Showing 12001 words to 15000 words out of 35354 words

Chapter 5 - KAINE SANADI BOOK COMPLETE (1 to End) By Sodangi & Khalisat .pdf

16 Mar 2025

3763

aikin ta nata kawo gaisuwa amman sam bata kula ko mutum
d'aya ba balle ta amsa, haka kawai ta rasa make mata dad'i yau d'innan, kwata kwata bata da
_rest of mind_ zaune tayi bisa lallausar koriyar ciyawar dake shimfid'e a wajan, Teena ce ta biyo
ta da kayan marmari shak'e a faranti, a gabanta ta aje ta juya.
Kallo d'aya taiwa farantin ta d'auke kai.
Wayar ta ne yashiga kuka, tafi minti biyu tana kallon shi yana kuka yana yankewa ana k'ara kira,
d'an guntun tsaki tayi ta d'auka ta kara a kunnin ta,
_"Hello"_

"uhm _sweetheart_ yakike?"
Dif tayi kamar bata jiba dan mamaki ne yacika ta, a hankali ta furta _wrong number_ ta kashe.
Sake kira akayi da sauri ta d'aga da niyyar tayi masifa saidai tunkan ta furta komi taji ance
_"Amatullah Ahmad Fage_" har yanzu baki gama tunani bane?"
"yaufa sati d'aya kenan ina sauraran ki".
Gaban tane ya yanke ya fad'i rass!! rass!! cikin rawar baki tace........





*DEDICATED TO*
*KUBRA USMAN BALA*
[4/11, 6:47 AM] +234 703 962 5239: *KAINE SANADI* 3⃣5⃣to4⃣0⃣




*WRITTEN BY*


*FIDDAUSI SODANGI*




*STORY BY*
*KHALISAT HAYDAR*




*®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA)*





_Wannan page d'in naku ne k'awayan ar'ziki, hakika ina alfahari daku domin kuwa kunzame min
jinin jiki na, ina alfahari daku akoda yaushe._

_KHALISAT HAYDAR_
_MAMAN SHAKUR_

_UMMI AYSHA_
_KAUSAR LUV_
_SADIYA LAWAL BALA_
_PHARTYMA ZAHRA_





"Meyasa kake da naci ne?"
"nagaya maka Amatullahi ba matar k'ananan yara bace! Me na sama yaci bare yabawa na
k'asa uhm?"
"ko kallon tsoro ka min ne?"
"babu soyayya a tsarin rayuwar Amatullah, auren ma zanyi shi ne dan yazama dole ayi, inaso
inyi koyi da fiyayyan alitta, ina sha'awar yara k'ana na, to nasani hakan bazai faruba sai ta
hanyar aure, so kaga aure yazama dole indai har inason cikar buri na.
"in yambaye ka mana?"
"uhm ina jinki".

"wanene kai?"
"ina nufin waye uban ka? Meye matsayin sa? Sannan nawa ka tara a duniya? Make gare ka?".
"ina buk'atar k'yakkayawar amsa dan inji ko zan iya maneji da kai albarkacin son da kake
kirarin kana min."
"karki damu zakiji komi akai na amman zaifi k'yau mu had'u gani gaki, idona cikin naki abin zaifi
bada ma'ana mai k'yau kingane ko"
"uhm! Badamuwa mu had'u a......... Da misalin k'arfe biyar na yamma, saboda inada _lectures_
2 to 4 kagane ko?"
_"yes ma"_


Washe gari Amatullah cikin shigar ta ta kamala ta nufi makaranta, kanta a k'asa take takun ta
tamkar mai tausayin k'asa, wasu littafai ne a hannun ta sai jakar ta dake makale a kafad'ar ta,
babu zato babu tsammani sukai karo dashi shima wasu littafan ne a hannunsa, gaba d'aya
littafan nata dana shi suka watse a k'asa, a lokaci d'aya suka D'uk'a kowa ya d'ibi nasa, fuskar
sa ta leka tana kallon sa kasancewar hular dayasa ta rufe masa fuska.
Wani guntun tsaki taja ta mik'e da sauri tana fad'in "bagidaje! Sai kace bai taba ganin mutum
ba, dan tsabagen k'auyan ci yana tafe yana kalle-kalle, tir da k'auyanci da gida danci! Ta watsa
masa miyau tayi gaba tana toshe hanci.
Kallo yabi ta da shi yana raya abu a zuciyar sa, wani guntun murmushi yasaki a hankali ya
furta, _Amatullahi Ahmad Fage_ kenan! Kinai min kallon biri inai maki na ayaba, a sannu zaki
gane hakan, lokaci nazuwa da zaki san waye _Muhammad
Hussein D'anbatta_ .
daga k'arshe yabi bayan ta ya shiga ajin shima dan d'aukar darasi.

***********


Masarautar Kano babban masarauta ce mai d'inbin tarihi, mai martaba sarki _Abdul
Rasheed Ganduje_ shine ya kasance mahaifi a gun _Aliyu Rasheed Ganduje_y'ay'an mai
martaba guda goma sha biyu ne, inda suka kasance mata guda goma sha d'aya, zuwan
amaryar sa Fulani d'iyar mai martaba sarkin katsina watau _Halimatus Sadiya_ shine ta haifa
masa Yarima Aliyu, wanda mai martaba ya d'auki son duniya ya d'aurawa wannan d'a nasa
kasancewar sa namiji guda d'aya tilo.
Yarima Aliyu ya tashi cikin soyayyar y'an uwa kowa na sonsa, Aliyu yaro ne mai farinjini da
k'warjini a ckin jama'a, ga jarumta da juriya, Aliyu yakasance miskilin mutum na k'arshe, sam
baya murmushi bare azo ga dariya, kafin Kaga murmushin Aliyu sai ka taki babban sa'a.
Aliyu mutum ne mai kirkin gaske da dad'in zama idan ka fahimce shi, yana da tsabta mai ban
mamaki, gashi k'yakkyawa na nunawa a sa'a, gaba d'aya karatun sa tundaga kan _secondary
school_ har gaba da ita har Master's d'in sa duka a _America_ yayi shi inda yagama yanimi
_lecturing_ a nan _Catholic University of America_ Aliyu baya da burin daya wuce yazama
_lecturer_ shiyasa daya samu ya rike aikin sa da mahimmanci sam baya wasa dashi, sam mai
martaba bai hana saba dan kuwa yasan burin Aliyu kenan tun yana yaro.
Rana d'aya Amatullah tazo ta rushe komi, wannan dalilin yasa shi d'aukar tsanar duniya ya
d'ora shi akanta, yasha alwashin sai ya wargaza farincikin ta yanda ta wargaza nasa.

******

_Muhammad Hussein D'anbatta_ ne zaune yana jiran isowar Amatullah, izuwa yanzu yagama
k'agara da zuwan nata, shikam sam baya son mutum mai saba alk'awari dan shi yana aiki da
lokaci ne, wannan dalili ne yasa ran sa ya d'an sosu, agogon hannun sa yake kallo a zuciyar sa
kuwa fad'i yake "d'an _Nigeria_ kenan komi sai yayi _African time_ wayar sace tashiga k'ara
inda ya d'auka ya kara a kunnin sa yana jira yaji mezata ce masa,
" bangan kaba "
"ina nan inda kika ce in zauna ki k'araso zaki ganni ya kashe wayar sa.
A hankali ta k'araso cikin takun ta ta tak'ama da isa, bayan sa kawai take iya hango wa nan
danan zuciyar ta ta tsinke, kujera taja ta zauna suna fuskan tar juna, lokaci d'aya duk wata gaba
ta jikin ta ta tsaya cak da aiki, wani irin bak'in ciki da takaici ya lullube ta, tamkar zata shak'e shi
ta mik'e tana nunasa da yatsa "kaiiii ni tsarar ka ce da zakayi wasa da hankali na?" "Amman lallai kacika mara mutunci,"
"to waima in tambaye ka?"
"shin aiko ka akai waje na ko kuwa kai d'in ne ka kawo kan ka da kanka guna dan maula!?"
"to bari kaji idan aiko ka akayi ka koma ka gayawa uban gidan ka ni _Amatullah Ahmad Fage_
nafi k'arfin sa nafi k'arfin uban daya haife shi."
"Idan kuma kai d'in ne ka kawo kanka dan tsabagen rashin kunya da rashin d'a a to ka bud'e
kunnuwan ka kaji ni da k'yau."
Tayi wani irin juyi a gaban sa tace "kalle ni da k'yau ka k'are min kallo, ko ba a gaya maka ba

kasan cewa nafi k'arfin gaba d'aya zuri'ar ku, to dan me zaka rainawa kanka wayau ka ha'inci
kanka da kanka?"
"Zanmaka gargad'i da babban murya, ka kiyaye ni ka rufa wa kan ka asiri kasamu ka gama
karatun ka lafiya idan baso kake kayi asarar _scholarship_ d'in ka bane, wallahi idan ba ka
kiyaye ni ka fita harka taba sainayi sanadiyyar barinka makarantar nan kaji na rantse maka,
kuma _video_ dakake min barazana dashi nice d'in ai ka gani ganin idon ka, na isa ne shiyasa
na aikata hakan, kai idan ka isa kayi hakan mana, idan ka ga dama ka turawa duka y'an duniya
kace ga _Amatullahi Ahmad Fage_ na fasikanci! .
Kanka kayiwa bani ba dan kunyar mara kunya asara ce, idan kuma iyayena kake tak'amar su
gani to su gani d'in sai me zai faru?"
"Babu abinda zai faru illa iyaka susani cewa d'iyar taso ta k'osa aure take so!"
"dan haka kayi gudu kaje ka fad'a masu kokuma inbaka _number Mr President_ d'in ne?" tayi
tambayar cike da rainin wayau tana kallon cikin idon sa.

Tsananin mamaki yasa _Muhammad Hussein D'anbatta_ kasa cewa komi illa binta da ido da
yakeyi, ta watsa masa harara ta wuce abin ta ta barshi nan zaune yana mamaki.
Wayar sa ya ciro yakira Aliyu ya shaida masa yanda sukayi, murmushin takaici Aliyu yayi yace
"ka k'yale ta kawai ka fita hanyar ta zansan yarda zamu bullo mata, intaki hagu ai bata ki dama
ba!.

******

Su Amatullah sun k'are jarabawar su lafiya inda da sun dawo hutu zasu shiga shekarar
k'arshe a karatun su, sai dai abin takaici shine gaba d'aya jarabawar data wuce wacce sukayi
Amatullah bata aikata abin kirki ba duk ta fad'i yawancin _courses_ d'in dan haka gamawa
_next year_ bada ita ba, aikuwa shugaban makarantar da kansa yakira mahaifin ta ya gaya
masa abin da ake ciki, godiya kawai _Mr President_ yai masa tare da tambayar sa koyasan
abin da ke d'aukewa d'iyar tasa hankali, kunsan bature shi bai wani iya saya magana ba kai
tsaye ya shaida masa cewa kila kan d'iyar tasa ba na d'aukar karatu bane shiyasa kullum take
fad'uwa jarabawa, amman shawarar dazai basa me zai hana ta dawo gida tayi karatun a gaban
sa kila za a dace, godiya _Mr President_ yayi masa sosai sukayi sallama cike da mutunta juna.
Bayan k'wana biyu da gama jarabawar su Amatullah ta ta tattaro ta dawo gida _Nigeria_
..........


_Tofa yanzu ne zamu shiga cikin labarin tsundun!_.





*DEDICATED TO*
*KUBRA USMAN BALA*

[4/11, 6:47 AM] +234 703 962 5239: *KAINE SANADI* 4⃣0⃣to4⃣5⃣


*WRITTEN BY*


*FIDDAUSI SODANGI*




*STORY BY*
*KHALISAT HAYDAR*




*®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA)*





"Yaron Malan da gaske nake aure nake so a nima min kacire maganar wasa dan haka
na wakiltaka kaje ka sanar da Fulani sak'o na."
Mamaki shimfid'e a fuskar Yaron Malan yake kallon Aliyu, wai yau Aliyu da bakin sa yake furta
yana son aure, Aliyu da ya tsani ai masa maganar aure harma iyayan nasa sun gaji sun zaba
masa mata, idan bai manta ba sati uku kenan da mai martaba yai tattaki har gidan gomna
shida mutanan sa suka nimowa Yarima Aliyu auran d'iyar gomnan wanda har anbasa ankuma
saka rana, dama mai martaba yace idan lokaci yayi za a d'aura auran akai masa matar sa can
k'asar idan bai zoba,
sai gashi yanzu da kansa yake masa wannan zancan, wannan shine *RUGUNTSUMI* _(NA
HAUWA JABO DA FIDDAUSI SODANGI)_

"Malan idan bazaka iya zuwa ba in tura Jakadiya! Naga ka tsare ni da ido kamar baka taba
gani na ba."
"Yarima bawai bazani bani amman gaskiya akwai matsala!"
"matsala? Allah ya raba mu da ita Yaron Malan".
Yarima da gaske nake fa, nan dai cikin k'wantar da murya ya shiga zaiya no masa abinda ya
faru.
Murmushi Aliyu yayi yace "Alhamdulillah Allah abin godiya! Gaskiya nayi farinciki da jin
wannan zance naka abokina, ya k'arayin murmushi tare da fad'in fad'uwa tazo dai dai da
zama!".

Da mamaki Yaron Malan ke duban sa da k'yar ya iya fad'in "Yarima dama itace kake so a nima
maka auran tane? Kafa san y'an matan biyu ne, Ya da k'anwa, ance anriga anyiwa yayan miji
shine aka baka k'anwar dan bama ta gama karatu ba shekarar k'arshe take".
Kafad'ar Yaron Malan Aliyu ya dafa yace "karka damu mutumina nasan abin da nake yi, kaje
ka gayawa Fulani sak'o na kawai,"
ya wuce abin sa yabar Yaron Malan sake da baki tare da binsa da kallon mamaki yana
al'ajabin hali irin na Yarima.

*****

"Shi Yariman ne ya turo ka da wannan maganar?"
Kan shi a k'asa yace "nayi masa bayanin abinda ke faruwa Fulani amman Yarima ya dage sai
nazo na gaya maku amman kuma abin mamaki shine Yarima yayi murna da zancan auran da
aka nima masa, to a nawa tunanin dai mata biyu yake so yayi da dukkan alama."

Murmushi Fulani tayi tace "hoo Yarima rigima, inban da rigima irin ta sa ina shi ina mata biyu a
yanzu?"
"Fulani kusawa abin albarka kawai, ina ganin babu abinda zai gagari Yarima da yardar Allah!".
"to shikenan Yaron Malan zan yiwa mahaifin sa magana muji ta bakin nasa insha Allahu".
"to Fulani Allah yasa a dace Yarima na godiya."

********


Cike da farinciki Mai martaba ke duban Fulani, "a ina ne za a nima masa auran ne?"
"d'iyar waye?"

"A'a nima bamuyi maganar da shi ba, Yaron Malan ne yazo min da zansan."
Jakadiyya mai martaba yasa akai masa kiran ta ya dube ta yace "Jakadiyya kunyi wata
magana da Yarima ne akan batun niman auran sa?"
"eh ya shaida min cewa sun k'ulla alakar soyayya shida y'ar gidan shugaban k'asa, yace
yana so a nima masa auran ta insan samu ne ma a yi bikin lokaci d'aya da wanda kuka nima
masa."

Murmushi mai martaba yayi yace "Yarima kenan, shi nan har zai iya rike mata biyu a shiririta irin
nasa?"
"ban tari numfashin kaba ranka ya dade Allah yaja da zamanin ka, Allah ya huci zuciyar mai
martaba sarki, ina ganin yakama ta animawa Yarima auran yarinyar nan, saboda yayi mana
biyayya ya amshi zabin mu batare da nuna bacin rai ba, mun dade muna matsawa Yarima akan
ya fiddo matar aure yak'i, to sai gashi yanzu da kansa yace ga wacce yake so, ina ganin bai
dace mu yi biris da zancan nasa ba, Yarima yaro ne mai ladabi da biyayya, bai taba ketarewa
umurnin muba, dan haka ina rok'on mai girma sarki dayayi duba ga maganar Yarima a amsa
mashi but'atar sa Yarima yana bawa sarki hakuri idan har maganar sa ta bata zuciyar mai

martaba."

"shikenan Jakadiya Allah yayi mana jagora ya shige mana gaba."
Gaba d'aya suka amsa da Ameen.

********



"kimin shuru Asma'u so nawa zangaya maku cewa bana son yawon da yarinyar nan take yi!
Yanzu k'arfe nawa?"
Tunda yarinyar nan ta dawo kullum ba ta da aikin yi daya wuce yawo! Sannan na hana ta fita
ita d'aya amman bataji, yanzu lokacin siyasa ne komi na iya faruwa Asma'u meyasa ba kwa
nima min kwanciyar hankali ne kullum keda d'iyar ki!?"
Na tabbar yawon gantalin ta take tafiya acan ba karatun take ba shiyasa kullum bata da aiki
saina fad'i jarabawa, amman komi yazo k'arshe insha Allahu, ku shirya gobe mai martaba
sarkin kano zai zo shida mutanan sa domun niman auran ta kuma nariga na yanke hukuncin
basu, dan haka zan amshi sadakin su a goben asa rana in kaudata kozan sami k'wanciyar
hankali, nagaji da tijarar yarinyar nan!".

Jiki a sanyaye _first Lady_ Hajiya Asma'u ke kallon sa kafin ta bud'e baki da niyyar yin
magana ya dakatar da ita ta hanyar d'aga mata hannunsa, "nariga nagama magana Asma'u
bana son jin komi!"
Suna a haka gimbiyar ta shigo da sallama d'auke a bakin ta, bata sami ikon k'arasawa ba
sakamakon had'a ido dasukayi da mahaifin nata, wani irin tsawa ya daka mata yana fad'in daga
ina kike?
A tsorace ta kalli mahaifiyar ta jikin ta na rawa, kauda kai uwar tayi taga k'arshe tama haye
sama ta barsu nan,
"badake nake ba daga ina kike nace?"
Bakin ta na rawa tace "Abbba _ice cream_ naje shaaa... Wani mugun tsawa ya daga mata tare
da mugun kallo, baya tayi da sauri tana kallon sa kamar ta zura da gudu take ji.

"Shan _ice cream_ da daddaran nan?"
" Amatullah bakida hankali ne?"
"k'arya kikeyi ba abinda yakai ki fita kenan ba! Kigaya min inda kikaje kafin in tattakaki!."

"Abba bikin k'awata naje kuma na gayawa _mum_ ........"





*DEDICATED TO*

*KUBRA USMAN BALA*
[4/11, 6:47 AM] +234 703 962 5239: *KAINE SANADI* 4⃣5⃣to5⃣0⃣





*WRITTEN BY*



*FIDDAUSI SODANGI*




*STORY BY*
*KHALISAT HAYDAR*




*®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA)*




_Wannan page d'in naki ne my sweet sister (Maman Rabi'a) Sodangi tana son ki tana k'aunar ki
tana kuma alfahari dake a koda yaushe._




Wani irin mugun kallo yake watsa mata kafin yafara fad'a cikin kakkausar murya,
"Amatullah meyasa baki gudun zuciya ta?"
"Sau nawa zan gaya maki bana k'aunar yawon dakike yi?"
"meyasa ni ban isa in gaya magana kiji ba iye!!?"
"watau kin d'auke ni mutumin banza ko, ga k'annanki nan suna tasowa duk abinda suka ga
kinayi suma shi zasuyi dan haka ki maida hankali kici gaba kada ki fasa kinji Allah yaba da sa'a.
Ya wuce yabar ta nan tsaye jiki a sanyaye.

Duk sai taji babu dad'i zuciyar ta kamar zai fad'o k'asa dan harbawa.
Cikin sanyin jiki ta haye sama kai tsaye d'akin mahaifiyar ta nufa, tasan tayi laifi dan haka ta

soma rabe-rabe, tsawa ta daka mata tace "haka mukai dake ko?"
"yanzu k'arfe nawa?"
"dak'yar ta iya bud'e baki tace _"am sorry mum_ wallahi bansan dare yayi sosai haka ba.
_"shut up!! Stupid girl!! Get out of my room_ kafin in

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login