Showing 66001 words to 69000 words out of 113579 words

Chapter 23 - So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel Document By Bulama.pdf

Bulama   

28 May 2025

8321

zai sa In hak’ura in bar killer d’in Ummi ya tafi free ba!
I’m sorry amman inaso kar ma ki sake yi min maganar nan dan Allah, saboda itace alfarmar ta
biyu da na ce miki daman ba zan iya yi miki ba
bayan mallakawa mutum d’aya a cikin su MT.”

A hankali Gramma ta sa hannu ta share hawayenta…

Ajiyar zuciya ya sauk’e sanann ya d’an matsa ya rungumota izuwa jikinsa ya shiga lallashinta
da kwantar mata da hankali.

Sai da yaga ta d’an dawo dede
tukunna yace “Yarinyar nan har yau tana nan?
It’s like a nan take dan tare nake ganinku”

Murmushi Gramma ta d’an yi kafin tace
“Ai har nan surukarta ta zo sata tafi da ita amma tayi ta kuka.
Ranar ina jinta tana waya
kamar da y’ar uwarta ne na wajen Maman ta
wai ‘In ta biyewa Aslam suka shantake da juna mutane za su ga kamar daman chan tana
sonshi!’
Wai ‘za ayi mata kallon butulu’.
Murmushi Gramma ta sake yi kafin taci gaba
“Ni wallahi dariya ma ta bani”.

Girgiza kai Granpa yayi kafin yace “Dariya ko abun haushi?
Wanann ai shirme ne!
Ita zata ke maida hannun agogo baya.”
Yana gama fad’in haka ya mik’e yace
“Zan yiwa Aslam magana ya zab’i gida zuwa gobe ya zo ya d’au keys, da sassafe
ki shiryata ki kaita gidanta
in yaso aa gyara a yi mata jeren suna ciki.”
Yana gama fad’in haka ya juya ya fita, da alamun ransa shima duk a dagule yake.”

Ajiyar zuciya Gramma ta sauk’e kafin ta mik’e ta d’auki wayarta ta danna kiran Mommy...

Washegari da safe,
kamar yadda Granpa ya buk’aci Aslam yazo ya karb’a keys haka aka yi…

Yana zuwa bayan sun gaisa ya cewa Granpa d’in ‘kawai ya zab’a mishi duk wanda yake ganin
yayi
Ya gode Allah ya k’ara arzik’i.’
Murmushi Granpa yayi yace “okay”
Sannan ya mik’e ya shiga ciki.
Makullin d’aya daga cikin gidanjen da ba’a tab’a bud’ewa ba ma ya d’auka ya fito.
Ya na fitowa ya gaya mishi gidan da number ya mik’a mishi.
Karb’a Aslam d’in yayi
ya sake yin godiya,
yana shirin mik’ewa Granpa d’in yace
“Ku yi sauk’a.
Gidan sabo ne, ba a tab’a shiga ba.
Sannan yanzun nan Gramma za ta kawo maka matarka
In yaso sai a gyara gidan tana ciki kawai ayi furnishing.”

A hankali Aslam yad’an russunar da kai yace “na gode”Sannan ya mik’e ya fita.

Da murmushi Granpa yake kallonshi har ya b’acewa ganinsa. Ya so bashi dariya yadda yaga
kamar ma yau d’in kunyar sa yake ji, zai so
ya ganshi tare da Abba yau d’in yaga ya zai yi….
K’arar wayarsa ce ta katse masa tunani.
Ganin number yasa ya d’aga ya kara a kunnenshi ya yi shiru.

“Assalama alaikom”
Baba Bashir yace.

Ba tare da ya fahimci waye ba
yace
“Ameen
Wa alaikummussalam”

Ajiyar zuciya Baba Bashir ya sauk’e kafin yace
“Kaka ne. Daga b’angaren Maryam Madu, yanzu
Arshaad yayi min texting numberka”

“Okay, okay”
Granpa yace yana gyara zama
kafin yace
“Ya iyali?”

“Alhamdulillah” Kaka yace
sannan ba tare da b’ata lokaci ba yace
“Na kira ka ne domin in sanar da kai cewa

a duk lokacin da kuka shirya kuna iya zuwa a d’aura aure.”

Sai da Granpa ya lumshe idanuwanshi ya bud’e
tukunna yace
“Weekend Saturday!
Rana ita yau, in sha Allah za mu shirya komai…mu zo.“

“Okay Na gode” Baba Bashir yace.

Murmushi Granpa yayi yace
“Mune da godiya, sai mun
had’u”

Daga nan suka yi sallama suka tsinke kiran.

Ajiyar zuciya Baba Bashir ya sauk’e.
Yana ajjiye wayar ya juya da niyyar fita su ka yi kicib’is da Baaba Talatu!

A hankali ya sauk’e ajiyar zuciya kafin ya fara k’ok’arin wuceta domin ya fita.

Da sauri ta tareshi ta hanyar shiga gabanshi, ta
fara hawaye sannan tace
“Mai yasa za ka yi haka?
D’an shekara d’ayan da zai yi da mu shi kake neman maidawa sati d’aya?
Dan na tabbatar muddin aka d’aura auren Maryam a gaban idonshi to tabbas a ranar zai cika!.

Ka barsu mana, ita kanta Maryam d’in ta amince
ta tausayi masa..
Nan da shekara d’aya ma fa ba zaka sake ganin Usman a doran k’asa ba.”

Sai da Kaka ya runtse idanuwanshi tukunna ya bud’e yace “Ke mahaifiyarsa ce,
ki daina yi masa baki haka
Usman ba inda zai je in sha Allah..
Bari kiji in gaya miki
d’azu na je akan In fahimtar da shi ya hak’ura kawai
tunda har ga Granpa ya zo da kanshi, ina zuwa k’ofar d’akin nasa
kin san me na ji suna tattaunawa?”

Cikin share hawaye Baaba Talatu tace
“Amman dai ko meye ne ka ji ai a ganina bai shafi..”

Cikin d’an fad’a fad’a yace
“Ki amsani kawai!

Kin san me na ji suna tattaunawa?”

A hankali ta girgiza kanta
alamun
‘A’a’

Sai da Kaka ya had’iye wani k’ululun takaici
kafin yace
“Akan maganar k’aryar takardun da suka yi na ji suna magana!
For your information
Usman garr!! Ya ke
babu mutuwar da zai yi in sha Allah. So yake kawai Maryam ta koma gidansa
ya cigaba da azabar da ita.

Wallahi Talatu kunyar Yarinyar nan nake ji. Ban tab’a b’oyewa Madu wani abu ba
amman tabbas zan b’oye masa wannan maganar
idan shekara ta zagayo aka ga Usman bai mutuba mu ce
Ikon Allah ne!
Dan ban san ta ina zan fara ce masa
Usman da Jamilu sun yi k’aryar ciwo da mutuwa a Usman d’in
dan kawai su yaudaremu ya aure masa y’a ya ci gaba da azabtar da ita, ba.
Ki dubafa ki gani
tsabar ya san bai kyauta ba
ya ma kasa fitowa a mutum yayi bikon ta dan bai san ta Ina zai fara ba!
Sai da ya had’a da k’aryar ciwon mutuwa..
Wanne irin deceiver ne wannan Yaron????

Kiga fa duk abunda ya yiwa Maryam amma tashi
d’aya ta hak’ura ta ji tausayinshi zata koma ta yi jinyar sa har ya koma ga mahalliccinsa
alhalin shi yana nan yanata yaudarar ta da mu kanmu..”

Cikin katseshi Baaba Talatu tace
“Ai dan ba ka san ya muka yi da Maryam d’in bane, ba ka
san ya akai ta yarda ba!
Ba ka san me na ce mata tukunna ta yarda ba.....”

Cikin tsananin b’acin rai
ya d’aga mata hannu ya ce
“Talatu!!!!”

Jin yadda ya daka mata tsawa ya sanya ta nutsu ta sha jinin jikinta.

A fusace ya fara magana

“Ban damu da in san me kika ce mata tukunna ta yarda ba,
tunda dai har ta yardan
to ta yi proving kanta ba as selfish kamar ke da d’anki ba!
Abu d’aya nake so in yi miki gargad’i akai
ko kuma ince In umarceki ki yi…
Ina so ki tsame hannuwanki a lamarin nan…ko da wasa idan kika sake yunk’urin had’a Maryam
da Usman su koma su yi zaman aure
wallahi!! Kin ji dai na rantse
sai na datse igiyoyin aurena kaff! Da su ke a kanki!”

A zabure ta ware idanuwanta tana kallonshi.

“Tabbas!”
Kaka yace cikin gasgasta maganar tasa sannan ya ci
gaba
“Tunda na lura son kan naki ya yi yawa..
Tun farko kike gwada son kai har yau kin k’i ki saduda Talatu
Usman d’a ne haka itama Maryam y’a ce!
Amman wani abun takaici
tunda kike Talatu
not once kika tab’a duba farin cikin Maryam
kullum kawai ke Usman!
Baki damu da kowa ba sai d’anki.
Kamata yayi ace yanzu kin nuna masa tsananin b’acin ranki
kallafa
k’aryar mutuwa yayi amman kina k’ok’arin yin burus da al’amarin saboda..........”
Shiru yayi sakamokon ido biyu da suka yi da Baba.

A hankali cikin mutuwar jiki ya k’araso cikin d’akin ya durk’usa a gaban Kaka da Baaba Talatu
ya fara hawaye a hankali ya ce “ku yi hak’uri, na san na yi
laifi amman ku yafe min
dan Allah kar ka bari su Abba su ji wannan maganar,
tunda har ita Maryam d’in ta yarda zata koma kawai ku kyaleta, daga baya duk abunda.........”

Marin da Kaka ya d’auke sa da shi ne ya sa ya yi shiru!
Cikin tsananin b’acin rai ya ce
“Usman inaso ka tattara kayan ka ka koma inda ka fito!
Kuma kar ka kuskura ka dawo
har a gama d’aurin auren Maryam a kaita gidan Abba!
Dan na lura imaninka ya fara rawa so zaka iya yin komai.
Ka tattara ku koma kai da Jamilu har a k’are tukunna ka dawo.

And one more thing..

Ko ka san cewa y’arka ciki ta yi?
Kuma Sadiya ta tura ta gidan su shi Yaron ta zauna
ta yiwa kowa k’aryar tana gidan Hansai??
Baka sani ba ko?
Badaban cikin ya zube ba
na tabbatar da sai ta haifi shege a cikin zuriata!.
Saboda kawai Yaron ya kasance mai kud’i
shiyasa tsananin buri irin na Sadiya ta gwammaci jikata ta je ta haifa shege
dan kawai ta dinga turo mata da kud’i!

Kana nan sake da baki kana k’ulla ta yadda zaka dawo da Maryam
instead of
ka tsaya ka kula da iyalinka Usman!!

Kaf y’ay’anka da matarka
babu wanda za a kalla a nuna a yi alfahari da shi! Dan shi
kansa Junaidu abun a bincika ne!
Amman daga kai har Jamilu da ya kamata ace kun tashi kun tsaya akanshi kun yi bincike,
kun zauna kuna k’ulla makirci da k’arya kamar mata! Kun zuba mana ido ni da Madu tsofai
tsofai da mu mu za mu yi komai..
To Ina so ka sani nima yanzu ta kaina nake yi, abunda kawai zan yi focusing akai bayan d’aurin
auren Maryam shine ibada!
In samu in gyara tsakanina da Ubangijina kafin In koma gareshi..
Duk wanda yaga zai gyara iyalinshi
to ya gyara
wanda kuma ya ga ba zai gyara ba shi ya sani kar ya gyara ya zauna ya ci gaba da shirme
yana biyewa so da buri.

Abu d’aya zan yi maka na taimako da ga shi ba k’ari!
Kasancewar Jalila y’a mace kuma yanzu na san tunda zance ya fara fitowa in an kwana
biyu ba lalle ta auruba, dan haka zan rufa mata asiri
In nema mata miji kamar yadda na yi da farko.
A yanzu Mati ya riga ya cike ta hud’u if not wallahi da tun a jiya da Zainab ta bani labarin ta
da tuni na aura masa ita.
Dan haka
yanzu zan bada sanarwa this time around ba a fili ba a b’oye
saboda kar Sadiya tace na yi talla da y’arta kamar farko..
Duk wanda ya zo ya ce yana so
daga nan zuwa ranar asabar rana ita yau
to za a had’a a d’aura aurenta
tare da na Maryam da Abba, in sha Allah.”
Yana gama fad’in haka ya juya ya fita dan yana so ya sanar da Madu an saka rana.
A ranshi ya gama rayawa

‘Ko Madun bai yarda ba wallahi sai dai kawai ya ga ana d’aura aure ranar Asabar!
Ai Maryam bazawara ce yanzu
sannan ba Yarinya bace ba, kowa ya san Abba take so
ba Usman ba dan haka
Madu
bashi da hurumin yi mata dole’.

BULAMA ✍️




So da Buri
Free Book
68

Mikiya Writers Association.
Tabbas Mommy taso ace ta gyara Huda kafin ta tare
amman jin bayanin gramma yasa kawai ta hak’ura
ta k’udurta a ranta zata had’ata da Gwaggo Asabe na kwana biyu. Allah yaso ta taho da
wayarta dan haka ta d’auka ta danna kiran Ummu.

Da sallama Ummu ta amsa kafin ta ce “Ina wuni Mommy ya gida”

“Alhamdulillah Ummu ya Yaran”
Mommy ta amsa ta.

Sai da taji amsarta tukunna tace
“To fa aikin gaggawa ya samemu.....”
…………
Lokacin da ta shigo d’akin Huda na toilet tana wanka
Gramma bata gaya mata komai ba daman ta fi so sai Mommy ta zo su yi mata bayani tare.

D’aure da d’an guntun towel ta fito gashinta a jik’e gaba d’aya wani ya zubo ta gaba wani kuma
yayi baya
Yana reto yana d’igar ruwa.
Sam bata ma lura da su waye a d’akin ba saboda duniyar tunanin da ta lula
‘Tabbas ko ta halin yaya ne yau dole ta je ta samu Mama!
They definitely need to talk..
She can’t believe abunda Maman ta gaya mata jiya
sannan Sakina ta tabbatar mata wai gidan Baba za ta koma!
Mai ya faru?
Ko dai gaba d’ayansu sun samu shigar aljanu ne!

Dan in ba haka ba
tayaya za ai ga Abbanta amma azo ace wai gidan wani Baba za ta koma!
Granpa fa dakanshi ya je ya samesu….
Wanne irin abune wannan?
Tun jiya ta kasa gane kanta har kawo yanzun nan…..’

“Dota”
Mommy ta kirata tana d’an kallonta ganin gaba d’aya hankalinta baya a kansu.

Firgigit! Ta yi ta d’ago, suna
had’a ido kuma sai ta tuna da towel kad’ai ne fa a jikinta shima kuma guntu
dan haka da sauri ta juya ta koma toilet d’in
tana cewa
“Mommy Ina kwana”
Bata jira jin me za ta ce baa ta rufoo k’ofar ta shiga neman bathrub.

Tana shigewa Mommy ta sauk’e ajiyar zuciya
kafin a fili tace
“Ko sai yaushe Hudan zata saba da ni kamar Maryam?
Sai Allah.”
Tana gama fad’in haka ta kalla Gramma tace
“Bara in je In fara shiri kafin su Ummun su zo.
Dan na san ba lalle ta iya sake fitowa ba balle ta sake mu yi maganar.

“Ok”
Kawai Gramma ta ce mata
daga haka Mommy ta juya ta fita.
Tana fita
dede Hudan tana fitowa itama sanye da bathrub.
Ba k’aramin dad’i ta ji ba ganin bata d’akin, dan har ga Allah tayi mugun jin kunya.

Tana shirin nufar gaban madubi Gramma tace
“Zo nan Huda”

A hankali ta k’arasa ta zauna a gefen ta tace
“Gani Gramma”

Sai da ta sauk’e ajiyar zuciya tukunna tace
“Shawara nake so in baki…
Ki daina nunawa Mommy kamar suruka take a wajenki
Instead ki d’auketa kamar Mama ki sake da ita. Tana matuk’ar k’aunarki, ki saki jinkinki ku saba
sosai,
za ki ji dad’in hakan.

Magana ta biyu…
Ki shafa mai ki jirani zan kawo miki kayan da zaki saka yanzu!
Granpa ya ce akaiki gidan ki
za a gyara kina ciki.”

Da sauri ta d’ago ta kalli Gramma.

D’aga mata kai tayi alamar gasgatawa sannan tace
“In kuma kinada ja to
mu je in raka ki wajensa”
Ta fad’i haka tana d’an b’ata rai
saboda ta lura In ba hakan tayi mata ba to fa sai an sha drama da ita
dan gashi idanunta har sun ciko da hawaye.

A hankali ta girgiza kanta alamun ‘a’a’
Sai kuma ta mik’e ta nufi gaban mudubi hawaye na bin fuskarta.


Tana gama shafa man Gramma ta shigo da wasu had’add’un kaya
riga da zani da alkyabbarsu
sai kyalli suke yi
sannan
kamar wanda aka yi design d’in edges d’in da gwal!
Tana ajjiyewa ta juya ta fita.
Bata dad’e ba ta dawo da kasko da wata robar Kaplas,
sannan ta sake komawa ta d’auko kujerar tsugunno.

Ita dai Hudan tana zaune kawai tanata binta da kallo
dan tunda ta gama shafa man ta dawo kan gadon ta zauna ta yi shiruu tanata tunani.

Gramma na gama shigowa da kayayyakinta ta sa kwaskon garwashin a k’asan kujerar
sanann ta bud’e kaplas d’in…
Wasu y’an k’ananan robobine masu murfi a ciki!
Sai da ta bud’e kusan duka ta d’eba wannan ta d’eba wannan tukunna ta tara akan murfin roba
d’aya, ta kalla Hudan tace mata “tashi”
Sai da ta tashi tukunna ta k’arasa ta d’auko k’atoton bargon kan gadonta sannan ta dawo ta
wareshi ta ajjiye a gefe
kafin ta d’auki had’in da tayi na kan murfin robar ta zuba a cikin kaskon wutar ta saman kujerar
tukunna
ta umarceta da ta zauna da wuri.

Sai da ta rufa mata k’aton bargon tukunna ta ce ‘ta kwance bathrobe d’in jikinta ta bata’
A hankali ta warware ta mik’a mata sai kuma ta fara k’ok’arin tashi dan wani zafi ne ta fara ji

yana ratsa ta saboda hayak’in ya fara turnuk’e koina a cikin bargon.

Sai da Gramma ta yi da gaske tukunna aka samu Huda ta zauna, har da hawayenta kuwa
fuskarnan ta yi jajawur.

Tana nan zaune suka ji ana knocking!
Sai da Gramma ta kora mata warning d’in karta motsa tukunna taje ta bud’e k’ofar.
Murmushi tayi sanann tace
“Ashe ma kishiyar tawa raguwa ce nake ta jin tsoro?
Shigo ki ga kuka wiwi a iya tsugunno kawai.”

Tana jin murmushin Ummu ta fahimci itace, ai kuwa ta fara zillo tana lek’awa nan suka had’a
ido. Tana shirin tashi Ummu tace “dalla zauna”
Cikin sigar tsokana.
Wani sabon farin cikin ta sake ji ya lullub’e ta sakamokon ganin Sakina sun shigo ita da mommy
suna yi mata dariya suma.

Cikin mutunta juna aka shiga gaggaisawa daga nan Gramma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login