Showing 18001 words to 21000 words out of 113579 words

Chapter 7 - So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel Document By Bulama.pdf

Bulama   

28 May 2025

8299

a gidan
K’iri k’iri Yaro ko secondary school bai gamaba amma ina
k’ok’arin maidashi maraya, har su Khadija ma da suke gidan Miji sai ta shafesu…

Ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, k’arshe ma
ko zama bata barni nayi ba itama ta koreni!”
Da sauri Umma tace
“Yanzu kenan a nan za ki zauna?”
Cikin share hawaye Anty Zainab tace “To ya zan yi?
Ina zan je?
Port harcourt ko Ina?”

Ajiyar zuciya Umma ta sauk’e kafin tace “Ki kwantar da hankalinki, zai mayar da ke, kin ji ko, In
sha Allah.”

Cikin kuka Anty Zainab tace
“Baban Khadija fa babban d’an ka’ida ne ke kin sani ba zai tab’a bari mu zauna da saki ukun
nan ba”

Cikin yin k’asa da murya Umma tace “Ki kwantar da hankalinki, za mu nemi mafita
In sha Allah.
Sannan ko hauka muke ba zamu bar auren nan ba yasin sai dai in me taurin ruhi ce kamar
Maryam wadda ta
nace sai da kyar! Tukunna aka samu ta bar gidan nan,
to kinga idan irinta ce
ba yanda muka iya
dole mu barta amman shima sai mun ci ubanta wallahi.

Maza basa kyautawa wallahi sam! Saboda Allah Ina ma lefin ya d’auko miki mai d’an shekaru.
Fisabilillahi Ina Baban Khadija Ina sa’ar su Khadija?Tsofai tsofai da shi.”

Da sauri Anty Zainab tace
“Kuma budurwa!”

Cikin karb’e zancen Umma tace “Ba zai ma yiu ba fa Wallahi! Dole mu san abun yi.
Ki kwantar da hankalin kar ki saka damuwa a ranki, zamu nemi mafita.
Bai isa ba wallahi, kin ji.
Su Shuwan nan suna bani mamaki, daga an yi magana suce wani wai kar mutum yayi shirme in
za ai mishi kishiya waye waye…
Bayan su basu san zafinta ba!
Tunda duk cikinsu babu wadda Mijinta ya tab’a yin koda budurwa ne a waje, sun
kafa sun tsare nasu mazajen amman sun iya tak’ark’arewa suna yiwa mutum nasiha akan
kishiya tsabar renin wayo!
Su bar waenda suka san zafin kishiya su yi magana mana ba wai su tsayayyun matan da suka
kafe mazajensu ba…”

Ita dai Anty Zainab mik’ewa tayi ta isa kan gado ta kwanta ta juyawa Umma baya, dan

taga abun nata kamar ya fara zama cin fuska kuma.
Tana jinta tana ta bambami daga k’arshe ta yi shiru ta
gyarawa Ya Ja’afar wanda yayi bacci kwanciyar sa ta lullub’e sa tazo ta nemi waje gefen Anty
Zainab itama ta kwanta….. Ta gama rayawa a ranta gobe zata koma wajen mutumin nan tayi
masa
maganar Anty Zainab asan abun yi dan gaskiya tayi mugun tausaya mata. Amman kuma
abunda yasa tayi shiru bata gaya mata gaskiyar lamarin yanzu ba shine
ta lura aikin mutumin kamar yakan iya juyewa kuma
waiwaye! Tunda gashi na Huda ya koma kan Anty Zainab d’in , dukda ya fad’a musu dama
amma still kamata
yayi ace aurenta da Aslam ne ya mutu ba wai na Anty Zainab ba tunda de Hudan aka yiwa
abun so it doesn’t matter ko waye Mijin nata ita ya kamata a sako….
Kanta ya kulle dole ta koma wajenshi amman ba zata bari suje da Anty Zainab ba dan yadda
take a rikicen nan haka kurum taje ta tunzura mutumin yayi mata nata aikin aje garin gyara nata
a tab’o na Jalila da bai gama had’uwa ba.
Ko da ace zata gaya mata Hudan ba Arshaad ta auraba to sai ta tabbatar Mutumin ya gama yi
musu aiki mai kyau! An d’aura auren Jalila da Arshaad ta kamashi sosai ta samu fada a
wajenshi tukunna, saboda kar aje aiki ya had’a masa biyu yak’i concentrating akan na Jalila
sosai, ko kuma kuma yaje ya gyara na Anty Zainab wani abun ya samu na Jalila….

A ranar dai haka suka yi bacci duk su biyun rabi da rabi.



Su Hudan suna shiga a parlourn suka tarar da Ummi da su Shuraim sunata shirya dining tare
da masu aiki.

Ummi tana ganinsu ta k’arasa inda suke tayi hugging Hudan tana mata sannu da zuwa.
Cikin girmamawa suka gaisheta ita da Aslam, ta amsa musu da kulawa, daga nan
suka gaisa da su Sudais,
murna kuwa a wajen su kamar suyi me tunba ma da suka ganta har da akwati ba’
Su suka ja mata suka kai mata har d’aki
Abba yaso su zauna a sama amman Aslam yace “a barsu a d’akin bak’i” shi da
cewa ma yayi ita akai mata nata kayan sama shi a barshi zai zauna a d’akin bak’i, shiyasa
kawai Abban yace “a kai mata akwatin ta nan d’akin bak’in”.

Ita dai Huda so take tace ‘a barta ta tafi d’akinta’ amman bata san ta ina zata fara ba!
Ta san a idon duniya da su Abba Aslam mijinta ne
amman taya ake expecting tayi sharing d’aki da shi bayan ga d’akuna birjik kala kala a gidan.


Su kuwa su Daddy dama tun kafin su fita daga gidan bayan Gramma ta kirasu suka

gama deciding akan zasu san yadda za suyi su taho nan gidan ita da Aslam d’in
daga nan kuma su ajjiyesu shi da Hudan a waje d’aya, dan
sun lura tabbas sai sun d’an taka rawa a relationship d’in nasu tukunna za a samu su ma fara
magana mai tsayi da hira a tsakaninsu.



Abba ne ya umarcesu da su je su yi alwala ayi sallah kafin ayi dinner.

Hudan so take su had’a ido da shi amman bata samu wannan damar ba. Abba kuwa sarai ya
ganta shiyasa ya maida hankalinshi gaba d’aya kan Dad suka shiga hira….

Ganin ta a tsaya ne ya sanya Ummi ta k’araso inda take ta rik’e mata hannu tana murmushi
kafin tace
“Muje to nan d’inma in rakaki.
Naga kin tsaya.
Aslam muje In taka ma Amaryar taka, kunyar
mu take ji naga alama”

Juyawa kawai yayi ya fara tafiya. Ita kuma Ummi ta ja hannun Huda suka nufi d’akin..

A bakin k’ofar bayan taga shigewar Aslam ta ja ta tirje
sannan ta kalli Ummi kamar za tayi kuka tace
“Ummi wai nima a nan d’akin zamu zauna kuma ni da shi?”

Dariya sosai ta bawa Ummin amman sai ta dake ta d’an b’ata rai kafin tace
“Eh mana!
So kike ya zauna shi kad’ai?
Wa zai dinga gyara d’akin yana wanke band’aki?
Ko so kike a dinga tura mishi su Linder suna shigar masa anyhow?”

Da sauri tace
“Ummi zan dinga zuwa kullum da safe ina mishi Allah”

B’ata rai sosai Ummin tayi this time around kafin tace
“Zamu b’ata da ke fa!
Dole anan zaki zauna Huda.
So kike idan yana buk’atar wani abu urgent sai ya nemoki kenan?
Kinga, gara ki shirya fa dan hatta girki ma sai kin dinga yi masa nashi special
ko da kala d’aya ne
Breakfast Lunch da Dinner Kullum!
Ko kin d’auka auren wasa ne?”

Tabbas ta san da waennan abubuwan dan sai da Shuwa ta tsara mata komai amman ita dai a
tunanin ta su Ummi da Abba zasu d’aga mata k’afa tunda ai ba shi takeso ba kuma sun
sani…… Wani k’ululun takaicine ya tokare mata mak’oshi!
Tayaya ma za ace saboda zata dinga yi mishi aikace aikace da abubuwa har wani kuma sai ta
zauna da shi a d’aki d’aya dole!
Sai kace wani baby..

Ji tayi Ummi ta ja hannunta sun shige d’akin sannann ta mayar a k’ofar ta rufe.
Sai da ta kaita kan gado tukunna tace
“Ki yi sallah ku fito dinner”
Tana gama fad’in haka ta juya ta fice daga d’akin........

BULAMA ✍️



So da Buri
Free Book
59


Sai da Ummi ta fita tukunna Huda ta fahimci Aslam baya d’akin…har ta fara murna
sai kuma ta ji k’arar ruwa a toilet. Kamar mara gaskiya haka ta zauna ta k’ame a guri d’aya har
ya fito.

Kallonta kawai yayi ya d’auke kai, ya fita.
Sai a sannan ta sauk’e k’akk’arfar ajiyar zuciya sannan ta zabgawa k’ofar da ya bi ya fice harara
kafin
itama ta mik’e ta shiga toilet d’in tayi alwallah ta fito ta tayar da sallah..
Ta jima tana adduar Allah ya dawo da Ya Arshaad, watak’il
idan su Abba suka ga idonshi su raba wannan auren, ta
samu ta auri wanda take so itama yake sonta. Bayan ta shafa ta mik’e ta fita zuwa dining.

Ummi da su Shuraim ne kawai akai, da alamun su Abba basu dawo daga mosque ba, Ummi
tana ganinta tace
“Ai yanzu nake shirin mik’ewa in lek’o ki, na ji shiru”

Murmushi tayi ta k’arasa wajen, har ga Allah Ummi tana burge ta Ubangiji yana son bayin sa
masu tuba bayan sun fahimci sun yi kuskure.
Tana zuwa ta ja kujerar gefenta ta zauna suka
fara hira ita da su Shuraim waenda suke a opposite d’insu ita da Ummi.

Ko 5 minutes bata yi da zama ba su Abba suka shigo..
Opposite d’insu Abba ya zauna , ga mamakin Huda sai taga Aslam ya ja kujerar gefenta shima
ya zauna!
Hakan kuwa ba k’aramin dad’i ya yiwa Abba ba dan
har kasa b’oye farin cikin sa yayi ya fara zuba murmushi…

Ummi itama murmushin tayi
kafin ta mik’e ta zagayo inda suke ta fara serving nasu..
Har ta gama Hudan tana zaune kyam! Sai da Ummin ta dawo tukunna k’asa k’asa tace mata
“Ta tashi ta zubawa Aslam mana”

A hankali ta mik’e dan ita har ga Allah wani abun ma kunyar Abba take ji.. Jiki ba kwari ta hau
serving nashi, tana gamawa ta tura masa komai gabansa itama ta zubawa kanta abinci kala
d’aya kawai d’an kad’an.


Baka jin k’arar komai sai cokula..
Although ba Hudan bace ta dafa abincin amma yadda
tayi serving nashi da yanda
take zaune kusa da shi tabbas zai iya cewa this is the best dinner da ya tab’a having a
rayuwarsa! Lokaci lokaci yake lumshe ido yana sauk’e ajiyar zuciya ba tare da kowa ya lura da
shi ba.

Abba ne ya fara jan tissue ya goge bakinsa ya sha ruwa yace “Alhamdulillah” daga nan ya mik’e
ya juya ya nufi hanyar fita.

Yadda ta san zai ji xeji, Ummi tace “Abba fita zaka yi ne?”.
Bai juyo ba, be kuma kalleta ba kawai yasa kai ya fice.
Ajjiye spoon d’insa Shuraim yayi ya mik’e ya bar wajen gaba d’aya ba tare da ya k’arasa cin
abincin nasa ba.

Jikin Ummi ba k’aramin sanyi yayi ba, ta san cewa tunda ta dawo Abba baya kulata
amma tayi tunanin tunda a gaban su hudan ne zai kulata yau, ta samu ta d’an ji sanyi a ranta. A
b’angaren Huda kuwa, ba k’aramin kunya taji ba shiyasa itama kwata kwata ta kasa ci gaba da
zama a wajen dan bata so su had’a ido da Ummin, ta lura da yadda Shuraim ya had’a rai ya
mik’e ya bar wajen, dan haka tana mik’ewa ta nufi sama side d’insu.. Tana shiga ta tarar da shi yana kuka! Da sauri ta k’arasa inda yake zaune akan gadon ta zauna
ta kamo hannunsa, k’ok’arin mik’ewa ya fara yi dan haka da sauri tace
“Shuraim wait, let’s talk mana.
Ka daina kuka ka fad’amin me yake damunka, ka ji?”

Ajiyar zuciya ya sauk’e ya share hawayenshi kafin yace mata “ba komai” kawai.

B’ata rai tayi sanann tace
“To shikenan!
Bara kaga in tashi in tafi kuma ina sauk’a zan d’auki akwatina in bar gidan nan gaba d’aya in dai
baka gaya min ba.
Sannan sai na gayawa Abba da Ummi kana d’aki kanata kuka”

Sai da ya gyara zamanshi ya fuskanceta sannan yace “Abba ne! Ya tsani Ummi.
Tun lokacin data dawo daga tafiya baya kulata baya yi mata magana kwata kwata.
Idan ita ta kula shima sai dai yayi mata banza ya wuce kamar yadda yayi yanzun.
Kullum sai naga Ummi tana kuka not once sometimes a rana sai tayi kuka sau wajen biyar shi
kuma he don’t care!
Ban san meyasa Abba ya tsani Ummi ba, dama chan baya sonta yanzu kuma ya sake
tsanarta!”

Da sauri Huda tasa hannunta ta toshe masa baki, sannan tace “kar ka ce haka Shuraim, kar in
sake jin irin haka a bakinka.
Abba bai tsani Ummi ba, ka ji ko?
Kawai maybe su d’anyi fad’a ne kad’an amman na san za su shirya soon, ka ji?
Ka daina sakawa a ranka
zasu shirya ya zama kamar basu tab’a yin fad’aba in sha Allah soon kuma, ka ji ko?”

Still kuka yake yi, dan haka Huda tayi ta lallashinshi har sai da ta samu yayi shiru ta tilasta
masa ya k’ara cin cookie a d’akin dan bai wani ci abinci sosai a k’asan ba tukunna ta mik’e ta
d’auko mishi tooth brush d’inshi da bathrobe ta bashi tace yaje yayi wanka yazo ya kwanta idan
ma game yake son yi sai su yi tare.
Shuraim a zuciyarshi ya ji ya sake jin k’aunar Hudan, yadda ta tsaya take k’ok’arin taga yayi
farin ciki hakan ba k’aramin dad’i yayi masa ba.

Karb’a yayi ya fad’a toilet d’in
ita kuma ta jona ps ta fara yi musu settings…
Sai a lokacin Ummi ta bar bakin d’akin tana rik’e kukan da ya taho mata...
Tana shiga d’akinta ta saki kukan, tabbas tayi kuskuren da ita kanta ba zata tab’a yafewa kanta
ba!
Kalla fa yadda Hudan take da hankali take k’aunar jininta
amman haka nan tayi depriving d’inta childhood mai dad’i! Ta rabata da Mahaifinta! Ta sanyata
ita da uwarta a k’unci basu ji ba basu gani ba duk saboda So da Burin mallakar Mijin da
a yanzu ta riga ta hak’ura dan ta san ba zai tab’a accepting d’inta ba….
Ummi ta yi kuka ranar kamar ranta zai fita, tabbas zata samu lokaci ta ware ta rok’i Abba ya
barta ta je taga Mama ta nemi yafiyarta sannan zata ta nemi yafiyar Hudan itama dan kwata
kwata ta kasa sukuni tana jin
zafi da dana sanin abunda ta aikata a baya

Inama ana dawo da hannun agogo baya.......


Abba Yana fita direct side d’in Daddy ya nufa, yana shiga ya tarar da su suma suna dinner su
uku abunsu.
………Yanzu Mom ta samu sauk’in Jalila biyayya take yi mata kamar zatai mata sujjada!
Duk abinda tace shi take yi sannan ta maida kanta k’asa kamar wata y’ar aiki, yau ma
ana gama abinci ta d’iba ta wuce d’akinta har da cewa
Mom d’in ‘ko akwai aikin da take so ayi mata?’
Murmushi kawai Mom d’in tayi mata sannan tace ‘ba komai’
already a ranta ta riga ta gama shiryawa akan gobe gobe za tayi mata korar kare!
In sha Allah…….




Kujera Abba ya ja ya zauna kusa da Daddy.
Duk da ya k’oshi amma sai da Daddy ya saka shi yad’an tab’a wani abun.

Auwal ne ya fara mik’ewa saboda yana da tulin aikin da yake son yi and yanaso yau ma ya
sake gwada sa’ar shi ko Allah zai sa Sakina ta amsa wayarshi.
Dan haka yayi musu ‘sai da safe’ ya wuce sama.

Daga nan itama Mom ta mik’e suka fara tattare dining d’in ita da mai aikinta..
Tana shigewa Abba ya dubi Daddy yace
“Daddy magana na zo mu yi akan Maryam!”

Juyowa Daddy yayi ya bashi dukkannin attention d’insa kafin yace
“Ina sauraronka, what about her?”

Soundin so worried and disturbed Abba yace
“Har yanzu bata d’aukar waya ta! Bata replying messages d’ina..
I think kawai mu je mu samu su Abba Madun maybe shi zai iya bata shawara ta d’auka”

Ajiyar zuciya Daddy ya sauk’e kafin yace “Abba,
I know what you are going through amma sai nake ganin kamar Maryam tana buk’atar more
time kafin komai. Ka duba kaga irin abunda Mijinta yayi mata sannan na san ta san Granpa ya
sallame mu daga estate saboda Huda
kuma na san yanzun ma Huda zata iya gaya mata ya sake korarta!
Gaskiya bana jin su kansu su Abba Madun za su goya mana baya ko da ace mun je mun same
su da wannan maganar.
Let’s assume ma sun goya mana bayan ni na san
Maryam ba zata tab’a yarda ba a yanzu, kuma kaga idan suka bata shawara itama ta basu nata

uzuri dole fa in aka auna aka duba za a ga ta fimu gaskiya ne.
Sannan Granpa!
Allah kad’ai ya san irin yawan y’an kallon da zamu kwasa da shi idan Maryam ta dawo gidan
nan a yanzu!.

Bawai zan yi backing out bane in daina goya maka baya ba
not at all Abba, all I’m saying shine
Ka kwantar da hankalinka
mu d’an jira kad’an tukunna, na san dole Granpa zai sauk’o kwanan nan tunda yanzu case d’in
ya shafi har Aslam, kaga daga nan sai mu san abun yi”.

Ajiyar zuciya Abba ya sauk’e kafin yace
“Na ji kuma na fahimceka.
Amman nima inaso ka fahimceni…
Daddy, Idan akwai abinda na sani wanda yake dahir! To shine
ko da ace Granpa ya huce mun koma yayi accepting d’inmu da Huda to fa ba zai tab’a
accepting Maryam ba
kuma idan aka taso da zancen
wani sabon case d’inne zai kuma b’ullowa, kaga
kenan an koma square 1!
So ni a gani na this is the right time da ya kamata muje ayi magana a gyara komai,
In yaso idan ma ya hak’ura kaga already Maryam tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login