Showing 72001 words to 75000 words out of 113579 words

Chapter 25 - So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel Document By Bulama.pdf

Bulama   

28 May 2025

8328

da wannan
k’addarerren cikin!
Dan ta ce babu kalar protection d’in da ba suyi using ba.

Ba yadda muka iya haka muka rufa mata asiri mu uku
muka nufi asibiti da ita
dan tace idan Baban ta ya san labarin wallahi na lahira sai ya fita jin dad’i!
Yadda kika ga Granpa to haka itama Babanta yake da mugun tsauri! Kuma ita abun nata ma
duka biyu za a iya cewa
dan Mahaifiyarta itama hakan take da tsauri.

Muna zuwa muka zubewa Likitan kud’i muka gaya mishi flushing muke so a yi mata duk da
tanata ce mana ance ‘tana da matsala cikin ba zai fita ba’ Amman still muka zab’i mu gwada
sa’ar mu..
Bayan y’an gwaje gwaje
unfortunately
Likitan ya zaunar da mu yayi mana cikakken bayani akan cikin nan ba zai fita ba!
Saboda tanada matsala
kuma in dai ance za a cire d’in tou it’s either ta mutu
ko kuma ta samu uterus failure.

Bamu da wani zab’in da ya wuce mu nemi Sageer duk da kuwa ta ce mana ‘tun last zuwanshi
da ta ce mishi tana da ciki
ya d’auke ta ya kaita asibiti aka gaya mishi abunda aka gaya mana!

Kwana d’aya kawai yayi mata a gidan da suke had’uwa
daga nan ya k’ara gaba
kuma tun daga ranar ko wayarshi ta kira a kashe take jin ta. Although bai nuna mata komai ba
dan faram faram ma suka rabu
ko amai idan ta yi shi yake kwashewa ya gyara gurin
yanata faman jera mata sannu’.

Wani babban tashin hankali da abun al’ajabin da muka fuskanta shine
Hatta gidansu Sageer da address d’insu da ya bayar a garin Gombe gaba d’aya fake ne!
Hatta sunan Babanshi
Alhaji Bashir mai galon da ya fad’a mana gaba d’aya k’arya ne. Har Gombe
d’aya a cikinmu ta rok’i saurayinta ya je
ya bincika mana
amman babu abu d’aya da yake gaskiya a cikin labarin Sageer!
Komai fabricating kawai yayi.

Da muka fahimci haka
sai muka koma wajen Bestien ta, to shima dai ta wajen na sa duk sammakal dan ce mana ya yi
shima Iyakar wannan information d’in da muka sani akan Sageer shima shi kad’ai ya sani, ya ce
a wajen ball suka had’u suka fara shiri
suka d’anyi business tare
ranar kuma suna tare ya ce masa zai je wajen k’awar shi shine yace zai rakashi.
Shi bestyn nata ma
cewa yayi
wai ‘mu yi ta addua gaba d’ayan mu
maybe aljani ko maye muka had’u da
Allah ya tak’aita’.”
Ajiyar zuciya Aaima ta sauk’e sannan ta ci gaba da cewa
“To yau dai Allah ya had’ani da Sageer!”
Bata gama rufe bakinta ba ta mik’a musu hoton data nemo a wayar tata tun d’azu………

Sakina ce ta fara karb’ar wayar
tana kallonta kafin ta sauk’e idonta a kan wayar.

A hankali Huda ta ce
“Innalillahi wa innailaihirrajiun”
Bayan itama ta l’eka ta gani.

Sakina kuwa lumshe idonta kawai ta yi ta bud’e
ta kalli Aaima idonta jazir tap kwalla ta ce
“Aaima are you sure??”

“Very sure Sakina!

Ki yi ta sliding za ki ga pictures da videos d’insu kala kala irin wannnan shi da Suhaila.

Daga nan ki gaya min Idan wannan bawan Allahn ba Ashraff bane ba.”

BULAMA ✍️



So da Buri
Free Book
69

Mikiya Writers Association.
Kai kana ganin fuskokinsu ka san suna cikin tashin hankali ba na wasa ba.

Kallo suke suna sake kallan pictures d’in amman ba ta inda za su ce ba Ashraff bane ba.

A hankali Sakina ta mik’a mata wayarta sannan ta ce “yana Ina?”
Ta yi mata tambayar tana k’ok’arin mik’ewa tsaye.

Cikin ruk’o hannunta Aaima ta ce
“Ya tafi”
Sannan ta d’aura da cewa
“Mai aiki nasa taje har chan waje ta shigo da shi parlourn Mammy.
Abunda ya bani mamaki ya kuma d’aure min kai
shine
yadda ya nuna kamar irin kwata kwata babu alamun yama tab’a ganina d’in nan
sannan kuma he looks calm and innocent!

Kasa hak’ura na yi bayan mun gaisa na ce mishi
“Sageer”
Amman sai na ga yana kallona da mamaki!
Ganin da nayi ban ma san abunyi next ba yasa kawai na ce masa ‘ya tafi, dan Allah yayi hak’uri
wani abun ya taso min urgent!’
Cikin fahimta ya nuna min ba damuwa ya mik’e ya tafi.
Sakina kaina ya d’aure saboda a ganina inda ace Sageer d’in ne to da ko a idanunsa zan
fahimci firgici! Da d’an alamun wani abun dole zai nuna amman kuma
ko twins banajin za su iya zama super identical haka kamar shi da sageer..
Hatta fa yanayin magana kallo tafiya komai nasu iri d’aya ne..”

Cikin katseta Sakina ta ce
“Kar ki damu Aaima, ba wani
Sageer

sunanshi Ashraff!
Shine!
Raina miki hankali kawai yayi.
Ga Abokin sa nan ma Abbakar a wanann hoton.”

Da sauri Aaima ta karb’i wayar ta kalla sai kuma ta ce
“Ai shine Saddik d’in”

“Hmm”
Kawai Sakina ta ce tana
mai dialing numbershi a wayarta.

Ajiyar zuciya Aaima ta sauk’e kafin tace
“Kuma kin san abunda zai sa ma mu sake gasgata shi d’in ne…
Ranar farko da suka fara zuwa
a ranar da ya had’u da Suhaila
da ya ce mata
‘I’m Sageer by name’
Sai da Abokin nashi ya juya a zabure yana kallonshi
sai kuma na ga ya fara murmushi yana girgiza kai.”

Dede nan Ashraff ya amsa call d’in Sakina…
Daman a handsfree ta saka
“Hello baby”
Suka ji ya fad’a.

Sai da Sakina ta sauk’e wata nannauyar ajiyar zuciya tukunna ta ce
“Ashraff ko Sageer?”

“My god!!
Waye ne Sageer d’innan ne?
Kin san i was just about to call you sai kika kira…
That cousin of yours
she looks confuse!
Tana ganina ta ce min Sageer itama.
Ask her ta yi miki bayani please dan i d.........”

Cikin katseshi ta ce
“Dakata Ashraff!
Ba ita bace confused, ni ce!
Bayani kuma ba ita za ta yi min ba kaine!.
So I’m all ears
Ina so inji

ta yadda ka chanja sunan ka
da kuma yanda kake planing zaka yi da mu
Ni da Suhaila da kuma d’an cikinta”

“Oh Noooo!
Innalillahi wa innailaihirrajiun
Sakina haba mana.
Tana ina ita cousin d’in taku?
Bata wayar please…
Wallahi daman yadda na ga tayi na san akwai matsala,
waye Sageer? Wacece Suhaila? Ciki kuma a Ina?.
Sakina na riga na gaya miki y’an mata biyu kawai na yi dating b4 you
and duk na nuna miki pictures d’insu, please Sakina
kar ki biye mata
i think akwai confusion a lamarinta
amman wallahi ni ban san wani Sageer ba,
bata wayar please”.

Fashewa kawai ya ji Sakinar ta yi da kuka, cikin kukan ta ce
“Haba Ashraff!
Despite abunda ka yi da k’aryar da ka yi
still kana so ka ci gaba da b’oye b’oye?
Wat have i ever done to you to deserve this?”

“Innalillahi wa inna ilaihirrajiun” kawai ta ji yanata maimaitawa kafin ya ce
“Shikenan Sakina,
na gane! Yanzu na fahimci komai…
Kina neman hanyar da za ki zillemun ki auri Auwal d’in da kike ta tunani kullum ko?
Ko kina tunanin ban saniba ne?
Idan ba kya sona ki fito fili kawai ki gaya min ki daina yi min kwana kwana!
Bawai ku had’a baki ba
ku k’ulla min sharrin abu mai muni haka ba.
Wallahi tallahi kin ji de na rantse miki
ni ban san wani Sageer ba
ban san wacece Suhaila ba
sanann wallahi Sakina da gaske nake sonki ba yaudara a ciki! Ke kad’ai ce a cikin zuciyata”
Ya fad’i haka yana me fashewa da kuka kamar k’aramin Yaro
sai kuma ta ji ya kashe wayar, kiit!.


Ashraff, yana kashe wayar ya kira Saddik yana d’auka bai jira jin me zai ce ba
ya ce
“Saddik, I’m doomed….”

Sanann ya hau koro mishi bayani hankalinshi a mugun tashe.

Shiruu Saddik d’in yayi
bayan ya gama ji
kafin ya ce
“Listen closely Ashraff..................”


Gaba d’ayansu hankalinsu a tashe yake, bama su san ta Ina za su fara ba.
Aaima ce ta yanke shawarar kiran Suhailar dan haka ta d’au waya ta shiga sunanta ta danna
call……

An fi thirty minutes tukunna aka samu layinta ya fita daga busy ta amsa kiran Aaiman.

Ajiyar zuciya Aaima ta sauk’e kafin ta ce
“Da wa kike waya haka?”

Sai da ta d’anyi jimm! Tukunna ta ce
“Wata friend d’ita ce”

Shiruu, Aaiman ta yi tana tunanin wacece k’awar Suhaila haka da bata san ta ba…
Sanin ba wannan ne a gabansu ba
ya sa kawai ta kawar da zancen ta hanyar bata labarin Sageer Ashraff from A -Z kafin ta ce
“Yanzu ko gidan su idan kinaso zamu iya zuwa dan Sakina ta ce ta san gidan
kuma zata bamu adress har number Mamansa.”

Cikin katseta Suhailan ta ce
“Mun gama case d’in Sageer fa!
Ki manta kawai please, kar ki
sake yi min maganarsa”

A rikice Aaiman ta ce
“Kin gama case d’insa da cikinsa a jikinki??”

“Please Aaima”
Shine kawai abunda Suhaila ta ce.

Aaima za ta yi magana kawai ta ji ta katse kiran.

Kasa cire wayar daga kunnenta Aaiman ta yi,
da kyar ta d’ago tana kallonsu still da wayar kare a kunnenta.

Kirane ya shigo wayartata

dan haka ta d’an zabura saboda a kunnenta wayar take har yanzu…
Tana ganin mai kiran nata ta d’auka da sauri ta ce “yauwa Khadija kin san me yake faruwa?
Yanzun nan....”

Cikin katseta Khadijar ta ce
“Sageer, yanzun nan ya kira Suhaila….
Suna fara magana ta tashi ta shiga bathroom, haka
kawai na ji inaso in yi mata lab’e saboda na san kusan wata nawa ana neman shi
sai yau kawai muga ya kirata.

A yadda na fahimta
Its like akwai wadda zai aura a yanzu! Wai family d’insu
sun zab’a masa
shiyasa ma ya d’auke k’afa
amman yayi mata alk’awarin aure nan da wata biyar
muddin ta yi shiru.

Ban gama dawowa daga mamaki ba
na ji conversation d’in ku a waya yanzu.
Meyene yake faruwa?”.

Ajiyar zuciya Aaima ta sauk’e rai a b’ace ta ce
“Wato shine Ashraff d’in ta tabbata kenan!…”
Nan ta d’an yi briefing Khadija a kan case d’in sannan ta ce
“Khadija Suhaila tana son
Ashraff
ba zata tab’a iya k’etare umarninshi ba!
Dan haka yanzu aiki yana a hannunki..
Ki taimaki y’ar uwar ki
tunda ni dai kinji yadda muka yi da ita.
Zan turo miki number Mamansa yanzu
daga nan ki kirata ki yi mata bayanin komai!
Lokacin b’oye b’oye ya wuce
dole iyaye su shiga case d’innan.
Mugun tantiri ne Ashraff d’innan wallahi! Kin san yadda ya nuna kuwa kamar bai sanni ba
amman kalli har ya kirawota munafuki d’an iska!
Kuma wallahi k’arya yake yi
shi ya ga Sakina ya ce yana sonta ba wani had’asu da akayi
Infact
Families d’insu ma basu san juna ba sai ata dalilin ita Sakinar da shi Ashraff d’in.

Wanne irin rashin wayone haka Suhaila take yi!
Dan bayan soyayya tabbas akwai dak’ik’anci a cikin lamarinta, saboda Allah ace wai Mutumin

da yayi maka wannan abun
tashi d’aya ya dawo ya kalallame ka kuma ka yarda?
Duk da ban san me ya ce mata ba amman ai ya kamata ta tambayeshi dalilin da ya sa ya bamu
fake adress ko?”

A hankali Khadija ta ce
“Tabbas”
Sannan ta ce
‘Ta tura mata number Maman ashraff d’in ta kirata yanzu ba sai anjima ba
kafin Suhaila ta dawo d’akin.”

Da “to” ta amsa sannan ta katse kiran
kafin ta kallesu ta ce
“Yayar Suhailan ce,
Itama ta san da zancen.
Ina number Maman nashi?”

Kamar yadda Sakina ta fad’a haka ta bada number Maman Ashraff bayan sun kwantar mata da
hankali da kyar! Dan da cewa ta yi sai ta je ta sameshi a duk inda yake!
Hudan ma harda y’ar kwallarta ganin yadda Sakinar duk ta firgice ta fita haiyyacinta tana ta
kuka wiwi.
Gaba d’aya sun gigita da lamarin Ashraff. ..........


Suna zaune a d’akin wata maid ta shigo musu da abinci kala kala..
Aaima da Huda ne suka d’an ci
Sakina kam har yanzu hankalinta a tashe yake,
ashe ita ta yi gudun gara ne ta tadda zago
ba tare da ta sani ba…


Sai bayan sallar Magrib tukunna Junaidu ya kirata ya ce “taje yana waje, su wuce.”

Aaima ce ta rakata har bakin mota bayan sun sha kukan su ita da Huda
sannan sun d’an yi mata y’ar guntuwar Nasiha suma, dan itama Aaiman ba komawa za ta yi ba
sunyi sallama kenan
saboda
ta san Huda tsaf sai ta rik’eta kamar yadda ta kanainaye Sakina.

Duk da halinda Sakina take ciki
sai da ta fahimci kallon da Aaima da Junaidu suke yiwa juna!
Tun d’azu dama da za a kawo Huda ta d’an lura
yanzu kuma ta sake tabbatarwa

dan har tana yiwa Junaidun magana ma bai sani ba.

Kasa hak’ura tayi bayan sun d’au hanya ta ce
“Ya Junaidu ko dai In had’aku ne?”

Wani lallausan murmushi ta ga ya yi kafin ya ce
“A’a fa Sakina,
tuwon girma ai miyarsa nama!
Idan na d’auko wannan ina da wajen ajjiyeta ne?”

Da sauri Sakina ta ce
“Ya Junaidu
ranar nan fa na ji Kaka yana cewa Gidajen ka wajen biyar a Kano kawai ga motoci
ga filaye.”

Dariya ya yi this time around
sanann ya ce
“Ki bar maganar nan..
Although har ga Allah i felt something
towards her
very strong
amman tunda na rasa Huda
i don’t think zan yi aure
idan ma zan yi d’in to
gaskiya ba nan kusa ba.”

Ajiyar zuciya ta sauk’e
tana kallon yadda fuskarsa ta chanja
lokaci guda.
Daga haka motar ta d’auki shiruuu
kowa da abunda yake sak’awa a ranshi, har ya kaita k’ofar gidan nasu ya ajjiyeta.

Tana sauk’a yayi reverse ya juya dan akwai ayyuka da dama akanshi.

Tana shirin tura gate d’in gidan ta ji ya ce
“Sakina”
Da sauri ta juyo!
Daman taga kamar motarshi a parke d’an gaba kad’an.

Ganin sa d’in ne kuwa yasa ta had’e fuska tamau! Kafin ta ce
“Naam, Sageer.”

A hankali ya k’araso inda take, sai da hasken globe d’in k’ofar gidan nasu ya haska fuskarshi da

kyau tukunna ta lura da abun mamaki..
Gani tayi yana
kuka wiwi
fuskarshi har ta kumbure da alamun ya dad’e yana yi.

Tana shirin yin magana shi ya rigata ta hanyar cewa
“Sakina komai Aaima ta fad’a muku gaskiyane
nine Sageer!
Amman asalin sunana Ashraff.
Ba zan b’oye miki ba…
Har ga Allah tun farkon had’uwata da Yarinyar na ji ina sonta
amman ba so na aure ba
sha’awace kawai irin wadda shed’an kan saka a zuk’atan waenda ya yi nasara.
Na san Abbakar Abokina ne tun Yarinta. Muna barin gurin ya tambayeni ‘dalilin b’oye mata
asalin sunana da na yi’
Ban b’oye mishi ba
na fad’a mishi k’udurina a kanta!
Ya ji ba dad’i kuma yaso nusar da ni amman da yake
shed’an ya riga yayi galaba a kaina yasa sam ban ji ba.”

Matsowa ya sake yi kusa da ita
wanda hakan yasa ta d’an ja baya.
Cikin kuka kamar Yaro ya ce
“Sakina na yi laifi, na san
na yi laifi!
Amman dan Allah ki fahimceni
ki fahimci k’aunar da nake yi miki ta tsakani da Allah ce.
Ki duba kiga yadda ita na fad’a mata fake adress fake suna and everything
Ke kuma na fad’a miki komai nawa! Har waya kuke yi da Mamana.
Dan Allah kar ki bari a rabamu,
ki toshe kunnuwanki, fight for our love! Ko wanne d’an Adam ajizi ne
ni ga nawa mistake d’in
dan Allah ki fahimceni
kin ga gashi
na fad’a miki komai ban b’oye miki ba,
ki yi min adalci Sakina.”

Girgiza kai kawai Sakina ta yi sannan ta share hawayenta ta ce
“Meyasa ka zab’i ka gaya min yanzu?
Saboda an kira Maman ku ko?
Kuma ka san dole case zai taso…
Bara ka ji Ashraff
magana d’aya kawai zan iya gaya maka

saboda at this stage ba zan ma iya tolerating ganinka ba! Saboda abubuwan da ka yi sunada
yawa ban san ta Ina zan iya farawaba…
Abunda nake so ince kuma nake so ka fahimceni da kyau
tunda naga kana da sharp brain
shiine
Ba zan aureka ba!”

A gigice ya d’ago yana kallonta.

“Kwarai!!
Babu wannan maganar.
Ga responsibility d’inka chan ‘Suhailat’
Ka koma gareta
ka nemi yafiya
ku haifi d’anku
ku zauna lafiya
ku reneshi a tare!”
Tana gama fad’in haka ta juya zata shige gidan ya yi saurin ruk’o hannunta.
A mugun fusace
ta juyo bata yi wata wata ba ta d’auke shi da wani irin mahaukacin mari
jikinta har karkarwa yake yi ta ce
“Na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login