Showing 21001 words to 24000 words out of 35354 words

Chapter 8 - KAINE SANADI BOOK COMPLETE (1 to End) By Sodangi & Khalisat .pdf

16 Mar 2025

3760


shan abinki,"

"Sannan kuma ki yawaita cin k'wad'on zogale da dafaffaen k'wai da tumatir,"

"Ki yawaita cin dabino wanda bai busheba da ruwa,shima yana taimakawa sosai kinji ko

Amatullah?"

"Sannan kuma ki sami madarar ruwanki da k'wai ki kada shi sosai harsai yabar kumfa ki
shanye abin ki tas,"

"Saikuma Abu na k'arshe idan Kin kusa gama period dinki kisamu alkama, a niko maki ita
sai ki soyata sama -sama, har yayi ja, dakinga kin kusa gama period dinki sai ki dama shi
kamar salala ki sha shi da nono sau uku, shima yana taimakawa kinsan period yana tafiya da
abubuwa dayawa."
"Amatullah Dan Allah kada kibani kunya ki juri yin wayan nan abubuwan dana lissafo maki
su, idan kikayi wannan bayan kwana biyu kuma saikiyi wannan insha Allah zanzo gidan naki da
yardar Allah, kuka sosai Amatullah keyi ga kunya tamkar ta nutse k'asa.
Haka dai sukai ta yi mata nasiha har zuwa lokacin da mahaifin ta ya tashi tafiya da ita.
_Mr President_ da kansa ya sakata a mota ya nufi gidan Aliyu da ita wanda yake a GRA
tsayawa fadin tsarin gidan bata lokaci ne gidan yahadu karshe, saidai d'an karami ne.
hannunta mahaifin ya ruk'o har zuwa palon.
Aliyu ya taso da sauri ya taresu, amman sam Amatullah bata lura shine ba domin kanta a kasa
yake, nan khadija ta gaida _Mr President_ cikin girmamawa, amman duk da haka Amatullah
bata dau murya ba domin ita hankalin ta ba a kwance yake ba.
ya amsa cikin sakin fuska sannan ya fa dayi masu fad'a mai tsuma zuciya Amatullah kuwa
kuka kawai takeyi tana karawa,
“Haka yaringa gaya masu yanda zaman aure yake a musulunci. da abinda ya halatta miji
yayima matar sa da wanda ya halatta Mata tayiwa mijinta. Yacigaba dacewa Aliyu ga amanar
Amatullah nan nabaka. Don Allah ka kular min da ita ka kula da hakkinta daya rataya a
wuyanka kada kaci amanar ta kada ka zulunceta idan taimaka kuskure ka ganar da ita cikin
ruwan sanyi yadda zata fahimta idan taimaka laifi Wanda yafi karfin hukuncin ka Dan Allah
kanimeni koda a waya ne. Nikuma in allah ya yarda zanyi maka maganin abin koma menene.
Yajuyo kanta yace kekuma Amatullah hakika nayi murna da farinciki da samun ya mai biyayya
kamar ki Ina alfahari dake nagode Allah yasaka maki da alheri Dan girman Allah Amatullah ki
zauna kiyi zaman aure Dan bakida abinda zakimin Wanda yawuce kiyi zaman aure Amatullah
kiyi biyayya ga mijinki yinayi Bari na Bari shine zaman aure kada ki sake mijinki yakawo min
karar ki kosau daya ne kinji nagaya maki kada insake inganki dasunan yaji! Kizamo mai boye
sirrin mijinki danaki. Kada ki tozarta mijinki koda sau daya kidaure duk abinda zai shiga tsakanin
ku kumagance ma kanku shi. Sai dai in abin yafi karfinku sai Ku gayama nagaba daku.
Amatullah kada kisake mijinki yakawo min kararki inakara shaida maki idan na bincika naji kece
bakida gaskiya to wlh Zan mummunar Saba maki.
kinsan halina sarai.
aure ba abin wasa bane kiyi biyayya aljannarki na karkashin kafarsa saiya daga zaki shige kina
jina ko?"
"Cikin kuka tace eh!"

“Yace ke kuma khadija kema ga amanar Amatullah nan nabaki dama ku aminai ne kun riga

kunsan halin junan ku,
dole sai kunayi kuna hakuri da junan ku, saboda zomu zauna zo mu saba ne.
Dan girman Allah Ku zauna lfy kuyi kishi irin na matan sahabbai ba irin kishin haukan da
akeyi yanxu a wannan zamanin ba Ina fata nasihata ta shige ku kuma zakuyi aiki da ita! Gaba
daya suka amsa da insha Allah sam Amatullah bata gane muryar suba har a wannan lokacin
dan hankalin ta a tashe yake duk idon ta duk sun kunbura da kuka. Amatullah kuka kawai take tamkar Zata shide. Ahaka yayi masu sallama yatafi,

” Aliyu ya raka sa har mota, yana fita Khadija ta mike tsaye ta shige d'akin ta dan ta lura sam
Amatullah bata shaida suba.
mik’ewa Amatullah ma tayi itama tanufi nata d’akin dan ganin d'aki biyu ne kawai a cikin gidan,
dan haka tasan tabbas nata ne d'ayan,
Wani bangare na zuciyar ta na mamakin yaza ai ya aje su nan gida saikace akurki.

Aliyu nadawowa ya nufi d'akin Khadija ya shaida mata yana son ganin su a Palo daga haka ya
fice abin sa yanufi palon ya zauna, wayar _land-line_ na palon ya d'auka ya kira Amatullah
wacce tuni tabar kukan tama tube tana shirin shiga wanka ne taji wayar na kara, kamar karta
dauka sai sai ta tabe baki ta dauka kawai. murya kasa kasa ya ce "kifito palo muna jiran ki ya aje wayar wani iri taji muryar tasa ba yanda
tasaba ji ba sai dai ta share kawai ta shige kewaye tayi wankan ta, saida ta bata lokaci sosai
sannan tafito ta tsaya gaban madubi ta karaci k'alailaitar ta tukun, sannan tasa kaya ta buga
dauri ta lullube kanta da babban mayafi ta feshe Jiki da turare.
Cikin tafiyar ta ta tak'ama da isa ta iso palon, tafiya take a hankali gaba d'aya jikin ta babu inda
baya juyawa, kanta a k'asa tana k'ara gyara lullubin kanta, kujera ta nima ta kame abin ta tare
da d'aura k'afa d'aya bisa d'aya tana kallon farcan ta daya sha jan farce alamar tana fashin
sallah. Aliyu wanda ke zaune kujera daya shida Khadija ne yayi gyaran murya cikin kakkausar
murya yace "ke ba a koya maki gaida mutane bane a gidan naku?"
"naga alamar baki da tarbiyya ko?"
Khadija ce ta d'an zungure sa alamar ya bari, yayin da Amatullah tayi wani irin zabura ta mik'e
tsaye tana zare ido yayin da mayafin kanta yayi k'asa. Shima tsaye ya mik'e dan ya shirya ma
hakan dama, a hak'e yake dama da shanya su data yi niyyar sa yayi k'asa-k'asa da ita idan ta
kawo masa raini. Cike da k'arfin hali tafara fad'in "uban wa ya kawo ka gida na! Taya ma akai har masu gadi
suka barka ka shigo?"
"lallai yau zaka raina kanka wallahi wallahi tunda har ka kawo kanka da kanka cikin gidan nan
ai dama nayi alkawarin sai na nimo ka duk inda kake a fad'in kano domin in koya maka darasin
rayuwa in nuna maka cewa Amatullah ba tsarar ka bace tafi k'arfin matsiyaci irin ka"....... Hannu
ya d'aga da niyyar ya sharara mata mari da sauri Khadija ta rik'e hannun nasa tana fad'in "haba
miji na! Taya za ai ka biyewa mace macan ma matar ka ta sunna wacce kake da k'arfin iko a
kanta har ta haddasa maka damuwa a cikin wannan dare mai cike da tarihi? Karfa ka manta
wannan daran alkairi ne a gare mu, dare ne wanda zamu nunawa Allah farin cikin mu muyi

masa godiya mu gode masa daya nuna mana wannan rana da ranmu da lafiyar mu, saboda
haka kacire kowacce damuwa a ranka gwarzon miji na, haba Aliyu gadan ga k'usar yak'i, haba
Yarima d'an sarki Angon Khadija Muhammad Dala da Amatullah Ahmad Fage, haba miji na da
babu tamkar sa a duk cikin mazajan duniya, haba Aliyu Haydar d'an sarki kuma sarki mai jiran
gado insha Allahu.
A hankali ta saki hannun sa tana kallon cikin idon sa yayin da take sakar masa murmushi mai
sanyaya zuciyar masoyi, a take ya jawo ta ya rungume zuciyar sa nayi masa wani irin sanyin
dad'i...............





​DEDICATED TO​
​KUBRA USMAN BALA
[4/11, 6:47 AM] +234 703 962 5239: *KAINE SANADI* 6⃣5⃣to7⃣0⃣





*WRITTEN BY*



*FIDDAUSI SODANGI*





*STORY BY*
*KHALISAT HAYDAR*





*®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA)*

Zuwa yanzu Amatullah tagama fahimtar meke faruwa, watau Aliyu ya aure tane dan ya
nuna mata iya karta shine ya had'a ta da khadija saboda yana so ya kunsa mata bak'in ciki,
lallai kuwa yau zaiga d'anyan kai a cikin akurkin gidan nan nasa.
Tamkar wata mahaukaciya Amatullah tayi kansu tana fad'in "wallahi wallahi baka isa ba Aliyu
kayi kadan daka aure ni! ka dube nifa, nayi maka kama da matar matsiyaci irin ka?"
"Wallahi kodai ka sake ni kokuwa inzamo ajalin ka dan wallahi wallahi sai nayi maka abinda
baka taba tunani ba matsiyaci kawai da'n iska! Nizaka rainawa wayau wallahi bazan yarda ba
dole in dau mataki a kanka. "
Da gudu tayi hanyar d'akin ta ta rufe tana rusar kuka.
Aliyu ya saki Khadija rannan nasa a bace yace "khadija daga yau sai yau bana so ki k'ara
hana ni yin abin da naga dama akan yarinyar can, in dai har kina son farincikina dole ki bani
had'in kai dan mu koya mata hankali, in kika lura sam yarinyar bata da tarbiyya dan haka kibani
had'in kai mu sai tata tadawo hanya kin gane ko?" "shikenan miji na na fahimce ka Allah ya bani ikon yima biyayya."

"kije ki shirya lokacin zuwa _dinner_ d'in yayi, kayan dana baki d'azu su zakiyi amfani dasu, jeki
d'auko min na wancan yarinyar su ne a d'aya jakar."
D'akin Amatullah ya nufa bayan khadija takawo masa jakar, bubbugawa ya shiga yi da k'arfi
amman taki budewa da alama ma ta zare _key_ d'in a jikin k'ofar, d'akin khadija ya koma ya
nimo gudan _key_ d'in ya bude d'akin ya shiga.
Tana k'wance tana kuka tamkar zata shid'e,
Cikin kakkausar murya yace "kee! Ki tashi ki shirya karki batawa mutane lokaci dallah!.
D'if tayi tamkar ba itace ke rusa kukan ba dan a ganin ta ai rainin wayau ne ma yaga tana
kuka.
K'ara daka mata tsawa yayi yace "badake nake magana bane! Nace ki tashi ga kaya nan ki
saka zamuje _dinner_ da abokai na suka shirya mana, ya kare maganar tare da wulla mata
jakar a fuska."
Wani irin mugun kallo tayi masa da idanuwan ta dasukai jawur cikin tsiwa tace "uban waye
zaije k'azamin _dinner_ ku ta k'ananan yara y'ay'an talakawa matsiyata masu warin baki?"
"to idan ma mafarki kakeyi ka farka ni ba tsarar ka bace kasani, dan haka ka kiyaye ni magana
in bata takarda ta bace to bana buk'atar kayi min ita kaji nagaya maka!".

Murmushin mugun ta yayi ya haye gadon kamar kiftawar ido ya murde mata baki da hannun
sa yana kallon cikin idon ta yace" k'ara maimaita kalaman ki inji?"
Azaba yasa takasa magana a gigice ta kamo hannunsa ta gartsa masa wani mugun cizo, da
sauri yasake ta tare da kifa mata wani wawan mari, "ni kika ciza?" lallai zanyi maganin ki yau
d'in nan, kafin tayi wani yunk'uri tuni ya had'e bakin su waje d'aya ya lalubo harshan ta ya
gantsara mata wani uban cizo a harshan da iya k'arfin sa, ai gaba d'aya Amatullah ta shid'e dan
tsananin azaba tafi minti biyar a haka kafin ta dawo haiyyacin ta, ta rik'e bakin ta hawaye nabin
k'uncin ta tana kallon sa tana tunanin abinda zatai masa, lallai yau ta k'ara tabbatar wa Aliyu
mugu ne baida imani, bata k'ara tabbatar da hakan ba sai da ta shafo harshan ta taga jini, baki
ta bud'e zatai magana amman ta kasa dan azabar zugin da bakin ta keyi.

Murmushi yayi yace "gobe ma ki k'ara kinji?"
"Kuma kitashi ki shirya kafin inyi k'asa k'asa dake anan!."
A hankali ta tashi tasoma k'wabe kayan jikin ta a gaban sa ko kunya bata jiba daga ita sai pant
da bra da sauri ya kauda kansa tare da ficewa a d'akin har yana tuntube, tsaki taja tace "d'an
iskan banza ai da ka tsaya!"
Kawai zata bisu wajan _dinner_ d'in ne dan ta nuna masu iyakar su acewar ta kenan a zuciyar
ta.

Jakar da ya wurgo mata ta bud'e da niyyar idan kayan ciki basuyi mata ba wallahi bazata
saka ba, sai dai tasa nata kayan, tana bud'ewa taga wata
doguwar riga na _Lace_ mai d'ankaren tsada, wanda _Style Temple_ ta d'inka, sai set d'in
zinari shima mai kyau, takalma ne na alfarma masu tsada da _clutch_ bag dinsu a hade.
Sai wani d'an goggoro mai azabar kyau, sai kuma mayafi mara nauyi mai kyau shima kalar
_lace_ d'in kayan dai sun had'u ba karya, ita kanta tasan kayan sunyi kyau gasu kuma kalar da
ta fi so ne, shiyasa ta ciro su ta soma sawa tana wani yatsine fuska.

Wohoho.... Wani kaya sai amale! Wai kuwa kunga yanda Amatullah tayi wani irin bala'in k'yau
cikin kayan? Abin sai wanda yagani, kayan sun zauna d'as a jikin ta tamkar a tare aka halicce
su, k'ugun nan yafito tamkar zai fasa rigar kai masha Allah Amatullah kam akwai _shape_ mai
k'yau tubarkalla. Zama tayi ta tsara k'walliya nagani na fad'a tamkar wata sarauniyyar k'yau.
Gaskiya ko d'an bakin ciki bazai ce batayi k'yau ba kam.
Goggoran ta saka a kanta bayan ta gama kwalliyar tasa d'an hannun da yan kunni tare da abun
wuyar harda wani sarkar k'afa, nan da nan tak'ara haskawa, kin saka mayafin tayi tayi wurgi da
shi bisa gadon.
D'an pos d'in dake had'e da kayan ta d'auko wanda ke shake da kudi a ciki, sai wayar ta data
d'auko tafito palon tagan su a tsaye alamar ita suke jira, itama khadija irin shigar Amatullah ne a
jikin ta sai dai kalar ya banban ta.
Aliyu ma Yayi bala'in yin k'yau abin dai ba a cewa komi.
Aliyu bai san sanda ya had'e miyau ba ya d'aure fuska had'e da buga mata tsawa "kije ki saka
mayafin ki baza ki bini a haka ba, bakida hankali ne?"
Tsaki tayi ta koma ta d'auko mayafin ta yafa a kafad'ar ta Aliyu yaji kamar ma yace bazata ba
dan shidai bai ga amfanin wannan d'an iskan mayafin ba.
A fusace yace "wai ke bakida wani mayafin dazaki iya amfani dashi ne dole sai wannan
gantalallan ko baki san ke katuwa bace mara tsarin gani?"
"kidube khadija mana ya fad'i yana nuna mata khadijan da hannun sa, baki ga yanda nata yai
mata dai dai ba zar sha'awa?"
"Amman ke abu wani gandandan dake babu ko k'yawun gani!"
Rai a bace Amatullah tace "ai kaine gantalallan daka d'in ko shi! Zaka gaya wa mutane
maganar banza! Ai wallahi wallahi k'arya kake kace bani da tsari dan kasan"...........Yaron malan
ne yashigo yana fad'in "Aliyu kuna fa batawa mutane lokaci kufa ake jira tuntuni dare nata yi
saboda Allah". Wani mugun kallo Amatullah tayi masa tace "watau kai ne munafukin da aka hada baki

dakai a ka cece ni ko?"
"to wallahi Allah bazai barku ba d'iyan matsiya ta kawai! "
Ido Yaron Malan ya zaro yana jinjina rashin mutunci irin na Amatullah, alama Aliyu yayi masa
dayayi shuru karyace komi, dan haka Yaron Malan yafice ransa a bace.
*Ficewa Aliyu yayi hannunsa cikin na khadija, Amatullah ma ta rufa masu baya.
Yaron Malan ne ke tukin yayin da Aliyu da matan shi ke baya sun saka shi a tsakiya, tsawon
minti biyar suna tafiya Aliyu da khadija suna ta hira k'asa-k'asa ko Amatullah da ke kusa dasu
bataji, yawani k'wanto jikin khadija kamar zai shigar da ita cikin sa, zuwa can khadija tasoma
wani k'yalk'yala dariya Aliyu nayi mata cakulkuli tana wani gantsarewa ko kunyar Yaron Malan
basa ji can ya fad'a jikin ta yana ci gaba dayi mata wasa tana k'wasar dariya ya manne ta a jikin
sa yana sakar mata _kiss_ ta ko ina, dariyar kamar zata shid'e, Amatullah taja wani wawan tsaki
tace "iskancin banza kawai tambad'ad'd'u kawai! Wayanda basu san ciwon kansu ba!"
Aliyu daga shi har khadija tamkar ma basu san Allah yayi Amatullah a wajan ba, Aliyu ya ci
gaba da wasa da matar sa haryana fad'in Amatullah ta d'an k'ara matsawa ta basu waje ta
matse su.
Sam Amatullah ta kasa kauda idon ta a kansu bak'in ciki, takaici tamkar ta had'e zuciya ita kan
ta bata san meye abin jin haushi ba dan suna wannan iskancin ba.
Yaron Malan kuwa tamkar ma babu shi a matar duk da yana sane da abinda ke wanzuwa
yana jinjina iskanci irin na Aliyu, lallai yanaso yasawa yarinyar nan hawan jini.

A haka suka isa wajan aka soma gudanar da komi cikin tsari inda Amatullah tazama yar kallo
tama kasa aiwatar da abin da tayi niyya ahaka har taron ya watse inda Yaron Malan ya maido
su gida.
Ko sauraran su batayi ba ta shige d'akin ta ta rufe tare da barin mukullin a jiki, wayar ta ta
d'auka ta kira uwar ta fashe da kuka tamkar ranta zai fita, a rikice uwar ke tambayar ta abin da
ke faruwa, takasa magana illa kukan da ta ke ci gaba dayi.
Da kyar ta soma magana "wallahi _mum_ bazan iya zama gidan nan ba wallahi bana son shi
na tsane sa _mum_ ki taimake ni ya sake ni wallahi bazan zauna ba"...... Wani irin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login