Showing 33001 words to 36000 words out of 113579 words
Chapter 12 - So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel Document By Bulama.pdf
Ina nema a wajen ki
amman In kikai duba zakiga kamar a cakud’e take da shawara! Shawarar da duk wani
masoyinki na gaskiya zai baki.
Sanann idan kikai haka za ki sanya mutane da yawa farin ciki..
Kinga na farko ‘Abba’
Ta biyu ‘Huda’
Sannan ta uku ‘Ni’.”
Da mamaki Mama take kallonta.
Murmushi Ummi tayi sannan tace “tabbas!
Dan ni gani nake yi ma ko Abba ba zai kaini farin ciki ba saboda kinga na farko
Zan ganshi cikin farin ciki Sannan zai daina blaming d’ina akan na rabaku
sannan idan ba gani nayi na gyara abunda na b’ata ba to
wallahi har abada har In koma ga mahaliccina ba zan iya samun nutsuwa ba!
Ganin ku tare a yanzu
living together happily
zan iya ce miki shine abunda nake da kwad’ayin gani a yanzu fiye da komai a rayuwata”
Zuwa yanzu Mama kam tama rasa bakin magana…
A hankali Ummin tace
“Ki yi tunani mai kyau.
Dan Allah Maryam”
A hankali Mama ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya
tana kallonta kawai..
Sai a lokacin Shuwa wadda shigo tun d’azu tayi musu sallama.
D’agowa sukai suna kallonta, itanma su take kallo har ta k’araso tsakiyar parlourn inda suke,
jikinta duk a sanyaye.
Cikin mutuntawa Ummi ta shiga gaisheta, Itama ta amsa mata cikin karramawa da kulawa kafin
ta k’araso ta nemi waje ta zauna
tana tambayarta “ya mutan gidan?”
Sun d’an jima kafin Huda ta sauk’o.
Shuwa na setin staircase dan haka da ita ta fara tozali!
Salatin da ta rafka sai da ya firgita su Mama dan
haka suka juya suna kallon inda sukaga tana kallo
Ita kanta Huda sai da ta tsorata.
Tun kafin ta k’araso ta rufeta da fad’a!
“Dan mai yasa za ta fito? Aslam d’in ne ya bata izini saboda shima sakare ne irinta!
Ko dai satar hanya tayi ta fito?”
Da kyar ta iya tsayawa ta amsa gaisuwarta daga nan tace “su kama hanya maza maza su koma
gida!
Wannan shirmen ba da itaba..
Ita tunda uwarta ta kawota duniya bata tab’a ganin amaryar da ta fito bata yi sati biyu ba!”
Da kyar ta yarda suka d’an jira driver bayan sun kirashi
amman da cewa tayi ‘bara ta yiwa Abban Ya Jamilu magana ya maidasu
Ai bai dad’e ta kawo Baba ba akwai mota shima a hannunshi.’
Ba a wani dad’e ba
Drivern nasu ya k’araso:
Ba yadda Hudan ta iya ta fara k’ok’arin tafiya ba dan taso ba
haka nan ta yi wa Shuwa sallama ta basu tsarabar da Aslam ya bata kud’i suka tsaya suka siya
daga nan
ta cewa Mama za suyi waya anjima dan da akwai maganar da itama ta shirya za suyi da
Maman.
Har mota Maman ta rakasu,
haka nan ta tafi tanata kumbure kumbure..
Sai da Shuwa taga fitarsu tukunna hankalinta ya kwanta,
yadda tabi ta d’aga hankalinta zaka ce Huda wani gagarimin laifi tayi…
Mama tana dawowa daga rakasu ta zo ta nemi waje ta zauna a gefenta kan 3 seater tace
“Kiyi hak’uri Hajiya nima sai da nayi mata fad’a wallahi.
Wai Ummi ta rako ne shiya sanya. Kin san su family d’in nasu boko ta ratsa su da yawa basu
wani damu da al’ada ba
amman duk da haka na san inda ace a waje d’aya suke da Mommy da ba zata barta ta fito ba.”
Ta k’arashe maganar tana d’agowa ta kalli Hajiya Shuwa wadda tunda ta fara magana ta tsareta
da idanu.
A hankali taji ta sauk’e ajiyar zuciya kafin tace
“Maryam”
“Naam” Maman ta amsa a hankali.
Wata ajiyar zuciyar Hajiyan ta sake sauk’ewa sannnan tace
“Naji duk abunda Ummin tace miki yanzu shigowa ta”
Wani yawu Mama ta had’iye kafin tace
“Hajiya na gama deciding tun tuni
Ba zan koma wa Abba ba!
Ba kuma zan komawa Baba ba!
A barni kawai, itama Ummin
dan tak’i yarda ta saurareni ne
da abunda na shirya gaya mata kenan tun da hakan ne ra’ayi na, bana jin kuma
zai chanja ko da nan da shekaru nawa ne”
A hankali Shuwa tace
“Mai yasa?”
Da tsananin mamaki Mama ta d’ago tana kallonta kafin ta sake yin k’asa da kanta tace
“Hajiya dan girman Allah kar ki biyewa Baaba Talatu wannan karon…har yanzu wasu lokutan
ina jin rad’ad’i a k’afata idan abun ya motsa, bayan k’afata har a cikin zuciyata ina jin tsananin
rad’ad’in azabar da na sha a hannun Ya Usman.
Dan Allah Hajiya kar kice In koma gidansa”
Ta k’arashe maganar
tana me d’ago kanta ta kalli Shuwan da idanuwanta da suka fara zubar da hawaye.
Ahankali Shuwa tayi wani sassanyan murmushi
sannan ta kamo hannunta duka biyu a cikin nata
ta bata dukkannin attention d’inta tukunna tace
“Gidan Abba fa?”
A zabure Mama take kallonta
saboda bata tab’a yin tunanin jin wannan maganar daga gareta ba.
Kasa magana tayi bakinta ya hau rawa da alamun akwai abunda take son cewa amman ta
kasa.
A hankali Shuwa tace
“Maryam, ko ni na kawo taurin zuciya duniya ba zan tab’a bari ki koma gidan Usman ba indai
inada rai a doron k’asa”
Wani kuka ne ya tahowa Mama lokaci d’aya ta sakeshi! Tana sauraron Shuwa tana cigaba da
magana
“A baya na yi kuskure, idanuwana sun rufe da takaici da kuma bak’in cikin ganin kina y’ata
amman kin kasa yi mini biyayya! Wanda hakan ya kaini ga jefa rayuwarki cikin taskun da na
kasa taimokonki kuma na kasa ganin hakan
har sai ranar da aka kawo min ke a karye.
Ban san da wannne baki zan baki hak’uri ba Maryam
ban san ta yaya sannan ta ina zan fara baki hak’uri ba dan laifukan da nayi miki sunada yawa…
Ina jin takaicin yadda na kasa fahimta da ganin laifi da badaidan da na ke ta faman aikatawa da
wuri ba.
Ki yi hak’uri ki yafewa mahaifiyarki Maryam
dan Allah”
Da sauri Mama ta d’ago tasa hannu ta toshewa Shuwa baki tana kuka bilhakk’i da gaskiya.
Cikin kukan ta hau girgiza mata kai alamun ta daina rok’on ta.
Da kyar ta iya cewa
“Hajiya dan Allah ki daina rok’ona, ke fa Mahaifiyata ce,
tayaya za kiyi ta rok’ona haka.
Laifin in dai kece kikayi min
to na riga na saka a raina na yafe miki tun kafin ma ki aikata laifin.”
Kuka itama Shuwa ta fashe da shi, a hankali tasa hannu ta janyo Mama ta rungume ta suna
kuka duk su biyun
gwanin burgewa gwanin ban tausayi.
Muryar Abba Madu wanda basu san da shigowarsa ba suka ji yace
“Ni fa? Za a iya yafe min nima?”
D’agowa suka yi duk su biyun suna kallonsa.
Murmushi yayi ya k’araso inda suke zaune ya zauna akan kujerar shima
A gefen Mama (ya zamana sun sakata a tsakiya shi da Shuwa)
A hankali yasa hannu ya dafa kafad’arta yace
“Za a iya yafewa Abba Madu shima?”
Da sauri ta fad’a jikinsa tana kuka at the same time tana d’aga masa kai alamun ‘eh’.
A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya, wani hawaye mai cike da tarin k’aunar y’arsa da dana sani ya
samu nasarar zubo masa ta ido d’aya!
Hannu yasa ya janyo Shuwa wadda itama take nata kukan ya had’asu guri d’aya da Maryam
d’in ya rungume…….
Mama, ta manta rabon da taji kwatankwacin wannan farin cikin a rayuwarta
a ranta ta shiga aiyyana..
‘ashe zata ga wannan rana?
Ashe zata sake samun wannan opportunity d’in a rayuwarta?
Allahu akbar!
Ubangiji mai zamani
duniya juyi juyi
mahak’urci mawadaci
Tabbas komai in yayi zafi maganinsa Allah
sannan duk nisa jifa k’asa zai dawo!……’
Kuka take yi tana godewa Ubangiji tana sake godiya…..
A hankali Madu ya shiga lallashinsu yana cewa
“Su yi shiru”
Da kyar ya samu Shuwa tayi shiru saannan ta tayashi lallashin Mama
tukunna itama aka samu tayi shirun.
A hankali tasa hannayenta ta kamo nasu sanann tace
“Abba Hajiya
Dan Allah nima kuyi hak’uri akan yadda na gudu na bi Abba, ku yafe min dan...”
Da sauri Abba Madu ya d’aura yatsanshi akan bakinta yace
“Ba komai Maryam, komai ya wuce, Allah yayi miki albarka.”
Juyawa tayi ta kalli Shuwa,
a hankali tana murmushi
Itama ta d’aga mata kai tace “ya wuce!
Allah yayi miki albarka.
Sannan ina neman alfarma nima a wajen ki, kamar
yadda Ummi ta fad’a
nima In ba gani nayi kin koma gidan Abba ba
to ba zan samu peace of mind ba, Ina so in gyara abunda muka taru ni da dangisa da su
Usman muka lalata.
In dai kin yafe min da gaske to inaso ki yi hak’uri ki koma gidan Abba, hakan shine abunda zai
sanyani farin ciki
shine abunda nake so da burin gani a rayuwata”
Cikin sheshshek’ar sabon kukan da ya tahowa Maman tace
“Amman Hajiya..”
Da sauri Hajiya Shuwa
tace
“Ba zan miki dole ba, ba zan
tilastaki ba amman inaso ki sani
Hakan shine zai sanyani farin ciki
hakan shine abunda nake so
hakanne zai tabbatar min
na gyara abunda na b’ata
ya kuma taimakamin wajen sanyani in yafewa kaina.
Ki daure, ni Shuwa Ina rok’on ki
ki koma gidan Abba,
na san har yanzu kina k’aunar sa.”
Sunkuyar da kai Mama tayi tana wani gunjin kuka mai d’aci...
A hankali Shuwa ta share hawayenta sannan ta sa hannu ta shafa kumatun Mama kafin ta
mik’e ta bar wajen da sauri.
Muryar Madu Maman taji yana cewa
“Kiyi hak’uri ki bi shawarar da duk wani masoyinki yake baki
Abba har yanzu yana k’aunarki
kema kuma na san kina sonshi.
Ki duba kiga
ko kwana biyun nan da suka wuce sai da suka zo nan shi da d’an uwansa akan maganarki
Maryama
a zamanin nan
ba lalle a samu mutumin da zai yiwa wata kwatan kwacin k’aunar da Abba yake yi miki ba.
Kamar yadda Mahaifiyarki tace to haka nima
ba zan yi miki dole ba
amman zan baki shawarar
ki bari ki yarda ki amince a maida aurenku da Abba,
hakan zai bashi nutsuwa da farin ciki na har abada
dan a yadda na ganshi ranar da suka zo na san ba abunda yake so da buri sama da a maida
aurenku, nima kuma hakan nake so
Mahaifiyarki itama hakan takeso
Y’arki ma hakan take so
above all
na san kema hakan kikeso
achan k’asan ranki
kawai dai obstacles ne suke son tsaidake ga isa inda zuciyarki take so.”
A hankali ya shafa kanta yace
“Ki yi tunani mai kyau
amman ina so decision d’inki ya kasance abunda kike so ne kuma ki tabbatar zai sanyaki farin
ciki har k’arshen rayuwarki.”
Yana gama fad’in haka ya mik’e ya fice dan lokacin sallah ya gabato….
A hankali Mama take sauk’e ajiyar zuciya, ta dad’e a zaune
sai da ta fara jin kiran sallah tukunna ta mik’e ta wuce d’akinta zuciyarta fal sak’e sak’e…..
Ta san cewa yanzu Abba baya tare da Granpa amman fa duk inda aka je aka dawo uba uba ne,
ba a chanjawa tuwo suna kamar yadda take da tabbacin k’iyayyarta a zuciyar Granpa ba zata
tab’a chanjuwa ba.....
Haka nan, har
dare Mama jikinta duk yayi sanyi kamar wata mara lafiya
Shuwa da Abba Madu basu sake yi mata maganarba
dan basa so suyi ta pressurizing d’inta..
haka nan suka yi dinner atare cike da da so da k’aunar juna suna hira gwanin ban sha’awa
Wani kalar farin ciki kawai Maama take ji wanda ta dad’e bata yi ba, yana ratsa zuciyarta.
A hankali from time to time take d’an fakar idonsu ta juya ta d’auke kwallar farin cikin da ta k’i
daina taruwa a idanunta.
Da daddare tana shirin kwanciya Huda ta kirata,
kamar had’in baki itama maganar Abba ce take so suyi,
bayan sun gaisa ta gama y’an kame kamen ta kafin ta rok’eta
Allah da Annabi ta dawo gidan Mahaifinta.
Cikin son kawar da zancen Mama ta sako wata hirar
ganin da Hudan tayi kamar bata son zancen ne ya sanya bata sake mata maganar ba har sai
da suka zo sallama,
nan d’in ma d’an shiru Mama kawai tayi, chan kuka tace mata “ta gaida Ummi da Aslam tayi
mishi godiya”
sannan ta katse kiran.
A hankali Hudan ta gyara kwanciyar ta akan gadonta ta kwanta rigingine tana mai kallon sama
...........
AFTER TWO WEEKS.
A zaune Ummi ta shigo ta tarar da Hudan ta rafka uban tagumi.
Murmushi tayi ta k’araso inda take ta zauna kafin ta dafa ta.
A hankali Huda ta d’ago tana kallonta wanda hakan ya sanya Ummin ta fahimci kuka tayi.
Karkatar da kai Ummin tayi kafin tace
“Huda ko nice Aslam fa
ba kawo kud’i ba ko
bikin Sakina za ayi ba zan barki ki je ba, wallahi.
Ke kika jawowa kanki
dan haka kar ki zauna kina wani kuka, ai baki ma yi kuka ba ki jira sai Abban ku ya dawo gobe,
na tabbatar in dai yaji labari wallahi da ni da ke kashinmu ya bushe!
Bar ganin yana lallab’a ki in dai yaji wannan zance to fa ba zaku kwasheta da kyau ke da shi ba.
Kuma yana zuwa zan gaya masa tunda ni kin raina ni
Da sauri Huda tace “wallahi Ummi ba rainaki nayi ba.”
Cikin katseta Ummi tace
“Raini ne mana Huda!
K’iri k’iri fa kika hanani number Mama saboda kin san in na kirata na fad’a mata
zata yi miki fada kuma dole ki yi abunda bakya so d’in
so bama kya so taji
ballantana har a kai ga tayi miki magana amma
ni Ina kallon ki kina kallona a cikin gidannan yau sati biyu
kina wasar y’ar b’uya da Mijinki kuma ban isa in hana ki ki hanu ba tunda ban Isa da ke ba”
Cikin kuka Huda tace “Allah Ummi kin isa”
Mik’ewa tsaye Ummin tayi kafin tace
“Idan har na isa to
ki tattara kayan ki da kika kwaso da hannunki ki maida
ki gyara d’akin
ki wanke toilet kafin ya dawo.
Wallahi na manta yaushe zan ce na tab’a ganin Aslam yana gyaran d’aki
amman jiya dakanshi har mopping naga yanayi
kuma ba yadda ban yi da shi akan ya bari a gyara ba amma ya k’i yarda saboda ya san nan d’in
turakarku ce bai kamata a shiga ba.
Dan maiyasa shi yana mutuntaki amma ke ba zaki kwatanta ba?.
Ki tashi kije ki koma
sannan idan ya dawo ki bashi hak’uri tare da alk’awarin ba zaki sake ba…
In dai har na isa da ke kenan, kamar yadda kika fad’a.”
Tana gama fad’in haka ta juya ta fice daga d’akin.
Sai da Hudan taci kukan ta
ta godewa Allah
tukunna ta tashi ta sauk’a k’asan…
Ta yarda zata zauna a d’akin
amman tabbas zata cire tsoro kunya da kawaici su yi agreement ita da Aslam!
Auren su ba na soyayya bane ba Infact k’ok’arin kawo karshenshi ma ya kamata suyi a yanzu
so
ba zai yiu ya hautsina mata kwakwalwa da zuciya ba
bayan ba son juna suke yi ba
so gara su san inda suka dosa kowa ya tsaya a iya limit d’insa…….
Tana shiga d’akin k’amshin turarensa ya mata sallama,
a hankali ta shak’a ta lumshe idanunta! A take wata nutsuwa da kasala suka dirar mata
sannan taji zuciyarta tana yin sanyi b’acin ran da take ciki kuma yana d’an raguwa.
Bud’e idanuwanta tayi ta shiga k’arewa d’akin kallo
tana ganin fuskarsa a idonta, murmushi ne ya sub’uce mata da ta tuna irin uwar hararar da ya
zabga mata sannan yace
“Ba zaki je ba!” ya juya ya fice.
A hankali tace
“Dama maza ma sun iya harara?”
Tana murmushin tana tunani ta shiga gyara d’akin cikin nutsawa kwarewa da iyawa.
Tana gamawa ta shige toilet ta wankeshi tsaf tsaf.
A wajen Ummi taje ta karb’o kasko da turaren wuta ta saka a d’akin sannan ta shiga kitchen ta
had’a masa spring rolls da tea, duk dan a barta ta fita.
Tana gamawa ta fito ta kai dining ta jera a inda taga yana yawan zama.
Tana cikin jerawa Ummi ta sauk’o, dariya tayi kafin tace
“Fad’a na ne?
Ko kuma biyayyar aure?
Ko dai bribe d’in a barki ki fita gobe??”
Turo baki Hudan tayi sannan ta d’anyi murmushi.
A hankali Ummi ta k’araso inda take ta dafa kafad’arta sannan tace
“Na gode Huda.
Kin nunamin nima na isa da ke”
Ta yi maganar tana murmushi.
Murmushi mai had’e da dariya tayi sannan ta fad’a jikinta tayi hugging nata
tace
“Ummina kin isa mana”
A haka su Shuraim suka shigo suka samesu, hakan ba k’aramin burgesu yayi ba kuwa, dan
haka Shuraim ya k’araso ya yi joining hug d’in Sudais kuma ya tsaya ya fara bubbuga k’afa shi
ala dole sai dai a cika su a yi mishi nashi special…
Cika su Ummi tayi yana ganin haka ya k’araso yayi hugging d’inta.
Ahankali ta zaroshi daga jikinta ta kama hannun Shuraim ta rik’e da nashi a waje guda sannan
ta kamo hannun Huda ta saka mata hannayensu a