Showing 6001 words to 9000 words out of 113579 words

Chapter 3 - So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel Document By Bulama.pdf

Bulama   

28 May 2025

8288

dangana sanann ya zab’awa
Hudan Arshaad da Aslam dukkan nin abunda yake alkhairi ne a rayuwarsu.

Tun jiya na hango silver lining.
Shiyasa yau na tilasta mishi yaje d’aurin auren!
Idan an d’aura auren Huda da Arshaad a gabanshi na san hakan zai taimaka mishi
akan ace ya gudu daga reality da nauyin hope!
Idan kuma an d’aura da shi to falillahil hamdu.”
Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin ta ci gaba
“Tunda har Aslam ya iya kawar da komai ya cire kunya ya furta mini cewa yana son Huda to
tabbas na san ba k’aramin so yake yi mata ba!

Ki duba kiga yadda suke shi da Arshaad da kuma kawaici irin nashi amman ya kasa hak’ura!

Na san Aslam tun yana Yaro k’arya ba abunda ya iya baneba besides why will he even lie?
All that I’m trying to point out miki anan shine
Hudan ta tafi gidan wanda yake k’aunarta matuk’a!
Ki kwantar da hankalinki ki bisu da fatan alkhairi.........”


Direct MT estate aka wuce da ita...
Already Mommy ta saka masu aiki sun share sun goge side d’in Aslam sai tashin k’amshin
turaren wuta yake yi.
Ba abunda babu na fannin furnitures, duk ragowar d’akuna ukun akwai gadaje masu kyau!
Parlourn ma yana d’auke da duk wani abun buk’ata.

Motocin suna gama yin parking aka fara firfitowa.

Tun a gate na estate d’in Anty Zainab taji inama bata zo ba!
Gashi mata y’an Maiduguri da suka shigo mota d’aya tare da su sai faman zuzutawa suke yi
suna
“Ma shaa Allah! Huda kam Allah ya bata duniya” ita kuma tanajin kamar ranta zai fita!
Sannan kanta ya d’an juye
dan cewa aka yi gidanta ita kad’ai ce yanzu kuma taga an kawota nan!.
A haka dai tana ji kamar zuciyarta zata fashe ta biyewa jamaa akai ta washe baki da ita, ta bari
akan In sun koma zata bugi cikin Khadija ta ji komai dan ta san idan ba bugar cikin nata tayi ba
to ba zata tab’a gaya mata ba!
Sun sha yin fad’a da ita Khadijar ba sau d’aya ba akan su Hudan.

Ummi da Ummu ne suka ruk’ota, suna zuwa main door na shiga gidan suka umarceta da ta

shiga da bismillah da k’afar dama, haka ma k’ofar side d’in Aslam da tazo shiga!
Yadda suka ce hakan take yi da fuskarta a rufe cikin laffaya tanata kuka.

Sai da suka kaita bakin gadonta sannan suka ajjiye ta da bismillah.

Bayan an d’an ragu a d’akin
Ummu ta k’ara mata da nitsatsiyar nasiha!
Basu wani dad’e ba suka fara shirin tafiya hatta gifts da abincin da Dad ya shirya musu ma
mota kawai aka kai
dan suna idar da sallar Magrib suka fara zuwa suna yi mata sallama suna ficewa……
Jama’a da friends d’insu in banda santin estate d’in da side d’inta ba abunda suke yi,
a haka kowa ya watse.
Aka barta ita da su Sakina da Khadija da friends d’insu guda biyu da suka zauna dan ragowar
cewa suka yi ‘za su wuce saboda basa so su yi dare’…..
Da kyar da sid’in goshi Huda ta d’an tsayar da kukan nata, bayan dogon lallashi daga su Sakina
ta yi shiru
ta bud’e fuskarta.
Tana jinsu suna ta hira ana shewa amman ta kasa tanka musu
Istigfari kawai take tayi
saboda sam! Tunanin Arshaad yak’i fita daga ranta.

Daga masallaci direct gida Aslam da Dad suka wuce side d’in Mommy.
Suna zaune ita da Gwaggo Asabe da alamun magana suke mai muhimmanci su Dad d’in suka
shigo.
Mik’ewa Gwaggo Asabe tayi zata fita Dad yayi saurin cewa “ta dawo ta zauna
Nasiha za su yiwa Ango!”….
Sun kusan 1 hour suna yi masa Nasihar
daga nan Dad ya mik’e yayi musu sai da safe.

Kana ganin Mommy da Gwaggo Asabe ka san suna cikin farin ciki.

Mommy ce tace
“To ka tashi ka je kuyi siyan bakin mana.
K’awayenta fa kai suke jira su tafi”

Kamar zai yi kuka yace
“Mommy siyan baki kuma?
Kin san fa a yanda auren nan yazo. Ki barshi kawai su yi tafiyarsu,
Ina son ganin Arshaad
first.”
Ya fad’a yana mai mik’ewa zai fita.

“Baya nan”

Yaji muryar Mommy.

Da mamaki ya juyo kafin yace
“Ina ya je?”

“No body knows”
Mommy ta fad’a tana mai mik’ewa ta k’araso inda yake.
“Baka farin cikine?
Yau?”

D’an Satar kallon Gwaggo Asabe yayi yaga hankalinta sam baya kansu…. A hankali ya sauk’e
ajiyar zuciya kafin yace
“Mommy ba wanda ya kaini farin ciki a kaff fad’in duniyar nan a yau!
Amman no matter how i tried sam! Na kasa ignoring some facts ne, If I were in Arshaad shoes I
would have die by now.
Gara ka san abu ba naka bane ba tun farko akan ka saka rai kuma azo baka samuba daga
k’arshe.”

Ajiyar zuciya Mommy ta sauk’e
kafin ta shafa fuskarshi
ta d’anyi murmushi
a ranta ta raya
‘Inama ace kowa irin zuciyar Aslam d’inta gareshi, da
duniya ta zauna lafiya’….
Muryarsa ce ta katseta
jin yana cewa
“Bara inje In fara nemansa”

“Ka fara zuwa ko kai da Auwal ne ya rakaka ko?
Karka janyo mata abun magana mana a wajen k’awayenta”

Sunkuyar da kai yayi
chaan! Ya d’ago yace “okay”
Sarai Mommy ta san ba iya kiran Auwal d’in zai yi ba
shiyasa ta yanke shawarar ta kirashi da kanta.

Yana d’aki.
Shi kad’ai…
Ya gwada kiran Arshaad yafi sau nawa amma baya d’auka!
K’arshema kashe wayoyinshi yayi dan in ya kira sai dai yaji ance switchoff!
Babban abubda yafi damunshi shine rashin sanin inda Arshaad d’in yake…
Suna dawowa gidansu ya nufa
Aaima ce take fad’a mishi yadda suka yi d’azun dan haka hankalinshi a tashe ya fita nemanshi

amman ba inda bai dubaba ya nemeshi ya rasa!
Yana a haka kiran Mommy ya shigo wayarsa. Bayan sun gaisa ne
tace
“Yazo ya raka Aslam wajen
Amarya, k’awayenta suna jiransu ba su tafi ba sannan
ya d’an taho da snacks da kaji”
Da “to” ya amsa ta
daga nan suka yi sallama.

Ko da suka gama wayar sai da ya kusan minti biyar yana tunani tukunna ya mik’e
ya fita….

Kamar Mommy ta sani Aslam yana fita d’akin shi ya nufa ya zauna shi kad’ai yanata tunani..
Chan kuma ya zaro waya ya fara gwada kiran Arshaad amman sai yaji a kashe!
Har ga Allah yana son Huda
fiye da tunani dan
inda ace bai sameta ba
to da bai san ya zata kasance da shi ba
amman kuma
yana matuk’ar jin tausayin Arshaad! Bai san me yake going through ba!
A fili yace
“Wannan wacce irin k’addara ce?
Ya Allah Astaghfirullah.”

Ya jima tukun yaji knocking.
Izinin shigowa ya bada ba tare da ya san wanene ba.
Kallon kallo suka tsaya yi wa juna shi da Auwal bayan ya shigo, chaan kuma Auwal d’in ya
k’araso yazo ya zauna kusa da shi.
Ko gaisawa ba suyi ba ya fara magana
“Yanzu ya za mu yi?
Su Abba sun k’ulla abunda zai iya janyo babbar matsala
su Mommy su kuma naga kamar they are okay with it!
Ko ka san yanzun nan ta kirani wai In taho da kajin Amarya muje in rakaka a yi siyan baki
As if ba abunda ya faru.
Aslam na san kaima baka son auren nan amma idan kace za kayi shiru ko kuma kace bara ka
yiwa su Abba biyayya dan kar su ji ba dad’i to akwai matsala fa!
I can’t even begin to tell you yadda Arshaad yake son Huda.
You have to speak tun kafin a lalata muku future ku duka ukun.
Dubafa yadda kayi fainting
amman bayin Allah n nan ba wanda a cikinsu yayi yunk’urin yace a raba auren!
Duba kaga Arshaad is no where to be found
amma ba wanda ya damu!
Ita kanta Huda na san ba zata ganu ba yanzu, Iya event d’insu da bai je ba jiya sai da ta shiga

tashin hankali!
Ku yi ending abun nan tun kafin ya janyo matsala Aslam
kar ka yi shiru ka cuci kanka.”

Tun da Auwal ya fara magana Aslam ya kafeshi da idanuwa,
sai da ya kai aya sannan ya d’auke idanunsa daga kansa ya mik’e tsaye kafin yace
“Like Mommy said!
Mu je ayi siyan bakin, a samu
a mayar da friends d’inta gida.”
Yana gama fad’in haka ya wuce yayi gaba.

Jiki a sanyaye haka Auwal ya mik’e ya d’auki ledar da ya shigo da ita ya bi bayanshi yana
mamakin firgici, b’acin rai da tsananin tashin hankalin da ya hango a kwayar idanun Aslam d’in.

Auwal ne ya kira Sakina…
Kamar ba zata d’auka ba
sai kuma ta d’aga.
Tana d’auka bai jira jin tsiwarta ba yace
“Muna parlour, ku fito”

Tana ajjiye wayar, ta fad’a musu dan haka suka mik’e suka fita.

Yadda al’ada take ake siyan baki haka aka yi..
500 thousand suka yi demanding Auwal kuma ya basu
1M!

Kud’in k’in shiga account d’aya yayi tashi d’aya sai da
suka bada account wajen uku
tukunna ya juye musu.....


K’awayensu kasa hak’uri suka yi sai da d’ayar ta d’an matso k’asa k’asa ta tambayi Sakina “ya
akai aka samu chanjen Ango ne?”

“Haka al’adar mu take!
Muna yin Angon bogi a wasu events d’in”
Haka kawai tace musu daga nan ta kauda kai.

Tabbas bata gamsu da ita ba
amman ganin yadda ta turb’une fuska kuma ta san halinta hakan ya sa kawai ta hak’ura ta
koma gefe ta ja bakinta ta yi shiru.

Ita kuwa Sakina ba wani abun bane ya sake tunzurata

sai d’ayar k’awar tasu wadda ta lura da ita tun da aka fara siyan bakin! In banda
rawar kai da shishshigewa Auwal ba abunda ta saka a gaba.
Duk da ta lura da yadda yake d’an basar da ita.....


Har aka yi siyan bakin aka gama in banda gaisuwa ba abunda ya shiga tsakanin su da Aslam.

Ana gamawa
ba tare da b’ata lokaci ba dan dare yayi Auwal yace
“su taso a maidasu gida”
Dan dauriya kawai yake yi amman baya jin dad’i, kamar shi ne Arshaad haka yake jinshi gaba
d’aya jikinshi yayi sanyi, kana ganinshi ka san baya jin dad’i duk yayi wani iri
gashi kanshi sai faman ciwo yake yi.
Ganin ba zai iya kaisu shi kad’ai ba yasa bayan sun fita ya nemi layin drivers d’in estate d’in
mutum biyu yace “su zo akwai ragowar mutane su taya shi maida su”
Cikin minti k’alilan suka shigo da motocin compound d’in gidan su Aslam
su biyu.
Tun kafin su gama parking ya bud’e gaban motar shi ya juyo yana kallon Sakina, suna
had’a ido yace mata “bismillah”
D’auke kai tayi ta kama hannnun Khadija ta fara ja tana cewa
“Zo mu je mu shiga wachchar..”

Da sauri wannan k’awar tasu tazo ta wuce ta gaban Sakina ta shige gaban motar Auwal d’in
inda ya bud’ewa Sakina ta zauna kafin ta juyo tana wani shu’umin murmushi tace mishi
“thankyou”

Sakina bata san ya aka yi ba kawai ganinta tayi a bakin motar a tsaye!
Batare da ta kalleshiba ta bud’e baya ta shiga ta zauna
Khadijah ma ganin ta cikata ta nufi motar ya sanya ta biyota itama ta shiga ta zauna ta rufe
matar dan tafiyarsu d’aya.

Ragowar y’an mata biyun kuma suka shiga motocin drivers d’in.


K’amewa Auwal yayi a wajen ya kasa motsi,
mamaki fal a ranshi,
da kyar bayan ragowar motocin sun fita ya samu ya ja k’afafuwansa ya shiga ya tada motar……

Da gangan ya saita madubin gaban motar daidai fuskarta
aikuwa ya ga ta had’e rai kamar an aiko mata da sak’on mutuwa!
A take ya ji
dariya ta taso masa, anya
kuwa abunda yake tunani shi d’in ne?

Sakina fa!?
Kenan daman ta san tana sonshi amma take ta faman wahalar da shi haka?
Woow!!
Allah yasa to hakan ne
dan in dai kuwa hakan ne da gaske to tabbas sai ya fi ko wanne d’an Adam farin ciki a fad’in
duniya…..
Haka nan shi kad’ai yana ta sak’e sak’e a ransa sai faman murmushi yake yi shi kad’ai yana
driving
wanda hakan kuma ba k’aramin tafiya da imanin k’awar tasu wadda ta shigo ta zauna a gaba
gefen shi yayi ba.

Sakina tana ganinta har wani
juyawa tayi tana facing Auwal d’in tana murmushi itama,
ji tayi kamar ta shak’o ta! In banda tafarfasa babu abunda zuciyarta take yi tun lokacin da k’awar
tasu ta shige motar ta zauna har kawo yanzu..
Numfashinta har wani d’ad’d’aukewa yake yi!
Itafa daman tun a school ta tsani Yarinyar nan dan ko ishashshen shiri ma basa yi
gata da k’aryar kud’i
tun suna school
dan duk waya idan ta fito a hannunta ake fara gani
(ta yi sneaking ta shigo da ita)
Gata da shegen rawar kai
da son a sani
shiyasa kwata kwata ita Yarinyar bata yi mata ba!
Ko inviting d’inta basu yi ba daga ita har Huda amma ba event d’in da bata zo ba!
Kalleta ba dangin Iya bare na Baba amman itace har kusan 11 a waje! Ta taho kawo Amaryar
da ba wani shiri suke yi ba...
Kamar idanuwanta za su fad’o haka ta tak’ark’are take zabgawa Yarinyar harara….

Sarai Auwal yana sane da ita don yana kallonta!
Wani farin ciki yake ji kamar ya zuba ruwa a k’asa ya sha.
Wai da gaske Sakina kishinsa take yi har haka?
Tayay to zai tabbatar?
Ya yiwa kansa tanbayar.
Wani malalacin murmushi ya saki ta gefen bakinshi…
A hankali ya juyo ya kalli k’awar tasu wadda ita ma shi d’in take kallo, tun
ranar cocktail ya tafi da imaninta, jiya har mafarkinshi ta yi!
Yau kuwa ba zata bari ya sub’uce mata ba in sha Allah…

Murmushi ya sakar mata
ganin itama shi d’in take kallo,
a hankali but yadda ya san Sakina za ta ji yace
“Hey dear beautiful, where to?”

Da sauri ta koma baya ta jingina da jikin kujera jin zuciyarta zata faso waje.
Wani sanyi Auwal yake ji yana ratsa shi dan yana kallonta duk ta cikin glass,
he won’t lie
this is the best day of his life!.

Sai da budurwar gefen nashi ta sake cewa “Lamido crescent”
Cikin rangwad’a da kashe murya tukunna ya jiyo ta
dan gaba d’aya hankalinshi yana kan Sakina.
“Okay”
Kawai yace
yana mai karya kan motar dan har sun fara gocewa daga hanyar da za ta kaisu Lamido
Crescent d’in.

Da mamaki Sakina ta mik’e ta zauna da kyau tana kallon yadda ya juya akalar motar ya d’au
hanyar Lamido Crescent.
Bata gama shan mamaki ba sai da taji budurwa tana cewa
“Ko za ka saka min digits d’inka!
Sai mu dinga gaisawa”

Murmushi mai had’e da dariya yayi yana mai kallon fuskar Sakina wadda tashi d’aya
idanuwanta suka cicciko da hawaye kamar zata fashe da kuka!
Har ga Allah yad’an ji tausayinta amma yana so yayi comfirming a yau d’innan
sannan idan ma bata saniba
to yana so yau ta san tana son shi. Dan haka ya juya yana kallon Yarinyar gefen nashi cikin
wani kalar voice yace
“Yes sure, kamar kin shiga zuciyata dan nima i was just about to ask for your number”

Tana shirin yin magana
suka ji Sakina tace
“Um, idan ka sha kwana za mu sauk’a”
Da saura Khadija ta juyo tace mata
“Ke da wa??”

Cikin fushi Sakina tace
“Ni da ke!
Idan kuma ba zaki sauk’a ba to ni zan sauka!
Kina gani fa sai ya kaita tukunna zai dawo ya kaimu
saboda ga gantalallu.”

Ya so dannewa amman sai da dariya tayi nasarar sub’uce mishi, hakan kuwa ba k’aramin sake
tunzura Sakina yayi ba
dan haka a zuciye ta sa hannu zata bud’e k’ofar motar a hakan ta tana tafiya ba tare da ta jira

an tsaya d’in ba.

Shi kuma Auwal yayi maza ya danna lock!

Murmushi Yarinyar gaban motar tayi
kafin tace
“Kaga dear mu je ka fara ajjiye su, in yaso sai ka dawo ka kaini daga baya”

“Alright”
Auwal d’in yace
daga nan taga ya saka signal yana shirin juya kan motar, a cikin ranta sai kuma ta raya
‘Kuma fa idan ya sauk’e su
tare daga shi sai ita zasu dawo a motar, a hanya su yi ta hira!’
Dan haka da sauri sai tace
“Da yake ke gantalalliyarce ba?
Kin gwammaci a kaimu sannan a dawo da ke?”

Yarinyar taji zafin maganar ba kad’an ba amman gudun kar ta zubar da girmanta a gaban sabon
saurayinta yasa taja bakinta tayi shiru
ta kawar da kai!.

Rai a d’an b’ace Auwal d’in ya juyo yace
“Sakina saboda ku fa tazo bikin nan!
Wanne irin attitude ne haka?”

Cikin fushi da bala’i tace
“Ban sani ba!”
Tana mai kauda kai.

Gani tayi ya juya kawai yana shirin d’aukar hanyar gandun albasa dan haka tace
“Wallahi baku isa ba!
Ka fara kaita ka ajjiye ta tukunna ka kaimu.”

Shiru ne ya biyo baya a motar
kafin Auwal ya juya ya nufi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login