Showing 9001 words to 12000 words out of 113579 words
Chapter 4 - So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel Document By Bulama.pdf
hanyar Lamido Cresent zuciyarshi fess…
Ganin yadda suka bawa iska ajiyarta suka shiga hirarasu kamar irin sun shekara da sanin juna
d’innan ne
ya sake tunzura Sakina
tun ba ma da Yarinyar tazo sauk’a ba Auwal d’in
har da wani ce mata
“yana isa gida zai kirata in sha Allah”
Ita dai Sakina da kyar take iya jan numfashi, wani irin tuk’uk’i take ji zuciyarta tana yi mata,
bata tab’a jin b’acin rai da haushin mutun irin na yau ba!
Ji take kamar ta rufesu da duka daga shi har ita.....
Da k’arfi taji
gabanta yayi wani mummunan fad’uwa..tabbas abunda take ji
kishi ne!
Kishin Auwal take yi, kenan
sonshi take yi?
Innalillahi wa innailaihirrajiun
How?
Taya ta bari haka ta faru da ita?
A take sai kuma ta fara jin haushin kanta…tayaya
ma zata nuna ta ji haushi k’iri k’iri har haka
Allah dai yasa shima Auwal d’in bai fahimci abunda ta fahimta ba….
Ba tare da yace wata ta dawo gaba ba
Ya ja motarshi yayi gaba yana waving wannan Yarinyar da suka sauk’e..
Yana d’aukar hanya
yayi deleting number d’in nata da ya karb’a
sannan ya danna mata block!
Sai da suka yi tafiya mai d’an nisa sannan ya d’an juyo kad’an ya kalli Khadija yace
“Y’ar uwar, dan Allah ki zama alk’alin mu”
Ya fad’i hakan yana maida hankalin shi akan driving d’in da yake yi.
Murmushi Khadija tayi kafin tace “ok Ina jin ka”
Sai da yad’an juya ya kalli Sakina yaga yanda ta kumbura kafin yayi dariya yace
“2 months kenan yanzu, Ina bin Sakina da proposal amman tak’i accepting.
Inaso ki gaya min me kika fahimta a attitude d’inta na yanzu a game da ni?
Please.”
Murmushi Khadija tayi
zuciyarta d’aya,
a abinda ta fahimta
tace “Kishi!”
Dai dai nan yayi parking a k’ofar gidan Madu.
Da sauri ta bud’e ta fito!
Shima shi da Khadija suka fito suna yi mata dariya.
Ganin tana k’ok’arin wucewa ne yasa yayi saurin rik’o vail d’inta
Khadija kuma tayi masa ‘sai da safe’ ta wuce
Ya amsa yana dariya
dan still dariyar bata gama sakinsa ba saboda ba k’aramin nishad’i yake ji ba….
Cikin tsananin farin ciki
ya dawo ta gabanta ya tsaya yace
“Okay, no more pretends, kawai ki yarda.....”
Maganarsace ta mak’ale sakamokon had’a ido da suka yi, da sauri ya matso kusa da ita yana
cewa
“Subahanallah Sakina daga wasa?
Yi hak’uri, goge hawayen dan Allah na daina”
Ya fada yana shirin sa hannu ya share mata hawayen nata
duk ya rud’e.
Da sauri ta buge mishi hannun
sai kuma wani sabon kukan ya taho mata wannan karon har da sauti! Cikin kukan tace
“Cika mini mayafi”
Da sauri ya cika yana
“Sorry Sakina, wasa ne fa.
Naji to ba kya kishina…”
Wucewa kawai yaga tayi
ba tare da ta waiwayeshi ba ta fad’a cikin gidan ta rufo k’ofar gate d’in da sauri....
A hanyar shiga parlourn taga Khadija tana jiranta su shiga tare amman kawai ta wuceta
ta shige, ko kallon inda take bata sake yi ba.
Bata yarda sun had’a ido da su Ummu da ragowar mutanen parlourn da suke zaune suna hira
kamar rana ba! Haka nan
ta wuce su da sauri bayan tace musu “Ina wuni”
Bata damu da jiran amsar su ba, ta haye sama abunta.
D’akin da suke kwana ita da Khadija da Hudan ta shiga,
tana shiga ta ajjiye vail da jakarta ta fad’a toilet da sauri ta saka sakata
Sai a lokacin ta samu damar sakin kukan da ya mak’ale mata…..
Kuka take tun k’arfinta kamar ranta zai fita, tabbas son auwal take yi
wanda ita kanta bata san ya akayi soyayarshi tayi mata mugun kamu har haka ba!
Gashi bata tashi farga ba sai yau kuma babban abun takaicin shine shima ya fahimta, Infact ko
waye ma yaga yadda ta dinga acting ai dole ya fahimta tunda
gashi ita kanta ta dalilin hakan ne ma yasa ta gane tana k’aunarsa.
Ba abunda yafi k’ular da ita irin yadda ta zubar da girmanta
ta fito k’arara ba tare da ta sakaya ba, kuma wani abun mamakin shine
har yanzu
zuciyarta tak’i yin sanyi
haushi da zafin budurwar nan k’awar su take ji..ji take yi kamar ta hau watsapp yanzunnan ta
gaggaya mata magana..
“Damn it!
Tabbas Ina son Auwal”
Ta furta a fili tana mai fashewa da kuka.
Ko Auwal ne kad’ai d’a Namiji a duniyar nan ta riga ta yiwa kanta alk’awarin ba zata tab’a auren
sa ba!
Tun ranar farko da ya furta mata yana sonta
Infact
ta san ma ba aurene ya kawoshi wajenta ba, idan
ma aurenne ita kam ba zata
tab’a iyawa ba!
Tayaya zata yarda ta zama surukar Granpa da wannan Mom d’in tasa da suka b’oye Huda!
Har gobe tana tuno wasu abubuwan da taji a bakin su Baaba Talatu waenda Granpa d’in ya
yiwa Mama tun farkon auren su da Abba
besides ita tun kafin ta kai haka take adduar Ubangiji ya tsareta daga auren womanizer!
Auwal kuwa ta san yaci uwar womanizer ma tunda gashi har d’a Jalila take shirin ajjiye mishi….
Tana kuka ta yanke shawarar abunda zata yi, duk da
kuwa ta san zata sha wahala
amman its the right thing to do.
Da kyar ta iya cire kayanta
ta yi wanka, ta na fitowa ko goge jikinta bata yi ba ta d’au waya ta kira Ashraff….
Tun lokacin da suka fara dating yake cewa yana so ya turo
bare ma da yaji zancen bikin Huda, ya so ace an had’a da nasu
Ita tak’i yarda..
Bayan sun gaisa ba tare da b’ata lokaci ba tace masa
“Anytime from now yana iya yiwa Mahaifinsa magana sai a fara maganar auren nasu”
Ba k’aramin murna Ashraff yayi ba, tana jin yadda
yake ta faman zumud’i da rawar kai a cikin wayar
Ita dai sai murmushi kawai take yi, k’arshema kasa hak’ura yayi yace mata
“Bara yaje ya duba idan Daddyn nasu bai kwantaba sai yayi mishi maganar yanzun”
Da kyar da sid’in goshi ta lallab’ashi dan 12 ma ta kusa
tace yayi hak’uri ya bari gobe ya sameshi da safe ayi maganar.
Ba dan yaso ba ya hak’ura…
Ya yi ta janta da hira,
ganin kamar a gajiye take dan daga ‘um’ sai ‘um’um’
take iya amsashi da su
ya sanya kawai yace mata “ta huta” dan shi tunaninshi bashi yayi gajiyar biki ce take d’awainiya
da ita.
Tana ajjiye wayar Khadija na shigowa, nan ta tusa ta gaba da zancen Auwal…
“Ta soshi mana, yana da hankali daga gani, ga
kyau, gashi zata zauna kusa da Huda…
Waye waye”
Ita dai Sakina k’arshe juya mata baya tayi, tayi mata banza kamar tayi bacci, ganin
haka yasa Khadijah kashe fitila, abunku da mai k’aramin ciki tuni tana kwanciya bacci yayi awon
gaba da ita!
Sakina kuwa yadda taga rana haka taga dare
Wani abun mamakin shine
duk wani labari da plans da Ashraff ya gama gaya mata na bayan aurensu yanzun
she can’t help it but to picture it ita da Auwal!
K’ok’ari take yi ta danna k’iyayyar shi a cikin zuciyarta
sai dai abunda bata saniba
ta riga ta makara dan
already zazzafar soyayyarshi ta riga ta rinjayi y’ar guntuwar k’iyayyar da take k’ok’arin dannawa
zuciyarta ta k’arfi da yaji.....
BULAMA ✍️
So da Buri
Free Book
57
Da kyar Aslam ya iya mik’ewa bayan fitar su Auwal.
A hankali yana jin yadda zuciyarshi take bugawa da mugun k’arfi ya isa bakin k’ofar d’akin da ya
ga su Sakina sun fito daga ciki.
Da kyar ya iya d’aga hannunshi ya fara knocking….
A hankali kamar mai kuka yaji tace
“Sakina shigo mana”
Dan ita har ga Allah ta yarda da Sakina wadda tace mata ‘bara su je su yi siyan baki ta dawo
Ai ita a nan ma zata kwana yau’.
A hankali ya lumshe idanuwasa ya bud’e
kafin ya murza handle d’in ya tura k’ofar ya shiga da sallama.
Da sauri ta d’ago jin muryar Namiji!…
Duk da su Sakina sun ja mata mayafinta kafin su fita amman tana iya hangoshi!
Har yanzun shadda ce a jikinshi abunda bata tab’a ganiba kenan. Sai taga yayi mata mugun
kyau!
Tsayi kamala surar jikinshi ta cikakkaen lafiyayyen Namiji ta fito sosai…
A take zuciyarta ta hau bugawa da sauri da sauri.....
Takowa yake yi izuwa bakin gadon wanda hakan da yake yi ji take kamar a kan zuciyarta
yake yin tafiyar..
Duk taku d’aya sai taji tamkar numfashinta zai d’auke ne!
Hakan yasa ta fara ja da baya..
Yana matsowa ita kuma tana ja baya.
Aslam shi bai ma lura da yadda take ja da bayan ba
har sai da yaga sun kai edge d’in gado tana neman mik’ewa,
dan shi har ga Allah
ba abunda idanuwanshi suke gane mishi sai ita, ruhinta!
shiyasa sam bai lura da movement d’inta ba…
Yana isowa dab da ita, ya jaa ya tsaya a bakin gadon.
Ita kuma sai k’ok’ari take ta mik’e amman k’afarsa da side drawer sun tokare ta gashi
har ta kai jikin fuskar gadon
so ba daman ci gaba da matsawa…
A hankali taga yana d’an sukuyowa….ji take yi kamar ta bud’e murya ta kurma ihu!
Ko kuma ta tashi ta yi tsalle ta fad’a tsakiyar gadon daga nan ta samu ta sauk’a ta d’ayan side
d’in…
Ita har ga Allah tun farkon had’uwar ta da shi, sam! Bata k’aunar zama a kusa da shi (Aslam)
Saboda muddin suna tare no matter how she tries kwata kwata zuciyarta bata barin wannan
mahaukacin gudun data rasa dalilinsa!
Gashi bata san dalilin da ya sa yaketa matsowa kusa da ita ba..
Ita fa yanzu abunda ya kamace su shine
su nutsu su yi tunanin ya za suyi da rayuwarsu da wannan auren da aka k’ulla musu
shiyasa duk a rud’e
sannan a rikice take kuma gashi yanzu ya zo ya sake rikitata……
Tana cikin wannan tunanin
ta ji fuskarsa daff da tata!
A hankali taji yasa hannu ya yaye lullub’in laffayar fuskarta..
Had’a idanu suka yi!
Da k’arfi zuciyoyinmu suka buga a tare!
Sai da ya lumshe idanunsa ya bud’e kafin ya sak’ale kwayar idanuwanshi da tata sannan yace
“Assalam alaiki, Maryama.”
Da mugun k’arfi ta runtse idanuwanta sannan
dai dai nan hawayen da bata san dalilinsu ba suka b’alle mata a take.
A hankali ya hau yi mata kallon k’urilla….
Cikakkiyar minti d’aya ya d’auka yana kallon fuskarta
kafin da kyar ya samu ya iya kokawa da zuciyarshi ya d’auke idanunsa yana mai lumshe su..
Wata zazzafar ajiyar zuciya ya sauk’e wadda itama bata san lokacin da ta sauk’e tata siririyar
ajiyar zuciyar ba
sakamokon numfashinsa mai d’umi da dad’in shak’a da ya ziyarci hancinta wanda
har zuciyarta sai da ta amsa!
Hakan ne kuma ya haifar mata da sauk’e ajiyar zuciyar da bata shirya wa ba…
A hankali ta ji sauk’ar wani lallausar tafin hannu kamar na jarirai mai mugun taushi
a kan kumatunta!
A mugun zabure ta bud’e idanuwanta da suka k’ank’ance suka yi jaa ta zuba masa su..
Bai damu da kallon da take yi masa ba! Kallonta kawai yake yi yana goge mata hawayen nata…
Idanuwansa da ya zuba mata ya kafeta da su ne ya sanya ta runtse nata idanuwan jikinta na
wani mugun rawa!.
Wata ajiyar zuciyar kawai ya sake sauk’ewa...yana gama goge hawayen ya mik’e da sauri dan
ba k’aramin kokawa yake yi da zuciyarsa ba tun lokacin da ya shigo!
Sai da ya lumshe ido na some seconds tukunna ya bud’e yace
“Ki taso mu je kici abinci”
Kafin ya rufe bakinsa tace
“N na na k’oshi”
Tana mai jan numfashi
har yanzu jikinta bai daina rawa ba.
Be ce mata komai ba, ya sa kai ya fice a d’akin.
Minti kad’an ya dawo
da ledojin da Auwal ya shigo da su..
Gefenta ya nema waje ya zauna a bakin gadon!
A hankali ya bud’e ledojin ya d’aura akan stool
kafin yace
“Oya, gashi ki ci.
Akwai wani abun da kike buk’ata?”
Da sauri ta girgiza kai alamar ‘a’a’.
A hankali ya mik’e
yace
“Sai da safe”
Tun kafin ya rufe bakinshi tace
“Allah ya kaimu”
Don so take ya fita.
Shima
lura da hakan da yayi ne dama ya sanya kawai ya mik’e d’in.
Ajiyar zuciya ya sauk’e kamar zai ce wani abun sai kuma kawai yace
“Allah ya tashe mu lafiya”
Yana mai juyawa ya fita daga
d’akin gaba d’aya”
Yana fita ta sauk’e wata wawiyar ajiyar zuciya…
Har ta d’an zauna sai kuma ta mik’e da sauri ta isa bakin k’ofar ta murza key ta zare ta taho da
shi ta ajjiye a kan side drawer tana ta tunani….
Ta dad’e bata sha mamaki irin na yau ba!
Yadda yake yin abu kan sa tsaye sannan kamar bashi da wata damuwa abun yayi mugun
d’aure mata kai!
Dubafa yadda ya wani zauna a kusa da ita sannan har da wani share mata hawaye..
Ita tana tunanin sai ta yi kusan kwanaki ma bata ganshiba
daga nan ya bata takarda yace taje ta auri Arshaad d’inta
Amman kalli abunda yayi tun yau..
Ba abunda yafi d’aure mata kai irin siyan bakin da aka yi
sai kace waenda suka yi auren soyayya…
Harga Allah yunwa take ji
sosai ma kuwa
amman d’aurewar da kanta yayi ne ya sanya ta mayar da kajin cikin ledarsu ta had’a da ledar
drinks d’in ta saka a d’an k’aramin fridge d’in data gani a d’akin.
Da kyar ta lallab’a ta yaye laffayar jikin ta ta ninke,
ta shiga toilet ta d’auro alwala tazo ta nemi waje ta zauna
dan
already sun yi sallolinsu Magrib da Isha ita da su Sakina.
A ranta ta gama ayyanawa
tabbas idan aka yi d’an kwana biyu taji Aslam bai yi mata wata magana ba
to ita kam zata tareshi da zancen ya saketa!
Idan ma Mahaifiyar Ya Arshaad ta hana aurensu
to zata hak’ura ta rungumi k’addara tayi facing karatunta
idan Allah ya fito mata da wani ta yi aurenta
amman ita kam ba zata iya zama da wannan murd’ad’d’en mutumin da bashi da alk’ibla ba!
Infact tayaya ma zata zauna da mutumin da kullum in dai suna tare sai taji zuciyarta tana
barazanar fashewa
haka kurum salon yaje ya fasa mata zuciya a banza ya yiwa Mama da Abba da su Sakina
asara,
Inaa ba zai yiu ba!
Da wannan tunanin ta kwanta akan lallausan gadon tana mai lumshe ido…
Nan kuma ta fad’a tunanin Arshaad!
Tana yi tana istighfari amma sam ta kasa dainawa.
Tabbas sai ka rasa abu kake gane yawan son
da kake yi mishi!
A lokacin da take tare da Arshaad bata san tana sonshi haka ba sai yanxu da ta san In ba da
kyar ba to ta rasa shi kenan har abada!
Dan muddin Mahaifiyarsa bata basu go ahead ba to ita kuma tayi alk’awarin ko sonshi zai
kasheta ba zata tab’a aurensa ba tare da albarkar ta ba!
Besides sai ma ta fara nemo mafita akan wannan auren!
She has to do something fast
saboda taga take taken Aslam kamar shi zai iya hak’ura ya zauna da ita don ya faranta ran su
Abba
Kuma ta tabbata idan hakan ta faru to haka za su k’are rayuwarsu
ba soyayya
tunda ita dai zuciya d’aya Allah ya bata kuma ta riga ta damk’awa Ya Arshaad
shima kuma Aslam d’in ta tabbata bai ya k’aunarta
sai dai ya kawai ya zauna da ita saboda ba yadda ya iya
To Ina riba?
Garama shi Namiji ne
anytime idan ya had’u da wadda yake so zai aura
Ita fa?
An cuceta an cuci Ya Arshaad d’inta..how she wish she can see him now..tana so
taga halin da yake a
ciki, bawan Allah d’azu ba kalar zargin da batayi mishi ba
ashe fin k’arfinsa aka yi….
Bata san lokacin da wani mugun kuka ya kufce mata da k’arfi ba.……
Tunani da kuka basu barta ta rintsaba sai around 2:00am
tukunna
bacci ya kwasheta
wanda bata yishi cikin dad’in rai ba.
Kafin asuba ta farka
sakamokon mugun ciwon kan da ya rufar mata,
da zazzafan zazzab’i
ko idanuwanta bata iya bud’ewa sosai in banda rawar sanyi ba abunda take yi.....
Tanaji ana kiran sallah
k’ok’ari take yi ta samu ta tashi amma sam ta gagara....
A b’angaren Aslam shima bai samu yayi ishashshen bacci ba
kusan kwana yayi yana nafila..
A nan kan daddumar ya samu bacci ya saceshi.
Kiran sallar farko da aka maka a masallacin cikin estate d’in ne ya farkar da shi, dan
haka ya mik’e ya shige bathroom…
Sai da yayi wanka ya d’auro alwala sannan ya fito ya d’an
kimtsa ya zura jallabiya ya gabatar da fajr nafl, ya zauna karatu.
Yana idarwa ana tada sallah
dan haka a gurguje ya fice ya nufi mosque..
Ya so ya duba Huda
amman gudun