Showing 87001 words to 90000 words out of 113579 words

Chapter 30 - So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel Document By Bulama.pdf

Bulama   

28 May 2025

8293

d’an dawo dede.

Ajiyar zuciya Granpa ya sauk’e kafin ya ci gaba da cewa
“Bincike yana tafiya
bayan an yi testing tukunyar an tabbatar da poison mai k’arfi ne a ciki sannan har da shinkafar
b’era. Sai kuma still
aka samu gidan allura a cikin dustbin d’in kitchen d’in
wanda ba komai ne a cikin wannan allura ba
face poison d’in da aka yi amfani da shi aka zuba a cikin coffe d’in. Tou a jikin syringe d’inma
kuma sai aka sake samun wani sabon tombprint d’in wan..........”

Shigowar Arshaad ce ta katse Granpa da kowa na wajen
gaba d’aya sai kallo ya koma kansa.

Shiruu parlourn ya d’auka na y’an mintuna kafin ya ce
“Assalam alaikom, sorry I’m late”
Bai jira jin me za su ce ba ya k’arasa gaban officer d’in kawai ya mik’a mishi hannayensa duka
biyu.

Kuka Dad ya saka kawai ya mik’e ya fita.
A hankali Granpa ya sunkuyar da kanshi k’asa
wasu zafafan hawaye suka zubo masa.

Da mamaki Mommy ta mik’e ta k’arasa wajen ta kamo hannun Arshaad cikin zaro ido ta ce
“Arshaad me ye haka ?”

Da kyar ya samu hawaye ya zubo masa a ido d’aya! A hankali yana kallonta ya ce
“Mommy ni ne!
Duk wannan bayanin da Granpa yake yi muku a k’arshe suna na za ku ji a matsayin mai laifi!
Ni na yi poisoning Ummi wanda Aslam naso kashewa tashi d’aya abun ya fad’a kan Ummi
dan haka
dan Allah taron nan ya watse haka, ku daina kwana kwana
kowa ya tafi
officer please arrest me”
Ya k’arashe maganar yana sake juyawa ya mik’awa officern hannuwanshi duka biyu kamar
farko.

Mik’ewa kawai officer d’in ya yi ya zaro ankwa.

Ba k’aramin tashin hankali Mommy ta shiga ba
bata san lokacin da ta shiga tsakaninshi da officer d’inba cikin fushi ta cewa officer
“meyene haka yake faruwa?”
Kafin ta juya ga Arshaad ta ce
“Arshaad ba zan bari ka tafi gidan yari ba!”
Ta fad’i haka tana nunashi da yatsanta dede fuskarshi alamun warning
tana hawaye sannan ta ci gaba da cewa
“Ko meye ka aikata ba zan bari ka tafi gidan yari ba wallahi!
Na san ba halin ka baneba
pushing d’inka aka yi
kayi hak’uri ka dawo Arshaad d’in da muka sani”

Cikin kukan ta k’arasa gaban Granpa ta ce
“Granpa Ummi kanta na san ba zata so haka ba!
Dan Allah in domin ita kake yi to ka yafewa Arshaad
ransa ne ya b’aci zuciya ce ta kaishi
ba laifinsa bane ba.”

Gani tayi kawai mutumin yana k’ok’arin sakawa Arshaad wanda ya tsaya kawai yana hawaye
ankwar, da sauri ta mik’e ta koma wajen ta fincike ankwar ta yar sannan cikin fad’a ta cewa
mutumin
“Wallahi bar ganin aikinka kake yi, na rantse da Allah idan ka saka mishi ankwa sai na tsinka
maka mari!”

Runtse ido Arshaad ya yi da k’arfi kafin ya samu ya bud’e ya juyo da Mommy ya ya kama
kafad’unta duka biyu ya fara magana cikin d’aci
Idanuwanshi jajawur
“Mommy ba laifi d’aya bane a kaina okay?!
Ko kin kawar da wannan dole zan tafi jail saboda Junaidu ya yi filing complaint a kaina and all
evidences are against me so just let it go this is wat i deserve.

Dan Allah.”

K’amewa kawai ta yi tana kallonshi.

A hankali Aslam ya k’araso wajen ya dafa shi ya ce
Arshaad!
Ka juya ka fita a parlourn nan
zan san abun yi please.
Dan Allah ka tafi kawai!
Meye ma ya kawo ka nan in the first place?!”
Ya fad’i hakan cikin d’an d’aga murya.

A hankali Huda wadda ta k’araso wajen yanzu itama tare da Aaima ta ce
“Ya Arshaad me ya had’aka da Ya Junaidu?”

Lumshe idanuwansa ya yi a hankali ya juyo yana kallonta ya ce “Kin tuna sharrin da aka yi
masa akan case d’in Chief Justice!?
Sannan akaso a sake d’auke shi bayan an sakeshi?
Those that ring a bell??”

A firgice wani kalan kuka yana taho mata ta ce
“Ya Arshaad dan Allah kar ka ce min kaiine!
Dan Allah Ya Arshaad”

Sai da ya matsa dede setin fuskarta tukunna yana kallon cikin idonta ya ce
“It was all me!”

Wani irin kuka ta fashe da shi
ta durk’ushe a wajen cikin kukan ta ce
“How??
Why???”

Ranshi a tsananin b’ace ya ce
Why?
Tambayata ma kike yi ‘why’!?
Bara ki ji dalili
‘It was all because of you’
And bari ki ji abunda ya faru…
Naga take taken Junaidu
At that very day
kuma kema naga kamar kina k’aunar sa, nuna miki ne ban yi ba amman
hankalina a matuk’ar tashe na bar wajen ki. Na biya ta wajen friend d’ina Jamil! Sai na samu
suna tattaunawa akan wata magana…Yanayi na yasa ya tambayeni dan haka ban b’oye mishi

komai ba
na fad’a mishi damuwa ta.
Ya san ki ya san yadda nake sonki shiyasa ya ce ‘in bashi number da information d’in Junaidun
kawai’.

Abun ya zo mana da sauk’i saboda already best friend d’in Junaidun Yaron Abokin nawa ne
Jamil.
A time d’in ban san me za su yi ba kawai ni dai nace ‘a san yadda za a yi min da Junaidu’
Sai da aka kashe mutumin tukunna na fahimci me sukayi.”
Cikin d’aci ya ce
“Kinsan wani abu?”
Be jira jin me zata ce ba ya ce
“Ban damu ba!
Kwata kwata ban damu da kisan kan da aka yi ba saboda
Idanuwana sun rufe
I was just selfish and bad!
And happy tunda Junaidu ya b’ace kenan babu abunda zai sake shiga tsakaninmu ko ya yi
yunk’urin raba mu.
Ban damu da yadda ya sha wahala a Prision ba
bayan an sake shi na sa a d’auko mini shi.”
Yana kallonta ya sake cewa
“Kinsan wani abu?”
Nan ma be jira amsa ba ya d’aura da cewa
“Ko da aka ce motar su ta kama da wuta
Hudan ban ji haushi ba ban ji babu dad’i ba
ban kuma fad’awa kowa na san wani abu ba!
Na take komai
na rufe idona duk dan inga na mallakeki!
I was bad!
Ban yi deserving freedom ba so pls dan Allah ku bari kawai su tafi da ni.”

Cikin fushi Aslam ya ce
“Ba za a bari ba!
Da kasa aka kama Junaidun ai kuma still kai kasa aka dinga bashi shelter da abinci mai kyau
Kaga hakan yana nuni da still akwai good in you Arshaad
you felt guilty which is good.”

A hankali ya juyo ya kalleshi kafin ya ce
“For your information nine na janyo aka rufe maka company d’in takalman ka!
Is there any good in me left?”
Ya fad’i hakan yana kafeshi da dogayen idanuwanshi.

A hankali ya ji Aslam d’in ya ce

“I know Arshaad
na san komai!
Tun kafin In tafi a time d’in da aka kirani na fahimci kai ne
So
dan Allah maganar nan ya wuce
please”.

Cikin katseshi ya ce
“Na so In kashe ka!
Ka bar duniya
gaba d’aya
In auri matarka!
Is there any good in me?
Still kana da hope a kaina ........”

“Ina za ki je?”
D’in da Granpa ya ce ne yasa gaba d’ayansu suka juya suna kallon k’ofar da Mammy ta nufa
sad’af sad’af zata fice.

A hankali Mom wadda tun d’azu take magana ba a jinta tace
“I have something to say”
Da d’an k’arfi.

Duk juyawa akayi aka zubawa screen d’in ido, suna kallonta
Idonta sharkaf da hawaye ta ce “Arshaad baka so kashe Aslam ba!
Ka dai yi yunk’urin yin hakan
amman kuma baka aikata ba
saboda baka so ba....……
A ranar birthday d’in su Shuraim!
Bayan Dad ya gama yi mana fad’a akan Sakina da abubuwan da muke yi..I was furious!
Sannan burin da na d’aura akan Auwal ya mallaki MT duk sai naga yana shirin tab’arb’arewa
tunda na lura shi soyayya ce a gabanshi a yanzu!
Hankalina bai sake tashi ba
sai da Mammy ta sanar min da cewar ta ga copies d’in takardun MT da Granpa ya mallakawa
Aslam a d’akin ka
a ranar
Lokacin da ta shiga
kai kuma ka fita ka barta a d’akin, wanda bamu san ma an mallakawa Aslam d’inba
kuma bamu san ya aka yi kai ka sani ba.

A take take ce min
‘Komai ya zo mana k’arshe ni da ita!
Amman ta samo mana solution

dan daman tun da taji labarin kyautar gidan da Granpa ya yiwa Aslam ta gama cire hope akan
MT a Yaranmu muddin Aslam yana raye!..
Dan haka yanzu it’s either I’m with her
ko kuma I’m doomed’.

Sai da muka keb’e mu biyu tukun ta yi min bayanin
abunda za a yi shine…
‘Ga shinkafar b’era nan daman ita da shirin ta ta zo
gara kawai a yita ta k’are!’.

Dukda
a lokacin i was furious
amman ban yi amanna da shirin nata ba, sai da ta yi mini
cikakken bayani kuma na lura komai ya kusan zuwa mana k’arshe tukunna na yarda but still sai
na ce mata ‘Gara mu zuba iyaka wadda zata la’antashi ko ta sakashi doguwar jinya
dan ni gaskiya ba zan iya kashe Aslam ba’.

D’ari bisa d’ari ta nuna min ta yarda, ban tashi sanin Mammy yaudarata ta yi ba
sai da na ga gawar Ummi a kan cinyata”.
Ta fad’i hakan tana fashewa da kuka.

Da sauri Mammy ta k’araso wajen ta ce “bana son munafurci!
Munafuka ai da ke aka yi....”
Wata mahaukaciyar tsawa Dad ya daka mata
ya ce
“wallahi idan kika sake yin magana sai na kasheki da hannuna kafin a tafi da ke gidan yari!”

In a serious tone Granpa shima ya ce mata
“Ki nutsu!
Ko In saka a fasa miki kai da bindiga”
Sannan ya juya ya cewa Mom
“Continue”

Cikin kuka Mom ta ci gaba da magana
“Muna tunanin ta yadda za mu shiga d’akin su Aslam mu zuba a lemon cikin fridge d’in da yake
a d’akin nasu
ko mu zuba a ruwa ya sha
sai Allah ya kawo sauk’i
muka ji ya cewa Huda “ta had’a mishi coffe”

Hudan na shigewa kitchen aka fara watsewa, muma muka fita
Mammy ta cewa Dad ‘zata tafi tare da k’awarta ta ajjiyeta a bakin gate yanzu’. A gaban sa ta
shiga motar kawar tata, motarsu shi da

Aisha tana fita ta fito ta yiwa k’awartata sallama muka zagaya baya ta ce min
‘in tsaya a nan baya in tabbatar babu wanda ya ganta
In yi keeping mata watch daga nan ita kuma zata shiga ta aiki Huda ko kuma dai ta d’an ja
hankalinta ta watsa gudun kar idan zance ya fito Huda ta ce ita ce ta aiketa’.

Har zata juya na rik’o hannunta na ce mata ‘ta zuba d’an mitsitsi kawai dan Allah’
A gabana ta nuna min d’an k’aramin da zata zuba
wanda na tabbar ko b’era ba lallae ya iya kashewa ba!
Na so ta bani ragowar amman sai ta ce ‘ko dai ban yarda da ita bane ba?’
Shiyasa kawai na yi trusting d’inta na barta ta wuce.

Kafin Mammy ta zagaya
ina zuwa bakin k’ofar kitchen d’in ta baya sai na ga
Hudan ta fita!
Ina shirin kiran Mammy a waya naga an shigo..
Wallahi Arshaad fuskarka da jikin ka a rufe suke ko’ina
amman tashi d’aya na gane ka.

A tunanina bakin ku d’aya kaida Mammmy sai da na ga
ka zaro allurar da bata cikin tsarin mu tukunna gabana ya fara fad’uwa.

Ba k’aramin sanyi na ji ba da naga har ka bud’e allurar zaka zuba kuma sai naga ka yi tsaki ka
rufe ka mayar ka ajjiye
alamun ka fasa”.

A take gaba d’aya kowa a falon aka ce
“Alhamdulillah”

Cikin kuka ta ce
“Garin lek’en ka da nake ta yi yasa har ka gannni
ka fito ba tare da ka d’auke allurar ba.
A cikin filawowi na b’uya kana wucewa na zagaya
ta k’ofar parlour
zan shiga kitchen d’in
tun a bakin main door na parlourn na hango Huda
tana shirin shiga kithchen d’in
amman ban hango Mammy a kitchen d’inba
wadda na tabbatar ita ce ta had’a da allurar da ba lalle ta gama sanin ta mecece ba ma da
shinkafar b’erar ta matse gaba d’aya a cikin coffee d’in wanda sanadiyyar hakan ne na rasa y’ar
uwa ta d’aya tilo
a duniya.

Da sauri na fita na zagaya baya. Ina zuwa bayan kitchen d’in na ga Mammy a wajen tanata

gumi, ta ce min ‘ta zuba amma fa saura kad’an Huda ta kamata’.
Jin kamar tahowar mutum ta bayan mu ne
ya sanya kawai muka yi sauri muka bi ta gaba muka bar wajen. Na saka driver ya mik’a Mammy
estate
ni kuma na koma part d’ina.”
Cikin kuka ta ce
“Arshaad ba kai za a kama ba
Mu za a kama…baka da laifin komai”.

Da sauri Mammy ta ce
“Ke dai za a kama munafuka!!
K’arya take yi min, duk abunda ta fad’a k’arya ne wallahi.”

A hankali Arshaad ya lumshe idanuwanshi wasu zafafan hawaye suna zubo masa.

Mom bata damu ba ta ce
“Another things…
Although ban san waye ya turo Mommy daga bene ba but Mammy nake zargi dan na ji tana
waya rannan kamar da malaminta ne tana cewa ‘a sake toshe mata baki a goge mata tunani
kar ta tona mata asiri kafin ta san abun yi next da ita’ da kuma na tambayeta sai ta k’i gaya min
komai dan haka bani da tabbas amman tabbas na san wanenen musabbabin ciwon nata tun farko
Mammmy ce ta yi mata asiri!
Har wajen bokan da yayi aikin idan kuna so zan kaiku.
Shiyasa tun a cell Mommy tana warkewa mu bama ma saniba
Ita kuma Mammy ta fara mugayen mafarkai
Inaga sauk’ar da akeyi a gidan nan kullum ne ya sanya
abun bai koma kanta ba
ta samu mafarkan suka barta.”

A hankali Aslam ya ce
“Ita ta turo ta daga bene”
Kafin ya kalli Mommy ya ce
“Mommy ranar da naje zan ce miki Ina son tafiya Uk
ana i jibi auren su Arshaad…
Pretending kawai na yi dan ban san ta Ina zan fara ba
sannan naji kin ce peace da kwanciyar hankali kawai kike buk’ata a yanzu
Amman tabbas na ji conversation d’inku ke da Dad.”

Mom ce ta sake cewa
“Sannan mammy.....”

Da sauri Mommy ta k’arasa gaban screen d’in ta had’e hannuwanta biyu ta ce

“Dan Allah dan Annabi Adama ki yi shiru”
Sai kuma ta fashe da wani sabon kuka.

A hankali Granpa ya ce “kowa ya zauna”

Ba ayi minti uku ba duk suka zazzauna har Arshaad da Granpa ya sake ce mishi
“Muhammad zauna kaima”

Da kyar Granpa ya samu ya ci gaba da magana….
“daZa mu yi amfani da tombprint mu hukunta mai laifi…
Second hannun da ya fito a jikin tukunya apart from na Huda hannun Rukayya ne!
Sannan ya sake fitowa a jikin syrinji tare da na Arshaad
wanda na tabbatar kafin ya saka safar da Adama ta fad’a ne ya yi mistake ya rik’e
dan bai fito a jikin tukunya ko murfin ta ba.
Ya fahimci hakan inaga
tun a ranar da aka d’auka samples d’in shiyasa ya yanke shawarar ya gudu!
Ban kuma san me ya dawo da shi ba dan haka yanzu inaso ka fad’i gaskiya da gaskiya tun da
an san komai
kuma muma mun fahimci komai.
Kaga waennan manyan y’an sanda da ss ne
kar ka cuci kanka
ka yi bayanin da zasu d’auki rahoto dan na yi alk’awari sai na hukunta duk wani mai hannu a
kisan Ummi!.
Shin maganar da Adama ta fad’a gaskiya ce?”

A hankali Arshaad ya girgiza kanshi kafin ya ce
“Ba haka bane ba!
Ni ne na zuba!
Ni na yi hacking wayar Sakina na kira Huda waje tana fita ni kuma na je na zuba!
Dama inada wannan plan d’in a raina tun dawowata saboda na fahimci Aslam yana son auren
shima.
Granpa na rok’eka da girman Allah ka barsu su tafi da ni.”

Tsabar takaici Aslam bai san lokacin da ya shak’o sa ba ya ce
“Meyene ribar ka Idan an tafi da kai?
Me za ka ji a jail!?
Arshaad ka san inane jail kuwa?”

Sai yanzu Gramma wadda tunda aka fara case d’in ta sunkuyar da kanta tana salati
ta samu ta fashe da kuka…
A hankali ta d’ago kanta ta taso ta iso inda suke
ta kama Arshaad ta mik’ar da shi tana kuka ta ce
“Aslam ka manta waye Arshaad ne?

Tun kuna Yara
Idan ya yiwa mutum laifi b’uya fa yake yi ko da ace mutumin ya yafe masa sai yayi kusan wata
yana wasan y’ar b’uya da shi. Ka san Arshaad yana da kunya yana da kawaici kuma yana
k’aunarka!
Na tabbatar laifin da ya aikata ne ya saka shi yake jin ba lalle a yafe mishi ba sanann shi kanshi
ba zai iya fuskantar kowa ba shiyasa ya gwammaci zaman jail

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login