Showing 18001 words to 21000 words out of 27403 words

Chapter 7 - ABDULFATAH by Fatima S Umar Jajira.txt

ba ne."


Shiru Abdulfatah ya yi dan yasan indai ya cigaba da biyewa Doctor Salis to zai kashi ya baroshi.


Kamar Dr Salis yasan me yake ayanawa ya ce


"Nasan cewa zakayi cutar ka zanyi, ni temakon ka zanyi bazaka gane hakan ba sai nan gaba."


Shiga ala Abdulfatah bai ara cewa ba, ya share Dr Salis.


Shikuwa Dr Salis guri ya samu ya ringa shiryawa Abdulfatah zance iri-iri har Abdulfatah ya gaji ya ce


"Wai dan Allah mene damuwarka akan tsakanina da iyalina?"


"Hmm kada ka manta ni me aunar ka ne kuma Amininka na ha i a bazan zuba ido kana ganin kashi da rana ka takaba amma tunda baka so shikenan na bari, amma zan maka tunatarwa guda aya ko ba ha in Soyayya a tsakanin ku da Islam akwai na aure kuma idan kayi watsi da su da gangan kaida uban gijin daya haliceka."


Yana murmushi ya mi e ya ce


"Na barka lafiya aboki."


Ya fice daga office in ya bar Abdulfatah cikin damuwa, kifa kansa ya yi a jikin table yana sauke ajiyar zuciya akai-akai yana jujjuwa magan ganun Dr Salis anya ba wayo yake so ya masaba?


Ya tanbayi kansa, amsar da zuciyar sa ta bashi shine
To mene hurumin ko ala ar Dr Salis da matarka ila da gasken shawara yake baka.


Da ya gaji da juya zancan a cikin ransa sai ya mi e ya fice, ya cigaba da zagaye yana duba marasa lafiya da yake da su.




Sai yamma likis ya nufi gida yana tafiya yana juya magan ganun Dr Salis yana so ya share zancan daga ransa amma ya kasa, can asan zuciyar sa cike yake da fargaba da baisan ta mece ba.


Wata mota yaga tasha gabansa yai saurin taka burki amma motar ta i tsayawa ga ba aya burkin motar ya shanye, salati ya saka yana ambatan sunan Allah, mumunan karo sukayi da motar dage gabansa wanda ya haifar da molewar motar Abdulfatah da shigarsa mawuyacin hali.




Jama'a ne suka kawo aukin gaggawa, aka kashe su akayi Asibiti dasu.


Wayar sa aka duba ba wanda yasan pin in wayar dan haka aka ajiyeta ko Allah zaisa wani ya kira.


Wani daga cikin wanda suka kawosu Hospital ne ya ce
"Nifa naga ID cart in sa likitane."


ayan ne da sauri ya ce
"Masha Allah, ako mu nuna musu ko sunsan inda yake aiki."


ID cart in suka nunawa wani likita da suka gani, cike da mamaki ya ce


"Wannan ai ID cart in Doctor Abdul ne, yana ina?"


Nuna masa inda aka shiga da Abdulfatah sukayi ya shiga da sauri.


Ganin halin da Abdulfatah yake ciki yasa ya kira Abba ya sanar dashi halin da Abdulfatah yake ciki, da yake ya san Abdulfatah sosai abokin sane nan suka shiga bashi taimakon da ya dace.




Mama ce a zaune Sarah na zuba mata tuwan shinkafa ta ce
"Yauwa idan kin gama zubawa kije kiyi Sallah Magrib sai kizo lokacin yayan ku ya koma gida sai na kirashi ya ha aki da Islam."


"Yauwa Mama nagode."
Cikin zumu i ta kamala zubawa ta ajiye gaban Mama zata fita suka kusa karo da Abba, gaban tane ya fa i gani yanayin da Abba yake ciki har zata huce taji ya ce


"Abdulfatah fa yana Hospital yanzu ya samu hatsari a hanyarshi ta komawa gida."


"Inalilahi wa'ina ilaihirraji'un!"


Abuda Mama da Sarah suka furta a tare cike da tashin hankali kenan.


Salatin sune ya jawo hankalin Ammi itama tazo ta tadda wannan mumunan labari.


Nan Abba ya kwashe su suka tafi Asibiti da aka kai Abdulfatah.


Lokacin da sukaje angama bashi duk wata kulawa amma yana halin suma a lokacin.


Abba ne yaje gun Doctor nan ya sanar dashi matsalar bamai yawa ba ce yadai samu karaya a hannun hagu sai kananan raunika da baza'a rasaba, godiya Abba ya masa ya fito.


Mama da kanta tasa Abdulmalik ya je gida ya tawo mata da matan sa dan suga halin da yake ciki.




Islam ta kamala Dinner ta yi wanka tasa wata atanfa pink me flowers green tayi kyau sosai, ta sako dan aukan nata abuncin taji salamar Abdulmalik, gaban tane yai wata irin fa uwa a fili ta ce


"Hasbunallahu wani'imal wakil."


Dakewa ta yi ta amsa salamar tashi ya shigo ya sakar mata murmushi, itama ta maida masa murmushin nasa.




"Barka da dare aunty Islam."


Kunya taji babba kamar Abdulmalik yake ce mata aunty, dukawa ta yi ta gaidashi ya amsa yana mamaki a ranshi halin dattaku irin na Islam ba kamar Mufida tijarariya ba.
Yana tsaka da wannan tunani hakimar ta fito dan ganin wanda ya zo, baki ta ta e ta ce


"Sabuda kun aura masa wannan kucakar har kuka samu damar yimana sitiri a gida dama sabuda haka kuka takura masa sai ya aurota ko."


Ta ri e ugu tana zaro masa ido, kallon sama da asa ya mata ya ce


"Na yarda duk inda shashasha ya ke baya sauya halin sa ke yanzu har wata tsiyar kuke da ita da zakiyi mana gori muna zuwa gidan nan ko mun muki kama da matsiyata."


"Aiga ar matsiyata nan."
Ta nuna Islam.


Tsaki yaja ya ce
"Kece babbar matsiya ciya wanda batasan mutunci ba."


Wata uwar ashar Mufida ta gunduma, Abdulmalik yaga abun nata ba hankali a ciki ya shareta ya dubi Islam da taketa bashi hakuri ya ce


"Jeki sako hijab in ki, kizo muje Hospital Ya Abdulfatah ba lafiya."


Dafe iji Islam ta yi tana karanto duk addu'ar da tazo bakin ta, hakuri Abdulmalik ya ringa bata ya rarrasheta ta sako hijab suka tafi, ita kuwa Mufida banda ura ashar ba abunda takeyi.




Wayar ta da take ruri ta auka ta kara a kune tare da cewa


"Hello Yunus ya akayi?"


Daga can Yunus ya ce


"Hajiya Marwa aiki ya kamala kamar yadda kika bu ata mun cire burkin motar sa yanzu haka ya samu mumunan hatsari yana Hospital, kamar yadda na fa a miki a farko bazan shiga wannan abun na kwana a cikiba sauran aikin kya arasa da kanki."


Murmushi ta yi ta ce


"Ai kayi me wuyar Yunus nagode sai kaji sa o."


Nan sukayi salama ya kashe wayar.


Wata number ta lalubo ta tura kora, bugu biyu aka auka cikin isa ta ce
"Yanzu haka yana Hospital in ku tabbata kun ilata munshi sosai."


"Angama Hajiya."


"Nasan zaku iya ai kawai ku kula sosai."
"To Hajiya."


Ajiye wayar tayi ta fashe da dariya ta ce


"Ka gama yawo ABDULFATAH.............!








By
*XAHRA*





*ABDULFATAH*



Na


Fatima S Umar Jajira




PAGE 41-42




___________ A daran an uwa da abokan arziki na Abdulfatah suka halara a Asibitin kowa yana jimamin halin da Abdulfatah ya tsinci kansa a ciki.


Da dare ya yi Duk suka fara tafiya gida Mama ta ce tunda har yanzu bai farko ba abar Abdulmalik ko Abdussamad wani ya zauna dashi tunda shi Abba bashida cikakiyar lafiya.


Doctor Salis ne ya ce zai zauna su kwana da Abdussamad sauran su tafi gida. Haka kuwa akayi harda Islam suka wuce gidan su.




Koda suka koma gida Mama taso surukar tata ta kwana da ita amma sabuda kara irin ta Islam ba ta ce a'a ba kawai sai ta ce bari ta dawo taje gurin Sarah ta turo ta gun Mama ta ce tare zasu kwana, murmushi kawa Mama ta yi ta ce


"Allah ya tashe mu lafiya."
"Amin Mama."


Sarah ta ce ta fito suka kwana da Islam.


Washe gari

Tun kafin su Mama su tashi Islam ta gama aikin gidan ta ha a bearkfast ta ajiyewa su Mama.


Sarah ce ta fara tashi taga duk aikin da Islam ta yi ta dubi agogo taga 09:30am cike da mamaki ta ce


"Yanzu har kin tashi kinyi duka wannan aikin? Kekuwa tun yaushe kika tashi?"


Murmushi Islam tayi ta ce


"Kudai zan tanbayi meyasa bakwa tashi da wuri? Nifa a gida idan nayi salar Asuba bana komawa, amma ku sai kukai Goma kuna bacci."


"Sannu da o ari aunty Islam, amma nasan yanzu Mama ta tashi sabuda ita indai wani abu mara da i ya faru to bata iya bacci sosai."


"Ayyah Allah sarki Mama ta."


Dariya Sarah ta yi ta ce
"Masu Mama manya."


Harararta Islam ta yi zatayi magana sukaji salamar Ammi, amsawa sukayi Islam ta du a har asa ta gaida ita Ammi ta amsa tana murmushin jin da i a ranta ta ce, ashe Mama ita tasan abunda ta hango ta dage akan auran nan, lalai wannan ita ce sirika ta gari a fili kuma ta ce


"Sannu da o ari Islam kin gyare mana gidan."


Kanta a asa ta ce


"Tare mukayi aikin ta Sarah ai."


Baki Ammi ta ri e ta ce


"Wannan malalaciyar ce zata iya wani abun arziki ai kidaina fa in hakama dan ki kareta kowa yasan halin ta a gidan nan."


Baki Sarah ta turo, Ammi ta harareta ta ce


"Bari na gida naga Mama naga bata fitoba."


"A fito lafiya Ammi."


Islam ta ce, Ammi ta mata murmushi ta shiga akin Mamai.


Akan gado ta tadda Mama tana kwance da alama bacci ta keyi girgiza kai Ammi ta yi ta juya dan tasan baccin dare ne Mama ba ta yi ba ta keyin na safiya.




Sai gurin 11 Mama ta tashi itama ta yiba da abunda Islam ta yi nan ta shirya bayan su Islam sun shirya abunci suka huce Asibitin.




Lokacin da sukaje Abdulfatah ya farka amma bacci yakeyi, duk sunyi hamda ga Allah da abun yazowa Abdulfatah da sau i.




A fusace ta ke kallon sa ta ce
"Kasan baza ka iya aikin nan ba kace zakayi?"


"Kiyi hakuri Hajiya jiya akwai abun....!"


Tsawa da daka masa ta ce


"Ya isheni haka, banason jin komai, tunda bazaka iya ba zan nemi wani."


"A'a Hajiya Marwa baza ayi haka ba kiyi hakuri zan yi abunda kika ce yau da dare."


Tsaki taja ta fice daga gurin ko kallon arziki bata masa ba.




"Hello awata kina ina? inason ganin ki yanzu."


Daga can agaran Nuratu ta ce
"Ina gida, me ya faru."


"Kizo gida na yanzu dan Allah."


Saida Nuratu ta yi jimmm sannan ta ce


"Okay gani nan zuwa."
Ta kashe wayar


Ba'a jima sosai ba Nuratu ta zo gidan, ko Salama babu ta shiga gidan tana wani yatsine fuska a ranta ta ce
Zamanki yazo arshe a gidan nan Mufida.


Mufida ce ta fito taganta ta washe baki ta ce


"Lah harkin araso, sannu dazuwa."


"Yauwa."


Nuratu ta fa a a ta ai ce.
Guri suka samu suka zauna nan Mufida ta sanar da ita halin da Abdulfatah yake ciki yanzu ta ara da cewa


"Nifa da na share su daga shi har dangin nasa da matar daya kwaso su arata gaba aya dan ba zuwa zanyi duba shi ba."


Murmushin mugunta Nuratu ta yi ta ce


"Kiyi dai-dai tunda shima ba mutunci gare shi ba, shawara ma kawai ki fito mu sha ata kan ya dawo daga jiyar tasa."


"Allah ko?"
"Eh mana."


Dariya suka saka a tare suka tafa.


Nan da nan Mufida ta ha o kayanta suka fice daga gidan.




Da dare Abdulfatah ya tashi ya gane kowa, dan haka sunyi farin ciki sosai, Doctor Salis aka kira Matar sa tana na kuda dan haka ya tafi gida.


Da zasu ta fi Mama ta ce


"Tunda Doctor Salis ya tafi ina ganin kawai abar Abdulmalik da Abdussamad su zauna a gurin sa."


Abdulfatah da yake kwance ya na jinta baiyi magana ba sai ya kamo hannun Abba, Abba ya kaleshi yaga ya girgiza masa kai, murmushi ya yi ya kali Mama ya ce


"Mara lafiyar da kansa ya ce baya wanda kika za a masa wata ila Matar sa ya koso a kusa da shi."


Murmushi Mama ta yi ta ce


"To shikenan tunda shi ka ai ne ku Asibiti naga sunada kulawa sosai tunda ku ine yake aiki shikenan sai ta zauna dashi."


Wani irin tu u i Abdulfatah ya ji a ransa da hanzari ya bu e baki ya yi magana, amma duk basu ji abunda ya ce ba suka kama hanya suka fice, rintse ido ya yi cikin ta kai ci, sabuda gudun raini ya ce baya so abar masa su Abdulmalik, yaso Abba ne zai zauna dashi, sai gashi an barmasa wannan jaririyar ko me zata iya tsinana masa oho.


Ita ma Islam kuka ne kawai ba tayi ba dan ita a yanzu kallon Abdulfatah tsorata ta ya ke sabuda irin kallon raini da yake mata.


02:00am wasu matasa kimanin su shida suka hauri Hospital in fuskokin su a rufe ba wanda zai gane su waye.


Kai tsaye akin da Abdulfatah ya ke suka shiga sunyi sa'a a bu e yake dan azu har Islam ta rufe Abdulfatah yasata dole ta bu e ta.


Tana zaune akan daduma taji mutane a cikin akin da hanzari ta mi e zata yi ihu wani ya rike mata baki hannun sa ta kalla taga yatsu 4 gareshi tunawa ta yi da wanda suka saceta tabas taga me yatsu 4 a cikin su, tsoran ta ne ya aru ganin sunyi kan Abdulfatah da yake kwance yana bacci da wu a sun sata wuyan shi ai batasan sanda ta...........!










By
*XAHRA*





*ABDULFATAH*





Na


Fatima S Umar Jajira




PAGE 43-44




_____________ Ta hanka e wanda ya ri eta ba ta kwala ihu da arfi ta nufi inda Abdulfatah ya ke, ganin haka wanda ya ako wu ar ya juya ya saita wuyan Abdulfatah ya fara o arin yankashi, ya kai wu ar wuyansa Islam tai saurin saka hannuta, yanka a maimakon wuyan Abdulfatah.




Azabar da tajine yasa ta ara sakin wata razananiyar ara ta janye hannunta wanda yake ta zubar da jini ka ba a autawa tana wani razanan nan kuka.




Wanda ya fara ri eta ya ce
"Oga yarinyar nan fa ta tona mana asiri gara tun kan azo a tadamu mu fece."


Kai Ogan ya gyada suka nufi hanyar waje, amma me? Karo sukayi da police da suke gadin Hospital in, nan fa ido ya raina fata, wannan Police suka tisa eyarsu sukayi gaba.


Wasu daga ciki suka dawo gurin su Islam, da sukaga yankan hannun ta babba ne basu kira Nurses in da sukwana suna aiki, sai suka kira babban likintan Asibitin.






Kuka takeyi sosai amma ta iyarda ya fito fili wai dan kar Abdulfatah ya farka, lokacin da likitan ya araso yaga raunin saida ya mata inki a hannun sannan ya bata magani harda na bacci dana rake zugi ya tafi.




Ta jima a tsaye tana safa da marwa da alurar kashe ciwon da aka mata ta saketa tana so tayi kuka amma bataso ta tashi Abdulfatah, haka ta ringa yarfa hannu har akayi Asuba ta samu tayi sallah a gurin da tayi sallah bacci ya auke ta.






Jin kamar ta yi bacci Abdulfatah ya bu e ido yana kallon inda take yama rasa me yakeji a zuciyar sa, tun ihun da tayi na farko ya tashi Allah bai bashi ikon motsawa ba amma yanajin komai lokacin da Doctor yazo ya duba ta komai ya sakeshi har bu e ido ya yi ya kalesu amma bai bari tasan ya tashiba sabuda yaga bata so ya tashi dan kartaji ba da i a ranta ya tashi shiyasa ya i bu e ido.






Tashi ya yi ya sako a hankali ya taka har inda take kwance, hannun sa me lafiyar yasa ya agota a hankali ya manta da jikin sa, zabi yaji jikin nata, ya girgiza kai ya matseta da hanun ya mi e da ita, kan gadon nasa ya orata ya rufe ta ya zauna gefan gadon, ya kamo hannun da aka yanke ta, gurin yayi zurfi sosai duk da anyi in a gurin kowa yana gani yasan babban yanka ne, kwatan tawa ya yi da wuyan sa, ajiyar zuciya ya sauke dan ya san da yanzu ya jima a kiyama. Ya jima yana kallon hannun kafin ya tashi ya lalla a ya yi sallah sannan ya koma inta yake zaune.
Idon sa a kanta yana mamakin jarumtar da sadaukar da ran da ta yi bacci ya yi awan gaba dashi.




Bugun ofar akin ne ya tashe shi, a hankali ya furta
"Waye?"


Muryar Abdulmalik ya ji ya ce
"Ni ne."


Tashi ya yi a hankali yana je ya bu e masa ofar ya shigo, ya ajiye abuncin da ya kawo akan table ya ce


"Yaya ina kwana."


"Lafiya."


"Ya jikin?"
Saida ya yatsine fuska ya ce
"Da sauki."


Kallon gadon ya yi ya ga Islam kwance da alamun batada lafiya da mamaki ya ce
"Yaya Islam bata da lafiya ne?"


Bai bashi amsa ta ya shiga bayi, alwala ya yo, Abdulmalik ya taimaka masa ya shin fi a masa dadduma ya yi Sallah, ya sa Abdulmalik ya zubo masa abunci ya yi bearkfast sannan ya ce


"Ina Mama?"
"Tana gida ta ce sai zuwa Azahar zata zo tunda Islam ta na nan."


Kallon inda ta ke ya yi sannan ya dawo ya dubi Abdulmalik ya ce


"Kira mun Abba."


Ba musu ya kira Abba ya mi a masa wayar, bayan sun gaisa da Abba ya masa sannu ya ce


"Abba akwai matsala fa."


"Subahanallah wace irin Marsala kuma Abdulfatah."


Dakewa ya yi ya ce


"Inda hali kuzo da Mama sai kuga abunda ya faru."
Bai jira cewar Abba ba ya katse wayar ya bawa Abdulmalik abar sa.




Ba'a wani jima ba su Abba suka zo Asibitin harda Ammi da Sarah.


Bayan sun gaisa yaga kowa sai kallon tuhuma ya ke masa cikin girma mawa ya ce


"Abba abaya na ta a sanar da kai akwai wadda na yiwa al awarin aure ko?"


"Gaskiya ne na tuna."


Ajiyar zuciya Abdulfatah ya yi sannan ya cigaba da magana


"To ita ce tunda ta ji nayi aure ta zata yau darar ta nayi ta ke tamun baraza na zata kashe Islam, da na auka fa a kawai takeyi bazata iya ba ashe da gaske ta ke" nan ya basu labarin abunda ya faru ranar bikin su da Islam ya ara da cewa, "hakan da tayi bai isheta ba shine ta turo a kwashe ni jiya" ya basu labarin abunda ya faru jiyan.


Salati gaba aya suka auka, ita kuwa Mama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login