Showing 18001 words to 21000 words out of 35354 words
Chapter 7 - KAINE SANADI BOOK COMPLETE (1 to End) By Sodangi & Khalisat .pdf
Bayan minti kamar goma suna ta d'an hirar su sama-sama k'amshin turaran tane yasoma
sanar dasu isowar ta kafin suka jiyo takun ta k'was k'was k'was, shuru sukayi suna jiran
shigowar ta, gaba d'ayan su fuskar su na kallon k'ofar dan suga Amaryar tasu ma'abociyar
kamshi da tsafta, dan da alamu zatai tsafta a cewar Aliyu a zuciyar sa, dan kuwa shi yana
girmama kamshi.
Shigowar ta had'e da sallamar ta shi yayi sanadiyyar tashin Aliyu Haydar a zabure tamkar
wanda aka tsikara da allaura, idanuwan sa a kanta itama haka, kallon kallo sukeyi wa juna
tsawon lokaci, wani irin farinciki had'e da mamaki mai tsanani yakama ta, tarasa a wani irin hali
take ciki, wai yau ita ce da _Aliyu Rasheed Ganduje_ matsayin wayan da zasu auri juna ikon
Allah sai kallo, wani zuciyar ne ya kwabe ta da fadin "uban wa yace maki Aliyu ne angon? Baki
ganin su biyu ne? Kika sani ko d'ayan ne angon naki?"
Aliyu ne ya katse ta da fad'in _"KHADIJA MUHAMMAD DALA!_"
"kece Amaryar tawa dama?"
Cikin wani irin murya mai cike da farin ciki yayi mata tambayar, sam yakasa boye farin cikin sa.
Hannun ta ya kama ya zaunar da ita akan kujerar da ke fuskan tar tasa, ya dubi Yaron Malan
yace "kaga yar k'yakkyawar Amarya ta a shema na santa student d'ita ce kuma aminiyar
_Amatullah Ahmad Fage_ ka ga ni wannan abu yaiwa dadi matuka, Allah ya k'arawa mai
martaba nisan kwana, gaskiya bansan irin farincikin dana ke ciki ba yau!." Yaron Malan ya galla masa harara yana fad'in "adai juri zuwa rafi....."
Katse shi Yarima yayi "dalla Malan kar ka cika min ita da surutu!".
Guntun tsaki Yaron Malan yayi yace "kiyi hakuri fa da halin wannan rigimammen mijin naki,
yacika rigima kamar wani kankanin yaro!."
Murmushin yak'e Khadija tayi tace "uhmm ai ni nasan yaya Ali na bashi da rigima sam mutum
ne shi mai gaskiya a koda yaushe, so fad'in gaskiya ai bazai taba zama rigima ba!"
Ta kare maganar tata tana Murmushi tare da kallon fuskar Aliyu wanda shi kansa ita yake
kallo.
"iyyeee!!!! Lallai Khadija ashe kema ba k'yalle bace! Watau kina bayan mijin ki kenan,
amman saboda Allah ko d'an irin karar nan babu?"
"To shikenan wallahi bari in baku waje kafin ku tarar min kuyi min d'an banzan duka dan dai ni
ba shuru zanyi ba, in naga abu dole inyi magana".
Ya mik'e ya fice daga palon yana fad'in kunga tafiya ta masoyan asali, koda yake duk burga ce
tun da yau Soyayyar ta samo asali.
Ya fice yana dariya.
Yana fita Khadija ta sunkuyar da kai k'asa tana sauraran Aliyu dayayi shuru sai kace bashi ne
yagama zuba yanzu ba.
Sunfi minti biyar shuru da alama Jinin sarautar ya motsa wa Aliyu Haydar.Can kamar daga
sama, Khadija taji shi ya jifo mata tambaya, "Khadija kunyi hutu ko?"
"muryar ta a danyaye tace "yaya Aliyu ai na bar _America_ a nan B,U,K nake yanzu."
Cikin mamaki ya dube ta yace _"why?"_
Sam Khadija bata iya k'arya ba wannan dalilin yasa ta faiyya ce ma Aliyu biri har watsiya, ba ta
boye masa komi ba dan gane da abinda ya faru tsakanin ta da Amatullah ba.
Murmushi Aliyu yayi kawai a hankali cikin izza yace mata "nagode da k'aunar ki a gare ni
Khadija."
"hakika ke masoyiya ta ce ta asali tunda har kika zabe ni kika bar kawar ki, sai gashi kuma
Allah ya dubi zuciyar ki yaba ki ni a matsayin miji, nikuma ya bani ke a matsayin matar aure,
dan haka sai mu kara godewa Allah a bisa wannan zabi dayayi mana na alkairi."
Nan dai suka ci gaba da tattaunawa irin ta masoya, in da Aliyu ya d'aukar mata alkawarin
kula da ita tsakanin sa da Allah har iya tsawon rayuwar sa. Khadija ta yi farin ciki sosai da jin
hakan, inda a k'arshe ya shaida mata cewa zai aure sune ita da Amatullah saboda ita zabin
mahaifiyar sace yayin da ita Khadija d'in ta zamo zabin mahaifin sa, yayi mata karyar hakan ne
dan kada tasa wa ranta wani abu daban .
Ai kuwa ba k'aramin gigicewa Khadija tayi ba, kuka tasamai tana fadin taya ya zata yarda ta yi
kishi da aminiyar ta, kuka sosai take yi tana fadin bazata iya ba, wannan ai abin kunya ne ana
barin halas dan kunya.
Da k'yar Aliyu ya shawo kanta ta yarda, yakuma shaida mata cewa ita kanta Amatullah bata
san shi zata aura ba dan haka ta kwantar da hankalin ta.
Haka suka ci gaba da hiran su daga k'arshe sukai sallama inda yacika ta da kudi, tayi mashi
rakiya har zuwa motar su inda Yaron Malan keta mata tsiya Aliyu na rama mata da haka dai
sukai bankwana cike da farin ciki Khadija nata yiwa Allah godiya daya cika mata burin ta na
samun _Aliyu Rasheed Ganduje_ .
*************
Bayan k'wana biyu Aliyu da yaran Malan suka shirya suka nufi Abuja dan kai gaisuwa ga
_Mr President_ cikin mutunci da karamawa aka amshe su, inda suka gaisa da _Mr President_
nan ma ruwa kawai Aliyu yasha, _first Lady_ Hajiya Asma'u ma tazo suka gaisa cikin mutunci,
inda ta fice tana fadin bari ta turo masu Amatullah d'in. Dama shi mahaifin nata tuni ya bar palon.
Aliyu ne ya mik'e yana fad'in "dan girman Allah Abokina kayi kamar yadda na umurce ka kada
ka kofsa mun dan Allah Wlh kanada babban k'yauta idan har ka tafiyar da komi yanda ya
kamata alkawarine wannan wallahi!".
"Dallah Malan ka fice kada tazo ta tadda ka nagaya maka zanyi aidai kasan ni ina girmama
alkawari ko? So ka kwantar da hankalin ka bakada matsala."
Ficewa Aliyu yayi daga palon ya nufi mota ya zauna yana jiran fitowar Yaron Malan.
Amatullah wacce tasha k'walliya kamar zata gasar cin sarauniyar k'yau ta shigo d'akin
bakin ta d'auke da sallama, nan Yaron Malan ya amsa mata tare da binta da kallo saboda ganin
tsabagen kyau irin nata ga d'iri tuburkalla, da k'yar ya iya cewa "barka da shigowa gimbiya
sarautar mata, dafatan nasame ki lafiya?" Amsawa tayi bayan ta nimi kujera ta zauna, suka gaisa sosai yaron Malan ya dube ta yace
masha Allah ashe dai Amaryar tawa k'yakkyawa ce, nayi wa Allah godiya, Amatullah ki godewa
Allah kina da kyau sosai, cikin jin dadi Amatullah tace nagode!.
Daga haka kowa yaja bakin sa ya tsuke, saidaga baya Yaron Malan yashiga jefo mata yan
tambayoyi tana basa amsa daga k'arshe yayi mata sallama tare da cika ta da kudi.
No rakiya batai masa ba tashige cikin gida zuciyar ta cike da murna tasami _handsome guy_
d'an gidan sarauta.
Koda uwar ta gaya mata su biyu zai Aura sam bata damu ba acewar ta mezai dame ta tunda
tasan kowa da nasa makeken gidan aljannar duniya ita ai batada matsala kwata kwata Allah dai
ya nuna mata ranar auran lafiya.
Uwar tace "wai ni Amatullah naga alamar kinma fimu matsuwa da wannan auran ne "
Dariya kawai tayi ta fice tabar uwar............
*DEDICATED TO*
*KUBRA USMAN BALA*
[4/11, 6:47 AM] +234 703 962 5239: [4/5, 4:53 PM] FIDDAUSI SODANGIí ½í²…: [4/5, 2:45 PM]
FIDDAUSI SODANGIí ½í²…: *KAINE SANADI* 6⃣0⃣to 6⃣5⃣
*WRITTEN BY :*
*FIDDAUSI SODANGI*
*STORY BY*
*KHALISAT HAYDAR*
*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION (NWA)*
*Godiya mai tarin yawa (ANTY SIS) wannan page d'in sadaukarwa ce a gare ki, hakika
Sodangi tana alfahari dake a koda yaushe Allah yabar zumunci, nagode da gudun mawar ki
agare ni*
Haka abin yaci gaba da kasancewa abu kamar wasa sai gashi k'aramar magana tazama
babba, lokacin biki ya k'arato, shirye-shirye ta ko ina yinsa ake babu kama hannun yaro.
_Programs_ d'in da Amatullah tayi d'ai d'ai d'ai har guda shida kuma duka babu ango domin
kuwa Aliyu ya sakar wa Yaron Malan komi shine angon Amatullah yayin da shi ya tsaya ma
Khadija a duka _programs_ d'in da tayi. Yaron Malan yabawa Amatullah uzirin sa kan cewa
abubuwa sunyi masa yawa shiyasa bazai sami zuwa can Abuja ba sai idan sundawo nan d'in
sun had'e, sam Amatullah bata damu ba sai hidimar da take tana wani rawar kan ita matar d'an
sarki ana tayiwa k'awaye kankanba.
Ba k'aramin k'ud'i Yaron Malan ya sakar mata ba domin ta guda nar da hidin damun ta babu
takura, ba k'aramin kuka kud'i sukayi ba a wajan sha'anin bikin ba, domin kuwa _first Lady_
zagewa tayi ta fidda y'ar tata kunya, kud'i kamar tsinto su suke.
Kayan da Amatullah kawai taringa sakawa ya isa mutum yagane anyi barnar kud'i a wajan,
kaya ne masu tsadar gaske d'inkin su kawai ma ba a nan k'asar akayi ba gaba d'aya a waje
akayi su.
Haka sukai ta gudanar da sha'a nin su har zuwa ranan alhamis inda _Mr President_ ya had'a
kan iyalin sa sukayi gida watau kanon dabo tumbin giwa domin a gudanar da d'aurin aure a gida
cikin dangi domin kuwa kowa yabar gida to gida ya barshi.
Rana bata k'arya saidai uwar d'iya taji kunya inji bahaushan mutum, a yaune aka d'aura
auran *ALIYU RASHEED GANDUJE* da *KHADIJA MUHAMMAD DALA* sannan aka kuma
d'aura na *AMATULLAHI AHMAD FAGE* da *ALIYU RASHEED GANDUJE* akan sadaki naira
dubu d'ari acikin babban masallacin juma'ar da ke nan cikin garin kano, bayan sallar juma'a inda
manya manyan sarakuna da yan siyasa da manyan y'an kasuwa suka cika ko ina, sai tarin
abokan Aliyu gaiyya guda, kai wannan d'aurin aure ya sami halarta mutane masu yawon gaske,
saidai muyi fatan ubangiji Allah yaba da zaman lafiya da zuri'a d'aiyaba.
bayan an k'are d'aurin auran ne gaba d'aya aka d'unguma zuwa gidan _Mr President_ domin
gudanar da _reception_ na maza, domin kuwa mai girma gomna Muhammad Dala abokin sa ne
na kud da kud, shiyasa suke gudanar da komi na bikin a tare.
"Amatullah wacce keta sharar kuka tun da safe babu irin rarrashin da _Anties_ d'in ta
basuyi mata ba amman taki hakuri tayi shuru,uwar da kanta tazo tana ta aikin rarrashi amman
ina tamkar ana dad'a zuga tane, nan tayi fushi ta k'yaleta.
yanzu ma kukan nata ne yakaru data tabbatar dacewar lallai zuwa yanzu ta tabbata matar
Aliyu ta sunna wanda a iya tsawon rayuwar ta sau d'aya ta taba ganin shi kullum uzuri yake
kawo mata baya zuwa.
haba saima kukan nata ya k'aru harda ihu, k'awayan ta dai sun saka mata ido suna kallon ikon
Allah.
Su dai sun san ba auran dole za aiwa Amatullah ba na soyayya ne amman saiwani abu dakeyi
haka su kam abin na Amatullah yafara basu haushi ya bar basu mamaki bata masu rai yake
kawai, babban yarinya da ita tana abu kamar wata y'ar k'auye, ai ko yaran k'auye sun daina
wannan yayin acewar su.
**************************
"Baba na mai kake nufi da wannan zance naka, duk yawan gida jan ka kace kai had'e matan
ka zakayi a gida d'aya? D'ayan ma mafi k'aranci daga gidajan ka? Gaskiya Baba na wannan
zancan banza ne, gidan nan yayi maku kad'an sosai, ai wannan gida ko mace d'aya bazan bari
ta zauna ba bare har su biyu gaskiya!"
Cikin k'wantar da murya Aliyu yasoma magana, Allah ya k'ara maka nisan k'wana akwai
dalilin daya sa zanyi hakan ne, amman bawai ina nufin a haka zasu ci gaba da zama ba a'a
kawai zasu zauna ne na wani d'an lokaci sai in maida kowacce gidan ta daban.
Dan Allah mai martaba ayi min wannan laminin wallahi tsari ne mai kyau nakeso in tsara.
Dak'yar ya shawo kan mahaifin nasa ya amince masa da buk'atar tasa.
Cike da murna da farinciki mara adadi yabaro fadar.
**************
*DA DADDARE*
khadija aka farawa kaiwa gidan miji bayan ta sha fad'a da nasihohi masu ratsa jiki, kuka
sosai take, tana jinjina yanda zatai zaman kishi da Amatullah aminiyar ta na kud da kud tun
suna yara..
Surutu da tsegumi yasoma tashi a bangaran yan uwan Khadija da kawayan ta na ganin d'an
k'aramin gidan da abokan ango suka kawo su matsayin gidan auran khadija kenan, mamaki da
Al'ajabi kowa keyi, ganin surutun yayi yawa ne Amarya da kanta ta shaida masu cewa ai yace
ba dadewa zatayi a nan gidan ba yana da dalilin kawo ta nan din zuwa wani lokaci, shiyasa
kowa yaja bakin sa yayi shuru,
Abokan ango sunshaida masu ba a kwana gidan Amarya a tsarin masarautar su Aliyu, dan
haka bayan wani d'an kankanin lokaci kowa ya watse aka bar amarya da halin ta.
​**************
Amatullah ta fito sak Amarya abinta, sai k'yalli takeyi ta d'au k'walliya abin saidai
Wanda yagani, idanuwan nedai suka kumbura alamar taci kuka ta gode Allah dama ga
idanuwan nata tubarkallah.
Anty Amina kanwar _first Lady_ ce ta shigo d'akin ta kamo hannun ta suka fito d'akin domin
ta kaita gun mahaifiyar ta da sauran dangi dan ai mata nasiha domin mahaifin ta _Mr
President_ yace shida kansa zaikai y'ar tasa d'akin mijin ta.
Suna fitowa palo nan jama'a suka d'auki bud'a, wata abokiyar wasan Amatullah tace
shakiyiyar banza kawai da iskanci ne yasaki lafewa kenan kinai mana kukan iskanci, dan kar
ace kina zak'wad'i, dama kin gyagije abinki yarinya gidan Aliyu tamkar ankai ki angama, in
kikayi tsiya kuma ince nafasa zaman d'akin, dariya sauran mutanan sukayi, janta Anty Amina
tayi zuwa sama.
Hajiya Asma'u _(first Lady)_ da wasu k'awayan ta tare da y'an uwan ta su ka iske a zaune
suna ta surutu akan gida d'aya da Aliyu yace zai hada matan sa, wai dan ma basu ga gidan ba
kenan, gaba d'ayan su suka bi Amarya da kallo nan d'akin ya dauki hayaniya kowa nafadin
Masha Allah Amarya tasha k'yau, kanta a k'asa ta zauna kusa da uwar ta a k'asa. Nan uwar
tayi mata nasiha sosai tasa mata albarka, in banda kuka babu abinda Amatullah keyi.
Wata yar Hajiya Asma'u ce ta soma yima ta nasiha kamar haka:
"Da farko Y'ata nasihar da zan miki shine, kikula da shinfidar mijinki."
"Y'ata kikula da in da mijinki yafi so ajikinki".
"Y'ata kikula da abincin da mijinki yafiso."
"Y'ata karki bari mijinki yaji wari a jikinki."
"Y'ata gidin ga girmama mijinki."
"Y'ake yata karkikuskura kiraina yan uwan mijinki." "Yake y'ata kibi mijinki sauda k'afa domin
aljannar ki na k'ark'ashin k'afar sa."
"Yake y'ata kifishi nuna farin ciki alokacin dayake farinciki, sannan idan yana bak'in ciki kifishi
nuna bak'in cikin ki, ki k'wantar masa da hankali."
" Yake y'ata ki lura da lokacin cin abincinsa, idan lokacin yayi toki tanadar masa kafin ma ya iso,
idan ya shigo kiyi masa tara irin ta darajawa ki gabatar masa da abincin sa basai yace ina abinci
naba?"
" Ya ke y'ata ki lura da lokacin da mijinki ke jin bacci ki barshi ya k'wanta ya huta kada
kidamesa." "Yake y'ata ina horan ki dayin ado, ki lura da inda yafi kallo ajikin ki da zarar yashigo
cikin gida."
" yake y'ata ki kiyaye kunnin mijin ki, kada kibari yaji mummunar zance daga bakin ki."
"Yake y'ata maganata ta k'arshe da zan gaya maki shine ki guji bakin kishi! "
Allah yabaku zaman lafiya da zuri,a dayyiba Ameen.
Wata k'awar Hajiya Asma'u mai suna Hajiya Fatima tace "Amatullah kina jina ko?"
" ki rike wayan nan abubuwan dazan gaya maki insha Allahu zakiyi alfahari da auranki, zaki
sami mijin ki a tafin hannunki batare da boka ko mallan ba dan Allah Amatullah kirike wayannan
abubuwan banda k'iuya, _please!_"
"Nan da sati biyu nake so ki fara wannan abin da zan gaya maki.
Kina jina ko? "
"ki sami tumatir da kankana, ki markad'a shi a blanda, sai ki samu dabino mai k'yau kicire
masa y'ay'a kisaka a tukunya da ruwa kadan ki dafa shi ya dahu sosai luguf, saiki Dame shi ki
zuwa a markadaddan tumatir da kankanar nan kisami madarar ruwa da zuma ko suga kisa aciki
ki juya sosai ki shanye abinki kinji ko ki jure yin hakan dan Allah,"
"Sannan kuma ki juri yin kunun dabino, kisami dabinonki mai k'yau ki cire k'wallon sai ki jika
shi harsai yayi taushi sosai, saiki markada a blanda ki zuba madarar ruwanki da zuma ki ringa