fa daga had'uwar mu..!"

Yana fitowa wani kallon tuhuma Ahmad yabi Hamzan dashi, yayin da Hamzan ya kaud'a kanshi
ga barin kallon shi domin a d'an zaman da sukai da Ahmad d'in ya fahimci be cikin irin matasan
nan masu sakaka.

"Hamza me kayi yanzu a bayi? me ka ai kata?!"

Shiru Hamzan yayi masa kuma ya fara murzama jikin shi hannu Ahmad ya kalle shi yana cewa,

"Hamza be kamata a ce ina maka magana amma kana shareni ba domin gani nake a yanzu
mun riga mun zama abokai kuma 'yan uwa dole in baka shawara kaima dole kabani sannan
dole ne mu rufama junan mu asiri kadda ka manta wannan zaman da zamu yi Allah zai
tambaye mu wata rana sabida haka dole mu sami abin fad'a, Hamza kasan ko cewa zina ce
kake yi da hannuwanka, hannuwanka dake d'aura alwala sannan ka d'auki alkur'ani dasu kaci
abinci dasu, sannan kazo kana yin zina dasu wannan wace irin k'azan tace Hamza?!"

Kana so Allah ya jarabceka da musibu kala-kala sanadiyyar wannan abun da kake aika tawa?"

Meyasa ba zaka d'auki maganar shugabammu ANNABI MUHAMMAD, S,A,W. ba inda ya bamu
shawarar yin azumi matukar bamu da halin yin aure ba, Yes! yanzu ba duka iyayen mu ke
yadda da muyi aure ba da wuri musamman idan suna so muyi karatu sai dai wani lokacin
wannan ba gata bane ba sabida da yawa zaka ga matashi ko auren fari beyiba kai ko
secondary school be gama ba amma sai kaji ance cutar HIV gareshi me yaja mishi kuma ina
yasa meta? amsar itace wajan neman mata...! wasu kuma sai dai su dinga lalata k'ananun yara
sabida rashin tausayi da imani, wasu kuma saisu dinga biyama kansu bukata da hannayensu
kamar yadda kake yi yanzu, wanda yawan cin matasa yanzu abinda suke yi kenan sai dai
wallahi kuskure ne babba suke aikatawa ba tare da sun sani ba, idanma sun sani toh sun take
shi. Ka daina Hamza dan Allah ka daina Hamza idan sha'awa ta da meka ka d'auki azumi
yunwa tana danne sha'awa sannan zaka sami lada kaga riba biyu kenan,

Amma idan baka dai naba to tabbas wata rana za kayi kuka da idanunka domin zaka had'u da
masifa wacce tafi karfinka. kamar yawan mantuwa ko cushewar numfashi rashin haihuwa ko
raunin gabanka wanda ba zaka iya tarawa da iyalin kaba nan gaba idan kayi aure, ko kuma
makanta, sannan wannan abin da kake fitarwa ba duka yake fita ba duk lokacin daka ga ya fita
to akwai saura, wanda ke tsaywa ajikin ka kuma bazai koma inda yake ba da can, zuwa gaba
zai iya zama tsutsa kuma ya cutar da lafiyar ka sannan kuma idan yayi sanadiyyar mutuwarka
kana ganin kana da abinda zaka gaya ma Allah?

Amsa shine babu domin ALLAH da kanshi yace bamu tab'a jarabtar bawa naba face sai naga
zai iya d'auka, ma'ana ba zai jarab ceka da wani abu da yafi karfin kaba, UBANGIJI kenan
gagara misali sarkin da bashi da d'a bare mata shi kad'aine kuma shine me duk wani abu da ka
gani a duniya. sabida haka kasan kalar matakin da zaka d'auka amma wallahi ka guji sab'ama
mahaliccinka domin zai iya kamaka ta lokacin da baka zata ba kuma bakai tunanina ba lokacin
ne zaka yi nadama wacce bata da amfani...."

Hamza wanda jikin shi ya gama yin sanyi likis sannan ga kwalla da ta gama cika mishi ido, ya
koma jikin Ahmad tare da rungume shi cikin jin dad'in yanda ya fahimtar dashi domin shi kam be
tab'a tunanin haka ba, shi yasa ilmin addini ya keda dad'i.

"Na gode Ahmad na gode sosai tabbas ka cika aboki nagari na gode maka Allah ya barmu tare,
sai yanzu na lura da abin da ke yawan saka ka azumi duk da bamu dad'e tare ba, insha Allah
daga yau ba zan kuma ba Ahmad domin dama komai sai kasa kanka sannan zai tsaya maka a
zuciya na gode sosai.."
Murmushin jin dad'i Ahmad yayi yana addu'ar Allah yasa ya dena sannan ya zame jikin shi daga
na Hamza yana mai murmushi........

*MAMAN KHADIJA*‍♀
[2/26, 9:28 PM] ⓠʊ¥ґѦ℮м℮¥: *DR.AHMAD*

18

*NA MAMAN KHADIJA*‍♀

Edit by *Hajja ce*

*HASKE WRITER'S ASSO....*
(Home of expert & perfect writer's)


_Wanan shafin nakune 'yan kungiyarmu ta *HASKE WRITER'S*, Allah ya k'ara basira da fasaha
ya baku ikon Isar da sakwanni masu amfani_

Special thanks goas to,
Phatymah Zara
Miss Xoxo
Billy galadanci
Dota Hajja ce
*A dinga sassautawa Ahmad ahee!! kubarshi da Matar shi babu ruwanku*☺


*BAYAN WATA BIYU*

*A* bubuwa da dama sun faru cikin watannin nan ciki kuwa harda k'ara girman da khadija tayi
da sauran abubuwa masu muhimmanci da Maman keta k'ok'arin ganin khadija ta kware akai
musamman ta b'arangaran ibada da kuma muhimman cin mijinta a gareta.

Ahmad kuwa karatu ya keyi cikin nutsuwa domin samun cikar burin shi amatsayin shi na d'an
talaka, kullum cikin kewar matarshi yake sai dai a wannan satin yake da k'udirin zuwa gareta
domin shima ya fara gajiya da kukan da take mishi kukan yaki dawowa gare ta.

Yana jin tausayinta sai dai yana jin tausayin kanshi fiye da ita shi kadai ya san halin da yake
ciki, sai yanzu ya tabbatar ma wa kanshi cewa daga gani jarabar yawan bukata zai yi tunda
gashi yanzu ya fara kasa barci tunkafin ma shekarun shi su kuma ja.

Shirya kayan shi ya keyi a hankali tare da kallon Hamza wanda ke kwance ya nata kallon shi
Ahmad d'in yace,

"Wato Hamza gaskiya idan naje gida sai nayi sati zan dawo sabida haka kai dai kawai ka adana
min komai yanda zan fahimta idan na dawo."

Dariya Hamzan yayi kamin yace "nimafa ina ga binka zanyi wallahi in wuce gida domin ba zan
iya zama a d'akin nan ba alhalin baka nan."

Duk suka yi dariya yana gama shiryawa suka fita, Sai da ya raka shi har tasha ya hau mota
sannan sukai sallama ranshi cike da farin cikin yau zai kwana jikin babyn shi 'yar khadyn shi
Matar shi abar alfaharin shi.


*****

"Khadija kifito kizo ki d'ora girkin mana rana tana kumayi nace zanyi kince a'a kuma kin shige
d'aki kinyi shiru bake ba labari ki."

"Mama ganinan kaya nake can zawa."

Cikin riga da wando ta fito na kanti da Mama ta siyo mata wani zuwa da tayi caranci, zama tayi
tare da fara kwabin d'anwake bayan ta d'ora ruwan tana yi suna fira, a inda Maman kebata
labarukan ban dariya ita kuma sai kyakyatawa take yi.

Tana sakin d'anwaken tana aiken Aminu yaje ya kara siyo mata kanwa gidan malam ilu ta kara
da cewa,

"Saura kuma ka kwance irin na rannan wallahi ba zan baka ba yau."

Da gudu ya bar gidan yana dariya Mama ma dariyar take yi musu.


A kwano d'aya suke cin abincin suna yi suna hira, Mama tace,

"Oh ni Habiba shike nan dai hafsat ta gujemu?"

"Uhunm Mama aini da haushima yayi min yawa ko maganar ta ban kuma yi ba."

Dariya suka kuma yi. sallama ya kuma yi a karo na biyu, da gudu Aminu ya tashi yai waje, aiko
ihun murna ya saki tare da kankame yayan shi yana "ga ya Ahmad ga Ahmad sannu da zuwa."

Cikin farin ciki ya idasa cikin d'akin Maman zaune ya tadda su mamaki ya hanasu ko motsi

musamman khadija wadda ta keji kamar tayi tsalle ta ganta ajikin shi domin tabbatar da cewa a
gaskene ba mafarki ba.

Cikin mamaki Maman tace "ah wannan wace irin tafiya ce ta ba zata?" dariya yayi tare da shafa
sumar kanshi wadda ta taru mai tsananin laushi yace "gani dai Mama kewar ku ce naji tana
neman halakani shi yasa na gudo."

Dariya tayi kamin tace "Ai kuwa muma munyi kewarka babana ya karatun?"

"Alhamdulillah Mama komai lafiya lau wallahi."

"To madallah Khadija had'a mishi ruwan wanka yayi sai yaci abinci."

"To Mama."

Tsam ta mike tayi room d'insu ya bita da kallo jakar kayan shi ya bata, ledar kuma ya bawa
Maman yace ga tsaraba.

Da kallo yabi d'akin yanda yaga ko ina kal-kal ta gyara ko ina sai kamshi ya keyi sai ta kuma
birgeshi tare da k'ara shiga zuciyar shi sabida tsabtar ta.

Cikin jin dad'i yayi wankan koda ya fito har ta aje mishi abinci da ruwa. Yana cin d'anwaken
yana kuma binta da wani mayen kallo yayin da ita kuma kunyarshi ta kamata dan haka sai tayi
ta sunne kai daga karshe ma sai ta koma d'akin Mama, sai dai tana komawa Maman ta korota
wai ya za'a yi ya dawo kuma shine zaki fito kibar shi. kunya ta hana ta magana ta fito ta koma
d'akin ta tana ta sunne kai.

Hannu wanta ya kama tare da d'orata saman cinyar shi yana sunsunar wuyanta jiya keyi kamar
ya lasheta sabida so yace,

"Babyna naga kamar baki yi murna da ganina ba ko na koma ne?"

kanta a k'asa tace,

"Nayi mana." bakin ta ya cafka ya fara tsotsa yana lumshe idanun shi lokaci guda jikin shi ya
fara rawa da sauri yake lalubar jikinta sai dai rigar ta kamata sosai, d'an tsaki yaja kamin yace,

"Khadija ki cire rigar nan baki jin tayi miki kad'an ne?"

Cikin shagwab'a tace "a'a ni dai batayi min kad'an ba ya Ahmad."

'Daukarta yayi suka shige kuryar d'akin su kan gado ya ajiye ta sannan ya kwabemata rigar da
kanshi gami da cire tashi shima yana yi yana romance d'inta kamar wani tsohon maye. Jin

kamar zai cinyeta d'an yane ya sata tsorata tare da fara tureshi. muryarshi a shak'e yake furta,

"pleased khadija kadda muyi haka dake kiji tausayina mana please let me in.....!"

Shiru tayi mishi lokacin da take jin irin jagulatan da yake yi, lokaci guda tafara jin wani iri ajikinta
domin Mama ba k'aramin gyara take yi mataba dan jin dad'in yaronta kawai.

Sai da yayi biji-biji da ita sannan ya sami nutsuwa, ita ko tayi lamo a jikin shi tana maida numfa
shi, kirjinta ya zubama ido ganin yanda suka fara cikowa cikin kasala yace,

"Khadija kin fara girma inyeee."

Shiru tayi mishi tana lumshe ido, kuma gyara mata kwanciya yayi ajikin shi yana d'an bubbuga
bayan ta kamin wani lokacin tayi bacci, sai da yaji numfashin ta ya fara sauka dai-dai sannan ya
lallab'a ya kwantar da ita.
sai da yayi wanka sannan ya fita daga d'akin kasa had'a ido da Maman yayi shi yasa itama saita
share shi.

"Mama zanje na rago sumata yanzu."

Tace "To a dawo lafiya babana."

Yana fita ta bishi da kallo tare da yin d'an murmushi tana girgiza kai.....









*MAMAN KHADIJA*‍♀
[2/26, 9:29 PM] ⓠʊ¥ґѦ℮м℮¥: *DR AHMAD*

19-20


*NA MAMAN KHADIJA*‍♀

Edit by *Hajja ce*

*HASKE WRITER'S ASSO.....*
(Home of expert & perfect writer's)


*A*hmad kam be samu damar dawowa da wuri ba dan saida ya biya shagwan d'inkinsu na
da, duk abokananshi suna nan harda oganshi nan shima ya zauna aka ci gaba dayin hirar dashi
harda masu yi mishi tsiya wai ina Matar shi ko tayi nauyi ne yayi banza dasu dan baya tunanin
zai iya fallasa sirrinsu.
Sai wajan k'arfe goma ya dawo lokacin Khadija da Mama na zaune a tsakar gida suna hira ya
shiga, kusa da Mama ya zauna yana furta,

"Washhh am tried Mamana."

"Babana kenan toh shi abinda ka fad'a a k'arshe mekake nufi?!"

Dariya suka yi shida Khadija ya kalleta itama ta kalleshi sai yaji tace,

"Kai Mama cewa fa yayi ya gaji."

"Au tohh! Uhmm kaji turawa toh Allah dai ya k'ara muku basira Mu ai karatun allo mukayi shima
dakyar Matar babana take bari naje."

Duk sun tausaya mata daga nan ta dinga basu labarai har wajan goma da rabi sannan ta
kallesu,

"Babana dare yayi Ku tashi ku shiga d'aki nima tafiya zanyi."

Shine ya fara tashi sannan Khadija ma tayi mata sallama suka wuce Mama ta bisu da kallo tana
musu fatan alkairi cikin rayuwarsu.

Kwanan Ahmad uku yayi musu sallama ya koma makaranta cike da kewarsu gabaki d'aya yana
sonsu yana jinsu a cikin jikinshi dan haka ya Kara d'aura anyar yin karatu mai d'orewa yadda zai
ciki burinshi.

*****

Ahmad kam ta b'angaran karatu sai dai ace sambarka domin kuwa ya samu abinda yake so
yana da kokari sosai kullum fatan shi ya cika burin shi na zama cikaken likita wannan shine
mafarkin shi tun yana da shekaru shida a duniya.


Kullum baya iyayin bacci indai baiji muryar masoyiyar shiba kuma abar kaunar shi farin cikin shi

mai kawar da duk wani buk'atunshi, yana son Khadija so mai tsanani so na hak'ik'a wanda babu
algus domin tayi mai hallacci musamman iyayanta fatan shi kar Allah ya kawo lokacin da zai
juya musu baya ko yayi musu wulakanci ta kowace hanya.


Ahmad kyakyawan mutum ne dogone yana da faffad'an kirji wankan tarwad'a ne yana da
doguwar fuska mai d'auke da dogwan hanci gashin girar shi mai d'inbin yawa wadda ta k'arawa
fuskar shi kyau da cikar zati, yana da d'an k'aramin baki zagayayye da idanuwa madaidaita sai
kwantaccen gashin baki wanda ya fara fito mai hakan kuma ya k'ara kawata fuskar tashi.

Yana son karatu sannan yana da yawan ibada baya son yaga yau yayi abinda zai sab'awa
ubangijinsa sai dai abisa rashin sani amma yakan yi iya bakin kokarin shi wajan ganin ya tsira
da mutuncinshi da zuciyar shi. Ahmad ko a wajan d'aukar karatu baya zama kusa da mata duk
yadda suke nanik'e mai baya yadda yw rab'u dasu domin sanin yadda zuciyar shi da gangarjikin
shi take na yawan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login