Showing 36001 words to 39000 words out of 44890 words

Chapter 13 - DR AHMAD BOOK COMPLETE BY Maman Khadija .pdf

16 Mar 2025

7231

ta mik'awa saida ya gaishe ta sannan tace mai,

"Dama zance idan zaka taho gida kad'an taho da kaji zan bama khadijan sabida jikinta."

"Ok toh Mama zan taho dasu ai yau karfe hudu zan dawo insha Allahu."

"Allah yasa toh."

"Amin Mama bye."

Maman khadija ce da Maman Ahmad zaune sunata hirarsu ko wanne fuska awashe anyi jika,
jariri ya fara kuka Mama tayi saurin d'aukar shi ta koma wajan khadijan tace,

"Kinga yaron nan bazai yi wani barcin kirki ba in bajin nono yayi abakin shi ba kallifa yanda ya
keta wawure-wawure kiba shi yaja hakanan ai nonon yazo yanzu."

Cikin shagwab'a khadijan tace,

"Mama kaddafa yayi min da zafi?!"

"Keni ban san shirme bashi yasha ni zai kashemin dodon kunne."

Ita dai Maman khadija na gefe tana dariya, Maman ta samu ta nuna mata yanda zata bashi aiko
da sauri caraf ya cafke da karfin shi ya fara zuka ihu khadijan ta saka tare da furta.

"Wayyo Allah nono na Mama."

Saida ya saki sannan Maman ta amshe shi tuni yayi bacci itako khadija hadda hawayenta wai
da zafi. mutane nata shigo musu barka domin tuni Aminu ya gama zagaye mutune da suma
sunyi sabon baby.

Da la'asar ya nufo gidan yanajin ya gaji sosai sai dai har yanzu farin cikin da khadijar ta shayar
dashi da sanyin safiyar yau be sake shiba dan haka nan yake murmushi shi kadai tun a cikin
asibiti.

Yana faka motar ya kwaso ledojin daya taho dasu ya nufi cikin gidan, yayi mamaki da yaji mata
nata mishi barka da arziki, kayan ya zube cikin kitchen ya nufi d'akin khadijan,
aiko zaune ya taddata da k'aton jariri ahannu tana kukan bashi nono shi kuma yana kukan sai
yasha.

Da sassarfa ya isa garesu sam be lura da matan dake cikin d'akin ba ciki kuwa hadda Maman
tashi. d'aya bayan d'aya suka bar d'akin ganin yanda malam Amadu ya rungume iyalin shi yana
jin wani farin ciki na ratsa zuciyar shi,

"Allah yayi miki albarka babyna Allah yayi miki sakayya da Aljanna yanda kike faranta min kema
Allah yafaran tamiki ashe kinajin ciwo da safe amma kika sani dole na dameki ko?gashinan
kinja na zunguro shi, nagode sosai yanzu kukan me kike yi shima yana taya ki ha?"

"Amin honey yaya na wai dole sai yasha nono kuma ko d'azu saida naba shi wallahi akwai zafi."

Bin yaron da kallo yayi yaga sai lasar bakin shi yake yana son saka hannu abaki, murmushi yayi

kamin ya share mata hawayen yace,

"Kin gafa kina kuka yana kallonki kadda kisa ya raina kifa bashi kad'an yasha saimu gaisa dashi
dan kar ya min kuka."
[3/14, 2:43 PM] ⓠʊ¥ґѦ℮м℮¥: *💗DR.AHMAD💗*

42

*NA MAMAN KHADIJA*🙇🏻�♀

Edit by *HAJJA CE*👈

*HASKE WRITER'S ASSO....*💡
(Home of expert & perfect writer's)


*B*ayan kwana biyu masu jego sunyi shar abinsu basu da wata damuwa sabida irin kulawar
da suke samu daga gurin duka side din, abba sai k'ara washewa ya keyi da wayau tubarkalla
Mama bata da aiki saina kallon abba tare dayi mishi rawa ita dai Allah ya jarabce ta dason
yaron wanda har bata iya boyewa.
AMINU kam kullum sai anyi daga dashi domin soya keyi ya dinga goyashi itako Mama taki
yarda khadija ko babu ruwanta daya ce bani take mika mishi haka Maman zatai tamata fad'a
amma bazai hana gobema taba shiba dan tana ganin bayan uban yaron to Aminu ne na biyu.

Malam Amadu kuwa tuni ya fara tsanewa atsaye duk da cewa kullum yanzu azumi yake yini
dashi amma dakyar yake barci sabida kewar matar shi.

Zaune yake cikin ofis d'inshi yau tun safe babu abinda ya tsinana gashi yanzu har anfara kiran
sallar azahar a wasu masallatan, wayar shi ya lalubo kamin ya dan na mata kira, cikin
shagwab'a ya furta,

"Babyna..!"

Murmushi tayi kamin tace "uhumm yayana ya aikin?"

"Na kasa baby wallahi yau jinake kamar zan halaka Mama ta daina jin tausayina wai har yanzu
baki fara sallah ba?"

Tunowa tayi da fad'an Mama dan haka da sauri tace mai,

"Eh ban fara ba, amma dai yau baka azumin ne?!"

"Inayi baby ya zanyi."

"Ayya toh shike nan dama cewa zanyi kai sauri ka dawo yanzu kamin Mama ta dawo ko ragewa
sai kayi, tunda kuma kana azumin shike nan.."

Ai tuni ya mike tsaye tare da furta,

"Ashe batanan amma kikaki gayamin tun safe? bari inzo ganinan."

Dariya ta fara yi mai bayan ta ajiye wayar, zuwa yanzu mijin nata ya daina bata mamaki sai dai
tausayi, sannan kullum adduarta gareshi shine Allah ya dauwamar da hankalin shi a kanta ya
kauda idanunshi daga kallon matan banza ballema harya kaiga ta yawa.

Jikinta ta gyara da turaruka sannan ta tsaya jiran shi tana addu'ar Allah yasa kar Mama ta dawo
da wuri. aiko sai gashi yau ko takan abba bebiba wata irin wawar runguma yayi mata akirjin shi
kamin ya fara sunsunarta da lasarta, jikinshi harwata tsuma ya keyi yana cewa,

"Babyna yaushe rabon da ko rungumarki nayi Mama ta hana komai wallahi na kusa mutuwa da
kyar nake daurewa, dan Allah da abun ya d'auke kimin magana ko sau d'aya ne nayi batare da
sanin maman ba kinji matata?!"

Sumarshi take shafa ahankali cikin lallashi kamin tace,

"Kayi hakuri kaji kayiwa Mama biyaya nima ka tayani yi mata abinda take so."

Bak'aramar murza ta shaba a hannunshi ba sannan ya samu ya rage damuwar shi, Allah ya
temaketa harya gama bired'ed'en shi hankalin shi be kai wajan abinba dan tasan da saiya gane
ta sami tsarki ita kuma tana tsoran kar Mama ta gane tayi mata kallon wani abun.

kwance yayi agadon yana sauke nunfashi, har lokacin idanunshi alumshe yake kuma hannunshi
na saman kirjinta yana cigaba da shafarta,

"Uhm! honey ya Ahmad to ka tashi ka shirya jikinka kamin Mama ta dawo ta taddaka kasan
fad'a zatayi kuma sai ta gane sannan ya maganar azuminka yana nan?!"

Dariya yayi kamin yace,

"Ai kema kin san yabi ruwa na yau babyna amma dai zanyi gobe insha Allahu ai na rage zafi."

Itama dariyar tayi kamin tace,

"To yaza kai da girkin da zatayi maa anjima?"

Janta yayi jikin shi yaci gaba da tsotsar lips d'inta idanunshi arufe tsawon lokaci domin harta
farajin zafi sai dai batasan ta katse shi domin samun nustwarshi itace tata.

Motsin yaron ya kwaceta dan haka da sauri ya tashi ya fara goge jikin shi ita kuma ta nufi abba
dake son fara kuka.

Wucewa yayi d'akinsu yana fad'in,

"Sorry bari inyo wanka yaron baban shi sai nazo in d'aukeka kajiko?"

Tana bawa yaron nono shi kuma ya shigo ya canza kaya sai kamshi ya keyi, ganin irin kallon da
take mishi yasa shi zama gefenta yace,

"Baby na can zamiki ne?!"

"A'a dadyn abba kawai dai naga kaimin kyaune sosai ina fatan zaka kauda idanunka daga
kallon haramun?!"

Abba ya amsa a hannunta kamin yace,

"Ki tayani addu'a babyna insha Allah zan kiyaye nagode da kulawarki gareni Allah yayi miki
albarka."

"Amin."

Wasa ya fara yima yaron kamar wani babba shiko yaro ya zubama fuskar baban shi ido.

"Kaga nidai kawoshi ka tafi kadda Mama ta dawo tayi tunanin ko wani abun kadawo mawa."

Yana mika mata yaron Mama na shigowa domin tunda ta hango motarshi taji hankalinta ya
tashi, sannu da zuwa sukai mata ciki-ciki ta amsa tare da jefama Ahmad din wani kallon
tuhuma,
kauda kashi yayi ga barin kallonta kamin yace,

"Mama ashe unguwa kikaje yanzu na shigo khadija ke gayamin gidan hassan naje shine nace
bari na biyo daga nan in gaya miki hadda d'an-wake zakimin na bud'a baki sabida na rabu dacin
shi wallahi."

Washe baki Maman tayi kamin tace,

"Au to shike nan yasu hassan d'in ai tun safe nafita dawowata kenan."

"Toh sannu rikeshi baby in wuce sai na dawo."

Kallon tausayi Maman tabishi dashi kamin ta maido kallonta gun khadija tana murmushi tace,

"Ashe yanzu shima ya dawo?!"

"Eh Mama shigowar shi kenan sai ya dauki abba toh kema sai gashi kin shigo kamar tafiyar ku
d'aya."

"A'a ni yanzu na shigo Allah ya dawo dashi lafiya."

"Amin Mama."


Irin gyaran da Mama takema khadija ya sanya tuni itama tafara adduar Allah yasa Mama taje
unguwa kosun samu su sake da juna dan ta tsumu iya tsumuwa, sai dai ina Mama ta tsare ta
rantse sai anyi arba'in cas.

"Please Mama na kiji tausayi na tunda tayi kwanaki 40 din kibarni da ita wallahi kamar zan mutu
nakeji ki tausaya min Mama dan Allah ki cetoni daga fad'awa halaka kamar yadda kika cetoni
tun kafin nakai haka girma.."

"Oh ni na bani babana nadai koma abokiyar wasanka kawai, yo in ba haka ba niza ka samu da
wannan maganar?!"

"To Mama ya zanyi kefa mahaifiya tace amma kin hanani ganin khadija bani da nutswa idan na
gaza hakuri na dauko wani zunubin wallahi hadda laifinki ciki Mama please, yanzu bakya sona
kin daina damuwa dani baki san ya nake kwana ba haba Mama ni nefa Ahmad d'inki babanki
d'anki wanda kikafi so a duniya."
Tashi tayi tabar mishi d'akin cike da jin nauyin maganar shi, aiko shima afusace ya bar gidan
yana cewa,

"Yaukam bazai yiwu ba wannan wahalallen barcin da nake yi ba dani ba, babu wani lemon
tsamin da zanshi...."

*MAMAN KHADIJA*🙇🏻�♀
[3/14, 2:43 PM] ⓠʊ¥ґѦ℮м℮¥: *💗DR.AHMAD💗*

41

*NA MAMAN KHADIJA*🙇🏻�♀

Edit by *HAJJA CE*👈

*HASKE WRITER'S ASSO....*💡
(Home of expert & perfect writer's)



*H*ararar yaron tayi kamin ta saka mishi nonon cikin bakin shi, dafe kafad'unta Ahmad yayi
ganin yanda take kankame jikinta kamar ma so take ta kwace abinta.

Yaron yaci gaba dajan abincin shi har sai da ya saki dan kanshi sannan Ahmad d'in ya d'auke
shi daga jikin ta ya rungumeshi yana ta sakin murmushi, kallon yaron ya keyi sosai ganin irin
kamar da yaron yayi dashi, Allah nagode maka da kamin wannan kyautar, Allah nagode maka
da arzikin da kamin ka bani dama in cigaba da gode maka."
Rungumo khadijan yayi tare da shafar kirjinta wa inda suke cike taf da alama ruwan nonon
yariga ya samu, kwab'e mishi hannu tayi tana hararar shi.

"Allah ya baki aljanna matata ina fatan Allah ya barmun ke babyna kin isheni zaman duniya
dana kiyama wallahi nagode nana khadijana..."

Murmushi kawai tayi tare da jawo ledar balangun da babanta ya aiko mata dashi d'azu sai
faman kamshi yake.

Kusan tare suka cinye naman har lokacin yaron na hannun abban shi, shiko Ahmad tuni ya
sami abin kallo gani ya keyi kamar banashi bane jiyake kamar za'a ce bani ba naka bane, ko
yaji ana tashinshi daga bacci yasan mafarki ne amma yaji shiru sai mamakin kanshi yake wai
shike da wannan zuk'ek'en yaron.
"Oh ikon Allah babana ka fita mana mutane nason shigowa amma sabida Allah kazo kayi
zamanka a ciki ko kunya."

Kallonta yayi da kyawawana idanun shi kamin yace,

"Mama ganin su fa na keyi, kuma so nake muje asibiti yanzu a duba su."

"Amma dai ai ka bari suyi wanka ko? tunda shi yaron ance so d'aya ya wadatar dashi."

Cikin shagwab'a khadija tace,

"Mama waini bake zakimin wankan ba to waye zai min?"

"Haba khadija nace miki gwaggonki zatayi miki amma sai tambayata kike yi tun d'azu."

Idanun shi awaje yake kallonsu kamin yace,

"Haba Mama wai kina nufin baby tubewa zata yi wata taga jikin ta bayan ni?!"

Harararshi tayi sam idanunshi sun rufe kamin tace,

"Kai tafi can, nifa ban san hauka gwaggonta ta tace wata? to eh ita zata yi mata."

Grgiza kanshi yayi kamin yace,

"Ahh no gaskiya Mama gaskiya ban yarda ba wallahi kuma ban amince ba indai ke baza kiyi
mata ba to gaskiya sai dai kibari ni nayi mata ko kuma a hakura da wankan, ya za ayi kowa sai
yaga jikinta dan Allah haba-haba.."

Batai mamakiba domin tuni tagane irin masifar kishin shi akan khadijan amma batai tunanin
abin ya kai haka ba. Kai ta girgiza kamin tace,

"Allah ya shiryaka to."

Sannan tabar musu d'akin.

Shi kam juyawa yayi wajan khadija yana tambayarta,

"Babyna babu inda kemiki ciwo ko?!"

Kallonshi tayi sannan ta kalli yaron dake hannun shi tace,

"Laah ya Ahmad wallahi da kai yake kama ka gani kuwa?"

Murmushi yayi tare da kashemata ido d'aya yace,

"Yoo yarinya angaya miki ni d'in na wasa ne ko matsalata ai tasa yaron yayo kama dani,
tambayarki nayi fa ina kemiki ciwo?"

"Jikina be min ciwo amma dai ina jin zafi awajan abuna."

Kwantar da yaron yayi kamin yajata can karshen d'akin saman gado yace,

"Kwanta in gani ko kinsami kari ne."

Bata yi mishi gadda maba domin tana jin zafin wajen sosai daurewa kawai take yi. cikin
nutsuwa ya dubata yaga tasamu amma dai beda yawa befi aimata d'inki d'aya ba kuma daga
waje ne, shafarta ya fara yi bayan ya gama dubawa musamman kirjinta da sun riga sun gama
tsokane mishi idanu, ganin yana neman fita hayyacin shi ne ya sata fara tureshi daga jikinta
sabida tasan bata da abin bashi sannan tasan shi wasan ninnan bawani yi mishi suke ba shi dai
kawai yajishi in.

"Nashiga uku ni Habi babana uban me kuke yi cikin kuryar d'aki kuma daga haihuwa yau
sakaran wofi kawai...? zaka fito ko saina ci maka mutunci yanzun nan?"

Zaro idanuwa yayi yana kallon khadija saida ya dai data nutsuwar shi sannan ya fito yanata
murmushi tare da shafar sumarshi yace,

"Kai Mama bafa wani abu zanyi ba dubata kawai nayi yanzuma idan kin yi mata wankan zanje
da ita sai nayi mata d'inki tukunna ta denaji ciwon."

Harararshi tayi kamin tace,

"To naji zoka fice waje dan Allah kabarta ta huta haba mana kadai. san yanda haihuwa take
yarinya nason hutu amma ka like da wanne kakeso taji?"

Hakuri ya bata tare da sumbatar yaron shi agoshi sannan ya bar d'akin bako kunya shi yanzu
har wata fitsara-fitsara yakeji sabida ya girna ya zama Abba.

***

Kullum gidan nan cike yake da mutane Ahmad sam be cikin sukuni domin idan yabar gidan tun
safe to be kuma dawowa sai dare sabida mutane. sosai yayi kokarin ganin yayima khadija da
yaron shi bajinta domin akwati uku yayima khadijan sannan yayi ma yaron akwati d'aya sabida
shi yaron kullum cikin samun kaya ya keyi daga abokanan shi da dangi kowa ya naso yaga
yayima Ahmad din wani abu da zaiji dad'i.

Sun bawa mutane mamaki domin kuwa kowa yayi tunanin zai sakama yaron sunan mahaifin shi
ranar sunan sai kawai sukaji an sakama yaro suna MAHMOUD, wato sunan malam Mamuda

mahaifin khadija sai dai sun saka mishi suna na alkunya wato Abba.

Har hawayen dad'i malam Mamuda yayi lokacin daya ji sunan yaron yayi farin ciki tare da
godema Allah, sannan ya shiga har gidan yayima Mama godiya sai dai itama godiya take mishi
hadda hawaye yayinda ta tuna irin halaccin dayayi musu a cikin rayuwar su.


BAYAN SUNA:-

"Mama inaga abarta anan kawai d'akinta zaifi tunda baba yak'i yadda ta koma can d'in kuma
mani sai naga dama nan da can d'in ai duk d'aya ne ko?!"

Wani kallon banza tai mishi kamin tace,

"Babana ban san meyasa yanzu ka rainani ba wallahi, so kake yi in bar maka yarinyar mutane
kasani jin kunya wataran? kaddafa ka kamanta nice mahaifiyarka na sanka ciki dabai dan haka
bazan bar khadija a d'akin taba zata dawo nan d'akina kai kuma ka zauna ana kun data gama
wanka saita dawo d'akinta idan tagama zaga dangi amma gaskiya bazan yadda da zamanku
tare ba sabida inajin tsoran halinka babana..."

Hakuri ya bata tare da barin d'akin cikin sanyin jiki. zaune ya taddata tana bawa yaron nono
shima jikinta ya shige har wani ajiyar zuciya ya sauke kamin ya fara d'an shafarta sama-sama
yana jin wata irin masifar kewarta jiyake kamar yayita tsala ihu ko za afahimci abinda ya keji
cikin jikinshi.
Daga shi har ita nisa suka yi,sai dai sukaji ihun yaron ashe Ahmad dinne ya kwace nonon daga
bakin shi ba tare da sanin lokacin da yayi hakan ba wato shi ya maye gurbin yaron, dariya suka
saka tare bayan yai saurin maidama yaron nonon cikin bakin shi.

Dariya suke yi sosai musamman khadija da harwani nuna Ahmad din ta keyi da yatsa, saida
Mama ta leko sannan sukai fargai-fargai dasu tace,

"Kukan me abba keyi haka?!"

Shiru su kayi kowan ne ya sadda kanshi k'asa, hararar Ahmad d'in tayi kamin tace hala yau ba
zaka fita ba ne ko?!"

Mikewa yayi ya shige ciki saida ya shirya ya fito, Maman tabashi hanya ya fice sannan taje ta
amshi yaron ta goyeshi ta fara had'a kayan da zasu bukata ta dinga kaiwa d'akinta ita dai
khadija nata ido kawai.

Saida ta gama kintsa komai sannan ta tasa khadijan zuwa d'akinta,

"Ke naga alamar bawani hankalin kirki gare kiba inba haka ba duka yaushe kika haihu da zaki
fara biye mishi tunda kin san ba hakuri ne da shiba? koda yake bazan yi mamakiba tunda shine
ya raineki babu abinda be koya mikiba ke ma kin zama shi."

Kunya tasa khadijan rufe kanta akan gado tun tanajin motsin Maman har barci ya d'auketa a
haka.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login