Showing 39001 words to 42000 words out of 44890 words

Chapter 14 - DR AHMAD BOOK COMPLETE BY Maman Khadija .pdf

16 Mar 2025

7233

*MAMAN KHADIJA*🙇🏻�♀
[3/14, 2:43 PM] ⓠʊ¥ґѦ℮м℮¥: *💗DR.AHMAD💗*

43

*NA MAMAN KHADIJA*🙇🏻�♀

Edit by *HAJJA CE*👈

*HASKE WRITER'S ASSO.....*💡
(Home of expert & perfect writer's)

*K*usan duk taji abinda ya faru tsakanin Ahmad da Mama dan haka agigice ta fara lalubar
wayarta tana sharar hawaye daga kwancen da take, tajima tana ringing sannan ya d'aga wayar
muryarshi tayi matukar yin sanyi da kaji kasan yana cikin damuwa.

Cikin muryar kuka ta fara magana,

"Ya Ahmad kadda kai min haka dan Allah ka rufamin asiri ka dawo gida kadda ka aikata wani
zunubin wanda zamu samu kamasho muma, ka dawo gida wallahi zan kwana a wajanka ko
Mama bata so amma kadda kaje wani wuri kaji dan Allah?!"

A kai-akai yake sauke ajiyar zuciya kamin yace,

"To ki daina kukan yanzu zan dawo."

"Nidai ban yadda ba ka dawo in ba haka ba wallahi bazan iya zama dakai ba sabida zanfara
zarginka gara ka dawo yanzu nasan ko nisa ba kaiba."

"Toh shikenan ganinan amma in taddake a d'akin mu kinji ko?!"

"Toh..."

Ta furta tare da ajiye wayar, idanu suka had'a da Maman wacce tuni tagama jin duk wata
magana da suka yi.

Idanun tane suka kuma kawo ruwa kamin tace,

"Mama kiyi hakuri tsoro na keji, wallahi tsoronake Yaya Ahmad bashi da hakuri ya riga yaje
makura kiyi hakuri.."

"A'a toh nikuma menene nawa khadija? ai kunfi kusa Allah ya baku zaman lafiya da hakuri da
juna, amma dai sai gobe zaki koma d'akin naku ko? sabida a d'an k'ara gyara shi.

Ba yadda zatayi tace,

"Toh Mama."

Goma saura ta sulale zuwa wajan mijinta domin tuni ya isheta da kira, lallab'awa tayi ta ajiye
yaron kusa da Mama tayi tafiyarta wajan Ahmad, kusan cin karo suka yi a hanya harya gaji da
jira zaizo ayi yanda za ayi, tana rungume jikin shi har gado ko kofar basu tsaya sakayawa ba
suka fara shagalinsu domin ba k'aramin hakuri Ahmad d'in yayi ba shi kanshi beyi tunanin zai
iya hakurin ba amma dai yasha wahala fiye da yanda masu karatu zasu fahimta....

Lokacin da tafiya tayi tafiya tuni malam Amadu aka fara sambatu da kiraye-kirayen sunaye
sabida ba karamin gigitashi babyn tashi tayi ba, sosai ta temaka mishi har wajan asuba suna
nanike da juna koya ta motsa saiya mai da ita jikinshi, sun manta da batun jaririn su abba da
yake dama yaron bawani damuwa da tsotsan dare yayi ba hakan yasa suka manta dashi.
Kasa fita sallar asuba yayi sabida wani irin matsiyacin zazzabi daya sakko mishi, koda sukai
sallah kuma nad'eta yayi ajikin shi yana kyarma itako tuni tafara mishi hawaye sabida tausayin
shi takeji dan har ta fara tunanin ko yanada shafar aljanu.

MAMA kam jin kamar motsi kusa da ita ya sata tashi zaune tare da haskawa,

"Lahaula wala kuwwata illabillahir aliyulazim ni Habiba nan ta kwangarar dakai kenan ta tafi
wajan mijinta, oh ni yaran zamani to banda shirme aida dashi ta tafi idan da ya tashi ni zan
bashi Nono ko kuwa..."

Kuma haska yaron tayi idanunshi biyu yatsa kawai yake tsotsa, hab'arta ta kama kamin tace,

"Ikon Allah zamani..."

Koda tayi sallar asuba rungumar yaron tayi jikinta tana mutmushi idan ta tuna shirmen iyayen
shi.

Koda gari yayi shaaa tuni Ahmad ya fara galabaita sabida aman daya keta shek'awa dan haka
arud'e khadijan ta nufi d'akin Mama tana hawaye.

A tsorace Maman ta mik'e dan dama bawani barcin kirkine ya d'auketa ba sabida tana gudun
kadda yaron yai kuka,

"Lafiya khadija?"

"Mama bashi da lafiya tun dare yanzu kuma amai yake tayi harya gaji."

"Innalillahi muje na ganshi."

Saida ta goya yaron sannan suka nufi d'akin yana kudundu ne a cikin bargo ya rufe har
fuskarshi, sannu Maman tayi mishi kamin tace,

"Ina wayarka akira maka ko Hassan ne ya duba ka?"

Muryarshi tai sanyi sosai yace,

"Mama tana falo."

Khadija ta kira dr. hassan da yake abokin aikin Ahmad d'in ne kuma suna abotaka sosai sannan
unguwarsu d'aya, saida tayi mishi bayani sannan yace gashinan zuwa.

"K'arb'eshi kibashi nono inje inrage ayyukan kamin yazo ya dubashin."

Zama tai kusa da Ahmad domin bawa yaron nono bayan fitar Maman d'akin Ahmad ya
rungumota jikin shi yana kallon yaron kamin yai murmushi yace,

"Kinga be kuka ba da dadaddare gunta zai dinga kwana ma kawai ko?!"

"Eh..!"

Ta furta a hankali kamin tace,

"Ya jikinka?!"

Kirjinta ya matsa da karfi har saida yaron ya kware da nonon kamin yace,

Koma dai menene ai kune kuka jamin tunda da kika biyema Mama akaita jamin rai."

Shiru tayi mai tak'i yin magana dan tasan tsiya yake yi mata,

"DR. ya haka?"

Cewar dr. Hassan dake dariya, shima Ahmad d'in dariya yayi kamin yace,

"Kai nifa bana san iskanci kaje kakawo min magani kawai insha."

Ficewa yayi yana dariya itama dai Maman bata kuma bi ta kan shiba dan tasan ciwon berasa
nasaba da tasowar kwantacciyar jarabarshi ba.

Sai wajan sha-biyu sannan ya warware nan da nan ya fara lalubar khadija, saima lokacin ne ta
tuna da zafin dataji jiya da daren domin bakaramar wahala yaba taba.

Marairaicewa tayi tace,

"Kai yayana daga warkewar ka?!"

Ko kulata beyi ba sai da ya sami nutsuwa sannan ya rungumeta jikin shi yana sauke numfashi
murya k'asa-k'asa tace,

"Khadija kin sauya da yawa wallahi jinake kamar in makale ajikinki na daina fita, ashe idan
mace ta haihu k'ara canzawa take yi?"

Murmushi kawai tayi aranta tana cewa inda gyara ko, ai wannan aikin Mama ne.

Aminu ne ya zabga sallama d'akin da sauri suka rufe jikinsu da bargo kamin Ahmad din yace,

"Kai Aminu ya akayi?!"

"Mama ce tace akawo shi kuka ya keyi kuma a cire mishi kayan sanyin rana ta fara zafi..."

"To kawoshi nan."

Ganinsu cikin bargo yasa aminun cogewa saida Ahmad din yace,

"Kawoshi mana a'a Maman shi barci take yi."

Daga kwancen ya karbi yaron Aminu ya fita yana waka shi kuma ya gyara mai kwanciya ajikinta
yace,

"Bashi yasha sai muje muyi wankan."

*****

Babu sauran wata b'araka tsakanin ma'auratan domin Mama ta tsaya musu tsayin daka wajan
ganin zaman nasu ya d'ore amataki na adalci da kyautatawa juna, haka rainon yaron kusan
awajanta yake indai ka ganshi hannun khadija to nono zai sha ya saba da Mama sosai sabida
yanda take kulawa dashi kullum wajata yake kwana idan ya motsa tabashi ruwa, be tab'a yi
mata kuka ba.

Ahmad ya fara cuku-cukun neman karatun khadija ya sami karin girma da transfer zuwa
katsina dan haka cikin farin ciki ya gayama Mama tare da shawarar komawarsu gaba d'aya can,
domin Maman taso kin zuwa sai dai tun alokacin khadija ta saka kuka tare da rantsuwar itama
ba zata bishiba matukar Maman baza taje ba.
_Kunjifa surukai ko masu shirin zama surukan ya kamata musan irin zaman da zamu yi da
matayen 'ya'yan mu tunkamin sufara mana adduar mutuwa sabida bak'in halin da muke nunawa
a garesu."_

Ckin sati uku suka koma cikin garin katsina da zama sai dai sunbar Aminu a gidan malam
Mamuda sabida makaranta idan ya kammala J.s sai ya k'arasa acan. satin su biyu da tarewa
khadija ta fara zuwa makaranta inda ta samu Omar musa 'yar aduwa, bata da matsala da abba
domin ya fara shan kamu wanda Mama ke had'a mishi na waken suya da madara har taje ta
dawo be kosawa da jiranta shima d'an albarkar....

44

*NA MAMAN KHADIJA*🙇🏻�♀

Edit by *HAJJA CE*👈

*HASKE WRITER'S ASSO...*💡
(Home of expert & perfect writer's)

*K*ullum shike sauketa a makarantar sannan shi kuma ya wuce wajan aikin shi, yana
matukar girmama khadija da duk abinda ya shafeta bejin kiwar yi mata duk abinda take so
sabida bata rageshi da komai ba musamman wajan bukatarshi koda bata so takan jure tak'i
nuna mai hakan har sai ya barta dan kanshi. kullun cikim gyaran jikinta take da kayan marmari

da kamshi sam bata yarda yajita da wani tashi wanda ba kamshi ba, tana matukar amfani da
shawarwarin surukar tata domin wasu lokutan ma ita da kanta take murzamata kankana da
madara ko kuma kwakwa da jikakken dabino ko kuma had'in kanunfari da zuma, had'i ne masu
matukar k'arama d'iya mace lafiya da kuzari tare da d'and'ano mara algush shi yasa kullum
mijinta yake like da ita bata ba shi damar kallon kowace d'iya mace ba awaje kullum cikin
shaukinta yake ga yaronta shima tabarkalla kullum kara girma yake yi da wayau. waye yayi
tunanin rayuwa zata zo musu a haka? sabida kowa yana tunanin rashin mahaifi shine
durkushewar rayuwa, wannan ba haka bane domin Allah baya tab'a d'orawa bawa abinda bazai
iyaba sai dai shi bawan ya d'orawa kanshi ma'ana be amince da kaddarar shiba.

Fitowarta kenan daga cikin makarantar sotake ta biya gidan wata k'awarta da keta fama da
laulayi taga yau kwana biyu bata zoba taji wayarta nata ringing ko bata duba ba tasan mijinta ne
domin kalar nashi daban yake dama.

"Hello.."

Ta furta cikin yanayi na rigima da gajiya yace mata,

"Babyna ya kike?!"

"Lafiya lau nake, ya aikin naka?!"

"Lafiya lau, sai kewarki data dameni baby ganinan a hanya zanzo in d'aukeki mudawo gida idan
na huta zuwa anjima saina koma."

Murmushi tayi wanda har saida yaji sautin shi kamin tace,

"Toh shikenan amma ka tahomin da abu me sanyi yayana sabida yunwa nakeji sosai."

"Ok as you wish madam."

Samun wuri tayi ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login