Showing 24001 words to 27000 words out of 35354 words

Chapter 9 - KAINE SANADI BOOK COMPLETE (1 to End) By Sodangi & Khalisat .pdf

16 Mar 2025

3765

tsawa uwar
ta daka mata, "wani irin maganar banza ki keyi haka Amatullah?"
"to wallahi ni babu ruwana badani ba a wannan rigimar dakike nima ki d'aukowa kanki ba,
gara ki rufawa kanki asiri ki kwantar da hankalin ki kiyi zaman aure kamar kowace mace,
amman ni babu ruwa na Karma kisake mahaifin ki yaji wannan mummunar zance a bakin ki,
kinji nagaya maki!" Daga haka ta katse wayar ta, Amatullah ta mik'e ta zare _key_ d'in ajikin k'ofar ta nimi waje ta
boye shi sannan ta dawo ta zauna ,
tasaki kuka mai cin rai tana niman mafita, haka ta kwana a zaune tana wannan kukan mai cin
rai.
Cikin rashin k'warin jiki ta mik'e ta nufi _toilet_ ta d'auro alwala tun kafin ta fito taji wani
masallaci suna k'ok'arin tada ik'ama.
Da sauri ta shimfid'a abin sallah tare da saka hijjabi ta bisu, domin tana jin karatun su rad'au
tamkar a cikin d'akin ake yi.
A in da tayi sallar anan bacci mai nauyi ya d'auke ta, sama-sama cikin bacci taji ana bugun
k'afar ta da k'arfi tare da fad'in "ke! Ke! Baccin uban me kike har zuwa wannan lokacin?"

A hankali ta bud'e idon ta tana ganin Aliyu ne da sauri ta mik'e tamkar wacce aka jonawa
wutar lantar ki, ta d'aure fuska tamau, ta kalle shi sama da k'asa taja tsaki, tare da fad'in "uban
wa yace maka ana tashi na daga bacci?"
"kokuwa salon ka jaza min ciwon kai ne? Har kake taba min k'afa! To wallahi Allah ya isa na
daka taba min k'afa da kazamin hannun ka!"
Murmushin mugunta Aliyu yayi yace "karki damu y'an mata har abinda yafi k'afa nakusa fara
tabawa kici gaba dayi min iskanci daidai nake dake fitsararra mara kunya, da alama ma kafira
ce ke hala baki sallah? Dan banga alamar kinyi sallah ba yau d'innan."

"kaji gantalalle! Ni da kai waye za a kalla acewa kafiri?"
"Wallahi ka rubuta min takarda ta in tafi gidan mu kaji nagaya maka!"

Dariyar mugunta Aliyu yayi harda tafa hannu, ya zo ya fad'a bisa gadon ya na k'yalk'yala dariya,
daga ni kasan na mugun ta ne zalla.
Can ya d'an tsagai ta da dariyar yayi ruf da ciki a kan gadon, ya d'ago kai yana kallon ta yace.
"yaro yaro ne, bai san wuta ba sai ya taka.
Bari na fad'a maki, idan kina tunanin zan rabu da ke to gara ki cire wannan a zuciyar ki, ki
watsar, dan yanda kika shigo gidan nan to babu mai fidda ki sai sai dai mutuwa."
"Shawarar da zan baki shine ki shirya zama da matsiyaci kamar yanda kike fad'a."
"Wallahi Aliyu baka isa ba kayi kad'an, wallahi na tsane ka kamar yadda na tsani mutuwa ta.
Kuma yazama dole ka sake ni tunda ba uban ka bane ya".... Bata k'arasa fad'a ba ya sauke
mata wani gigitaccan mari ji kake tasss!!!

Da sauri ta dafe kuncin ta, tsabar taurin kai irin na Amatullah sai cewa tayi "uwar kace ka
mara d'an iskan....." wani marin yak'ara saukewa d'ayan kuncin nata a haukace taci kwalar sa
tana sake d'ura masa ashar.
Hankad'a ta yayi fan yaga idan yabiye mata sai yayi mata illa.
Cikin kakkausar murya yace _(This is my last warning to you)_ wallahi wallahi duk rannan
dakika kuma zagi na sai na baki mamaki wallahi.....
Katse shi tayi da fad'in sai dai mubawa juna mamaki wallahi Aliyu! Kayi kadan kabani
mamaki mu zuba nida kai cikin gidan nan tabbas za a k'washi gawar mutum d'aya koni ko kai
shege ka fasa...............






*DEDICATED TO*
*KUBRA USMAN BALA
[4/11, 6:47 AM] +234 703 962 5239: *KAINE SANADI* 7⃣0⃣to7⃣5⃣

*WRITTEN BY*



*FIDDAUSI SODANGI*





*STORY BY*
*KHALISAT HAYDAR*







*®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA)*





_Masha Allah My Mentor! Hakika ina alfahari dake a koda yaushi, dole ne Sodangi takawo
jinjinar ban girma a gare ki_ *KHADIJA SIDI* _hakika kin cancanci yabo, nagode da sadaukar
war dakika min na littafin ki kacokan mai suna_ *BINTU DIYAR BAYI* _nagode sosai Allah
yabar so da kauna Sodangi tana matukar kaunar ki fiye da tunanin ki._





Bai k'aracewa da ita komi ba cikin tsananin bacin rai yafice a d'akin, yana fita ta zube a
k'asa ta soma raira kuka, wani irin tsanar Aliyu take ji har a zyciyar ta, tabbas yau ta k'ara
tabbatar wa cewa tashigo cikin sabon rayuwa.
Sai da ta gama raira kukan ta mai isar ta sannan ta d'auko wayar ta tashiga kiran layin uwar
sai dai abin takaici a kashe layin yake, nan ranta yak'ara baci, a take ta tuno da Anty Ameena
har ta soma kiran layin sai tayi sauri ta kashe dan zuciyar ta bai bata ba ta tuno da nasihar ta a

gare ta inda take fad'in.

Amatullah na, ki kasance mai hakuri da juriya, sannan mai boye wa mijin ta sirrin sa.
Ba komi ne zai faru kice zaki buga ki sanar da wani halin da kike ciki ba, ki daure ki cije, shi
zaman aure ya gaji hakan, dama akan hakuri ake yin sa, daga kai har mijin naka, shi yayi hakuri
dake kema kiyi hakuri da shi.Allah ya tsinewa mace mai tona asirin mijin ta, musamman wajan
sirrin ma'aurata. Don haka Amatullah na kizama jaruma mai juriya akan duk wani k'aluballe dazaki fuskan ta a
gidan zaman auran ki, dole ne zaki ringa ganin abubuwan takaici wayan da zasu tsallake
tunanin ki, amman idan kikayi hakuri wata rana sai labari.
Duk wata mace da kika ganta gidan mijinta, to sai ta had'a da hakuri, don haka koni
Amatullah ban yarda kigaya min duk wani abu dake gudana a gidan auran ki ba, matukar kina
so muyi shiri nida ke.
Kuka ta sake fashewa da shi harda ihu kamar wata tababbiya.
Dole kiyi masa biyayya ga dukkan abinda ya umurceki kiyi matukar bai sabawa shari'a ba,
domin a k'ark'ashin sa kike, don sai ya d'aga k'afar sa sannan zaki sami aljannar ki, tunda auran
nan dai yariga ya kullu dole kiyi hakuri da juriya babu yardda zakiyi, don kisamu ki dace miji ba
abin wasa bane. A Karo na biyu tasake tunawa da nasihar mahaifiyar ta.
Ajiyar zuciya mai k'arfi ta sauke ta tashi ta shiga _toilet_ ta shek'a wanka tafito tayi ado mai
d'aukar hankali sannan ta bud'e k'ofa ta fice palo.
Wani d'an k'aramin _fridge_ ta ci karo da shi kai tsaye ta nufe shi ta bud'e, ido biyu tayi da
mutumin ta watau _fresh milk_ nan ta d'auko shi ta d'auki kofi ta tsiyaya ta soma sha tana
lumshe ido, alamar yana mata dad'i wani irin sanyi ne ke ratsa mata mak'oshi.
K'amshin turaran Aliyu ne yacika mata hanci da sauri ta dube shi daga shi sai guntun wando
sai y'ar shimi ta maza da sauri ta d'auke idon ta bayan ta watsa masa mugun harara.
Da sauri ya k'arasa inda take ya amshe kofin yana fad'in "uban wa yabaki izinin sha min
madara?"
"uhmm?"
"to ki sani bashi kika sha saikin biya ni!"
Tsaki taja masa tabar wajan ta nimi kujera ta hard'e tana karkad'a k'afa.
Dagani kasan kiris take jira.
Wayar Aliyu ne yashiga ruri dama a hannunsa yake da sauri ya d'auka ganin Fulani ce ke kiran.
_"Hello"._
_"ok_ babu laifi su shigo kawai "
Ya dubi Amatullah yace "Allah ya soki yau fulani ta hutassheki ta aiko da abinci da yanzu sai
kin shiga _kitchen_ kinyi mana _breakfast_ dan Khadija ba ta da lafiya bazata iya girki ba."
Wani mugun kallo ta watsa mashi bata ce komi ba.
Suna cikin haka Sarkin gida ya shigo tare da wasu barori su kusan shida kowanne d'auke da
hadaddiyar kula mai kyau,
Bisa _dinning table_ suka shirya su reras, gwanin ban sha'awa, nan suka zube suka soma
kawo gaisuwar su gun Aliyu da Amatullah.

Bayan sun amsa sarkin gida yayi waje yayi masu sallama, yayinda barorin suka nimi waje suka
kame tamkar wasu gumaka.
Aliyu ne ya nufi _dinning table_ d'in ya zauna, nan Amatullah ma ta taso dan yunwa take ji,
da sauri biyu daga cikin barorin suka iso gun jikin su na rawa suka shiga bud'e kulolin, nan wani
hadaddan kamshi bai bala'in dad'i ya daki hancin Amatullah bata san lokacin da ta had'e miyau
ba. Nan suka dubi Aliyu suna fad'in "Allah ya k'arawa Yarima lafiya meza a zuba maka?"
"duk abin da zata ci nima shi zanci!"
Abinci ne na alfarma babu wanda babu aciki, tun daga kan na gargajiya harna turawa da
larabawa duka gashi nan birjik.
Duk'awa d'ayan tayi tana fad'in "Allah ya taimaki Amaryar Yarima d'an sarki Allah ya k'ara
maki lafiya Amarya ke nake sauraro ki bani umarnin me kike so kici?".
Yatsina fuska Amatullah tayi ta gyara zama cikin isa da mulki ta shiga zaiyyano mata abinda
zata ci cikin tak'ama da izza.
Cikin jin dad'i tace "Allah ya taimake ki uwar d'aki na anyi an gama da wannan dama dana
samu."
Nan ta shiga zuzzuba masu ta turawa kowa a gaban sa, sannan ta duk'a tace.
"A kammala lafiya"
Nan suka bar palon gaba d'ayan su,
Nan Aliyu yayi mata wani irin kallo yace "ina fata kinsan cewa ni angone domin kuwa jiya nayi
kwanan farinciki, don haka yazama dole ki taso ki ciyar dani in koshi kafin kicika naki cikin ina
fatan kin fahimceni?"
Wani mugun kallo tayi masa tare da murgud'a masa baki tace "ni ba a koya min haka a gidan
muba dan haka kada Allah yasa kaci yunwar cikin ka ya kashe ka!".
Taja _plate_ d'in ta gaban ta tashiga cin abincin ta cikin kwanciyar hankali.
Da k'arfi ya damki hannun nata harsai datayi k'ara yace "ai nan ba gidan ku bane, gida nane
nike iko dake dan haka dole kimin abunda nakeso".
"baka isa ba kayi kad'an!"
"ta fad'i kanta tsaye."
Hannun ta yasaki dan hango khadija dayayi tana tahowa, a hankali take tafiya tana dafe bango
kamar wata mai koyan tafiya sai wani cije baki take yi kamar zatayi kuka.
Da sauri Aliyu ya mik'e ya tare ta ya rik'o ta a jikin sa suka k'araso yaja kujera ya d'ora ta
kamar wata y'ar yarinya yanai mata sannu.
Wani dogon tsaki Amatullah taja tamkar harshan ta zai katse ta dalla masu harara sannan ta
d'auke kai taci gaba da cin abincin ta.
Matsowa yayi da tasa kujerar ya had'e su waje d'aya yaringa dibo abincin sa yana bata a baki
shima yana ci, can ya dube ta ya wani rungume ta a jikin sa yana fad'in
"nagode nagode khadija."
"hak'ik'a jiya kin shayar dani farinciki, kin d'ad'ana min daddadan zuma a baki, bani da abinda
zan saka maki dashi illa inringa yi maki addu'a Allah ya shayar dake ruwan alkausara, ina yi
maki fatan alkairi a rayuwar ki khadija Allah yasa ki gama da duniya lafiya. "
"Ameen mijina, ina alfahari dakai hakika kai gwarzon namiji ne da babu irin ka a duniya."
"Allah yabar mu tare yaraba mu da sharrin makiyi da mahassada."

"Ameen ya rabbi matata."
"wajan ya daina zafi kuwa?"
Yafadi yana kallon cikin idon ta yana kuma satar kallon Amatullah wacce tayi kicin kicin da fuska
tamkar zata fashe.
Kunya ne yakama Khadija ta mik'e tana wannan tafiyar tata mai kama da tatata.
Da sauri ya sunkuce ta kamar wata y'ar bebin roba yana fadin muje inmaki tausa ai dole akwai
gajiya dan kin nuna jarumta sosai waiii mace haka kamar zuma waiii wannan ai shine cakwala
dadin.
Ya shige d'akin ta da ita ya bugo k'ofar da k'arfi da k'afar sa.

Tsaki Amatullah tayi ta tashi tabar abincin nan ta shige d'akin ta zuciyar ta tamkar zata fito waje.
Wajan awa d'aya da rabi taji ana ta buga mata k'ofa a sakwanne ta bud'e, ido hudu sukai da
Aliyu sanye cikin manyan kaya farare tas da su, babbar riga da yar ciki sai wando, kansa sanye
da hula sai kamshi yake da ka ganshi kaga sabon ango,
Duk da bai burge taba amman tasan yayi kyau matuka.
"zanje fada mu gaisa da mai martaba nida Yaron Malan,"
"Ko kina da saka'o?"
Harare ta galla masa ta shige ta barshi nan rike da k'ofa a hannu.
"bazan samu koda d'an _kiss_ bane wanda zaisa intafi cikin nishadi ba?"
Ya fad'i cike da zolaya.
Wani irin shan kunu tayi ganin rainin wayan nasa Yayi yawa.
_come on_ ke nake jira.
A fusace tace "dallah Malan kabar min k'ofa insha iska angaya maka ni y'ar iska ce irin ka
banza d'an tasha!"
_ok_ to bari in shigo in nuna maki halin iskancin nawa!
Ko kad'an batai tsammani ba sai ganin shi tayi ya shigo cikin d'akin da k'arfi ya fisgo ta jikin sa
ya had'e bakin su gu d'aya yashiga shan shi irin na mugun tar nan hannunsa na kokarin zuge
zip d'in rigar ta........






*DEDICATED TO*
*KUBRA USMAN BALA*
[4/11, 3:52 PM] +234 703 962 5239: *KAINE SANADI* 7⃣5⃣to8⃣0⃣

*WRITTEN BY*





*FIDDAUSI SODANGI*







*STORY BY*
*KHALISAT HAYDAR*






*®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA)*







_Wannan shafin naki ne_ *Eeesha Bagwai* _nagode da soyayyar dakike nunawa wannan littafi
nawa, dan haka na sadauk'ar da wannan shafi a gare ki, ina godiya matuk'a Allah ya bar
k'auna._




Da k'arfi taci nasarar ture sa ta tattaro miyan bakin ta ta watsa mashi a fuska, sannan
tasoma sababi, "wai kai Aliyu wani irin d'an iskan mai rai ne?" "Meyasa baka da buri a kullum
sai nason ka taba min jiki?"
" To wallahi bari kaji ingaya maka wannan tsadaddan jikin nawa yafi k'arfin ajin ka wallahi

wallahi! Dan haka koda wasa kada ka k'ara gigin taba min jiki da kazaman hannuwan ka, balle
har ka ringa k'ok'arin had'a kazamin bakin ka mai wari da nawa, ina k'ara gaya maka ka kiyaye
ni kayi harkar gaban ka kadai na shiga sabgata kaji nagaya maka."
K'wafa yayi ya fice yabar mata d'akin dan karta bata masa lokaci abokan sa najiran sa a waje.
Yana fita taja wani wawan tsaki tana fad'in "k'aramin d'an iska!".

**********


Fada ta cika makil, hakimai da dogarai sai fad'uwa sukeyi suna kawo gaisuwar su gun mai
martaba, wannan yazo ya fad'i ya kawo tashi gaisuwar sannan ya mik'e ya tafi sai wani ma
yazo, shikuwa zagi na fad'in "gyara kintsi da kyau".
Bayan ya fad'i sunan ka da kujerar ka.

A na cikin haka sai ga Yarima da tarin abokan sa duk sun sha manya kaya, Yaron Malan ne a
gaba sai Yarima a gefen sa, nan fadawa suka shiga yimasa kirari, nan ya fad'i a gaban mai
martaba ya kwashi gaisuwar sa.
Haka sauran abokan sa ma suka kawo tasu gaisuwar.

Bayan kowa yagama kawo tasa gaisuwar ne mai martaba yayi ma yarima nasiha mai ratsa jiki,
daga k'arshe Yarima da abokan sa suka shiga cikin gida dan gaida iyayan su mata.
Kai tsaye sashin uwargidan mai martaba yayi nan ya tadda wajan cike da jama'a kasancewar
yan biki basu gama watsewa ba, ga kuyangi nan birjik ta ko ina suna ganin sa suka hau yimasa
kirari da kuran ta shi, nan kansa ya kara girma, nan ya gaida ta suma abokan nasa suka
gaidata. Nasiha sosai itama tai masa nan ya bari shiyyar jikin sa a sanyaye.

Bangaran Fulani suka nufa watau mahaifiyar sa, nan suka zube suka kwashi gaisuwa daga
k'arshe kowa ya watse a ka bar d'an da mahaifiyar sa domin su gana.
"Fulani na gode Allah ya biya ki yabiya maki bukatun ki na duniya dana lahira yak'arawa Mai
martaba nisan k'wana. "
Murmushi tayi irin na manyan mata da mulki yagama ratsa su, cikin k'asaita tace "Yarima kai
farinciki ne a gare mu dole kullum mu ringa k'yautata maka yanda kake faran ta mana a kullum
dole ne muma murin ga kokarin saka ka farinciki.
Yanda zaka dinga samun nasara a kullum."

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login