Showing 63001 words to 66000 words out of 113579 words

Chapter 22 - So da Buri Part 3 Complete Hausa Novel Document By Bulama.pdf

Bulama   

28 May 2025

8292

sannan tace
“Sannu da zuwa,
ya hanya?”

A hankali yace “Alhamdulillah”
Yana d’an satar kallon inda Huda take zaune ta sunkuyar da kanta.

Murmushi Gramma tayi sannan ta sa kai ta fice ta ja musu k’ofar dan ta lura idan ta ci gaba da
zama a d’akin Aslam na iya zuwa ya rungumo matarshi a gabanta.

A hankali ya ke takawa har ya k’arasa inda take ya tsugunna a gabanta.

Da sauri ta lumshe idanunta ta fara k’ok’arin nemo nutsuwa da lakkar jikinta dan ta gaza
samunsu.
A hankali ya kamo hab’arta ya d’ago da fuskarta
yana kallon yadda ta runtse idon da k’arfi!.
Ajiyar zuciya ya sauk’e kafin yace “I miss you..
Sosai!!!”

Bata bud’e ba kuma bata yi magana ba,

tana nan a yadda take.

A hankali ya fesar da numfashi yace
“Ko you still need more time?”

Sai a lokacin ta bud’e idanunta da suka d’an tara hawaye tace
“Moree time for?”

Ba tare da ya bari ta jaa numfashi ba yace
“Us!
More time for us..
ranakun da na baki sun yi miki kad’an ko?.
I was so eager to see you
amman ke naga ko murna ma ba ki yi da ganina ba”
A hankali yana kallonta yace “ko arzik’in sannu da zuwa ma ban samu ba.
Ya fad’i hakan yana d’an cika hab’arta sannan ya gyara zaman shi yana fuskantar ta.

Da sauri ta yi k’asa da kanta tana jin yadda k’irjinta yake dukan uku uku.
A hankali ta ji ya ce “Umm??”
Cikin wani kalar yanayi da siga.

Sai da ta sake yin k’asa da kanta tukunna tace
“Ina wuni, ya hanya? Ya aiki?”

Ajiyar zuciya ya fesar kafin yace
“Lafiya,
hanya Alhamdulillah
Aiki kuma, was terrible!
Na d’an samu matsala
har ya kai ga an rufe company d’ina na chan.”

Da sauri ta d’ago ta kalleshi
kafin tace “Subhanallah.
Garin yaya?”

Ya ji dad’in yadda ta damu da alamarin ba kad’an ba. A hankali ya d’anyi murmushi
cikin son kawar da zancen company d’in yace
“Don’t worry,
ba komai.
Ai inada wani ni da Abba..
Daman bawa ya kan samu abu
at any time kuma ya kan rasa,
wannan yana daga cikin k’addarar bawa,

fata kawai shine ya zamo mai yarda da k’addara mai kyau ko marar kyau”
A hankali ya sa hannu ya kamo nata yace
“wata biyu baya!,
Ubangiji yayi mini kyautar da sai da na suma tsabar farin ciki!
Ya bani abunda na riga na fidda rai da samu,
Amma yanzu ace dan na rasa company sai in damu?”
Yayi mata tambayar yana wani sassanyan murmushi.

A hankali k’irjinta yana wani mahaukacin racing tun da ta fara jin bayaninsa, ta d’ago tana
kallonshi.
Har yanzu murmushi yake mata.

Wasu hawaye ne suka zubo mata dan ta so ta fahimci inda ya dosa!
Cikin son fahimtar da shi da kuma kawo k’arshen bagwaren relationship d’in nasu
a hankali tace
“Ya Aslam shike nan yanzu Granpa zai sake cewa ni bad luck ce kenan”
Sai kuma ta sunkuyar da kanta da sauri ta fara share hawayenta.

Shi da farko ma bai fahimceta ba saboda yadda ya shagala da kallon lips d’inta, sai da
yaga ta fara kuka tukunna yad’an dawo dede sannan ya fahimceta!
Dariya ma shi ta basa
dan haka a hankali yayi y’ar dariya kafin yad’an matse hannunta wanda yake a cikin nashi yace
“In ya fad’i hakan, sai yaya?”

Da sauri ta d’ago tana kallon yadda yake mata wani murmushi mai tsada!
Cikin zubar hawaye tace
“Masoya ma wasu in sun lura zaman su tare zai na causing problem hak’ura suke yi da juna,
ballantana kuma mu.
Tun kafin abu yayi nisa
azo tun Granpa yana magana shi kad’ai har kowa ya fara gara kawai mu rabu da juna Ya Aslam
ka samu wadda kake so ka aura
nima in........”

Da sauri ya d’aura d’ayan hannunshi akan lips d’inta yace “shhh…”
Bai jira jan lokaci ba
yace
“Ni already na samu wadda nake so
Hudatie
bana jin kuma zan sake son wata a gaba sai dai wani ikon Allahn.
Tunda Allah ya bani ke ya gama mini komai.”
A hankali ya cire hannunsa a lips d’inta ya yi cupping fuskarta a cikin palms d’insa biyu ya d’ago
da kan da take ta k’ok’arin b’oyewa
yace “open your eyes”.

Gam!! Haka ta sake runtse idanuwan nata
k’irjinta na dukan uku uku da wani kalar mahaukacin sauri.

Cikin matso da fuskarsa daff da tata ta ji yace
“Open your eyes before i kiss you!”
Da sauri ta ware idanuwan nata tarr! Ta zuba su a cikin nasa…..
Kallonta yake yi itanma shi take kallo ta ji yace
“I love you”

Da sauri ta runtse idanunta sai kuma hawaye sharr! Kamar an bud’e fanfo..
A hankali cikin kuka still yana rik’e da face d’inta tace
“Ya Aslam dan Allah kar ka yi haka. Za aga kamar daman chan muna son juna.
Za a ganmu kamar butulu.
Ba sona kake yi ba,
idan muka rabu ka had’u da true love d’inka zaka fahimci hakan. For now dan Allah let’s just
end this relationship............”
Muryartace ta mak’ale sakamokon had’e bakinsu da yayi waje d’aya!….
Wani Irin salo ya shiga aika mata da shi wanda ya kusan tarwatse kwakwalwarta.
Sai da ya ji tana shirin sume masa tukunna ya janye a hankali ya bud’e rinannun idanuwanshi,
yana maida numfashi, a hankali yace
“Those this feel fake?”

Fashewa tayi da kuka ta fara k’ok’arin kwace fuskarta amman yak’i bata dama
Instead ma kawai sai ya janyo ta izuwa jikinshi yayi hugging d’inta ya shiga shafa bayanta
alamun rarrashi
yayinda zuciyoyinsu suke bugawa a tare da mugun k’arfi......

Jin yanda take kuka sannan ta ma k’i ta saurareshi
yasa ya cikata a hankali yace “ki gayawa su Shuraim
Granpa yana son ganin kowa
after sallar isha.”
Yana gama fad’in haka ya mik’e ya fice dan yaga kamar tana buk’atar fitar tasa......

BULAMA ✍️



So da Buri
Free Book
67

Mikiya Writers Association.
Tunda Baba Bashir ya shiga gida yake ta faman kai kawo,

ba wai tunani yake akan wa Mama zata aura tsakanin Baba da Abba ba
a’a
tunani yake yi ta yadda zai fahimtar da Baaba Talatu
dan already ya gama deciding
tunda dama Mama tace ‘saboda Granpa yasa ba zata koma ba’ Gashi kuma yanzu Granpa d’in
ya zo da kansa
to kuwa in sha Allah ba zai yi k’asa a guiwa ba sai yaga an d’aura auren Mama da Abba.
Kawai shi yanzu damuwar shi Baaba Talatu ce dan ko
jiya da kyar tayi bacci!
Halin da Baba yake ciki ya tada mata hankali ba kad’an ba
so take kawai taga farin cikin shi ta ko wacce hanya
tsananin tausayinsa take yi.

Ya dad’e yana nazari kafin ya d’au hanyar d’akin da Baba yake jinya dan yana ganin gara su
fara maganar da shi tukunna.
Yana zuwa ya d’aga hannu kenan zai tura k’ofar ya ji suna magana shi da Ya Jamilu..........


MT ESTATE.
Kamar yadda Granpa ya buk’ata,
ana fitowa a masallaci su Abba suka bi bayanshi
zuwa gidansa..
A nan parlourn suka tarar da Mommy Mammy Gramma Huda da Aaima.

Ko ciki bai shiga ba ya nemi waje ya zauna a kan cousion ya fara bin ahalin nashi da kallo one
by one waenda suke nan jere a gabanshi wasu a kan kujera wasu a kan kafet.
Ajiyar zuciya ya sauk’e sannan ya kalla Aslam yace ‘ya bud’e taro da addua’.

Cikin nutsuwa ya jagoranci adduar suka yi suka shafa tukunna Granpa ya gyara zama yace
“Abubuwa uku! Zuwa hud’u ne suka sanya na taraku a nan.
Na farko
Aisha,
Kafin Zainab ta cika ta rok’eni akan in tayata neman yafiya da gafarar ki!
Sannan nima in nema yafiyarki
dan tabbas an zalinceki a baya,
da fatan za ki yafe mana.”

Ajiyar zuciya Mommy ta sauk’e
a hankali tace
“Komai ya wuce.
Na yafe na manta da komai
Allah Ubangiji ya ji k’an Zainab ya sa tana aljanna Firdausi.

Ahankali duk suka ce “Ameen”.

Sai da Granpa yad’an lumshe idonshi ya bud’e
tukunna ya kalla setin da Abba da Daddy suke yace
“Yusuf, Yakubu,
kuna iya dawowa estate anytime from now.
Komai ya wuce.”

A hankali Dad wanda tunda suka zauna yake ta k’ok’arin ganin bai bari kwallarshi ta zubo ba ya
sa hannu ya goge hawayen da suka samu nasarar zubo masa.

Ahankali kamar had’in baki su duka ukun suka ce
“Alhamdulillah”
A fili, kafin Daddy ya ce “mun gode Granpa
Ka yi hak’uri ka yafe mana.”

D’an guntun murmushi yayi kafin yace
“Ni za ku yafewa
Ina neman.....”

Da sauri Abba ya katseshi ta hanyar cewa
“Dan Allah kar ka rok’emu yafiyar komai,
kai Mahaifinmu ne kuma
d’an Adam ajizi ne,
kasancewarka Mahaifin mu ya sanya tun kafin ka yi mana wani abun ma mun riga da mun yafe
maka!
A Yanzu ba abunda muka fi buk’ata kamar yafiya da albarkar ka saboda tabbas na san mun
kwashi zunubi ata dalilin k’ok’arin mu na ganin mun nuna maka daidai.
Ka yi hak’uri Daddie a ko da yaushe zan baka hak’uri ne in yi ta baka hak’uri har k’arshen
rayuwata”
Ya k’arashe maganar hawaye suna tsilalo masa.

Mik’ewa Granpa yayi ya k’arasa inda yake ya kamo hannunshi ya mik’ar da shi tsaye sanann
yace
“Magana ta uku,
na amince maka ka auri Maryam!
Na yi accepting d’inta
sannan ina yi maka albishir d’in d’azu mun je ni da Aslam na nema maka aurenta da kaina
kuma an baka!
Ka zab’i gida d’aya a cikin gidajen estate d’innan ko wanne yayi maka
ka gyara mata
dan iyayenta sun ce anytime from now za su nemeni akan batun d’aurin auren.

Sannan Aslam shima ya zab’i d’aya su zauna shi da matarsa Huda!
Allah yayi muku albarka.”

K’ok’ari Abba yake ya rik’e kukan da ya taho mishi
amman sam ya gagara!
Dan haka kawai ya rungume Granpa a jikinshi ya sa kuka kamar wani Yaro.

A hankali Granpa yake murmushi mai had’e da dariya
kafin yace
“So kake ka k’arasa ni ne, Abbana.”

Wannan karon hatta Gramma sai da ta sa kuka…..

A tsakaninsu
Abba Dad Mommy Daddy Gramma sam aka kasa samun wanda zai lallashi wani.

A hankali Daddy shima ya taso yazo ya rungume su su biyun duka, haka shima Dad yana
hawaye yace “ba za ayi babu ni ba”
Ya k’araso shima yayi joining hug d’in yana dariya.

Gramma ce ta ce
“Kar fa ku kadashi k’asa”
Tukunna suka cikashi suna murmushi, Dad ya ja mishi k’aramar kujera mara nauyi ta study ya
zauna akai,
tukunna suma suka zauna.

Sai da parlourn yad’an yi shiru
tukunna
Granpa ya ci gaba da magana
“I was wrong!
Duk tsahon wannan lokacin ina kan ba dai dai ba
Allah ya ji k’an Zainab
Ita ta fara nasarar nuna min gaskiya sanann bayan dogon nazarin da nayi na fahimceta.”

Shiruu, ya d’anyi kafin ya cigaba da magana
“Na san dukkan nin ku anan kun san yadda nake jin Zainab a raina, ba abunda yake d’aga min
hankali irin in na tuna she was killed!
Sanann by an insider.”

Tsit!! Parlourn ya d’auka ko k’arar numfashi bakaji.

Kafin Granpa ya ci gaba da magana
“Tun ranar da ta rasu nayi alk’awarin sai na yi punishing killer d’in no mattaer how smart he or

she thinks they are! Dole zan yi bincike in nemo su kuma zan hukuntasu
dan ba zan yarda jinin Ummi ya tafi a banza ba.

30 days guda aka yi ana binciken caterers da waiters d’in da suka yi serving da girkin abincin
birthday
and an gano basu da hannu a ciki, sannan an binciki masu gadi kuma an bincika akan
ko sun ga wani abun
shima bamu samu komai ba
shiyasa nace muku its an incider!
Therefore bincike zai fara daga yau yanzun nan!
Ku yi hak’uri amman dole kowa ya amsa tambaya sannan ayi investigating d’inshi including me.
Daga nan banaso inga k’afar kowa a mansion d’in chan inda incidence d’in ya afku
har sai an gama komai..
Menwhile, Aslam”
Granpa ya kira sunan Aslam yana kallon sa.
A hankali ya d’ago idanuwanshi ya kalle
shi sannan yace
“Naaam Granpa”
Sai da ya sauk’e ajiyar zuciya kafin yace
“Ka je first building by your left
akwai bak’i a parlourn k’asa,
ka taho da su nan.”

A hankali cikin girmamawa Aslam d’in ya mik’e
ya fice…

Ba a yi 20 minutes ba suka shigo shi da wasu maza
su biyar!!

……..Da kyar suka had’iye yawun da ya tokare musu mak’oshi,
In banda “innalillahi wa innailaihirrajiun” ba abunda suke maimaitawa a tare!…….

Gaisawa bak’in suka yi da Granpa kafin yace
“Bismillah,
you can start.”
Ta kan Granpa suka fara…
Tambayoyine suka yi masa
akan relationship d’inshi da marigayiya sannan when last ya ganta?
Akwai misunderstanding d’in da ya tab’a had’asu?
Akwai wani secret ko
magana da ta tab’a gaya masa?
Ta tab’a gaya mishi sun yi fad’a da wani ko wata a cikin estate d’in? d.d.s……….
Daga nan

suka d’auko wani abu kamar na tomb print amman babba
suka ce “ya d’aura hannusa akai duka gaba d’aya biyun”
Hakan yayi, sai da hoton palm da yatsunsa suka fito a kan fuskar computer da suka jona a jiki
tukunna sukayi gaba.

Gramma ce next suna gamawa da ita sai Daddy sai Dad sai Aslam, Sudais Shuraim Arshaad
Aaima tukunna
Mammy sai ta kusan kuka
dan yana yin yadda suke tambayar tasu ko kana da gaskiya sai ka rikice
kafin wani ya rufe baki wani ya jeho maka wata…
Da akazo kan tambayar ‘ta tab’a fad’a mata sun yi fad’a da wani?’
A take ta hau zuba tana bada labarin yadda Abba baya sonta sannan ta tab’a ce mata sun yi
fad’a da huda!
Yana yin maganar tata yasa kawai d’ayan ya tsayar da ita ya d’anyi y’an rubuce rubuce akan
takardar ta
yace “shikenan. Ta d’aura hannayenta”.

Successful suka yi suka gama da Abba da Huda
sannan d’ayan ya kunna computer ya ajjiye a gabansu,
ga mamakinsu sukaga Mom da Auwal suma ana yi musu nasu binciken exactly kamar yadda
akayi musu.

Ana gamawa suka yiwa Granpa sallama suka fice.
Suna fita tun kafin Granpa ya fara magana Arshaad ya kalli Granpa d’in yace
‘Please idan an gama yana so zai wuce,
Yanada aiyyyuka da ya tara da yawa.’

Sai da Granpa yad’an yi shiru
tukunna yace
“Ok,
you can go.”

Yana fita aka yi addua aka watse kowa ya kama gabanshi…..


A hankali Granpa ya tura k’ofar d’akin Gramma ya shiga,
yana lura da ita tun d’azu
kamar jikin ya motsa dan bata da lafiya dama gashi
ta hanashi ya fad’awa kowa.

Yana shiga da Hudan ya fara tozali tana daddanawa Gramma d’in k’afa
dan zuwa yanzu kam ta gagara b’oye mata ciwon nata.

Hudan tana ganinshi ta sauk’e k’afar Gramma dake a kan cinyarta sannan ta mik’e ta d’an
russunar da kanta ta wuce ta fita.

Sai da ya ga fitarta tukunna ya juyo ya fara takawa inda Gramma take nan kwance akan gadon
ya zauna a inda Hudan ta tashi ya d’auki k’afafun nata ya d’aura akan cinyarsa!
Tana k’ok’arin mik’ewa ya ce mata
“Stay still”.

A hankali ya shiga matsa mata kamar yadda yaga Hudan tanayi……
Sun d’an jima a haka kafin chan yace
“K’afar dai?
Ba kya feeling kwata kwata?”

A hankali tace
“Ina ji, ba kamar d’azu ba.
Da k’afafuna na fita meeting na shigo nan fa d’azu”
Ta fad’a tana d’an murmushi alamun so take ya bar maganar.

Sai da ya sauk’e ajiyar zuciya kafin yace
“Maijidda, ko wanne family fa suna da nasu issues d’in!
Ba a kan mu farau ba, dan Allah ki kwantar da hankalinki.
Kin dai ga yadda d’azu jinin ki ya hau da muka gwada a d’akina, gashi har ba kya feeling side
d’in jikinki!
Kar kije ki samu stroke fa,
ki yi hkr ki rungumi k’addara
komai zai dawo normal.”

A hankali ta mik’e ta zauna sannan ta sauk’e k’afafuwan nata k’asa
kafin tace
“Daddie dole in damu.
Ace wai
a cikin zuriata an samu killer!
Taya kake so in kwantar da hankalina?
Bayan ban san k’arshen wannan musibar ba…
Suma fa y’ay’a za su haifa
kuma mugun hali da bak’ar zuciya jini yake bi, sannan Ina
tsoron idan zance ya fito
kar zuriar Ummi suma su zuciya su yi tunanin d’aukar fansa bayan sun girma
duk da kuwa ba Mahaifiyar tasu aka so a kashe ba.”
Ajiyar zuciya ta sauk’e kafin ta cigaba da cewa
“Daddie dan Allah idan result ya fito, aka kawo
muka ga wanda muke zxargi d’inne
Dan Allah karka baiyyana sunanshi a gaban kowa

dan Allah.”

Ajiyar zuciya Granpa ya sauk’e kafin yace
“That! I cant promise you Maijidda.
Saboda dole In cire rotten seed a cikin family d’ina…
An yi masa laifi
tabbas amman hakan ba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login