Showing 12001 words to 15000 words out of 113579 words

Chapter 5 - So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel Document By Bulama.pdf

Bulama   

28 May 2025

8300

kar ya makara yasa ya fita da niyyar ana idarwa zai dawo ya duba ta.

Azkar kawai yayi daga nan ya fito daga masallacin.
A k’ofa suka had’u da Dad
dan haka suka jera yana d’an yi mishi nasiha har suka iso gidan..
Jan hankalinshi yake sake yi akan ya rik’e amana dan Allah kar ya wulak’anta matar da suka
zab’a masa, ya
taushi zuciyarshi ya bata dukkan hakkin ta da kulawa
wata rana zai k’aunaceta in sha Alla…

Shi dai Aslam da ‘to’ ‘in sha Allah’ kawai yake ta binshi
dan ya rasa dalilin da yasa zuciyarshi taketa faman azalzalarshi akan yaje ya dubata..
Sam ya kasa sukuni ballantana ya samu ya bawa Dad d’in hankalinshi..

Da kyar ya samu Dad ya barshi ya wuce side d’inshi,
bayan yace mishi “ya tabbatar sun je sun samu Granpa”…
..saboda ta watsapp yaji yace mishi zai nemeshi tun jiya amman har yau shiru,
kar aje ko fushi yayi
shi kuma har ga Allah baya so ya je ya sameshi gudun rigimarshi yake kuma bai san a wanna
mataki ya saka maganar auren Aslam d’in ba
gara idan Aslam d’in yaje da kanshi maybe abun yazo da sauk’i…

Da ‘to’ Aslam ya amsashi
sannan suka yi sallama
ya wuce side d’inshi

yana dariya da mamakin Dad d’in
k’iri k’iri ya hango tsoro a tartare da shi..wato sun yi abu amman kuma suna tsoro
shine bara su tura shi..
Da wanna tunanin ya Isa bakin k’ofar d’akin da Huda take ciki ya d’anyi knocking sannan ya
murza handle d’in da niyyar turawa amman k’ofar sai ta k’i motsi, a hankali yad’an sake yin
knocking amman still yaji shiru…
Yayi mata knocking yafi sau biyar amma yaji shiru
dan haka ya d’an sassauta murya ya matsar da fuskarshi jikin k’ofar ya fara kiran sunanta…

A take gabanshi ya yanke ya fad’i! Dan in dai kunnuwanshi sun ji mishi dede to
kamar sheshshek’a da jan numfashi yake jiyowa yana tashi daga d’akin!

Da mugun sauri ya koma d’akinsa ya d’auko spare key
sannan yazo ya zura ya murza ya tura da sauri ya shiga

A k’udundune ya hangota a kwance tana rawar sanyi
Da sauri ya k’arasa ya d’agota ya zaunar sannan ya fara shafa goshinta wanda ya ji ya d’auki
zafi ba na wasa ba.
A firgice yake kallonta,
gaba d’aya ta jik’e da gumi kamar an watsa mata ruwa,
pillow ya jawo ya kwantar da ita sannan ya mik’e ya nufi toilet ya jik’o towel ya fito..

Hannuwanta da tafin k’afarta sai saman goshinta ya shiga shafawa towel d’in amman kamar
k’ara mata zazzab’in ma yake yi dan haka kawai ya
mik’e ya je d’akinsa ya d’au waya ya kira Doctor tukunna ya dawo ya ci gaba da goga mata… ji
yake kamar yayi kuka gani yake yi duk laifinshine dan inda a d’aki d’aya suke da tun farkon
zazzab’in nata zai yi noticing ya san abun yi…..

A hankali ya ga tana bud’e idonta, da sauri ya matso yace
“sannu ya jikin?”

A hankali ta shiga motsa bakinta a lamun magana take son yi..

Hannunshi yasa a a gefen kumatunta yana kallonta kafin yace
“me kikeso? Tell me.
Yanzu Doctor zai zoo kin ji, sannu” ya k’arashe maganar
a hankali yana kallon bakinta da take k’ok’arin yin magana..

Murmushi ya ga ta fara
kafin yaji tace
“Ya Arshaad!
yaushe ka zo?
Ina ka tafi ka bar ni?”

Tana mai kallon cikin idanunsa.

Da sauri sannan da mugun k’arfi Aslam ya runtse idanuwanshi.....

Magana take yi amman ba ya fahimta, babu abunda yake iya ji sai
‘Ya Arshaad’ d’in da take ta ambata a duk k’arshe ko farkon maganarta!…..

Ya so ya zauna ya cigaba da shafa mata jik’akk’en towel d’in a samu fever d’inta ya sauk’a
amman sai ya kasa!
A hankali ya mik’e tsaye daga kan gadon yana ganin dishi dishi…,

Ji yayi kawai ta fashe da kuka
sannan ta fara k’ok’arin ruk’o hannunshi, cikin kukan tace
“Dan Allah kar ka tafi,
mu zauna a cikin mafarkin nan da nake yi
ni da kai har abada,
kar ka tafi ka barni
bana so in farka
idan kuma zan farka to sai ka yi min alk’awarin zaka dawo gar....”

Wucewa yayi da sauri ya fice a d’akin ya barta nan tana ta faman surutai..

Da kyar ya iya kai kanshi d’aki
yana zuwa ya dafa bango da d’ayan hannunsa d’ayan kuma ya dafa goshinsa yana jin
yadda zuciyarshi take harbawa da tafarfasa tamkar zata fashe!
Sunayen Allah ya hau karantowa sannan ya fara k’ok’arin controlling kanshi…
Tabbas ya san zafin zazzab’i ne ya sanya ta take
hallucinating amman hakan bai hanashi jin kamar zai mutu ba!
Da kyar ya samu ya zaro waya ya kira Mommy yace mata “ta zo Hudan bata da lafiya”
Daga nan ya lallab’a ya koma bakin gado ya zauna ya jingina bayanshi a fuskar gadon ya
lumshe idanuwanshi.....



Kamar yadda su Umma suka tsara!
Yau da sassafe k’arfe 7:00 na safe Anty Zainab ta biyo mata suka kama hanya…
Tafiyar awa uku ce ta kaisu d’an k’aramin k’auyen da za su je wanda tsaf In ka tsaya zaka iya
k’irga gidajen wajen kaff d’insu.
Wani gida isolated a chan nesa suka nufa, a dai dai hanyar gidan akwai wata y’ar majalisar
wasu matasa a k’asan wata k’atotuwar bishiyar mangoro dai dai suna zuwa za su wuce wani a
cikinsu yace
“Ga wasu b’atattun yau ma sun zo”
Sarai sun ji sa

ba wannan ne a gabansu ba dan haka suka wuce suka yi cikin gidan….

Sai da suka d’an jirashi ya karya sannan ya samu damar ganinsu. Suna shiga suka nemi waje
suka zauna.

Da kyar Umma ta iya ce mishi “Ina kwana”
Bata jira amsawar shi ba
ta hau zuba…
Har da cewa da ya san ba zai yi aikin ba tun jiya da bai ce ta k’ara mishi kud’i ba!
Sai da Anty Zainab ta d’an zungureta tukunna aka samu ta yi shiru.

Gyaran murya Anty Zainab d’in tayi sannan tace
“Ni a ganina yanzu aikin gama ya riga ya gama,
tunda har ta tare.
Yanzu abunda muke so shine a tabbatar da auren Jalila da shi Arshaad d’in
sannan a san yadda za a yi a taimakawa Jalila ta fitar da Huda daga gidan!”

Shiruuu, mutumin ya d’ab yi ya lumshe idanuwanshi..
Chaan! Ya bud’e, ya kalleta yace
“Na riga fa na yi abunda zan yi!
Kun tabbatar anyi auren ita Huda da shi Arshaad d’in kuwa?
Dan ni gaskiya bincikena bai nuna min an yi ba.”
Da sauri Umma tace
“Shirme kenan!
To bari kaji..
Jiya ma a gidanshi ta kwana k’arshen magana kenan.
Kuma na tabbatar idan aka bincika ma yanzu haka ciki gareta!
In dai binciken tsakani da Allah za a yi”.

Murmushi kawai yayi
kafin yace “shikenan.
Ku d’an jira ni”
Daga nan ya mik’e ya
fita.
Kamar minti biyar haka
ya dawo…

Wata bak’ar laya kawai
ya mik’o musu bayan ya zauna
Anty Zainab ce tasa hannu ta karb’a dan ita Umma in banda tura baki da kumbure kumbure ba
abunda take yi.
Sai da ta karb’a sannan yace
“Ku nutsu! Ku bani dukkan hankalinku!

Dan kunga wannan abun da na baku shine kankat!
Amman muddin kuka yi ganganci aka samu matsala
to abun zai dawo kanku ne!
Kun amince?”

“Eh”
Suka had’a baki duk su biyun.

Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin ya sake cewa
“Shawara itace..
Ku sake bincikawa
ku tabbatar an yi auren
dan in dai basa tare kuma
akayi wannan aikin mai zafi to
idan ya tafi bai samesu ba kan ku zai dawo! Bi ma’ana
Auren d’aya daga cikinku ne zai mutu.”

Murmushin takaici Umma tayi
kafin tace
“Mallan”
Yace “Na’am” tace “fad’a mana yadda za ayi amfani da ita kawai!
Maganar tare kam
Huda da arshaad suna tare.”

“To shikenan.
Aikin ba mai wani wahala bane ba, ita wannan abar dana baku
cikin dare za a tashi a k’ona ta k’urmus! Shikenan
Ko wanne irin kalar aure aka k’ulla musu
sai sun rabu!
Rabuwa ta har abada, idan har kinga sun dawo sun zauna
to sai dai in za a iya maida layarnan ta koma dede yadda take kafin a k’onata!.
Sannan shi kuma wannan” yayi maganar yana basu wani turare
kafin yace
“Ita Jalilar za ki bawa ta shafa a jikinta, ta tabbatar shi Yaron ya shak’a da Mahaifiyarsa da
Mahaifinsa da duk wani wanda zai iya shige mishi gaba wajen auren, in sha Allah ba za ayi awa
24 ba za a d’aura musu aure.”

Sai a sannan Umma tayi murmushi tace
“sun gode”
Daga nan
suka d’anyi wasu maganganun ragowar matsalolinsu….

Sun d’an jima tukun suka mik’e suka fara shirin tafiya..

Har suka fita Malamin nan yana ta nanata musu “su tabbatar sun yi conforming auren Huda da
Arshaad kafin su yi amfani da layar na”.

Zuciyoyinmu fess haka suka fito
Umma ta karb’a kayan ta danna a jaka
suka wuce.....



A gigice Mommy ta shiga d’akin Huda!
Hakan yayi dai dai da k’arasowar Doc shima.
Aslam bai bari Mommy ta gansa ba, suna zuwa k’ofar d’akin shi da Doc d’in ya fara jiyo
muryarta a rikice tana yiwa Huda magana dan
haka yana nunawa Doc d’akin ya juya ya koma d’akinsa.

Sai da ta sha allurai sannan aka jona mata drip tukunna ta fara gane waye a kanta.

Mommy kuwa da ta samu Huda ta d’an farfad’o
sai ta hau fushi da Aslam.
Bawan Allah shi kam bai ma san tana yi ba yana
d’aki yana fama.

Ita da Gwaggo Asabe ne suka yi jinya, kafin dare ta d’an warware amman ba sosai ba
Sai a sannan ta samu ta kira su Mama….Lokacin ita d’aya ce a d’akin
Gwaggo Asabe ta tafi kitchen
Ita kuma Mommy taje shiryawa Dad table….
Ba yadda bata yi dasu ba akan su turo mata Sakina bata jin dad’in zaman ita d’aya
amman sam suka k’i
suka ce “in ita bata da hankali to su suna da shi” K’arshema fad’a suka rufeta da shi
Mama tayi ta gama ta bawa Ummu itama ta yi nata ta mik’awa Shuwa!
Haka nan ta hak’ura ba yadda ta iya.
Bata ce musu bata da lafiya ba dan karsu d’aga hankalinsu.


Mommy a d’akin suka kwana tare da
Ita da Gwaggo Asabe.
Ita Huda har mamakin tattali da k’aunar da Mommy da Gwaggo Asabe suke nuna mata take yi,
ko tari tayi nan
da nan hankalinsu zai tashi,
ba abunda yafi d’aure mata kai irin yadda Mommy take cika bathtub da ruwan d’umi tace ta
shiga, a ranar sai da tayi mata sitbath yafi sau biyar!.
Ita dai abun mamaki yake bata har ga Allah, gashi duk da ba wai son Aslam take yi ba
amma sai ta tsinci kanta da mugun kunyar Mommy da Gwaggo Asaben,

sam ta kasa sakewa a d’akin.
Da kyar ta d’an samu bacci kad’an, daga nan ta farka idonta ya bushe, sam ta kasa komawa
dan haka ta mik’e tayi alwallah ta fito ta d’au hijabi a cikin akwatin kayanta da tazo dashi ta tada
sallah.

Shima Aslam bai samu wani isheshshen bacci ba, so
yake yaje yaga jikin nata
amma d’azu k’iri k’iri Mommy ta hanashi shiga d’akin da suka had’u a k’ofa!
Kuma tak’i kulashi. Kafin ya kwanta ya kirata yafi sau nawa amman tak’i d’auka, dan
haka shima da yaga ya kasa baccin sai ya mik’e ya fara jero nafilfili…..
A Daren ranar ne kuma Umma ta k’ona layarta!
Bayan ta yiwa Jalila waya tayi mata kwatancen mansion d’in da suke ita kuma tayi
mata alk’awarin ‘gobe da safe zata zo mata ta sak’on da zai saka ta auri Arshaad’ Sannan tace
mata “ta kwantar da hankalinta zata fitar da Huda a gidan in shaa Allah”
Sai a sannan Jalila ta d’an nutsu dan tun jiya da taji a wajen Umman an kai Huda gidan
Arshaad shikenan ta birkice ta susuce ko bacci bata yi ba sai kuka take
ta yi duk ta fita hayyacinta.
Ba k’aramin dad’i taji a rantaba kuwa.
Haka ta kwanta zuciyarta fess
tana kwanciya bacci mai mugun dad’i yayi awon gaba da ita!
Wanda ta dad’e bata yi ba.

Washegari da sassafe y’ay’an Gwaggwo Asabe su biyu suka iso, da y’an yaransu k’anana.
Yadda Gwaggo Asabe take da kirki haka suna y’ay’anta.
Sai a sannan Huda ta d’an sake ta d’anji sauk’i dan
a cikin wuni d’aya suka saba
ta sake sosai da su, hakan
kuwa ba k’aramin dad’i ya yiwa su Mommy ba.

Da yamma jikin nata da d’an kwari dan haka Mommy tace “ta shirya ta fito main parlour kar
zaman d’akin ya gundureta.

Suna zaune da yamman
Huda na gefen Mommy akan kujera 3 seater a zaune ana hira a main parlour Aslam ya fito!
Mommy tana ganinshi ta kauda kai gefe ta had’e rai.

Dariya Gwaggo Asabe tayi
tana tuna yadda d’azu ma yazo tayi hakan, ba
yadda basu yi da ita ba amman tak’i kulashi
k’arshe sai hak’ura yayi ya tafi kamar zai yi kuka..
Ita kam Huda rabon ta da shi tun ranar da aka kawota shekaran jiya
da yayi mata sai da safe ya fita bayan ya kawo mata kaji.

Gefen Mommy yazo ya zauna ya kamo hannunta ya b’ata rai kamar zai yi kuka.
Bata kula shi ba bata kuma kwace hannunta ba
amman ko kallon inda yake bata yi ba.

Yaran Gwaggo Asabe
Karima da Laurat ne
Suka hau tsokanarshi
dama sun saba.
Daganan kuma aka hau gaggaisawa
Karimar Yaranta uku maza itace Babba
sai Laurat tana da twins y’an biyu mace da Namiji..
Aslam yana mugun son Yara dan haka ya sake yayi ta wasa da Yaran sunata yi mishi surutunsu
na shirme.

Da ido Gwaggo Asabe tayiwa Huda sign bayan sun had’a ido.
Duk sai taji kunya ta rufeta,
ita tama manta ashe basu gaisa ba!
A hankali ta d’an kalleshi kafin tace
“Ina wuni”
Sai da ya ajjiye k’aramin Yaron Karima akan kafet
sannan ya juyo yana kallonta yace
“Alhamdulillah,
ya jikin?”
Sunkuyar da kanta tayi kafin tace
“Alhamdulillah”

Hannun Mommy da yake a cikin nashi yad’an damk’e kafin yace
“Mommy bara mujewa Granpa”

Bata kula shi ba.
Hakan yasa ya mik’e tsaye yana mai sakin hannun nata yana murmushi kafin ya cewa Huda
“D’auko hijabin ki mu je”

Juyawa tayi ta d’an kalli Mommy.

Muryar Gwaggo Asabe ce ta katseta jin tana cewa “ku je mana.
Yi maza ki d’auko hijabin.”

Ko da ta fito parlourn bata same shi ba, Gwaggo Asabe ce tace mata “yana compound”
“To” tace sannan tacewa Mommy “yace za mu fita”
Sai a sannann
Mommyn tace
“A dawo lafiya”

Tanaji gabanta yana fad’uwa!
Dan bata san ya had’uwar Huda da Granpa zata kasance ba.

Su Karima ta juya ta cewa “sai ta dawo” da Gwaggo Asabe
sannan ta sa kai ta fita.

A tsaye ta hango shi chan bakin gate dan haka ta k’arasa..
Tunda ta taho ta lura da irin kallon da yake yi mata
har ta k’araso inda yake ta tsaya.

Sai da suka yi kusan 1 minute ba wanda ya motsa a cikin su
kafin yace
“Jikin da sauk’i sosai ko?”

“Um”
Kawai tace mishi
dan ita haushima ya bata
meye nashi na wani nanata tambayar!
Bayan already ya riga ya tambayeta tun a ciki.

Yanaso ya tambayeta ko akwai abun da take buk’ata
amman ya lura kamar bata son yawan maganr tasu
dan haka ya rabu da ita kawai,
yace “muje” yana mai juyawa.

A jere suke tafiya
gwanin burgewa… Har suka k’arasa gate d’in gidan Granpa.
Cikin girmamawa mai gadin ya bud’e musu gate d’in suka wuce bayan ya gaidasu.

A k’asa Aslam suka tsaya ya kira Granpa ya bashi izinin hawa tukunna suka hau!
Gaban Huda na dukan uku uku..

A chan sama suka sameshi,
Parlournsa!
Yana zaune a kan kujera ya baza takardu yana dubawa…

Tunda suka shigo ya d’ago ya kafe Huda da ido!
Hudan kasa k’arasowa tayi sakamokon yadda fad’uwar gabanta ya tsananta
saboda yadda taga Granpa ya kafeta da ido…
Har Aslam ya kusan k’arasawa inda yake sai
kuma yaji kamar bata tare da shi dan haka ya juya.
A chan farkon parlourn ya ganta tsaye ta sunkuyar da kanta.

Granpa ya kalla sanan ya juya ya kalleta, d’an
lumshe idanunsa yayi ya bud’e
tukunna ya koma ya je
inda take a tsaye, bata yi
auni ba kawai taji ya kamo hannunta!

Da sauri ta d’ago zata yi magana taga ya tsareta da kyawawan idanuwanshi,
a hankali taji yace
“Muje mana” still yana kallonta
sannan da kyar ya samu ya iya zare idanuwanshi a nata ya juya ya fara tafiya…

Tsintar k’afafuwanta kawai tayi suna takawa suna binshi.
Sai da suka k’arasa gaban Granpa sannan yace mata “ta zauna”
Shima ya ja ya zauna a kan kafet.

A hankali yace
“Granpa Good afternoon.”

Ajiyar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login