Showing 3001 words to 6000 words out of 27403 words

Chapter 2 - ABDULFATAH by Fatima S Umar Jajira.txt

*ABDULFATAH*





Na


Fateemah S Umar, Jajira




PAGE 7-8






_____________ party na murnar cikar ta sati d'aya a gidan Abdulfatah,
DJ suka sa anata rawa maza da mata ga kayan ciye-ciye dana lashe-lashe kowa yana kaiwa ka k'a warta Nuratu ce taja hannun ta suka shiga d'aki ta na murmushi ta ce


"Tun jiya Alhaji Sani yake kiran wayata wai lafiya baya samunki, kawai saina ce masa mahaifin ki ne bashi da lafiya a k'auye kinje duba shi kuma ba network a k'auyan."




"Hmmm wallahi Nuratu na gaji da auran Abdulfatah ga ba d'aya baya zama a gida gashi yadda nake zaton zan juyashi abun ya gagara, wulak'an tani ma yakeyi son rasa."




Da fata Nuratu ta yi ta ce


"Wallahi duk abun da yake faruwa ke kika so kinaji fa Malamin da mukaje gurin sa ya ce ko bayan biki ki koma a cigaba da baki temako sabuda wannan mijin naki taurin kai gareshi."


Ajiyar zuciya ta sauke ta ce


"Yanzu yau she zan samu lokacin da zamu koma."


"Duk randa kika shirya yana fita office kema ki fito mu tafi."


"To k'awata nagode."


Daga haka suka fito falon nan aka k'ara sakin kid'a shiga Mufida ta yi tana rawa da ita da k'awayan nata Maza da Mata.




Parking ya yi a harabar gidan sautin kid'an da yakeji na yau yafi na ko yaushe ga hayaniya dayake taji acikin gidan,


Fitowa ya yi ya kira Baba me gadi ya ce


"Baba suwaye suka zo gidan nan bayan na fita?"


"Kana fita Hajiya ta fito ta ce na siyo mata lemuka, nace ba akwai a gidan ba ta ce ba dashi zatayi anfani ba, na amsa na siyo shine naga k'awar ta tazo suna ta shiri harda me DJ aka d'auko duk motocin da ka gani a waje na maza ne da mata da suka zo gidan nan, d'azu na fito naji wata a cikin 'yammata da sukazo tana cewa wai party takeyi na cikarta sati a gidan mijinta."




Murmushin ta kaici Abdulfatah yayi ya ce
"Okay nagode Baba."


Daga haka ya hashiga motar sa ya fice daga gidan dan yasan idai ya shiga raine zai b'aci gara ya rabu dasu su gama haukar su.




Islam kuwa tun ran da ta had'u da Sahal,
Soyayya me k'arfi ta shiga tsaka nin su kulum suna mak'ale a waya
Yauma tana Hospital ta na rike da wayarta tana ta sheka dariya da masoyin nata




Daga can b'agaran ya ce


"Gaskiya na matsu naga munyi aure Baby na."


Murmushi ta yi ta ce


"In banda abunka My yaushe muka had'uma da kake zancan aure."


"Hmmm bakisan abun da nakeji bane shiyasa kika ce haka amma inaji a jikina kamar kwace mun ke za'ayi shi yasa na keso nayi nai wuf da ke."




Dariya sosai Islam ta yi ta ce


"Allah sarki My idai ina raye bazan auri kowa ba sai kai."


Ajiyar zuciya ya yi ya ce


"To Allah yasa."


"Ameen My."


Nan suka ciga ba da hirar su ta Soyayya.




Mama ce zaune ta na kalon Abdulfatah ta ce


"Ya naga ka dawo bayan kace ka gaji gida zaka tafi."




Kai ya sosa ya ce


"Am da na tafi kuma sai na tuna ma ta na da baki shine na dawo nayi wanka a nan."




Ido Mama ta kura masa ta na son gano wani abu dan daga ganin yanayin sa ransa a b'aca yake,


"To ina ruwan ka da baki ba gidan ka bane."


"Eh amma banaso na takura su."


"To shikenan kaje kayi wankan a d'akin Abdussamad."


"To Mama"


Ya ce ya mik'e ya fice ranshi ba dad'i.






Badan zai iya wankan ba ya shiga d'akin Abdussamad ya kwanta ranshi ya na suya,
Mufida ta gama raina shi ta maida shi wani sauna shashasha wanda bashida iko da gidan sa amma da sannu zai gyara mata zama.




Ranar Abdulfatah bai kwana a gidan ba Hotel ya kama yai kwanciyar sa.


Bayan kwana biyu


Mama ta kira Sara ta ce tazo ta kaita gidan Abdulfatah tunda akayi auran bata tab'a zuwa ba,
Shirya wa sukayi zasu tafi.


Ammi ta fito same su a falo ta ce


"Har kun shirya?"


"Eh Ammi."


Mama ta ce tana murmushi,


"To idan kunje Ku gaida Mufida, Allah ya tsare."


"Ameen, zataji in sha Allah."


Nan suka fice


Abdulmalik ne ya d'auke su a motar sa ya kai su,


A kofar gidan ya tsaya ya ce


"Mama nidai zan juya bazan shiga ba anjima kad'an zan zo na d'auke ku."


"To Allah ya tsare."


Maman Kaduna ta ce


Suka shiga gidan da Sara.




Salama suka ringayi amma shiru har suka gaji suka zauna a parlour,


Sun jima a zaune amma bata fito ba Sarah ta kali Mama ta ce


"Bari na shiga na mata magana muna zaune."


"A'a ki rabu da ita ko bacci takeyi."






Shiru Sarah tayi suka cigaba da zama har kusan minti talatin amma shiru har Abdulmalik ya kira ya ce yazo zai mai dasu tunda ganin gida suka zoyi,




A fusace Sarah ta ce


"Gaskiya Mama nagaji kamar ba mutum acikin gidan nan taya zamuta jiranta ta fito tak'i fitowa nidai tafiya zanyi Islamiyya zani."




Murmushi Mama ta yi ta ce


"Idan bazaki juraba kije Abdulmalik ya mai dake ki tafi makaranta ya dawo ya d'auke ni."


Mik'ewa ta yi ta ce ta tafi,


Sarah bata fi miniti 3 da fita ba sai Mama ta ji takun sakowa daga bene anata shek'a dariya,


Gaban Mufida fad'uwa ya yi da taga Mama a zaune bata santa a zahiri ba amma ta santa a hoto tunda Abdulfatah yana nuna mata Maman,




Amma da yake 'yar duniya ce saita mazai saida ta raka bakwanta har waje san-nan ta dawo tana hura hanci ta ce,


"Wace iriyar bakuwa nayi wadda bata iya salama ba."


Ko d'agowa kasayi Mama ta yi sabuda bak'in ciki da b'acin rai,
Jitake dama tabi Sarah sun tafi tare da wannan b'acin ran da ta gani.


Muryar Mufida taji tana cewa


"To koma wace ta gaba tar da kanta ban gane ta ba."


Mik'ewa Maman Kaduna tayi ta ce


"Duk da nasan baki tab'a ganina ba amma inda ke 'yar arziki ce to bazaki kali kwayar idona ki ringa tanbaya ta ni wace ba ko na shigo ba Salama, amma dama Hausawa sunce d'anku ne mai jawa uwarsa jifa."


Tana gama fad'in haka tafi ce daga gidan


Da kalo banza Mufida ta bita tai haye warta sama.




Mama na fita ta fara tafiya a k'afarta dan bata san ida ta dosaba sabuda b'acin rai tunani kawai takeyi a ina Abdulfatah ya d'ako wan-nan mara tarbiyar mara kunya,


Bataji kunyar ta ganta da wani a gidan ba amma harda ci mata fuska ita da gidan d'anta.




Tarine ya fara sarketa a hanya ta zauna a wanu dakali tana ta tarin,


Amma tak'i denawa nufashin ta ya fara sarkewa lokaci duda Asumarta ta tashi ta ringa kokawar yin nufashi harta fara galab'ai ta ta tafi luuuu zata zube a gurin.............!






*Wannan* *litafi* *na* *ABDULFATAH* *na* *kud'ine* *me* *son* *karan* *tawa* *zai* *biya* #200 *kacal*
*Dan* *karin* *bayani* *zaku* *iya* *tuntub'ata* *ta* *WhatsApp* *number* 08166077167




COMMENTS
AND
SHARE








by
*XAHRA*





*ABDULFATAH*





Na


Fateemah S Umar, Jajira




PAGE 9-10






_____________ Jikin wata yarinya ta fad'a cikin tashin hankali yarinyar take cewa,
"Inalilahi wa'ina ilaihirraji'un sannu baiwar Allah."


Ganin kamar me asuma ce yasa ta fara laluba jakarta ko zata samu abuda suke shak'a, cikin sa'a kuwa taga inhelar da temakon ta Mama ta ringa shak'a har nunfashin ta ya soma dai-dai ta, ajikin budurwar ta saki baccin wahala,




Rasa yadda zatayi da matar tayi kawai dabara ta fad'o mata takira zaro wayar ta takira wata number,


Salama tayi aka amsa sannan ta ce


"My kana ina na had'u da wata mata Asumar ta ta tashi kuma yanzu tayi bacci a jikina na rasa ya zanyi da ita."


"Okay gani nan kina dai-dai ina?"




"Ina layin su Sajida."


Ba'a d'au lokaci ba sai gashi ya zo a d'an sahun sa da temakon sa suka sa Mama a babur d'in ya tafi dasu Asibiti,




Bayan suje na Asibin ne an duba Mama an bata temakon da ya dace suna zaune da ita, ta bud'e ido a hankali tana salati,


Da hanzari Islam ta matsa kusa da ita tana mata sannu amsawa ta yi ta ce


"Yarinya a ina nake?"


Nan Islam ta bata labarin abun da ya faru duk da Maman tana cikin mawuyacin hali ta tuna abun da ya faru tayi murmushi ts ce


"Nagode baiwar Allah."


Itama Islam Murmushi ta yi ta ce


"Ayyah bakomai Hajiya ki d'auka 'yar cikin ki ce tamiki ba bare ba."


Ajiyar zuciya Mama tayi ta kalon Islam tanajin dad'i yarinyar tana da tarbiya irin ta ya dace ta samu matsayi suruka ba Mufida ba,




Wayar Mama ce ta fara ruri Islam ta d'ako ta mik'o mata,


Maman ta mik'e zaune da kanta ta d'aga wayar,


"Hello Mama kina ina mu dawo da Sarah amma bakya gidan."




"Ina Hospital Abdulmalik matar Abdulfatah ba matar kwarai ba ce."


"Inalilahi kiyi hakuri Mama gamunan isuwa wace Hospital kike?"


Tan bayar Islam Mama tayi wanda tunda taji an ambaci sunan Abdulfatah gaban ta yake fad'uwa, ta fad'a mata sunan Asibitin ita kuma ta sanar da Abdulmalik,


Mintina kad'an suka k'aso,


Godiya sosai suka yiwa Islam da Sahal har Sarah ta amshi number Islam d'in dan suringa zumunci.




Salama suka musu suka tafi gida.






Zaune take ta kurawa Abdulfatah ido shima ita ya kalo tayi ajiyar zuciya ta ce


"Gaskiya na gaji da ga fara sa banga k'ahoba Abdulfatah ya da ce nasan matsayi na a gurin ka."


Murmushi ya yi ya ce


"Marwa kenan zaki gani very soon."


"Na gani ai da kayi aure ka barni, to wallahi idan kayi aure kana ganin na rabuda kai ban tanka ba to karka k'ara yaudara ta in bahaka ba kasan wace Marwa dan wallahi saina kashe duk wadda tayi yinkurin shiga tsakanina da kai."








Murmushi me k'aya tarwa ya yi ya ce


"Kinsan ina sonki Marwa tun farko Kyan Mufida ne ya sa naji ina son auran ta amma yan ba abunda zai shiga tsakanin mu."


Harara ta watsa masa ta ce


"A bayama haka kake cewa ba son ta kakeba ita take son ka amma sai bikin ka naji a gari, yanzu yaushe zamuyi aure?"


Idon sa na kanta ya ce


"Yanzu bazan tukari Abba da zancan aure ba tunda wata na d'aya kacal da aure amma bayan wasu 'yan watani zan masa maganar auran ki."


"Hmmmm Abdulfatah kenan kar kamun dad'in baki kamar na baya kasani ni ba kawar lasa ba ce na fi k'arfin raini yanzu."


Ido ya lumshe ya ce


"Ki daina zargin zan rabu da ke Marwa ki sa a ranki kin malaki Abdulfatah na kine ke kad'ai."


Murmushi ta yi ta ce


"Ko wannan kucakar matar taka saita bar gidan zan shiga."


Magana zaiyi kira ya shigo wayar sa,


Abdulmalik ne dan haka ya d'auka ya kara a kune.




Salama Abdulmalik ya yi Abdulfatah ya amsa yana tanbayar lafiya, nan Abdul malik yake sanar dashi abunda ya ke faruwa,


Da sauri Abdulfatah ya mik'e ya cewa Marwa,


"Marwa Mama ba lafiya tana Hospital Asumar ta ta tashi."


Ya tsina fuska ta yi ta ce


"Ayyah ka mata sannu."


Bai jira ta k'ara cewa komai ba yabar gurin da sauri.


Hospital d'in yaje yaga Mama ma a zaune ajiyar zuciya ya yi yaje kusa da ita ya zauna ya kamo hannun ta ya ce


"Sannu Mama ya jikin naki?"


"Da sauki."


Kalon Sarah ya yi ya ce


"Me yasa baku kaita Hospital d'in na ba? ku kirani ba kuka kawo ta nan?"


Shiru ta yi kanta a kasa ta na raba ido,




Ya bud'e baki zai fara fad'a Mama ta ce


"Ba laifin su bane nice na ce akawo ni nan kar a ta dama da hankali."


Ajiyar zuciya ya sauke ya ce


"Da kun sanar dani to da nan basu baki kulawa yadda ya dace ba fa?"


Murmushi Maman Kaduna ta yi ta ce


"To in sha Allah nan gaba zan sa su kira mun kai."


"Allah ya tsare Mama na ya kikaye gaba."


"Ameen Abdulfatah."


Nan suka ciga ba da hira har Doctor yazo ya bawa Mama Salama dan ta warware.




Sai da Abdulfatah ya kaisu gida sannan ya wuce nashi gidan.


Sarah ce ta shiga d'akin Mama ta ajiye mata tea d'in da ta had'o mata, ta zauna kusa da ita ta ce


"Amma Mama meyasa baki sanar da Yaya Abdul gaskiyar abun da ya faru?"


Murmushi Mama ta yi ta ce


"Sabuda nasan halin Abdulfatah da zuciyar da yake da ita zai iya zuwa yai wa 'yar mutane ila akan wannan abun amma na bata lokaci zan d'au mataki da kaina dan bazan zuba ido d'ana yana da tarbiya ya auri mara tarbiya ta b'ata mana zuri'a da 'ya'ya marasa tarbiya ba."




"Hakane Mama amma wana mataki zaki d'auka?"


"Bazan raba Abdulfatah da matar sa ba amma zai k'ara aure dole na nemo mata me tarbiya wadda zata iya gyara masa gidan sa ta haifa masa yara masu tarbiya."




Ajiyar zuciya Sarah tayi ta ce
" kuma shi Yaya Abdul zai yarda ya yi aure yanzu? bayan bai jima da yin aure ba."




"Kinsan Abdulfatah duk abun da muke so da Abban ku idai bai sab'a shari'a ba to zaiyi shi."


"Hakane Mama."


Nan suka ciga ba da hira da yaba kirki irin na Islam.


Mufida tunda ta ga Mama ta fita hankalin ta ya tashi dan ta na tsoran ta fad'awa Abdulfatah a samu matsala.




Ta na zaune taji shigowar sa gidan a tsorace ta mik'e ta na zare ido ta ce ................!






Free page ya k'are duk meso ya karan ta wannan litafi har k'ar she zai biya #200 ta wannan number 08166077167






*Wannan* *litafi* *na* *ABDULFATAH* *na* *kud'ine* *me* *son* *karan* *tawa* *zai* *biya* #200 *kacal*
*Dan* *karin* *bayani* *zaku* *iya* *tuntub'ata* *ta* *WhatsApp* *number* 08166077167




COMMENTS
AND
SHARE








by
*XAHRA*



*ABDULFATAH*





Na


Fateemah S Umar, Jajira




PAGE 11-12






_____________ "Am ka kadawo." Ido ya zuba mata ya na mamakin abun da ya rud'ata haka, tsaki kawai ya ja ya haye sama ya barta a gurin.


Ganin beyi magana ba tayi ajiyar zuciya ta koma kan kujera ta zauna, aranta ta ce ko Mama bata fad'a masa ta zo ba?
"Koma mene tunda na tsira shikenan"


A fili tayi maganar dai-dai lokacin da ya sako, tsayawa ya yi da mamaki ya ce


"Kodai wani abun kika sha?"


Harara ta watsa masa ta mik'e ta shige d'akin ta.


Da kallo ya bita ya na mamakin ya akayi Mufida ta zama mara kunya, kafin ayi auransu ko magana bata agawa sama da tasa ko da kuwa zai huni a kanta yana mata fa a amma yanzu har tsaki ta ke masa ko ta harare sa kamar ba mijinta ba ta huce.


Girgiza kai kawai ya yi ya shiga kitchen dan ya ora abunda zai ci.






Dariya ta ke ta yi tana rike da waya sai kokawar sa talami take,
Ummi na tsaye tana kallon ta ta girgiza kai ta ce


"Dan Allah ayi hakuri da wayar nan a bari agama shirin tukuna."


Sahal dake bawa Islam labari yana jin muryar Ummi yai sauri ya kashe wayar.


Islam ta turo baki ta ce


"Kai Ummi ya jiki fa."


"To seme Sahal in bakona ne ko me?"


"Duk da haka Ummi da ki....!"


Da uwa Ummi tai mata ta ce


"Nayi maganar yanzu Asibiti zaki ta fi amma kinfi awa guda kina shiri bayine kawai bakije da wayar nan ba, kuma sai a hanani fad'ar gaskiya."


Takalmin tasaka ta rataya jakar ta ta ce


"To kiyi hakuri nidai na tafi."


"Allah ya tsare uwata."


"Ameen Ummina."






Fita Islam ta yi ta samu babur ta huce gurin aiki.


A can ma Sahal yana ta kiranta amma ta i auka sabuda tasan in dai ta aga bazai barta ta yi aiki ba kuma shima bazai fita ba.




Mi ewa ta yi ta shiga office in Doctor Rukayya.


Salama ta yi, Doctor Rukayya ta amsa da fara'a, zama Islam ta yi ta ce
"Dama zuwa na yi mu gaisa yau ban shigo mun gaisa ba."


"Gaskiya ne ya gida? Ya Ummi?"


"Lafiya alau muke aunty Rukayya."


"Masha Allah haka akeso, jiya na baki wata peppers ko ki ajiye mun."


"Eh anyi haka amma kiyi hakuri wallahi na manta ta a gida."


"Ayyah gaskiya banji da i ba inda hali ki tashi ki gida ki kawota sabuda ta Doctor Abdul kuma yanzu zaiyi anfani da ita."


Ido Islam ta zaro ta ce


"Meyasa baki fa a mun tun jiya tashi ce ba da ban ansaba wallahi."


"Nidai ki daure kije ki ako."


Tashi Islam ta yi ta fita da sauri.


Suhal ta kira a waya ta ce tayi mantuwa ya zo ya maida ita gida.


Ba'a au wani lokaci ba yazo suka koma gida,
Takadun ta ako suka dawo Asibiti.




Fi towa ta yi daga cikin adaidaitar, shima Suhal fitowa ya yi ya matso kusa da ita ya ce


"Gaskiya mukayi aure daina wannan aikin zakiyi."


Murmushi ta yi sannan ta ce


"Nima haka nake tunani bazan ha a aure da aiki ba."


"Kinyi tunani me kyau Baby."


Dariya ta yi ta ce


"Yanzu dai ka tafi aikin ka Sweetie. "


"To Baby ki kula da kanki."
"In sha Allah."


Ya koma ya tashi babur in yabar gurin Islam na tsaye ta na ta aga masa hannu har ya acewa ganin ta.


Duk abuda ke faruwa Abdulfatah yana cikin motar sa ya na kalon su.




Hakan nan ya ji ranshi ya aci da kamar zai share sai ya fito daga motar ya nufo ida ta ke,


Ta juyo zata shiga ciki ta yi ido hu u da shi yana jifan ta da mugun kallo.


Jikinta ne ya auki rawa za ta yi magana ta ji ya ce


"Wato iskan cin naki ya huce a waje har Hospital ina kike kawo gardawa ko?"


Ran Islam ne ya aci bata ta a tanka masa ba sai yau taji baza ta iya rabuwa dashi ba.


Cikin acin rai ta ce


"Ya isheka ai batani da kakeyi ba ci kake bani ba sha kake bani ba amma ka takurawa rayuwa ta kulum cikin askan tani kake ka ta a kamani da wani ne da zaka ringa ai batani ni nayi kaina a talaka ko ba a da ka tsaneni duk wannan abun sabuda ina aikine a ar ashin ka ne ko to in sha Allah na daina har abada bazan sake dawomaka Hospital ba arziki na Allah ne muma wata rana zai azur tamu."




Tana maganar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login