Showing 15001 words to 18000 words out of 35354 words

Chapter 6 - KAINE SANADI BOOK COMPLETE (1 to End) By Sodangi & Khalisat .pdf

16 Mar 2025

3764

taso in k'wad'e ki kinjawo min fad'an shi
hankalin ki ya kwanta."
"ki fita nace!".

Jikin ta a sanyaye ta fito daga d'akin ta nufi nata.
Tana saka k'afa a cikin d'akin wayar hannun ta yasoma kuka, ganin bakuwar _number_ yasa
taki d'auka harya katse.
katsewar wayar ne yasa ta ajiye shi gaban Madubinta hawaye na ci gaba da bin kuncinta,
_bathroom_ ta nufa don ana ta kiraye kirayen sallar isha'i ne gashi ko Magrib bata yi ba.

Ta dad'e zaune kan darduma bayan ta idar da sallar, daga bisanni ta mik'e da k'yar ta fita
zuwa _kitchen_ don yunwa take ji, tukunyar dake kan gas ta bude taga miyar _Vegetable_ din
da _first Lady_ tayiwa Abban ta na dare, dan shi baya cin girkin kowa in bana matar saba,
shiyasa duk tafiye tafiyan dazai yi da matar sa yake tafiya.
yatsine fuska ta yi ta rufe tukunyar a hankali kamar tana tsoron kar a gane ta bude, indomie
guda daya ta dauko cikin _store_ duk da ba shi bane a ranta, kawai dai bata jin yin girki ne
kuma bata jin zata iya kiran wani d'an aiki dan yai mata girki yanzu.
ta ciro kwai biyu da zata dafa, cikin minti goma ta gama hada Indominta ta dauka ta fita zuwa
dakinta, gaban Madubinta ta ajiye indomie d'in ta shiga _bathroom_ don yin wanka,
Ta riga ta saba ba ta iya cin abinci da zafi sai ya huce, shiya sa ta shiga wankan ta don ya huce
kan ta fito.
tana fitowa daga wanka ta d'an shafa mai ta feshe jikin ta da turaruka masu k'amshin dad'i,
sannan tasa kayan baccin ta.
_TV_ ta kunna ta sa _series_ d'in da take kallo, sai kusan k'arfe sha d'aya ta kashe kayan
kallon don ta gaji, sannan ta mik'e ta nufi indominta dake gaban Madubi har lokacin, bata damu
da sandarewar da yayi ba ta d'auka zata bar wajen wayarta ya shiga _vibrate_, ta k'ura ma
_screen_ d'in wayar ido sannan ta d'aga a sanyaye, ta kara a kunne, sallama yayi mata cikin tsadaddan muryar sa, can k'asa, ta amsa sannan tace "waye ne?"
gyada kai yayi kamar tana ganin sa yace “mutum ne mai daraja"
tayi shiru kamar ruwa ya cita tana tunanin inda ta san muryar, shima shurun yayi bayan kamar
minti biyu yace _"Amatullah Ahmad Fage_"
"Ashe abinda ya faru da ke kenan?"
Tsabagen dakikanci da jahilci yasa baki ci jarabawa ko d'aya ba! Kai!! Gaskiya kinyi asara
wallahi anyi asarar kud'in tara.
Yaja wani ajiyar zuciya sannan yayi murmushi mai fidda sauti wanda saida taji shi har ranta,
yace "bama dai wannan ba ina fata dai kina cin abinci sosai danni kinsan bana son mace y'ar
sololuwa kamar a hure ta fad'i dan haka ki dage da cin abinci gaskiya, dan kinsan ni jarumi ne a
wannan fannin shiyasa bana son mace lange lange karta karye.

Murmushin mugun ta yakuma yi kafin a hankali kamar mai tsoron magana yace, _"nyc nyt rest,
u pray b4 goin to bed”_ ya katse kiran,
Sororo tayi rike da wayar a hannu ko shakka babu wannan _Aliyu Rasheed Ganduje ne_ to me
kala mansa suke nufi?
Lallai Aliyu na niman ta da rigima, yazama dole ta gyara masa zama.
kasa cin indomin tayi, ta nemi yunwar da take ji ta rasa, ta kalli agogo sha d'aya da rabi, ta bude
k'ofar d'akinta a hankali rike da plate din indomin ta nufi _kitchen_ta bude k"ofar bck yard ta
zubar cikin waste bin sannan ta rufo k'ofar ta dawo cikin _kitchen_ta wanke _plate_ din ta ajiye,
ta dauki _cup_ ta hada _tea_ ta koma d'akinta, a bakin k'ofa suka had'u da mahaifiyar tata zata
sauka k'asa harara ta watsa mata da sauri Amatullah ta d'auke kanta ta shige d'aki zuciyar ta
babu dad'i ta tsani fushin iyayan nata.

A hankali take kurban _tea_ d'in ta tana tuna kalaman Aliyu nan da nan zuciyar ta tashiga k'una,
gaskiya idan ban maida ma Aliyu martani ba ya cuce ni! Da sauri ta jawo wayar tashiga rubuta
masa _messsge_ kamar haka:
_"Kanada asara ne dan na fad'i jarabawa? Kokuwa uban kane ke biya min kud'in
makarantar? Banza d'an iska kawai uban y'an shishigi ba a damu da shiba sai kutsa kai yake
babu k'warjini!_.

Ta tura masa ta kashe wayar ta gaba d'aya ta k'wanta bayan tayi addu'ar k'wanciya.

Da safe sai k'arfe sha biyu da rabi sannan ta sauko k'asa, bayan tayi wanka ta shirya cikin
wata y'ar karamar dogowar riga wacce da kadan ta wuce guiwa ta sauka k'asa nan ta tadda
ma'aikata cike sai hidima sukeyi da alamar dai yau bak'i za ai a gidan nasu duk da basu rabo da
baki amman da dukkan alamu na yau sunsha banban da na kullum. Kad'an ta d'an tsakuri abincin ta tashi ta nufi d'akin mahaifiyar Murmushi tasaki ganin yanda
uwar tayi masaifar k'yau kamar zata wani gasan k'yau.
_"wow!! You look so cute Mum!"_
"Allah ya barmin ke _my sweet mother_"

Murmushi uwar ma ta sakar mata tare da fad'in _thank you sweetheart_ da alamar harta huce
dai, da gudu Amatullah ta k'araso ta rungume ta tana murna tare da sakar mata sunba a
kumatu.
_"daughter_ ga kaya nan ki d'auka kije kisake wanka kisaka su kiyi k'walliya tamkar za a kai
ki d'akin miji, in nace k'walliya ina nufin kiyi k'walliya wanda ni kaina zan kasa gane ki kingane
ko?"
"mum yanzu fa nayi wanka kuma ina ma zamu haka mum ko bak'i Abba zai yi ne?"
"banason surutu Amatullah kiyi abinda nace kawai".

A sanyaye ta isa jikin gadon ta sa hannu ta sunkuci d'an akwatin da kayan ke ciki ta fice a d'akin
kamar wacce k'wai ya fashewa a ciki..........

*DEDICATED TO*
*KUBRA USMAN BALA*
[4/11, 6:47 AM] +234 703 962 5239: *KAINE SANADI* 5⃣0⃣to5⃣5⃣



*WRITTEN BY*

*FIDDAUSI SODANGI*




*STORY BY*
*KHALISAT HAYDAR*




*®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA)*



*ARASHI!*

_k'irk'ira, tun ma ta labari irin na zube ba, aba ce wacce ta ke k'ulluwa da zururruka ma su
kishiyan juna, ta fuskar halaiya da d'abi'u, wad'anda suka sha banban daga wannan mutum
zuwa ga wancan mutum, daga wancan gida zuwa ga wancan gida, daga wannan gari zuwa
wancan gari, daga wannan kabila zuwa ga wancan kabila, daga wannan Al'umma zuwa wancan
Al'umma._
_Don haka wanda wani hali a cikin wannan labari yayi kaman ce danata to arashi ne aka
samu, kamar yanda na cikin labarin bazai ce wani mutum dayake a wajan labarin ya daukar
masa hali ba, to shima wanda yake a waje kada yace an aikata halin sa, haka kuma kamar
yanda kowani dan adam yake tauyaiye ba cikakkeba, Allah shi kadai ya kebanta da siffar cika,
don haka labari ma zai iya zama dai dai da ra ayin mai karatu kuma zai iya zama akasin haka,
idan aka sami dayan biyun wayan nan to badaga marubuciyar bane daga wayanda abin ya
shafa ne acikin labarin, .idan an tashi suka wanda abin ya shafa za a soka ba marubuciya ba,
nayi wannan maganar ne da masu cece kucen cewa bai dace aiwa Amatullah kishiya ba, ina so
kusani cewa kowani mutum da tasa kaddarar, kuma kishiya ba aibu bace ba dan haka a kiyaye,

Sodangi tana maku fatan alkairi_.





Wani wankan ta sake yi kamar yadda uwar ta umurce ta dayi, tana fitowa ta zauna
gaban madubi ta tsantsara kwalliya nagani na fad'i tayi azabar k'yau tamkar a sace ta a ruga.
Akwatin ta bud'e ta sanya d'an kunni da abun wuya da d'an hannu na zinari mai bala'in k'yau
sannan ta ciro riga da zani na less d'in dake cikin akwatin ta sanya rigar ta soma kici-kicin
d'aura zani saidai sam takasa d'aurawa, a haka ta rik'e zanin a hannu ta fita zuwa d'akin
mahaifiyar tana tura baki gaba. Ido uwar ta tsura mata tun shigowar ta dan ganin irin k'yaun data yi,
"mum wannan zanin yaki d'auruwa nayi nayi na kasa, mum kinsan fa ni bana son zani dan ban
iya d'aura shiba sai yai ta son yada mutum k'asa, nidai gashi ki taya ni d'aurawa, ta k'arasa
maganar tamkar zata fashe da kuka.
Zanin uwar ta k'arba a hannun ta tace ta bud'e k'afa sosai ta d'aura mata ya zauna tsaf kuwa
kasancewar Amatullah tubarkalla akwai k'ugu,
D'an k'walin ta kuma amsa ta d'aura mata shi tamkar an nad'a goggoro, nan da nan Amatullah
tayi kyau na d'aukar hankali, abin ba a cewa komi, tayi kyau iya kyau.
_"Wow daughter kinyi kyau sosai you look so cute_"
_"thank you mum_"
"mum wai suwaye zasu zo ne?"
"kiyi shuru da bakin ki zaki gani"

************

Da misalin k'arfe biyu da rabi na rana mai martaba sarkin kano da tawagar sa suka iso vila
k'arba ta mutunci akai masu tare da karrama su, mai martaba yayi matukar farinciki da irin
tarbar da akai masu, liyafa sosai aka had'a masu,bayan sunci sun sha nan suka gabatar da
abin da ya kawo su, inda atake _Mr President_ ya basu d'iyar tasa inda ya amshi sadaki naira
dubu d'ari acewar sa mafi k'arancin sadaki yafi albarka.
Nan aka tsaida rana nan da wata uku mai zuwa idan Allah ya kaimu, anan mai martaba ya
shaida masa auran daya nimawa Yarima, inda sam _Mr President_ bai nuna damuwar saba illa
farincikin daya taya su tare dasawa abin albarka, a zuciyar sa kuwa yana jinjina gata irin na
yarima. _Mr President_ yai kiran _first Lady_ tazo ta k'washi gaisuwa gun mai martaba inda yai mata
kyautar makudan kudade.
Sun dade suna tattauna matsalolin da ya shafi al'umma daga k'arshe suka gano inda
matsalar take nan _Mr President_ yace insha Allahu za a duba a gani domin akawo k'arshan
abin da izinin Allah.
Mai Martaba yasa akira masa surukar tasa Amatullah domin kuwa yana jin k'aunar ta har a
zuciyar sa, abinda Yarima Aliyu keso ai dole ne yataya shi son sa.

K'ara gyara Amatullah mahaifiyar ta tayi inda ta raka ta har kofar palon da bakin ke ciki inda ta
k'ara jaddada mata ki kama kanki banda kallon mutane tsage tsage ki nuna kunya sosai sarkin
kano ne da mutanan sa.
Tana shiga palon bakin ta d'auke da sallama kanta a k'asa dogarai suka soma yi mata kirari,
"barka da shigowa Gimbiya, sannu y'ar Toron giwa. Alherin Allah ya kai maki y'ar farin jini,
Tauraruwa sha haske, Hasken ki baya k'arewa matukar kina tare da wata, Y'ar shugaban k'asan
matar d'an sarki kuma Sarki mai jiran gado, Allah ya kashe makiyan ki ya bar mana ke ya nuna
mana ranar auran ki da yarima, mace d'aya tamkar da goma, Alkyabbar mata".
Wani irin gingirin gin Amatullah taji, nan da nan taji kanta yayi k'ato duk da kalaman nasu sun
d'aure mata kai matuk'a, k'asa ta zube ta k'washe gaisuwa gun mai martaba, kafin ta gaida
sauran mutanan, nan dogarawa suma sukai ta kawo nasu gaisuwar gun ta, nan mai martaba ya
dafa kanta cike da farin ciki yata saka mata albarka, yayi mata addu'oe sosai sannan daga
k'arshe yasa aka mik'o masa wani had'addan k'wando mai ado sosai da kansa ya bude ya ciro
wani had'addan alkyabba yasa ka mata, nan da nan ta haska gurin gaba d'aya, ya ciro damin
k'udin ya bata amman sam taki karba babu yanda baiyi ba, bata karba ba, hakan ba karamin
burge mai martaba yayi ba.
Saida mahaifin ta yasa baki sannan ta yarda ta karba, nan ta yi masu sallama ta mike da k'yar
ta bar palon, mahaifiyar tata ce ta tare ta tana fadin _"Wow my sweetheart_ kinga yanda kikayi
kyau kuwa?"
_"so tell me what happened there?"_
Nan Amatullah ta shiga zaiyano mata komi babu abinda ta boye mata, jindadi shimfide a
fuskar uwar, ta nuna tsananin farincikin ta, nan ta sanar da Amatullah abinda ke faruwa,
Wani irin ihun murna Amatullah tayi tare da tsalle, tana fadin, "masha Allah, Allah na gode
maka".
ta fashe da wani irin dariya tana fadin, "lallai za ayi ta! Amatullah a masarautar kano! _Wow_
lallai zanyi wulakanci son raina! Intaka uban da nake so inyi iko inyi takama son raina!"
Takara fashewa da dariya, tace "Aliyu! Yazamar min dole innimoka a fadin kano in nuna
maka iyakar ka."
"Aliyu wallahi Allah saina muzan taka na wulakanta rayuwar ka! Dole in koya maka darasi, in
nuna maka cewa bakin rijiya ba wajan wasan yaro bane."
"Aliyu! Aliyu! Aliyu! _you will pay for it._"
Sororo uwar ke kallon ta, kafin tace ke ki kama kanki fa duk wani mugun hali dawani rawar kai
dole ki aje shi gefe da yanzu ba da bane! Kinji na gaya maki.

Bayan mai martaba da mutanan sa sun gabatar da sallar la'asar suka d'auki hanyar komawa
kano daga abuja..............





*DEDICATED TO*
*KUBRA USMAN BALA*

[4/11, 6:47 AM] +234 703 962 5239: *KAINE SANADI* 5⃣5⃣to6⃣0⃣



*WRITTEN BY*


*FIDDAUSI SODANGI*





*STORY BY*
*KHALISAT HAYDAR*




*®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA)*




_Afuwan y'an hidimomi ne suka saka ni gaba shiyasa kuka jini shuru k'wana biyu._




Bayan k'wana biyu mai martaba yayi ma Yarima umurni daya je _government house_
shida Yaron Malan domin yagana da Amaryar sa, ba a son ran Yarima ba ya shirya shida Yaron
Malan suka nufi _government house_ d'in Yaron Malan sai zolayar sa yake, "iyyee!! Yarima
d'angata mai mata biyu, Allah yasamu a danshin ku. A fusace Yarima ya dube shi yace "dallah Malan ka sarara min nima ba a son raina ba dan
duka babu zabi na a cikin su kawai dai kaddara ce ta hau kaina amman ina Aliyu ina mata biyu!
"
Cike da mamaki Yaron Malan ke duban sa, dak'yar ya iya bud'e bakin sa yasoma yiwa Yarima
tambaya, "bangane babu zabin ka ba a cikin su harda Amatullah d'in da ka rikicewa mutane a
kanta?"
Guntun tsaki Yarima yaja kafin yace "Amatullah zan aure ta ne kawai saboda d'aukar fansa!,
Zan auri Amatullah ne saboda in nuna mata cewa ni Aliyu Haydar ba tsaran ta bane, in nuna
mata cewa tabbas akwai banbanci tsakanin mace da namiji, in nuna Mata cewa abin da namiji
zai iya mace bazata taba iya k'watan kwacin shiba.

Amatullah ta raina ni raini na k'arshe so ina so mu goge raini ni da ita ta gane waye babba a
tsakanin mu."

" Ita kuma wannan yarinyar da bansan sunan taba zan aure ta ne saboda biyayya wa mai
martaba, zan koma k'yautata mata in zauna da ita saboda Allah albarkacin mahaifina."

Ajiyar zuciya Yaron Malan yayi yace "hooo!! Yarima sarkin rigima, to me ita Amatullah d'in
tayi maka ne haka? Kokuma in ce mai kayi mata har ta raina ka haka, kukeyiwa junan ku irin
wannan kiyayya haka mai zafi?"
"Hmmmm!!!! Bazaka gane ba, ka k'yale ni da yarinyar nan kawai!."
"Hmmmm Yarima kenan, nidai shawarar dazan baka shine kabi a hankali, saboda nariga
nasan ka na san halin ka, duk abinda ka tsana tsana mai tsanani to tabbas wata rana zaka
soshi so kuma mai zafin gaske, dan haka kabi a hankali kaji na gaya maka."

Wani wawan tsaki Yarima yaja ya d'akawa Yaron Malan duka a cinyar sa dan shi ke tukin yace
"Allah ya tsare ni, bakin ka ya sari danyan kashi, wallahi bakada mutunci Yaron Malan ni
kakeyiwa wannan fatan?"
"gaskiya na fad'i Yarima ka yarda ko kada ka yarda haka kake.
Suna cikin wannan gardamar suka isa _government house_ an riga ansan da zuwan su dan
haka har cikin a ka shigar dasu, a babban, palo akai masu masauki inda y'an aikin gidan suka
cika masu tebur da kayan mak'ulashe fannin abinci da kayan marmari, sai laimuka masu sanyi,
Yarima yaji dad'in yanda aka tarbe su da mutunci, ruwa kawai ya d'an kurba, Yaron Malan ne
yad'an sha _fruits_ d'in shima ba da yawa ba, sun zauna na kusan minti sha biyar har Aliyu
yasoma hassala sai ga mai girma gomna ya shigo palon da sallama, cikin fara'a yace "A'a yau
Yarima ne da kanshi a gidan namu?"
Cikin jin kunya Aliyu ya sauko da ga kan kujerar shima Yaron Malan ya sauko suka gaida shi
cikin girmamawa, fuskar sa a sake ya amsa da yake mutun ne shi mai raha nan yaita jansu da
hira daga k'arshe yai masu nasiha mai ratsa Jiki ya mik'e yace bari ya turo masu Amaryar tasu,
ya fad'i cikin tsokala, godiya sukai mashi sosai cikin jin dad'in.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login