Showing 9001 words to 12000 words out of 27403 words

Chapter 4 - ABDULFATAH by Fatima S Umar Jajira.txt

ji irin ba in cikin da ya ji.






Duk yadda Islam taso dane damuwar ta kar Ummi ta gane kasawa tayi dan har ta rame so tari Ummi tana kamata tana kuka amma bata canza ra'ayi ba.


Tana yawan kiran Sahal amma baya auka daga arshe ma wayarsa dai na shiga tayi gaba aya.




Yauma tana aki a kwance tana ta faman kuka Ummi ta shiga, saurin goge hawayen fuskarta ta yi amma Ummi ta riga ta gani zama ta yi kan gadon tana kallon artata da tausayawa ta ce


"Ban sani ba ko namiki laifi dan na rabaki da Sahal amma inaso ki san wani abu, ita rayuwa ba komai kake so kake samu ba kamar ke da kika damu da Suhal Allah zai iya jarbatar ki ta rabuwa da shi, kuma ki sani matar mutum kabarin sa ki godewa Allah da addara rabaku ta yi da Suhal ba kasheshi ta yi ba."


A tsorace ta ke kallon Ummi.


Ummin ta gya a kai ta ce


"Ina mamakin yaran yanzu da baku yarda da adara ba kudai in kuna son abu to ko a mutu ko ai rai shi za'a baku, kun mata da iyayen ku bazasu za a muku abunda zai cutar da kuba, abunda baku sani ba shine yadda iyayen suke sonku ku bakwa son kanku haka amma gani kuke kamar tsanar ku akayi ko?"




Kai Islam tai saurin girgiza wa ta ce


"Wallahi Ummi ban ta a ji a raina zan sa a miki ba kuma na yarda da za in ki gare ni duk da basan waye ba ban ta a ganin sa ba amma na amunce a haka kawai na kasa man tawa da Suhal a zuciya ta lokacin da Doctor Abdulfatah yana cusgunawa rayuwa ta shine ya ke faran ta mun kuna na yarda so na gaskiya ya ke mun."




Dafata Ummi ta yi ta ce


"Na sani amma ki duba alfarma da girma irin nasu Mama amma tazo har inda nake ta nemi alfarmar abasu auran ki badan komai ba da sun yaba da tarbiyar ki da iliminki basu duba matsayi ko arziki ba kinga kuwa wannan mutane bazakayi dana sanin ha a zuri'a aya da suba kuma nasan zasu mutun taki shiyasa badan arzikin su ko wani abuba in da a mutun taki nake hange, shi Suhal da kike so zata iya kasan cewa dagin shi ba sa sonki to wallahi idan auran ya yi tsayi sheni ya shekara duk son da yake miki sai sun cusa masa iyayyarki shikuwa wannan kodan son da iyayensa suke miki dole ya rungimeki hannu biyu indai an mutun ci ne."




Ajiyar zuciya Islam ta sauke ta ce


"Hakane Ummi nagode Allah ya saka miki da gidan a aljana."




"Amin."


Ummi ta ce tana murmushi tai ta jan Islam da hira har ta saki ranta.






Ko salama babu ta shigo falon tana ya mutsa fuska dai-dai lokacin da Mufida ta fito daga akin ta,


Kallon juna suka kamayi kowa da abun da yake rayawa a cikin ransa,


Tsaki Marwa ta yi ta cigaba da tafiya ta nufi akin Abdulfatah,


Gaban ta Mufida ta sha ta ce


"To daga ina naga kina shirin shiga akin mijina."


Fuska Marwa ta ya mutsa ta ce


"Bai ta a sanar da ke yana da wata matar bayan ke ba? To tun wuri ki matsa daga gabana dan ni ko mayan maza an daba tsorona sukeji sabuda sunsan halina zan iya kashe mutum ba wani abu bane."




Tsaki Mufida ta yi ta ce


"Ni kuma baki isa ki shiga akin mijina ba saidai duk uban da za'ayi ayishi."




Murmushin mugun ta Marwa ta yi kafin Mufida ta ankara ta zaro wani arfe a jikinta ta kafa mata a..........!








By
*XAHRA*



*ABDULFATAH*





Na


Fateemah S Umar, Jajira




PAGE 19-20






_____________ Hannu amma ba ta yi na sarar samun ta ba taji an rike hannun ta juyawa ta yi ta ga Abdulfatah ne yana watsa mata mugun kallo kafin wa ce


"Wannan wane irin haukane Marwa raunata ta zakiyi."


Huci ta farayi ba ta ce komai ba ya juya yana hararar Mufida ya ce


"Na rasa yaushe zakiyi hankali ki ringa kama kanki mtss."


Ya ja tsaki ya cewa Marwa ta biyo shi ya shige akinsa.




Saida Marwa ta juyo ta watsawa Mufida kallon banza sannan ta shige akin Abdulfatah.




Zubewa Mufida ta yi a gurin ta na kukan ba in ciki,
Ganin kukan bazai amfane ta ba ta mi e ta shiga akin ta.




Wayarta ta ako ta kira number Nuratu.


Tana agawa ko magana Mufida bata bari ta yi ba ta ce


"Kina ina nazo na sameki?"


Cike da mamaki Nuratu ta ce


"Ina gida mana amma da zan fita."


"Okay jirani ina zuwa."




Mayafi kawai ta zura ta fice daga gidan.




Zama ta yi kan gadon tana turo baki,


Murmushi ya yi ya ce


"Mene abun damuwa kuma?"


"Hmmm wai a gaban wannan kucakar matar ta ka kake mun fa a."


"Ba haka bane Marwa gidan ta kika zo dan haka duk matakin da ta auka a kanki bata da laifi."




"Hakane amma kasan bana aukan raini ko, naso ka barni na ilatata wallahi amma yan zuma zamu ha u zanyi maganin ta."




Shidai Abdulfatah bai magana ba sai komawa da ya yi ya kwanta ya barta tana ta mita ita ka e.






Da salama ta shiga gidan Nuratu ta amsa tana fi towa daga aki ta rungume ta,


Murmushi ya e Mufida ta yi ta ce


"Akwai matsala Nuratu."


"Wace irin matsala Mufida?"


"Abdulfatah ya daina sona Nuratu duk shirin da mukayi ya tarwatse har mata yake kawowa gida yanzu."


"What."


Nuratu ta fa a da arfi tana zaro ido,


Kai Mufida ta gyada ta ce


"Yanzu mene abun yi?"


"Hmmm abunyi ayane mukoma gidan Malamin daya mana aikin tun farko."




"To amma kinsan bani da ku i yanzu ya daina bani komai."




"Ke kikayi sake har ta kaiku ga haka, amma zuwa zakiyi gurin Alhaji Sani kice har yanzu haifin ki ba lafiya za'a mishi aiki ya daure ya baki ku i ki biya ku in aikin."




Rungume ta Mufida ta yi ta ce


"Gaskiya wannan shawara taki tayi awata taso muje tun yanzu ba sai anjima ba."


Tashi Nuratu ta yi suka fice daga gidan.




Har office in Alhaji Sani suka je ya yi mamakin ganin Mufida gashi ta ara iba ta yi kyau sosai.




Bayan sun gaisa ne Mufida ta kalle shi ta ce


"Kayi hakuri Alhaji mahai finane ba lafiya shiyasa baka ganina ko a waya baka samu na gashi yanzu ance aiki za'a masa gashi bamu da ku i murasa yadda zamuyi shine na yanke shawarar zuwa gurinka ka taimaka mum."






Murmushin rainin hankali Alhaji Sani ya yi sannan ya ce


"Bakomai turo account number amma a ina zaki kwana tunda dare ya yi baza ki koma auye yan zuba?"


Muryar ta na rawa ta ce


"Am dama gidan Nuratu zan kwana."


"Okay basai kin ora mata nauyi ba muje gidana ki kwana."


Kallon juna sukayi da Nuratu,
Nuratu tai saurin gyada mata kai,


Fuska ta marairaice amma Nuratu ta harareta batasan sanda ta ce


"To Dear nagode amma bari buje na oko kayana gidan Nuratu."


"Ba matsala idan kin shirya ki kirani nazo na taho da ke."


"To."


Ta ce suka masa salama suka fito.


Bayan sun hau an sahu Mufida ta ce


"Nidai gaskiya gida zan tafi taya zan kwana da wani ato bayan kinsan yanzu inada aure."


Tsaki Nuratu ta yi ta ce


"Yanzu ba mijin nakine ya kai wata atuwa gidan kiba?"


"Hakane amma tsoro nakeji wallahi."


"Sai kace ba Mufida da na sani ba ki saki ranki yarinya."


Zigata Nuratu ta ringayi har ta amunce da kudirin Alhaji Sani.


Duk abunda suke tattaunawa Alhaji Sani yana sauraran su ta wayar Nuratu saida suka sauka ta kara a kune ta ce


"Yanzu ka yarda Mufida ta ci amabarka ta yi aure."


"Na yarda kuma na gode da kika sanar dani da wuri zan bari naga iya gudun ruwanta sannan na hukun ta ta."




"Shikenan sai na jika."


Sukayi Salama tai saurin kashe wayar ganin Mufida ta nufo inda take.




Bayan kwana biyu da amun cewar Islam Ummi ta kira Mama ta ce sun amunce.


Ba aramun farin ciki Mama ta yi ba taringa yiwa Ummi godiya, Ummi ta bata address in dangin uban Islam dan Ummi ta ce acikin satin nan za'aje a gama komai ba taso bikin ya ja lokaci, sukayi salama cikin girma ma juna.






Abdulfatah na zaune a falo ya rasa abunda yake masa da i tunani yake ina Mufida ta shiga sai yanzu yake na damar barin Marwa ta zo inda ya ke.


Message yaji ya shigo wayarsa ya duba rubutu kamar haka.




SALAM BARKA DA DARE ABDULFATA NASAN YANZU KANA ZULUMIN INDA MATARKA TAKE TO KA KWANTAR DA HANKALIN KA MUNA TARE DA ITA A HOTEL ITAMA ZATA RAMA IRIN CIN MUTUNCIN DA KA MATA.


Yana gama karan tawa hotuna suka shigo wanda Mufida ta ke shiga hotel gata da wani katon mutun a aki tare...............!








by
*XAHRA*





*ABDULFATAH*





Na


Fateemah S Umar, Jajira




PAGE 25-26






_____________ Ya bu e baki zeyi magana kuma komai ya tuna saiya fara ya juya zai shiga motarsa, ya ara juyowa ya ce
"Kuskure mafi girma da zakiyi a rayuwar ki shine ki yarda da aure saina wula anta rayuwarki."
Yana gama fa in haka ya shige motarsa ya bar gurin.


Sai lokacin Islam taji wani irin hawaye masu zafi sun taho mata ta juya ta shige gida tana o arin oye damuwar ta kar Ummi ta gane.




Ranshi a dagule ya koma gida amma wani abun takaicin Mufida ya tarar ta dawo gidan.
Tana ganin sa tasha jinin jikinta muryar can asa ta ce
"An dawo lafiya?.
" Mtsss."
Tsaki kawai yaja ya huce yabarta a gurin.
Da harara ta rakashi har ya shige akinsa, taja tsaki itama ta samu guri tai zamanta.
Yana shiga akin nasa kan gado ya zube, ya na tunane-tunane. Yanzu shi bashida iko da kansa sai abunda akaso shi za'a masa ance sai ya yi aure ya yarda, ya saki mata an dawo masa da ita.
To me ake nufi dashi? Ya tanbayi kansa, ka annansa Abdulmalik da Abdussamad ba wanda ya takura su sai shi aketa sa masa ido a rayuwar sa.




Kirane ya shigo wayarsa ya duba yaga Marwa ce, saida gabansa ya fa i ya dake ya aga kiran ya kara a kune tare da yin salama.
Bata amsa ba sai cewa da tayi.


"Abdulfatah kasani kowa yaci tuwo dani miya yasha, wallahi baka ci bulus ba tunda ka yaudare ni kaci amanata to nima saina rama, akan wata ar matsiyata ka rabu dani ko? To nasan komai game da Islam wallahi saina lalata rayuwarta."
Kit yaji ta kashe wayar.



Jikin Abdulfatah ne ya yi sanyi yasan Marwa batada mutunci ya na tsoron ta cutar da ar mutane da bata ji ba bata gani ba, kiran wayar ta yayi amma yaga tanasa Busy alamun tasashi a black list girgiza kai ya yi, ya mi e ya nufi gidan ta.






Gidan Marwa yaje amma ba ita ba alamunta haka ya baro gidan jiki a sali e dan ya na tsoron abunda zaije ya dawo.




Anata shirye-shiryen biki har an kai lefan Islam akwatina 8 duk sha eda kaya na alfarma, Mama tafi kowa farin ciki da okin bikin an nata dan gani take kamar auran fari zeyi.




Mufida kuwa sai yawan malamai takeyi wai dole sai ta hana auran da taga ba sarki sai Allah saita hakura amma tasa Abdulfatah a gaba masifar yau daban ta gobe daban, shidai baya biye mata rabuwa yake da ita ta araci haukarta.






Yau saura kwana biyu biki Islam tasha gyara tayi kyau sai she i da warwali takeyi har kunshi ammata kanan yasha gyara gashi har gadon baya, tana zaune suna hira da an uwansu na Meduguri yaro ya shigo ya ce


"Wai Ummi ta ce Islam taje tayi ba i a waje."


Tashi tayi tasa hijab ta fita wajan.
Wanda ta ganine yasa hantar cikinta ka awa ya sa kar mata Murmushi ya ce


"Amarya bakya lefi."


Jikin ta ne ya fara rawa, ya matso cikin nutsuwa ya ce


"Islam bazan oye mikiba har kwanan gobe ina son ki kuma basan sanda zan daina son kiba, ina tunanin da sanki zan mutu Islam."


Duk kansu hawaye sukeyi ya ara da cewa,


"Amma Allah bai addaramun auran ki ba duk da ya jabaceni da sonki amma Alhadulilah da na kasance me yarda da wuhuncin ubangiji, koranar da nami wannan abun acin raine amma na fahimceki kuma na gane kema biyaya ce, shine nazo yau namiki salama da fatan alkairi Allah ya baku zuri'a ayiba."


Kuka Islam take kamar ranta zai fita ya zaro leda daga aljihunsa, karona farko ya kamo hannunta ya danka mata ledar ya ce


"Ga gudun mawa ta nan nagode da Soyayyar da kika nunamun Allah ya ha a fuskokin mu a aljana dan ba lalai ki ara ganina a rayuwar ki ba, nasiha aya zan miki kiyiwa mijinki biyaya ki manta sa Sahal a rayuwarki ki auka baki ta a sanina ba fatan alkairi."


Yana gama fa in haka ya shiga kafu babur dinsa yabar gurin.


Durkushewa Islam tayi a gurin ta saki wani kuka me sauti har shi ewa take sabuda azabar kukan da take.






Wata ar uwarsu ce tazo fitowa taga halin da Islam take ciki, hannunta ta kamo ta mi ar da ita tsaye suka shiga gidan.


Inda ba kowa ta kaita cikin damuwa ta ce


"Haba Islam yaufa ranar farin ciki ce a gareki meyasa kike irin Wannan kukan kinsan gidan da jama'a ai saiya zama abun magana."


Kasa tsada kukan ta Islam ta yi dan ji takai kamar ranta zaifita, rarrashi ta Zahira taitayi har ta samu ta tsagaita da kukan ledar da Sahal ya kawo mata ta bu e, ai batasan sanda tasa wani sabon kukan ba a fili ta ce............!








by
*XAHRA*





*ABDULFATAH*





Na


Fateemah S Umar, Jajira




PAGE 27-28






_____________ "Shikenan na rasaka Sahal me yasa adara zata rabani da kai? Ta ha ani da wanda baisan kimata ko mutuncina ba, inalilahi wa'ina ilaihirraji'un."


Ta arasa maganar cikin kuka. Zahira ce ta dafata ta ce


"Dan girman Allah kiyi hakuri ki daina wannan kukan haka dan Allah."
Mikewa Islam tayi rungume da sarkar da ya kawo mata tashige akin ta.


Da kallo Zahira tayi tana bita da kallon tausayi.


Kwanan zaune Islam ta yi ranar sabuda bakin ciki ai kuwa ta tashi da ma tsanancin ciwo kai, ko ido bata son budewa.




Ummi ce tazo dan Zahira ta sanar mata komai, cikin damu ta ce
"Haba Islam kar kizama cikin bayi marasa yarda da adara me kyau ko mara kyau, ki sani komai kiga Allah ya hukunta maki to da hikimar yin hakan dan Allah ba azalimin bawansa bane, shi Sahal da kike so ba shine mafi alkairi a rayuwar ki ba, kulum ina miki wannan nasihar kinajin haushi bazaki gane ba sai nan ga."


Cikin kuka ta ce
"A'a Ummi wallahi ban a jin haushin ki ba, kiyi ha uri dan Allah."


Nasiha Umma tayi mata sosai duk da ita ma zuciyarta ta karaya amma bata nuna ba.




Shima Abdulfatah yau da mugun ciwan kai ya tashi har takai ko office ya kasa fita, yana aki a kwance ya na tufka da warwara.


Mufida da take jiran fitowar sa ta are masa tadani taji shiru har 10:30am bai fitoba, gajiya tayi da jira ta mi e ta shiga akin nasa.


A kwance ta hangosa cike da mamaki ta arasa kusa dashi ta zauna hañnu tasa ta ta a wuyansa taji zafi sosai jikin ta ne yayi sanyi cikin tausayawa ta ce


"Dama baka da lafiya Abdulfatah?"
Idanunsa da sukayi ja ya bu e a hankali yana kallon ta ya tsana ko kallon fuskar Mufida idan ya tuna salwantar da cikin sa da tayi.


Cikin acin rai ya nuna mata hanyar fita ya ce
"Fita ki bani guri, in ba haka ba kuma rainkine zai aci."




Harara ta watsa masa ta mi e ta ce


"Shidai me hali baya fasa halinsa."
Ta fice tana kunkuni, duk da cikin zuciyar ta tana son sanin halin da Abdulfatah yake ciki amma baza ta iya rarrashi ko banhakuri ba.




Kiran wayar Abba ne ya shigo wayarsa,
Da kyar ya iya mi ewa zaune ya kara wayar a kune.


Salama ya yi
Abba ya amsa da cewa
"Lafiya Abdulfatah kasan gobe ne aurin auran nan kuma na sanar da kai ina son ganin ka, amma baka zoba, ko katafi Hospital ne?"


Cikin arfin hali Abdulfatah ya ce
"Abba ina kwance bana jin da i."


"Subahanallah, me yake damunka?"


Ajiyar zuciya ya sauke ya ce


"Kaina Abba kamar zai cire."


"Ayyah sannu Abdulfatah Allah ya baka lafiya amma ka rage sa damuwa a ranka sai komai yazo maka da sauki."


Kai ya gyada kamar Abba ya na ganin sa.


"Ka kira Doctor ya dubaka?"


"Nasha magani Abba kuma nasan in na samu bacci zanyi dama-dama."


"To Allah ya sawake."
"Amin Abba."


Sukayi salama ya kuma ya kwanta ya na rintse ido cikin tsananin tashin hankali, wai da gaske wannan ba ar yarinyar za'a aura masa? kuma gobe? Kanshi ya ara dafewa cikin tashin hankali ya na maimaita


"Inalilahi wa'ina ilaihirraji'un!.


Har bacci yayi yawan gaba dashi.






Wani ranar sukuku Islam ta yi shi duk wata walima da suka ha ama sai hakura sukayi sabuda Amarya ba lafiya.




Washe gari


Abdulfatah yasai ya tashi kan ya daina ciwo sai dai fa uwar gaba da yaketa fama da ita.
Sa anin Islam da ciwo sosai ya kwantar da ita dole tasa Ummi ta sa aka kaita wani gida a makotansu sabuda hayani ya da bakin mutane.






Gida ya shirya ya tafi dan Abba ya na ta kiransa.


Mama ta ha a taro biki gagarumi har ya nunka na farko a cewarta yanzu tayi sirika.


Ya na fita Mufida ta kira Nuratu ta zo gidan, kuka sha e-sha e Nuratu ta ta da ita tanayi cikin mamaki ta ce


"Lafiya kuwa?"
"Ina fa lafiya yaune bikin Abdulfatah."


Zabura Nuratu ta yi ta ce


"Me kika ce yaushe ya auroki da yake yin kurin aro wata."


Tsaki taja ta ce


"Mtsss dalla ba yinkuri

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login