Showing 15001 words to 18000 words out of 27403 words
Chapter 6 - ABDULFATAH by Fatima S Umar Jajira.txt
kine ko a kwararo ya tsintoki shiyasa zaku are a gantali a tit......!"
Saukar marin da taji a kuncin ta yasa ta ha iye sauran maganarta ba shiri,
Cikin acin rai Abdulfatah ya ce
"Kar ki ara dubana kice ina yawan ta zubar sannan kinsa wannan matata ce ci mata mutunci ya zama haramiyarki in ba haka ba kuma zaki koma inda kika fito."
Ya juya ya kalli Islam ya ce
"Malama huce muje."
Binsa tayi suka fice, ita kuma Mufida ta ringa zazzaga ruwan ashar harda saita one gidan kowa ya wuta.
Nuratu ce ta kale shi ta na murmushi ta ce
"Jiya akayi bikin mijinta na kamala duk wani aiki da kasani yanzu saura ka cika mun alkawarin da kamu sannan ka salame ni."
Murmushi Alhaji Sani ya yi ya ce
"Gaskiya aikin ki ya yi kyau Nuratu kuma naji da i amma wani hanzari ba guduba bakya ganin yanzu ya yi wuri Mufida tasan inda kika dosa."
"Hmmm Alhaji kenan, ai ni yanzu bana tsoran ta mutu balai tai rai kuma ita Mufida da kake magana ba abunda zata iyayi sabuda ko matsala ce ta sameta bata iya magan cewa da kanta saita ne meni kaga kuwa ba abuda ta isa tayi kuma ko ta sani kafin tayi yin kurin ramawa muncita daya i."
"Hakane zanji da komai kedai ki kasance cikin shiri."
Murmushi ta yi ta ce
"Baka da matsala dani Alhaji."
Ku i ya ako masu yawa ya bata ya ce
"Ga wannan kisa kati sannan ki kirani in kina bukatar wani abu."
Amsa ta yi ta na washe baki, ba godiya ta mike tare da aga masa hannu ta ce "bye." Ta fice abunta.
Ta na fita ya auki wayar sa ya kara a kune ya ce
"Kusamun ido a kanta duk inda zataje da abunda zatayi."
Ya kashe wayar yana murmushi a fili ya ce
"Harni zakiyi yiwa wayo Nuratu ance miki kwakwalwata irin ta Mufida ce da zakiyi wasa da hankalina." Saiya ara sakin murmushi.
Asibiti ya kaita aka duba raunin doctor ya ce da Abdulfatah sai an mata gyara a gurin, "to." Abdulfatah ya ce ya kalli Islam cikin tsana yana watsa mata harara ya ce
"Ki matsa zai duba miki afar."
Shiru ta yi, ita bata matsaba ita bata ce komai ba, fusata ya yi ya daka mata tsawa
"Ba dake akai magana ba."
Kawai saiya ga hawaye takeyi, tsaki ya ja wanda yasata goge hawayen ta mi e ta arasa gurin doctor da zai duba ta.
afar ya fara ta awa da Islam taji zafi saita kwace afarta ta na yarfa hannu da hawaye, yin duniya ta miko afar ki tayi da Doctor ya gaji sai ya kira Abdulfatah ya sanar dashi ta i tsayawa, a fusace ya zo gurin, ya zata ganin sa zata bari a gyara amma ko gezau, sai kuka da takeyi.
Haushi kamar ya kashe Abdulfatah jiyake kamar ya kashe yarinyar nan, doctor ne ya kalli Abdulfatah cikin nutsuwa ya ce
"Da alama bazata bada kafar nan a gyara ta da in raiba kawai abunda zai faru ka riketa sai a gyara inba haka ba wahala zata bamu."
Da farko Abdulfatah cewa yayi a'a saida yaji Doctor ya ce
"Wai ba matarka ba ce in baka rike ta ba wazai riketa."
Ba yadda ya iya yanajan tsaki ya arasa gabanta fuskar nan a hade ya ce
"Idan baki tsaya kin nutsu an gyara miki afarki ba to zan tafiyata tunda ciwan a jikin ki yake ba ruwana."
Hararar sa ta yi tayi kamar bata jisa ba, doctor da zai gyara mata ciwon ne ya araso ya tsuguna dai-dai kafar ya cafkota zabura Islam tayi ta kwala ihu zata kwace Abdulfatah ya sa hannu ya riketa ram yadda bazata iya kwace wa ba.
Saida aka gyara tass Abdulfatah najan tsaki ganin kukan da take sakin ta yayi zai miki, yaga tayi baya zata fa i da sauri ya tarota jikinsa, jiya yi jikinta zafi zau da alama zazzab'i ya rufeta a gurin ga nunfashi da take fitarwa da gyar, da jikin bango ya jinginata ya tashi, yaje gurin Doctor ya rubuta musu magani ya dawo ya ce da ita tami e su tafi.
Da gyar ta iya tashi amma kafa taki takuwa, dole sai Abdulfatah ne ya kamata suka fita yanata kauda kai war kar ace wannan black girl din ce matar sa.
Da kashi ya bude mata mota tashiga ya maida ita gida ya shige office.
Ta na in gisa afar ta tashiga falon da salama, ido ta zaro da sauri cikin mamaki ta ce..............!
By
*XAHRA*
*ABDULFATAH*
Na
Fateemah S Umar, Jajira
PAGE 35-36
_____________ "Aunty yaushe kuka zo?"
Murmushi aunty ta yi ta ce ki shigo mana, araso wa ta yi taga falon a cike duk da an uwan ta, farin ciki ne ya lulu e ta ta zauna suka gaisa sannan ta je ta bu e musu akin nata suka shiga suna yaban tsaruwar gidan.
Sun jima a gidan kafin su mata salama zasu wuce duk sunyi gaba, Yagana ar uwar Ummi ta dawo ta same ta a aki ta zauna kusa da ita ta ce
"Kafin ki dawo kishiyarki ta wula an tamu amma ba komai ki cigaba da hakuri sannan ki ringa gasa kanki da ruwan dumi idan na koma gida akwai abuda zan aiko miki zakiga yadda zaki afani dashi a rubuce."
Kanta a asa ta ce "to aunty nagode."
Salama Yagana ta mata ta wuce kai ta girgiza ta san duk aukan su Yagana Abdulfatah ya kwanta da ita abunda basu sani ba tsanar da Abdulfatah ya mata bazai bari ya iya ha a shifi a da ita ba.
A aki ta wuni sabuda zazzab'in da ya kwantar da ita amma taji afar ta daina mata zugi ba kamar azu ba.
Abdulfatah sai dare ya dawo gida bayan yaje akin sa ya yi wanka ya sauya kaya ya nufi kitchen dan ya samarwa kansa abunda zaici kamar yadda ya saba.
Tayi bacci ta farka taji tanajin hinwa tanajin jiri-jiri ta fito ta nufi kitchen.
Kanta a asa ta shiga ji tayi ta ci karo da mutu a tsorace ta ago dan ganin waye.
Yana tsaye yana kallon ta cike da tsoro ta ce
"Kayi hakuri ban kula da kaiba."
Bai mata magana ba ya fice daga kitchen in ya rabu da ita. Baki ta ta e ta shiga ha a abunci duk da bata jin da in jikinta.
Saida ta gama tass ta zuba a filet ganin girki Abdulfatah yake son yi tayi murmushi ta sauke masa wanda ya fara ta zuba wanda tayi a food filas ta ajiye masa, ta fice.
Saida yaga fitar fa daga kitchen in sannan ya koma kanshi girki kawai yakeji amma ya basar ganin an sauke masa nasa girkin ya fusata sosai har zai fita ya hango kula ya koma ya bu e, saida ya lumshe ido sabuda kanshi daya ji ya daki hancin sa, bashiri yasa spoon ya fara cin abunci tun a gurin.
Mamaki yake a ransa dama ammatan yanzu sun iya girki haka? To meyasa ita Mufida bata iya ba sai wannan ar tala kawan? Baiyi aune ba yaga ya kwashe girkin tass, sai lokacin yaji haushin kansa ya kamashi to menene ma na ta a abuncin wannan azamar yarinyar, tsaki yaja ya fice da sauri.
akinta ya shiga tana zaune tana cin abuncin nata a nutse wani mugun kallo ya watsa mata ya ce
"Da izinin wa? Kika sauke mun girki?"
Muryar ta na rawa ta ce
"Bansan ranka zai aci ba kayi hakuri gani nayi gamu har mu biyu a gidan nan zaka ringa girki da kanka."
"Ke a matsayin ki na wa? Ko kin zata matsayin matata kike? kinsa kuwa menene matsayin mata? To ki daina kai kanki inda Allah bai kaiki ba kuma girki tunda kinji kin gani kuma da ma kin saba da wahala to kulum ke zaki ringa yinsa dare da safiya idan kika sake na kamaki bakiyi ba ranki saiya ace." Har ya juya zai fita ya juyi ya ce "idan kin gama zaki iya samuna a aki ki amshi maganinki."
Ya fice yabar akin.
Ajiyar zuciya Islam ta sauke da taga fitar sa ta ajiye abuncin da take ci ta cigaba da tunanin hali irin na Abdulfatah, shi a rayuwar sa za'a ta a burge shiba.
Mikewa ta yi ta zura hijab in ta, ta sauka zuwa akin sa.
Da salama ta shiga bai amsa ba kuma bai ko ago ya kali inda ta keba saida ya gama abunda ya keyi a hankali ya ora idonsa a kanta, ta e baki ya yi ya ce
"Makaranta zakije da kika sako wannan aton hijab in? ko ance dake akwai wani abu da mutum zai kalla a jikin ki ya burge shi? Haka kike tunani ko."
Girgiza kai kawai ta keyi ya watsa mata harara ya ce
"Ga maganin nan ki auka idan kinga dama sannan duk girkin da zakiyi kiyi a kitchen din ki na sama amma idan girkin na ne ki sako kiyi a na gida."
"To." Ta ce ta auki maganin ta fice daga akin.
Akan idon Mufida ta fita hankalin Mufida a tashe ta shiga cikin akin nasa kamar an jefata.
Dogon tsaki Abdulfatah ya ja kawai sabuda yaga abun na Mufida kulum karuwa ya keyi, ita kuwa a hasale ta ce
"Wai me kake nufi dani Abdulfatah? Tun jiya naga kana rawar afa akan wannan yarinyar kana fifitata a kaina sabuda kaga ina kyaleka ko."
Ko ci kanki bai ce da ita ba ya tashi ya shige bayi.
Hannu ta ora a kai ta ce
"Lalai Abdulfatah ya mai dani ma mahau kaciya to zakayi magana bari naje na targa a wace muna fukar zaka fito."
Da sauri ta juya ta nufi akin Islam.
A hankali ta kalli Dady da yake ta yi mata fa a cikin acin rai ta ce
"Haba Dady in kai zaka iya yafewa ni bazan iya ba taya za'ayi wannan mutumun ya kusa halaka ku na rabu dashi wallahi sai na auki fansar abunda ya muku."
Da sauri ta mi e ta fice a fusace, Dady ya na ta kiran ta
"Marwa! Marwa."
Amma ko juyowa ba tayi ba tai tafiyar ta...........!
By
*XAHRA*
*ABDULFATAH*
Na
Fateemah S Umar, Jajira
PAGE 37-38
_____________ Da sassafe Islam ta tashi ta ha a musu abun kari harda Mufida tajere a darning table taje har kofar akin sa gaban ta na fa uwa ta buga masa ofar a hankali dan a zaton ta ya makara ne gashi yau ranar aikice.
Mufida da take zaune kusa dashi ta tsare shi da korafin da ta saba, taji bogun ofar mikewa ta yi zata fita, ya riko hannunta ya ce
"Ina kuma zakije?"
Harara ta watsa masa ta ce
"Wanda yake buga mana kofa zan ciwa mutunci."
Sai lokacin ya tuna da zaman Islam a gidan kafin ya yi magana ta kwace hanunta ta yi gaba da sauri ya mi e ya bi bayan ta ya rikota, dai-dai lokacin da ta bu e ofar, Islam da ta juya zata tafi motsin da taji yasata juyawa.
Mufida ta na ganin ta juyo tai saurin shigewa jikin Abdulfatah tana yatsina fuska ta ce
"Malama ya haka zaki zo da sassafe ki tashemu a bacci ko ance miki nan irin kangon gidan kune da ba'a baccin safe."
Murmushin ta kaice Islam ta yi kafin ta ce
"Ai kangon gidan mu ya fi mun wannan gidan so dubu tunda gidan mu gidan katun al-Qur'ani ne ba gidan she a nufa."
Abdulfatah ne ya ture Mufida daga jikin sa ya arasa inda Islam ta ke ya kaleta sama da asa ya ce
"Waya fa a miki gidana gidan she a nune?"
Ta kaici hana Islam magana ya yi ta juya zata bar gurin da sauri yasa hannu ya jawota, ta fa a jikinsa atare suka rintse ido, ita na tsoro shikuma na sauyin da yaji a jikin sa, ya yi baya ya kafeta da ido ya ce
"Naga alamar baki da kunya to zan gyara miki zama dan baki isa kizo gidan mu ki aga mana hankali ba."
Dariya kawai Mufida ta keyi ranta fari tasss, har Islam zata yi magana da tsiwa kome ta tuna ta fasa ta ce
"Kuyi hakuri bearkfast na gama shiyasa na tashe ku."
Tana gama fa in haka ta juya da gudu ta haura sama.
Komawa ciki Abdulfatah ya yi saida ya yi wanka ya sauya kaya sannan ya zo ya fara karyawa.
Mufida ce ta fito ta gansa cikin acin rai ta ce
"Haba Abdulfatah girkin wannan yarinyar ka ke ci?"
Ko kallo bata isheshi ba saida ya gama tass ya tashi ya rataya jakar aikinsa ya ce
"Kila da naki a cikin zaki iya zama kici."
"Allah ya kikaye wallahi."
Kafa a ya aga alamun ko a jikin sa yai ficewarsa ya barta a tsaye a gurin.
Islam kuwa tunda ta hau sama ta ke aikin kuka yanzu haka zata zauna miji ya tsaneta kishiya ta adabeta? wallahi bazata yarda ba saita kwatowa kanta anci in ba haka ba ta naji tana gani zasu maida ita baiwa a cikin gidan.
Nuratu hankali a tashe ta ke tafiya a titi har ta arasa gaban wata mota, asa akayi da gilas in motar aka mata magana da sauri ta shiga ciki aka figi motar da uban gudu akabar gurin.
Sunyi tafiya me nisa har sun fita wajan gari sannan suka gangara sukayi parking suka fito.
A baya tabi mutumin har suka kai wani guri da Alhaji Sani ya ke tsaye gaban motarsa.
Durkusawa ta yi a gurin ta saki kuka me sauti, murmushi ya yi ya ce
"Nuratu kenan ni ba aramun yaro bane da zaku maidani kamar doll keda awarki tuntuni na gano so kike na cutar da Mufida kuma ki samu wasu ku i masu yawa a gurina ki aure mijinta ta hanyar asiri, saidai duk da ke ka ai kike shirinki na ganoki shiyasa na ce bazan rabuda kuba dagake har Mufida dataci amanata ta yi aure."
Cikin kuka Nuratu ta ce
"Kai mun duk hukunci da zaka mun amma dan Allah kar ka bari su cutar mun da ata."
Dariya Alhaji Sani ya yi ya ce
"Nasa aka kawomun ar kine sabuda zaki mun wani aiki."
Da sauri ta ce
"Ko nene zan maka shi indai zaka rabuda ata."
Murmushi ya yi ya ce
"Kin oye gaskiyar ke wace a gurin mu bakisan zamu iya gano wa ba to yanzu aiki aya zaki mun, ki kashe auran Mufida ta dawo gidan ki da zama."
Kaita gya a da sauri ta ce
"Na yarda wallahi."
"Shikenan zaki iya tafiya."
Da sauri ta mi e da gudu tabar gurin.
Alhaji Sani ya kali yaron sa ya ce
"Duk sanda kuka tabatar ta gama aikin da na sata kuyi abunda na ce, ni asar zan bari sabuda gudun ko ta kwana."
"Okay Sir."
Duk suka shiga motar suka bar gurin.
Marwa ce zaune kusa da wani mutum ranta a ace ta ce
"Ina bu atar taimakon ka Yunus."
Kallonta Yunus ya yi ya ce
"Shawara aya zan baki Marwa ki rabuda wannan mutumin ya fiki kwanya zaki iya kwana a ciki."
Harara ta watsa masa ta ce
"Idan bazakayi ba kawai ka fa amun?"
Kai ya girgiza ya ce
"Zan taimaka miki amma bazanyi da kaina na kwana a ciki ba."
"Okay hakan ma ya mun."
Nan suka cigaba da tattaunawa akan yadda zasu gabatar da aikin na su.
Islam na kwance ta ji salamar Sarah da gudu ta mi e suka rungume juna cikin farin ciki.
Zama sukayi Sarah ta ce
"Amaryar Ya Abdulfatah ya kike da halin sa kuwa?"
Hararar ta Islam ta yi ta ce
"Bazaki tanbayi lafiya ta ba sai halin yayanki."
"Hmmm Aunty Islam kenan, ai halin ya Abdulfatah zaifi komai damunki idan yaso mugun tarsa."
Dariya Islam ta yi ta ce
"To nidai halin yayanki ya fi komai burgeni da shi yanada kirki sosai."
Ido Sarah ta zaro ta ce
"Da gaske kike?"
Kaita gyada mata tana dariya
"Gaskiya ke ta daban ce aunty Islam."
Share zancan Islam ta yi da cewa
"Ya Mamata?"
"Mama tana lafiya duk sunce na gaidake ita da Ammi."
"Ina amsawa."
Hira suka sha sosai har yamma Sarah tana gidan sai da sukayi aikin gidan gaba aya sukayi girki sannan Ya Abdulmalik yazo ya tafi da ita.
Da gudu ta shiga akin Mama ta rungume Mama tana dariya ta ce
"Gaskiya Mama sai yanzu Ya Abdulfatah ya yi aure."
Dariya Mama ta ringa yi mata ita kuma sai yabon halin Islam takeyi.
Yana zaune a office ya na tunanin halin mata yaji anyi salama an shigo, ganin wanda ya shigo yasa ya amsa salamar,
Zama Doctor Salis ya yi yana murmushi ya ce
"Ango kasha amshi gashi sai annurin Angonci ka keyi."
Harararsa Abdulfatah ya yi bai kulasa ba.
Dariya Doctor Salis ya yi yai asa da muryar sa ya ce
"Ina fatan dai ka ajiye wannan girman kan naka ka rungumi matarka ko?"
Tsaki Abdulfatah ya yi ya ce
"Na rasa wazan runguma sai wannan yarinyar."
Ido Doctor Salis ya ce
"Kana nufin wai girman kai ka tsaya yi har yan zu?"
Ganin Abdulfatah baiyi magana ba yasa ya kwantar da murya ya ce.............!
By
*XAHRA*
*ABDULFATAH*
Na
Fatima S Umar Jajira
PAGE 39-40
___________ "Haba abokina wataran saika ringa abu kamar bakaje School ba."
Wata uwar harara Abdulfatah ya watsa masa ya ce
"Amma dai Salis bakada hankali ko? Ni zaka maida aramin yaro, kasa yarinya ta rainani."
"Da ina da kai rashin fahimta wallahi, tayaya zata rainaka? Kai ko raini ne a tsakanin ku zata daina sannan ta ringa maka biyaya sabuda ta gane kasan abunda kakeyi ke me ilimine ba irin jahilan mazan nan