Showing 33001 words to 35354 words out of 35354 words
Chapter 12 - KAINE SANADI BOOK COMPLETE (1 to End) By Sodangi & Khalisat .pdf
GANDUJE*
anci ansha anyi shagali sosai.
Haka zaman su yaci gaba da kasancewa cikin kwanciyar hankali, sai dai Amatullah bata taba
koda batan wata bane, tayi amfani da shawarwarin da khadija ta bata inda cikin kankanin lokaci
Aliyu ya haukace mata sai ririta ta yake yi tamkar kwai.
Ita kuwa kullum bata da aiki sai na niman gafarar sa, yariga yace ya yafe mata amman kullum
bakin ta baya gajiya da furta hakan.
A cikin wannan yanayin ne kuma akayi zabe inda mahaifin Amatullah watau Alhaji Ahmad
Fage _Mr President_ ya fadi zabe, inda ya sauka ya tattara ya dawo gida daga Abuja.
Anan ne mai martaba sarkin Kano watau _Alhaji Abdul Rasheed Ganduje_ ya bawa mahaifin
Amatullah sarauta inda aka nada shi a sarkin kudu.
Anyi shagali sosai a ranan inda Amatullah tayi kuka sosai tare da kara nadamar irin rayuwar ta
ta baya.
Nan ta kalli Aliyu tace hakika ina alfahari da kai miji na *KAINE SANADIN* shiryuwa ta nazama
mutum sosai.
*KAINE SANADIN* da yasa na san darajar d'an adam nasan cewa lallai mutum ko yaya yake
ba abin wulakantawa bane.
Aliyu kayi min halacci sosai a rayuwata banida bakin da zan gode maka, Aliyu *KAINE
SANADI*
*KAINE SANADIN* komi Aliyu *KAINE SANADIN*.........wani irin ciwon ciki ne ya murde ta
wanda yasata kankame Aliyu tana salati hade da kuka.
A rikice Aliyu ya rike ta yana fadin "meya same ki? Menene?"
Tuni Amatullah ta shid'e a guje ya sure ta yayi mota da ita, khadija wacce shigowar ta kenan
ta hango su tunda ga gate ta fallo da gudu ta fada motar a rude take tambayar sa meya sami
Amatullah d'in?
Bai kulata ba illa motar daya fisga a guje suka nufi asibiti.
Likitoci ne suka rufu a kanta suna niman ceto rayuwar ta, sai dai ina abin yaci tura.
Amatullah rai yayi halin sa.
"Inna lillahi wa'inna ilaihirraju'un."
"kullu nafsin za'ikatil maut".
Aliyu najin wannan labari ya yanke Jiki ya fadi, ita kuwa khadija kamar wata tababbiya haka ta
koma, kai mutuwar Amatullah ta daki jama'a da dama.
Fad'in irin gigicewar da iyayan Amah sukayi bata baki ne, a matsayin ta na babbar y'arsu
sun d'imauce sun gigice, saboda matuwar tazo masu a bazata.
Amman daga k'arshe haka suka hakura suka fauwalawa Allah lamarin sa..
Suna k'ok'arin yi mata addu'a da sadaka da niyyar Allah yakai ladar kabarin ta.
Mutuwar Amatullah ta tsayawa Aliyu da khadija a rai, mutuwar bakaramin shigar su tayi ba,
gaba d'aya gidan nasu ya hargitse babu wani kwanciyar hankali saboda tunanin irin rayuwar da
sukayi da Amah, ta addabe su tun daga lokacin da take Amar ta har Allah ya sa ta shiryu.
A bangaran Aliyu kuma wani irin son Amah ne ke d'awainiya da shi, mutuwar ta gigi tashi
sosai rayuwar su da ita tundaga farkon haduwar su har zuwa lokancin da sukayi aure yanda
suka kwashi dirama da yanda ta shiryu ta ringa kokarin kyautata masa tare da son su zauna
lafiya abin ya tsaya masa a rai.
*******
*BAYAN WATA SHIDA*
komai ya fara dawowa _normal_ a gidan _Aliyu Rasheed Ganduje_ in da suka hakura suke
k'ok'arin yima Amatullah addu'ar samun rahma wajan ubangiji.
Iyayan Amatullah sun d'auki son duniya sun d'aurawa _little_Amah, koda yaushe suna tafe
gidan dan ganin _little_ Amah, tare da d'inbin alherin su.
Soyayya mai tsafta a ke shimfidawa a cikin gidan Aliyu, tsakanin sa da khadija, tamkar zasu
cinye juna haka sukeji.
Haka sun d'auki son duniya sun d'aurawa d'iyar su Amatullah.
Amatullah nada shekara biyu khadija ta sake samun wani cikin, murna a gun Aliyu da su mai
martaba abin ba a cewa komi.
Sai kace ba a taba haihuwa a gidan mai martaba ba haka suke ji.
Sannu a hankali suka ci gaba da rainon cikin har Allah ya sa ya isa haihuwa, inda khadija ta
haifi santalelen d'an ta mai kama da mahaifin sa tamkar kwabo da kwabo.
Fad'in irin hidimar da aka sha lokacin haihuwar nan tun kafin suna bata lokaci ne,
Ranan suna yaro yaci sunan mahaifin marigayiya Amatullah watau Ahmad, iyayan marigayiyar
sunyi matukar farinciki da hakan, sun nuna farincikin su sosai, sunyi hidima sosai da mai jego
da d'an ta wanda suke kira da *SULTAN* saboda dama wannan shine burin marigayiya
Amatullah ta samu ciki ta haihu tasawa d'an sunan mahaifin ta.
********
Bayan suna da k'wana biyu, Aliyu ya kwashi iyalin sa suka tare a tamfatsetsan gidan su,
haka rayuwar ta ci gaba da kasancewa a tsakanin Aliyu da iyalan sa, suna yawan tunawa da
Amatullah sunayi mata addu'ar samun rahama.
ni kaina mutuwar Amatullah ba karamin gigita ni yayi ba,wannan dalilin ne yasa na aje
alk'alamina ina hawaye ina yiwa _Aliyu Rasheed Ganduje_ ta a ziyyar matar sa _Amatullah
Ahmad Fage_ Allah yajikan dukkan musulman dasuka riga mu gidan gaskiya, mu kuma idan
namu yazo ubangiji Allah yasa mucika da kyau da imani Ameen summa Ameen.
_ALHAMDULILLAH_
_ANAN NAKAWO K'ARSHAN WANNAN LITTAFI NAWA MAI SUNA KAINE SANADI IN DA
NAYI KUSKURE UBANGIJI ALLAH KA GAFARTA MIN_.
_WANNAN LITTAFI NAWA SADAUKAR WACE GAREKI KAWATA TA KAINA, KUBRA USMAN
BALA_
_JINJINA TAKI CE UWAR DAKINA_
_KHADIJA SIDI_
_ALLAH YABAR KAUNA, HAKIKA INA ALFAHARI DAKE A KODA YAUSHE._
_WANNAN LITTAFIN NAWA TUKUICI NE A GARE KI MAMAN RABI'A WALLAHI BANIDA
BAKIN DA ZAN GODE MAKI AMMAN KI SANI INA KAUNAR KI HAR A ZUCIYA TA ALLAH YA
BAR KAUNA._
_KUNE ABIN ALFAHARI NA KAWAYE NA DA BANIDA TAMKAR KU A DUNIYA._
_1:KHALISAT HAYDAR_
_2:MAMAN SHAKUR_
_3:UMMI AYSHA_
_4:KAUSAR LUV_
_5:SADIYA LAWAL BALA_
_6:PHARTYMA ZAHRA_
_KIN ZAMA JININ JIKINA_
_ANTY AMEENA IBRAHIM_
_INA ALFAHARI DAKE A KODA YAUSHE, BAZAN TABA MANCE KARAMCIN KI A GARE NI
BA._
_KUNFI KOWA KAUNAR WANNAN LITTAFIN_
1:MRS XOXO
2:ZARA BUKKAR
3:SADIYA LAWAL BALA
_BAN MANCE DA KU BA_
_NEW JENERAL JOINT_
_PHERTY NOVEL'S_
_MATAN KWARAI_
_KHALISAT HAYDAR NOVEL'S_
_MUSHA KARATU_
_MAMAN ABBA NOVEL'S_
_ZAUREN ADDA BENA
_ANTY SIS, ANTY SIS, ANTY SIS._
_WALLAHI BANMA SAN ME ZANCE MAKI BA, KUKA ZANYI NE KOKUWA DARIYAR
FARINCIKI ZANYI NE DA IRIN GUDUN MAWAR DA KIKE BANI A KODA YAUSHE?_
_NAGODE NAGODE NAGODE ALLAH YASAKA DA ALKAIRI YA KARA GIRMA._
_ALLAH YARABAKI DA SHARRIN MAKIYA DA MAHASSADA YASA KI GAMA DA DUNIYA
LAFIYA._
_ALLAH YA RAYA MANA SULTAN RAYUWA TA ADDININ MUSULUNCI AMEEN, SODANGI
TANA KAUNAR KI MATUKA TANA KUMA ALFAHARI DAKE A KODA YAUSHE._
_A GAISHE KI DA BABBAN MURYA UWA MABADA MAMA, UWA MAFI UBA KODA KOWA
UBAN YAZAMO SARKI NE._
_NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)_
HAKIKA MUNA ALFAHARI DA KUNGIYAR MU _ALLAH YAYI MANA JAGORA YACIKA MANA
BURIN MU NA ALKAIRI, INA GAIDA DUKKANIN MEMBERS NA NAGARTA_
_INA KUMA YIWA SHUGABAR MU WATAU BENAXIR UMAR FATAN ALKAIRI A RAYUWAR
TA UBANGIJI ALLAH YABADA ZAMAN LAFIYA YABADA ZURI'A D'AIYYABA, AMEEN._
_LITTAFAN MARUBUCIYAR_
YARGATA
JAWAHEER
KAMILA
ALIYA
A ZUMUNTAR MU
WAHEEDA
GIMBIYA AMEENATU DAN MUSA
KAINE GATANA
REAL AMANI
RUGUNTSUMI
MAKIRA
KAINE SANADI
_FOR ANY COMMENTS OR CORRECTION_
07034992740
www.fiddausi.wordpress.com
*WRITTEN BY*
*FIDDAUSI SODANGI*
*SHARHI*
*Alhamdulillahi*
*Masha Allah*
*FIDDAUSI SODANGI*
FIDO
FIDO
FIDO
*MY REAL AMANI*í ½í²–
_Congratulations swthrt_
Warra buk
Warra story
Kai naji dadi, nayi farin ciki musamman idan ana cin uban Amah har ji nake kada wajen ya kare.
*Fiddausi* kin fadakar,kin nishadantar,kin waazantar kin kuma ilmantar sbd duk mai tsoron
muzanci na rayuwa zai raba kanshi da hali irin na Amah yar President.
Alal hakika kinyi namijin kokari wajen tabo mana wannan muhimmin maudu'een mai taba zuciya
wanda muka dauki masifa muka dora ma kanmu na wulakanta dan Adam.
Da farko dai a cikin Al-qur'ani mai girma Allah yace *"HAKIKA ALLAH YA KARRAMA DAN
ADAM"*
Ubangijin daya haliccemu ya karrama dan Adam kai waye da zaka wulakanta shi???????
Hakika babu babbar asara da tabewa irin wulakanta dan Adam sbd Allah ya daukaka shi ya
kuma karramashi fiye da ko wace halitta. Amma Allah ya kawo mu zamanin da wulakanta dan
Adam, muzantashi da disgashi ba wani abu bane a wajen wasu tsabar rashin tarbiya da rashin
sanin hakkokin addini.
Duk wani dan Adam daka gani a rayuwa da tashi kalar baiwar da Allah yayi mai don haka idan
ka wulakanta shi zaka ga hukuncin hakan a gaba ko a dunia ko a lahira.
Musamman talaka,yanzu an rainamu an maidamu ba kowa ba,idan har kai talaka ne shikenan
baka da sauran daraja ko kima a idon wasu yan uwanka talakawan da uwa uba masu kudi. Sun
maidamu bola,juji, shara alhalin basu San kalar matsayinmu da baiwar da Allah yayi mana ba.
Sometimes raini da wulakanta dan Adam baida rana sbd u can mess wt d wrong person kamar
yarda ta faru da *Amah ta Fido* inda ta raina *Aliyu* sadauki ta daukeshi kaskantacce alhalin
bata san ina ya fito ba,tana kiranshi talaka,tana zaginshi harda tofa yawu not knowing dan
*Sarauta* ne,yama fita asali da matsayi a rayuwa.
Wani har idan zaka mai mugun abu zai kudurta ramawa komin wuya komin rintsi Kamar yarda
*Aliyu* ya gwada ma Amah matsayinta ta hanyar aurenta don yayi *Ramuwar gayya* wadda tafi
ta gayya zafi. Wani na nan asiri zai maka,wani zai iya nakasa rayuwarka,wani zai iya illataka har
karshen rayuwa. Ya kamata muyi ma kanmu karatun ta natsu mu dena wulakanta dan Adam komin talaucin shi
komin rashin claz dinshi.
*Dunia makaranta* haka ma nake cewa *GIDAN AURE MAKARANTA* Amah ta dauki nata
karatun da taga uwar bari. Tsabar isgilanci, taurin kai da rashin mutunci irin na *Amah* bai sa ta
saduda ba lokacin data auri *Aliyu* sai ma iskanci da wulakanci daya karu kawai
Zagin miji,zagin iyayenshi haba mana fisbilillahi wane irin namiji ne zai yi shiru mace na antaya
ma iyayenshi zagi sai dai asirtacce ko kuma lalatacce sbd iyaye sunfi komai kuma suna gaba
da komai bayan ubangijinmu. Wlh mata muji tsoron Allah rashin da'ar nan babu inda zai kaimu
sai halaka, *ALJANNARMU NA* *KARKASHIN KAFAR MAZAJENMU* Fisbilillahi ta ina zaa shiga Aljannah ana zagin miji anan tsine mai ana mai dibar
albarka???????
Ya kamata muji tsoron Allah mu gyara gaskia.
*Amah* takadara irinta nasiha da lallashi baya masu amma taji dunia tunda gdn aure yabi da ita
duk da diyar President ce amma shi aure babu ruwanshi da diyar wane ko dan wane. Zunubi
daya ne haka ma lada.
Allah yasa mu dace ya kuma shirya masu hali irin na *Amah*. Gata jarabba sbd dama haka
system dinta yake cikin jaraba da masifa so her hormenes are always active and triggered
desperately waiting 4 alert
Its her nature haka Allah ke halitta kowacce mace da irinta. Haka kuma diri da kira bashi bane
zaman aure.
Hakuri,juriya ladabi da biyayya shine aure. Wanda *Amah* ta kasa kwantar da hankali daga
farko sai da taji uwar bari. Inda *khadeejah* tayi amfani da wannan damar tayi mata fintikau
gashi kuma ta fita komai na dadin rayuwar auren.
Abun nan ya zama ruwan dare game dunia. Rashin da'a,dibar albarka, rashin kunya,rashin
mutunci ta zama wata dabia ta ado ga yaranmu,basu ganin mutuncin kowa,basu girmama kowa
balle sanin darajar kowa
All wat *FIDDAUSI* is saying wulakanta dan Adam baida kyau sbd baa san inda zaa hadu ba
nan gaba. Mu dena tunanin social media ce,ko ba garinmu daya ko kasarmu daya da juna ba.
Allah ne mai caccanza Al ammura kuma yana iya canzawa akan kowa. Wanda ka raina ya
dawo karkashinka ko kuma ka koma makaskancin shi.
Alal hakika littafin nan yayi maana ya kuma waazantar kuma har aka gama banga laifin *Aliyu*
ba sbd koni zan iya fin abinda yayi ma Amah and anybody in his shoes can do same or worst
sbd itace *SANADIN* komai
*KAINE SANADI* *ALIYU* ne sanadin gyraruwar Amah da shiryuwarta.
*MUTUWA RIGA CE* tana wuyan kowa
Allah sarki rayuwa *Amatullah* duk an gama komai na rayuwar an koma ma ubangiji. Inda Allah
ya sota ta tuba (taubatan Nasuuha) ta nemi yafiyar mijinta ya yafe mata har suna zaman lfy da
mijinta da abokiyar zamanta.
*Firdausi* kinyi namijin kokari sbd ba kowa ne zaiyi yadda kikayi ba amma nasan kin nuna
mana cewa mutuwa bata *alert* sai dai ka jika cikin kabari a kowane hali kake a dunia. Inma
kana cikin shirme da garari irin na *Amah* part one ko kuma ka tuba ka natsu kana biyayyar
aure ko biyayyar iyaye irin na *Amah* part two. Allah yasa mu dace yasa mu cika da kyau da imani.
Allah ubangiji ya bamu ikon tarbiyantar da yaranmu ya rabamu da masu hali irin na Amah yasa
mu gama da dunia lfy.
Firdausi Allah ya nuna mana aurenki lfy yasa kin dace abokin zama nagari
Allah yasa ma karatunki albarka ya baki aiki mai albarka .
Kip rocking í ½í²ƒí ¼í¿¾and continue d gud jobí ½í±Œí ¼í¿¿
#Muna tareí ½í¸»
*ILYSVM*í ½í¸í ½í¸˜
*AuntySis*í ½í²ždinki ce