Showing 24001 words to 27000 words out of 27403 words
Chapter 9 - ABDULFATAH by Fatima S Umar Jajira.txt
zata ce ba ya shige toilet.
Tana ganin ya shiga toilet ta fice abunta, Abdulfatah ma ya mugun raina mata hankali wai baya iya kwana shi kad'ai sai kace batasan gantalin da matarsa ta keyi ba zai raina mata hankali, ya gama azabtar da ita a waje nan kuma ya maida ita baiwa to bazata lamunta ba.
Dagonta ta haye tai kwanciyar ta hankali kwance.
Yana fitowa daga toilet ya ga babu ita, kai ya girgiza ya ciza lips in sa, lalai yarinyar nan ta gama raina shi, kwafa ya yi, ya sauya kaya zuwa na bacci sannan ya kashe komai na akin ya fice.
Sama ya haura akin Islam, lokacin da ya shiga akin nata tayi bacci dan haka bataji shigowarsa ba, maida kofar akin ya yi ya rufe, sannan ya haura gadon.
Fuskarta ya kurawa ido, bata da hasken fata amma kyakykyawa ce duk da bacci ta keyi amma batayi muni ba kuma a nutse take cib.
Tunawa ya yi da lokacin da yake wula anta ta a Hospital in kuma yau gata matsayin matarsa, ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya kai hannu kan fuskarta, da yake Islam bata da nauyin bacci tai saurin ware fararan idanunta akan fuskarsa.
A tsorace ta tashi zaune ya ha e rai ya ce
"Ba na sanar da ke cewa bana iya kwana ni kad'ai ba? Nace ki zauna a akina ki maye gurin Mufida, amma sabuda kin rainani shine kika sa afa kika futo ko?"
Kai ta girgiza masa cike da tsoro ta ce
"Allah ba haka bane, bana iya kwana da......!"
Sai kuma ta yi shiru, ya watsa mata harara ya ce
"Ai bazaki iya arasa maganar ki ba sabuda kinsan baki da gaskiya, in gaskiya ne ki sanar da su Mama bazaki iya kwana dani ba kar a auramiki ni, ko bake bace harda zama jinyata a Hospital?"
Shiru tayi takasa magana ya ce
"Tunda har baki iya kwana da mutum ba to karkiji komai daga yau zaki daina ki sama da kwana da wani a kusa da ke."
Duk yadda Islam ta so ya rabuda ita a wannan dare ya i yadda ta masa garda ma haka ya mata, tasha wahala har takai saida hankalin ta ya gushe ta daina fahimtar komai.
Lokacin da hankalin sa ya dawo jikinsa ne ya kula Islam tana halin suma, sai lokacin ya ji haushin kansa, meyasa ma ya biyewa zuciyar sa ya kusanci Islam yanzu, karfa raini ya shiga tsakanin su. Kauda wannan tunani ya yi a ransa ya fara bata taimakon gaggawa kasan cewarsa likitan mata bai shawala gurin bata kulawar da ta dace ba.
Har akayi kiran Asalatu Islam bata farka ba shikuwa wanka ya yi ya wuce masalaci.
Yana fita ta fara bu e idonta a hankali tana kallon akin abunda ya faru ne ya fara dawo mata, da sauri ta yinkura zata tashi amma takasa, komawa ta yi ta kwanta, tanaji har aka idar da Sallah a masalaci ta kasa motsi, hawaye ne kawai suke zarya a idanunta har ya shigo gidan ya tadda ita tanata kuka ya arasa inda ta ke kwance ya ce
"Ya isa kukan haka komai ya wuce ai."
maganar sa ma tsora ta ta takeyi tayi asa da kanta dan ko fuskarsa bata son gani murya na rawa ta ce
"Shikenan mutuwa zanyi na kasa tashi."
Ta bashi dariya ya yi murmushi ya ce
"Ba abuda zai sameki ki godewa Allah ma yariya da baki aruba."
Sautin kukan ta ta ara, dole tasa ya taimaka mata taje bayi ta yi wanka a zaune ta iya Sallah ga ciwo da kanta yake mata kan kace me zazzab'i ke zafi ya rufe ta.
Sosai ta bawa Abdulfatah tausayi tunawa ya yi da lokacin auran Mufida, sai yanzu yasan cewa mata suna suka tara bai ta a tunanin har yanzu akwai matan da suke da sauran mutunci ba sai yanzu, kalaman da ya ringa fa a mata lokacin da yaganta da Sahal suka ringa dawo masa, ya cije lips in sa yana tuna muzanta ta da ya ringayi dan ta kasance ba a ashe halinta yafi nasa haske ma tunda ta sadaukar da ranta akansa.
Tunanin da yake ne ya katse jin ana buga ofar gidan, a sanya ye ya mi e ya nufi ofar gidan.
Bu e wa ya yi da mamaki ya ke kallon..........!
By
*XAHRA*
*ABDULFATAH*
Na
Fatima S Umar Jajira
PAGE 51-52
____________ Doctor Salis, ya ce "lafiya kazo da sassafe haka."
Murmushi Dr ya yi ya ce
"Amma dai ko mene ka bani guri na zauna sai ku tatttauna ko."
Wuce wa ciki Abdulfatah ya yi Doctor Salis ya bi bayansa suka zauna a falo kafin Dr ya ce
"Abdulfatah ya jikin naka kuwa?"
"Da sauki."
"Allah ya sawake."
"Amin nagode."
"Am dama maganar zaman kotu da za'ayi gobe ne nace ya dace kaje da Islam sabuda ko bincike zai biyo ta kanku."
Girgiza kai Abdulfatah ya yi ya ce
"Idai zanje amma Islam bazata fita ba."
"Sabuda me? Ka barta mana sheda cefa."
"A'a Dr bazan bari taje wannan gurin ba kuma ma kobadan hakaba ma batada lafiya bazata iya zuwa yawon shara'a ba."
Mamaki ne ya kama Dr kafin ya yi murmushi ya ce
"Okay zuwa goban sai nazo muhuce tare dan nima Bauchi zan tafi yanzu sai dare zan dawo shiyasa nazo yanzu na sanar da kai."
"Okay Allah ya tsare."
"Amin Doctor Abdul, Allah ya bamu sa'a."
"Amin."
Nan sukayi salama Doctor Salis ya yi waje shikuma Abdulfatah ya kule gidan ya koma ya kwanta a falo yana cigaba da tunanin duniya daya saba.
Sai Azahar Islam ta yi tashi lokacin har Abdulfatah ya siyo musu abuncin da zasu ci, itadai kasa ci ta yi dan bakinta ba a i, tea ya dafa mata saida ya aure fuska taga ba sarki sai Allah sannan ta sha ya bata magani.
Bayan ya fita ta sako ta fito falo dagyar duniyar ma juya mata takeyi tana zama kira ya shigo wayarta taga Sarah ce ta auka tare da yin salama.
Amsawa Sarah ta yi tana cewa
"Labari da umi- umi sa kishiyar ki dai taje wayan gida awa gobara ta one su to ita awar tata ma ta she a barzahu ita kuma ta babbake kaga aya."
"Inalilahi wa'ina ilaihirraji'un, Allah sarki, Allah ya bata lafiya ita kuma wadda ta rasu Allah ya ji anta."
"Hmm amin dai, abuda ta shuka ne ta fara girbar abunta."
"A'a Sarah jarabta ce ta ubangiji muma bamufi karfin Allah ya jarabce mu ba."
"Ai koda yaushe muna cikin jarabawa amma itama da mugun hakita."
"To Allah ya kyauta."
"Amin aunty Islam, mura kikeyi ne naji muryarki haka?"
Magana zatayi suka ha a ido da Abdulfatah ta ya shigo yanzu shima kafeta ya yi da ido dan ya ji abunda Sarah ta fa a tuda a speaker tasa wayar, saurin cewa ta yi
"Eh."
"To Allah ya sawake da fatan kina kula mana da yay......!"
Katse wayar Islam tai saurin yi, murmushi ya yi ya zauna ya ce
"Ki barta ta fa i abunda ta ke son cewa mana."
Shiru ta yi kanta a asa tana wasa da wayar hannun ta
"Okay kidai san duk abuda ya shiga tsakanin ki da mijinki ko wane iri ne sirrin ki ne ba'a sanar da wani ko?"
Nan ma shiru ta yi ya ta e baki, kunyar Islam har tayi yawa ba kamar Mufida ba da batada kunya ba.
Washe gari Doctor Salis ya zo kamar yadda sukayi jiya da Abdulfatah suka tafi kotu tare.
Idan shari'a ta yi kyau akan yankewa Marwa da tawagarta hukuncin zama a gidan gyaran hali na shekaru 20.
Abdulfatah ya yi godiya ga Allah da ya rabashi da musifa.
Doctor Salis ne ya ce yazo ya rakashi wata dubiya, nan suka tafi Hospital inda suka shiga wani aki, warin da Abdulfatah ya ji ne yasa shi toshe anci Salis yaja hannusa suka arasa jikin gadon.
Cike da tsoro Abdulfatah ya kali Salis ya ce
"Inalilahi Salis wace wannan ta kone haka?"
Da fashi Dr Salis ya yi ya ce
"Kaleta da kyau baka gane ta ba?"
Kura mata ido Abdulfatah ya yi kamar yasan fuskarta amma yadda ta yi baki ta kone ya kasa gane wace,
A sanyaye Salis ya ce
"Wannan matarka ce Mufida ta gamu da iftila'i gobara ita Nuratu ma ta rasu."
"Inalilahi wa'ina ilaihirraji'un!!"
Abdulfatah ya ringa maimaitawa zuciyarsa ta karaya sosai lalai idan baka mutuba ba'a gama ma halita ba dubi Mufida duk kyan nan nata da kwaliya amma ta babbake haka, tsoran Allah ya ara shigar sa yana nadamar abubuwa da yawa a baya."
Kukan da yakeyi ne yasa Dr Salis ya fito dashi daga akin ya zaunar dashi a waje, murya a sanyaye ya ce
"Abdulfatah kaga yadda duniya take maida me rai ko? Idan idan kaga Mufida zaka ta a tunanin wannan rayuwar zata risketa? Abun tsoron muma zata iya riskar mu ko wadda bata kai haka muniba ko wadda ta zarce haka tunda muna nunfashi, rayuwa batada tabbas Abdulfatah na tsorata sosai danaga wannan abun."
Shiru duk sukayi Abdulfatah ya dubi Salis ya ce
"Duk da ba aure a tsakanina da Mufida kuma ta aikata mun laifuka da yawa amma ta bani tausayi sosai."
"Hakane amma ya kamata ka taimaka mata Abdulfatah tunda bata da kowa sai Allah."
"Ina iyayenta?"
"Hmm Abdulfatah kenan ai na arya ne ba wanda yasan asalinta ita da Nuratu su kansu basusan asalin junaba."
"Wannan wace irin rayuwa ce Salis? Amma duk da haka zai taimake ta muje gurin Doctor da yake dubata."
Tashi sukayi sukaje office in Dr Abdulfatah ya biya duk wasu ku i da aike bu ata, ya dawo gida jiki ba kwari.
Islam ta na kitchen tana girki ya shiga da salama, amsawa ta yi ta masa sannu da zuwa, ya amsa ya na cewa
"Baki da lafiya amma kike wahalar da kanki kina aiki haka."
Murmushi ta yi ta ce
"Naji sauki zan iya."
Kai ya gyada ya ce
"Okay idan kin gama ki sameni a aki."
"To." Ta ce, shi kuma ya fice.
Kamar yadda ya fa a mata tana gamawa ta shiga akin nasa.
Yana zaune ya yi ta gumi, ta zauna ta ce
"Gani."
Ya jima kafin ya iya furta
"Abubuwa da dama marasa da i sun shiga tsaka nin mu a baya, kuma nasan nine ban miki adalci ba amma ina fatan zaki ya femun."
Mamaki da al-ajabi ne suka kama Islam wai yau ita mutum me aji da izza kamar Abdulfatah ya ke bawa hakuri, a fili kuma ta ce
"Ban ta a ri on ka a zuciya ta ba, kuma kadai bani hakuri wallahi komai ya wuce najima da manta abunda ya faru a baya."
Rungumeta Abdulfatah ya yi cike da farinci ya ce
"Allah ya miki albarka yasa kigama da duniya lafiya."
"Amin kai maha."
Murmushi ya yi yana kodewa Allah, yana godewa su Mama da suka tsaya tsayin daka ya auri Islam da yanzu ina zai nemota ya nemi gafarar ta.
Yana tafe a motarsa yana kallon garin Kano yana Murmushin bankwana ya dubi driver ya ce
"Yanzu idan nabar garin nan ba zan kuma dawowa ba sai nan da shekaru 3 lokacin wannan yaran sun zama kwarangwal."
Dariya driver ya yi ya ce
"Gaskiya ne wannan Alhaji, kaga ba masu zarginka da babbake su."
Dariya duka sukasa, sun shagala da dariyar basusan cewa wata katuwar tifa ta fito daga wani logu sai jikawai sukayi..........!
By
*XAHRA*
*ABDULFATAH*
Na
Fatima S Umar Jajira
PAGE 53-60
_____________ Tifa ta yi awan gaba dasu.
Mutanan da ke gefan hanya ne suka ta so wasu na salati wasu na ihu sabuda motar su Alhaji Sani tariga ta tashi daga aiki ta mole kamar kwankwani, kana ganin motar kasan ba za'a samu me rai a ciki ba saidai wani iko na Allah amma da wuya.
Da kyar aka iya zaro gawar wakin su Alhaji Sani, motar Asibiti ta zo aka wuce da su.
Yau Islam ta yi kwanan farin ciki dan taga kulawa da tarairaya gurin mijin nata wanda bata ta a zatan haka daga gareshi ba anan kusa.
Da safe ita ta taimaka masa ya yi wanka yai shirin office, bayan ta bashi bearkfast ya ci ya dube ta ya ce
"Munyi waya da Mama ta ce mun yau zasu zo da Ammi wata kila harda mayarki Sarah."
Murmushi ta yi ta ce
"Ai baza su soma zuwa ma ba ita ba, ita ce jagorar ta fiyar."
Kai ya girgiza ya wuce tana masa addu'a ya ce "ameen." yana jin wata nutsuwa da da i suna ziyartar zuciyarsa.
Sai azahar su Mama suka zo harda Sarah, Islam ta ji da in zuwan su, ta ringa nan-nan dasu, Mama kuwa da i ne ya isheta sai yanzu tasa tayi sirika da zata zo gidan an ta hankali kwance ba'a tashe ba.
Sai yamma suka ta fi Islam harda kuka, itadai Sarah dariya ta ke mata, Ammi ce ta riga rarrashin ta, har ta yi shiru, Sara na tsokanar ta suka tafi gida.
Bayan wata uku:
Yanzu hankali Islam ya kwanta ta yi kyau tayi kiba sosai ta ara haske duk da har yanzu black beauty ce batayi wannan haske ba.
Yau ta shirya Abdulfatah zai kaita gidan Ummi tunda akai bikinta bata jeba itama Ummi bata zo ba, shine ta gaji ta ce bari ta je yau daga nan ma saita bawa Ummi IV bikin Abdulmalik da Sarah da za'ayi next week.
Suna tafe a mota suna hirar Soyayya Abdulfatah ya ce
"Har gobe na kasa mantawa da rayuwar baya Heartbeat, gani nake kamar duk abunda zan miki bazan goge laifina na baya ba."
Murmushin ta me narkar da zuciya ta masa ta ora hannunta akan nasa dayake su i ta ce
"Ba abunda nake buri a rayuwata irin naga ka manta da abunda ya faru a baya, Allah yana kallo ni najima da mantawa, adama rashin fahimta ne yanzu da muka samu gashi Hospital ima yana hannu na."
Tana rufe baki danja ta tsaida su ya kashe motar, ya kamo hannunta ya mana masa kiss ya ce
"Ina tausayawa duk namijin da ya yi asarar mace ta gari irinki Heartbeat, na rasa wane irin so zuciya ta take miki, kamar zan moto haka nakeji."
Dariya ta masa zatayi magana, wata ba ar mata, tazo bakin window da Islam ta ke tana cewa
"A taimaka mun da sada zan siyi magani a Asibiti."
Zare hannun ta tayi daga nasa ta bu e jakarta ta zaro ku i ta mi a wa matar.
Suna ha a ido taga matar tabar gurin a hargitse, da mamaki ta juya ta kali Abdulfatah ta ce
"Meyasa ta tafi kuma?"
Jikinsa a sanyaye ya tada motar dan an basu hannu yana cewa
"Ai bazata amsa ba sabuda ta sanki."
"Nikuma a ina."
Bai bata amsa ba saida ya bari sunje ofar gidan Ummi ya yi parking ya juyo yana fuskan tarta ya ce
"Wannan matar da ta i kar ar ku iki Mufida ce."
Cike da tsoro Islam take kallo sa jikinta na rawa, kasa furta komai ta yi sai kuka.
Ha ata ya yi da jikinsa ya ce
"Menene abun kuka kuma itafa ta za awa kanta irin wannan rayuwar da ta tsaya tabi aure bata ci amar aure ba da bata shiga wannan halin ba."
Kukan da take ta tsagaita ta ce
"Yanzu bayan konewar da ta yi bara ta koma?"
Kai ya gyada mata, ta ce
"Mukoma dan Allah, ka tausaya mata kamai da ita gidan ka koba komai taci arzikin Soyayya."
Murmushin takai ci ya yi ya ce
"Islam, Mufida ta riga ta haramta a gareni domin kuwa saki uku na mata, ko ba saki uku ma bazan sake gaggaci maida ita gidana ba wallahi dan ni a yanzu bayan ke bana ganin wata mace zata samu guribi a cikin zuciya ta."
Ajiyar zuciya ta yi ta ce
"To dan Allah ka taimaka mata, inkai bazaka iyaba ni ka bani dama na taimake ta."
"To."
Yace ta ita ya share mata hawayen, yaringa janta da wasa har saida yasata dariya sannan suka fito suka shiga gidan Ummi.
Ummi ta ji da in ganin su, bayan su gaisa, Abdulfatah ya wuce, ita kuma Islam anan gidan ta wuni suka ringa hirar yaushe gamo da Ummi.
Sai dare Abdulfatah yazo ya tafi da ita, dan baya bari taje ko ina saidai ya kaita, duk da tanada motar hawa amma baya bari taje ko ina saida rakiyarsa.
Ba hanyar gida taga ya yiba, ya kaita wani gida ya dubeta ya ce
"Duk da na rubu da Mufida rabuwa ta har abada amma ban daina taimakon ta ba, ban bari tasan ni nake biyan ku in maganin ta ba harta warke ba, da aka salameta tana gararanba ba gurin zuwa ni na bawa wata mata gidan nan nace tace na tane su ringa zama suna kwana tare, ni nake cidasu duk sabuda albarka cin ta ta a zama matsayin mata a gareni, bansan meta rasaba take bara, na kamata yafi sau goma, bansa dalilin ta ba, zaki iya shiga ki taimaka mata kamar yadda kika bukata na miki."
Shiru Islam ta yi kafin ta ce
"Ina zuwa."
Fita ta yi ta shiga gidan, ta tadda su suna cin abuci suna hira da salama ta shiga matar ce kawai ta amsa,ita kuna Mufida tashi ta yi ta na cewa
"Lafiya me kika zo yi nan?"
Cikin nutsuwa Islam ta ce
"Gurin ki na zo."
Nan ta zauna ta zayanewa Mufida abunda Abdulfatah ya ke mata ta ce
"Na sanar da ke ne badan komai ba sai dan ki gyara rayuwarki kidaina bara ko nawa kike bukata ki sanar dani zan miki banason ganin ki cikin wannan halin shiyasa na yanke shawar na fa a miki gaskiya ko kya nutsu ki daina bara."
Kuka sosai Mufida ta keyi ta ce
"Bani da bakin gode muku, nagode dan Allah ki yafemun sannan ki roka mun mijinki ya yafe mun."
Islam ta yafe mata sannan ta riga yimata nasiha ta ba ta kudi masu yawa ta baro gidan.
A mota take fa awa Abdulfatah ta sanar da ita gaskiya, da ya tanbayi dalili ta ce sabuda idan taji haka zataji kunyar fitowa bara, yanajin haka ya ce shikenan Allah ya kyauta.
Ansha bikin Abdulmalik da Sarah, su Islam sune kirjin biki,