Showing 45001 words to 48000 words out of 126208 words
Chapter 16 - ALKAWARIN ALLAH BOOK BY HUGUMA.pdf
a
hankali a hankali tana tayata jin radadin.
Aqalla sun shafe awa guda cur a haka,harsai da kukan ya soma sassauta ta soma rage sauti
ya koma sai hawaye,mintina talatin ta sake qara mata zuwa sannan hawayen ya sake raguwa
"Me ya faru shahida?,garin yaya haka ta kasance?" Bata boyewa anty zubaida komai ba kanta
na saman cinyarta ta warware mata dukkan yadda akayi ta soma shan wani abu da niyyar rage
baqinciki da bacin ran dake damunta,sannan ta zarce da rabuwarta da anwar sannan ta dora da
cewa "Baqinciki na shi ya kashe abbana anty,shaye shaye yabarmin tabon da har na mutu dashi zan
mutu,na kashe abbana da takaicina!" wanda hakan ya sake bude sabon shafin kukanta,kai anty
zubaida take girgizawa
"Kuskurenki na farki shahida shine da kika saki Allah,kika manta da cewa babu wani babban
abu dake yaye qunci da baqincikin a zuciyar bawa ya samu nutsuwa da kwanciyar hankali irin
kusanta kai da Allah,babu wani abu da zai kawo miki farinciki da walwala irin karatun
qur'ani,shan wani abu a wajen dan adam domin gusar da baqinciki bacin rai ko kuma damuwa
bashi da wani tasiri a gareshi,baya haifarwa da bawa komai face sake sanyashi cikin
damuwar,baya yaye damuwa ta har abada face ya sake sanyaka cikin wasu sabbin
matsalolin,ya haifar maka da ciwuka masu kai d'an adam ga kushewa,Kana daukan cuta ne
kana laftawa kanka,kana kashe kanka da kanka,Allah S W T da kansa yace kada ku kashe
kawunanku,shan abun maye ba komai bane face kashe kai,don baka da maraba da mutumin
daya dauki makami ya dabawa kansa,domin kuwa shaye shaye ba cutar da baya
haifarwa,lalacewar qoda,lalacewar hanta,ciwon cancer,ciwon zuciya,yana nakasta hunhu,yana
kuma lalata qwaqwalwa wanda hakan yake jagoranci zuwa ga haukacewa,dukka daya daga
cikin wannan cututtuka idan aka bar mutum dasu sun isheshi azabar nan duniya,sun ishi mai
hankali gujewa abun maye"ajiyar zuciya anty zubaida ta saki sannan ta dora
"A duniyance shaye shaye bai haifar maka da komai sai zubewar qima da mutunci,mummunar
dabi'a ce dako wanda yake yinta yake boyewa,kuma baiso a sani,dabi'ace dakan gusar da
imani da hasken fuska,dabi'ace dake barin tabo cikin rayuwar wanda ya taba aikatata,sannan
ba'a sanyaka cikin sahun managarta mutane ko mutane masu dattako har abada,saboda kowa
kallon mahaukaci yake maka,sannan a addinance manzan rahama yace dukkan wani abu da
zai saka maye haramunne,musulunci yafimu sanin cewa kayan maye abubuwane masu
cutarwa ga lafiyarmu,shi kuma ko yaushe tattalin lafiyarmu yake,sannan addini ne dake kare
mutunci da martabar dan adam,bambancin mutum da dabba hankali,kinsha abinda zai gusar da
hankalin me sunanki kenan a wannan lokacin?,dalili kenan daya sanya aka haramta mana
su,duk sanda kake cikin maye babu kunya tattare dakai,hakan na nufin ba alkhairi a tare dakai
kenan,saboda ma'aiki ya gaya mana duk inda kaga kunya akwai alkhairi a wajen,sanda kuma
babu kunya tare dakai zaka iya aikata dukkan komai ciki kuwa harda kisan kai!,tunda kike sha
din damuwarki ta taba tafiya gaba daya?" Kai shahida ta girgaza,don da zarar ta farka dukkan
wata damuwa take dawo mata sabuwa fil,harma tafi ta dazun
"Zaki iya tuna sau nawa kikayi loosing sallah saboda tazo ta riskeki kina cikin bacci sanadin
abinda kika sha?"shuru shahidan tayi tana tunani hawaye masu dumi nabin fuskarta har cikin
kunnenta,kome take komai runtsi sallah bata taba wuceta ba sai a wannan karon,sai data shiga
wannan mugunyar dabi'ar
"Kina tunanin hujjace da zaki gayawa Allah ranar gobe qiyama na dalilin jinkirta sallahrki?" Ta
jefo mata tambayar data sanya shahida fidda sabuwar qwalla,dana sani da nadama mara
misaltuwa na sake shigarta,kaico da rayuwarta da haduwarta da fiddausi
"Kina da yaqinin sanda kika farka kika ramata Allah zai amsa ya saka miki a mizanin ayyukanki
wajen sallahrki na lokacin bazai tashi blank ba?,bayan kina baccin sabo ne bana ibada ba?"
Sabon kuka shahidan ta sake saki,tsoron Allah na sake kamata,tana jin kaman yanzu Allah zai
amshi rayuwarta,me ta tanada?,wacce amsa zata bayar?. "Allah yana karban tuban bayinsa ne matuqar ran bawa baizo gargara ba,sannan kuma rana
bata fito daga mafadarta ba,bai halatta bawa ya jinkirta tuba kan wani aikin sabo da yake
ba,yace har sai Allah ya shiryeshi,don haka yana daga cikin alamar 'yanwuta,kuma alamace
dake nuna bawa ya tabe,sannan alamace ta toshewar basira,anaso koda yaushe bawa ya
dinga gaggauta tuba saboda baisan randa ajalinsa zai riskeshi ba"
"Astagfirullah...astagfirullah" shahida ta dinga maimaitawa a fili har na tsahon wani lokaci,sai
data fuskanci ta samu nutsuwa sannnan ta dagota suna kallon juna
"Shahida...maganar anwar....." wani abu mai ciwo taji ya tokareta,abinda yayi mata ya dinga
yawo cikin idanunta kamar tariyar film,da sauri ta katsi antyn
"Anty...don Allah ki daina kiramin sunanshi....don Allah anty ki dainamin maganarsa,yanzu bashi
a gabana,yadda ya buqaci na barshi na barshi har abada...yadda ya nuna bai buqatata saboda
wani kuskure dana aikata nima bana buqatarsa har abada" murmushi anty zubaida tayi tana
karantar yanayinta da yadda maganar ke fita daga zuciyarta zuwa harshenta,kai ta girgiza tasan
cewa wani bacin raine dake qonata tun daga cikin jiki zuwa zuciyarta,kowa ya shaida irin qauna
da soyayya dake tsakanin shahida da anwar,koda baka sansu ba labarinsu ba shakka ya
iskeka,bata da tabbaci ko yaqinin kan abunda shahidan ke furtawa saboda ta riga ta sani cewa
soyayya ba qarya bace,ba qaramin dalili ne yake da qarfi da isar da zai karyata ba,karyawa ta
har abada,karayar da ba zata doru ba
"Duk wannan lafazin shahida ban buqatar jinsa daga bakinki,ba'a ciwa soyayya alwashi kuma
ba'a cika mata baki....kiyi addu'a kawai a yanzun,ki tattara hankalinki waje guda,ki karbi
qaddararki,kiyi moving forward,stop worrying about what u have to loose,and start focusing on
what u have to gain,har yanzu yarinyace ke,shekarunki nawa?,me kika soma gani cikin
rayuwa?,akwai abubuwa daya kamata ace kinyi achieving a rayuwarki,karki bari wani abu guda
daya ya tsaidaki waje guda,ya ruguza dukkan wani kyakkyawan tanadi daya kamata kiwa
rayuwarki,wannan abun daya faru ba komai bane cikin rayuwarki,daya daga cikin challanges
kenan na rayuwa,ki godewa Allah kina da chance,kina da dama,kamar ya baki wata dama ne
naci gaba da gina sabuwar duka rayuwar da kikaso kikaga dama,just choose tobe strong rather
than letting it drown you" wadan nan sune ire iren kalaman da anty zubaida ta dinga amfani
dasu tsahon shekara biyar don dawo da rayuwar shahida cikin nutsuwarta.
Cikin qaramin lokaci taji anwar din ya wanke mata a rai tas,ya sire mata,ya fice mata daga
ruhinta,taji zata iya rayuwa babu shi,taji abune mai sauqi hakan,saidai baizo mata da sauqi ba
yadda ta tsammata,ta share darare da yawa bata samu bacci ba,ta ga wuninnika da darare
masu tsaho da tsauri cikin rayuwarta a wannan lokaci,ta cika bangon dakinta da shafukan
littafanta ta kalaman qarfafa kai da qarfafa gwiwa akaran kanta,ta siya littafi tayi rubutu mai
tsaho da yawa kan rayuwarta har kawo bigiren da yau take kai,ta tattara duk wani abu da zai iya
tuna mata da anwar ta ajesu waje daya,ta shiga tsara yadda rayuwarta zata kasance nan
gaba,tun saga lokacin ko masoya ta gani sai taji tana tausayinsu,musamman mace idan taga ta
zura jiki da yawa.
Bayan umma ta fita takaba uncle hisham shi ya karbi ragamar daidaita musu duka
al'amuran gidan,sannan suka yanke shawara dashi shahida zata koma hannun anty
zubaidan,tunda har yanzu bata gama daidaita ba,saidai cikin kaso dari an samu sauyi na kaso
shida,rabata da unguwar da duk wani tsohon memory dinta zai sake taimakawa wajen saita
tunaninta,da wannan suka dauke shahidan ta koma wajensu.
Makarantu daban daban anty zubaida ta sakata wanda zata qaru ta fanni da dama,wasu na
koyon harshen larabci wani na koyon turanci bawai don bata iya ba,a'ah saidon ta maidata busy
sosai wanda hakan zai sanya bata da lokacin zama ma ta tuna wani abu mara dadi daya faru
da ita a baya,tayi hakanne kuma kafin wata shekarar ta zagayo su nema nata admission
saboda wannan shekarar ta qwace mata.
Rayuwarta ta soma samun sauye sauye,kullum kwanan duniya saitayi kukan dabi'ar shaye
shaye data ta taba tsintar kanta a ciki,kullum sai tayi nadamar sanin fiddausi a rayuwarta,sai
tayi nadamar sakin jiki ga duk qawar data kutso rayuwarki sama taka,abune mak wahala da
idan ka sake ka jefa kanka da wuya ya fice daga rayuwarka salin alin ba tare daya haifar maka
da nadama da danasani ba,bai kuma bar maka qatoton tabo ko baqin fenti a rayuwarka ba,ta
godewa Allah da yayi gaggawar fiddata tun batayi nisan da ba zata ji kira ba kamat yadda
tagani ta kuma ji labari da yawa akan wasu,wanda ta shiga bincike ne akai bayan ita Allah ya
tsamota,gefe daya kuwa yaqi take tuquru da kanta game da lamarin anwar,wata irin tsana da
bata taba tunanin tanawa wani dan adam ba ita ke taso mata,duk wani abu da yayi mata da
yadda ya dubu qwayar idanunta ya gaya mata magana,fiddota daga gidanshi da sauransu,uwa
uba hotunan yarinyar da yake gaya mata ya sake ya sauyata a madadinta,kullum qoqarin goge
duk wani tabo ko abun tunawa daya barwa rayuwarta take,tanason ta nuna masa ta kuma
nunawa duniya she can survive without him,tana son watan watarana yaga cewa shi din ba
komai bane da ba zata iya rayuwa babushi ba.
*Cikin rashin kunya murjewar ido dajin wannan karon dai dai take da kowa,zata iya karawa da
kowa,a shirya take ta rabu da kowa saboda shi,bata jin akwai abinda ya isa yayi mata hijabi
tsakaninta dashi,koda waye,koda mahaifiyarta data haifeta,koda mahaifinta da yayi silar
zuwanta duniya*
*"Allah ya isa ban yafe ba duk wanda yayi silar rabani da Zamab,ko wayeshi bazan taba yafe
masa ba wallahi, dan an haifeka ai ba halittarka akayi ba, kai ma babu wanda yayi maka auren
dole, haka a addinance babu inda Allah yace ayiwa mace auren dole"*
*kalaman da suka fito kenan kai tsaye daga bakin Basmah zuwa ga mahaifinta Ya Mu'allim
tana dubanshi kai tsaye ba kunya ko rusunawa*
_SAKI RESHE KENAN littafin da zaizo muku daga jarumarku haziqar marubuciya HAUWA A
USMAN JIDDERH_
*WANNAN WACCE IRIYAR DIYACE HAKA?,ME YAKE FARUWA ME KUMA YA FARU?,DON
JIN CI GABAN WANNAN LABARI DAKE QUNSHE DA BADAQALA,SAKIN RESHE DA
SAGEGEDUWA ZAKA BIYA NAIRA 300 KACAL TA WANNAN HANYA,BA TARE DA BATA
LOKACI BA ZA'A SADAKA DA WAJEN DA ZAKA SAMU NAKA*
Hauwa Auwal Usman
GT bank
015325259310
*saiki tura shaidar biya zuwa ga wannan number*
07020489340
*katin waya kuma xaku tura 300 ta watsapp ta wannan number*
07020489340
_kar ayi babu ke,maza garzaya ki nemi
naki_♀️♀️♀️♀️♀️https://www.youtube.com/channel/UC4kJO342hmb_Pd2luKHBjFA/videos
*zafafa biyar na kudi ne,idan kika gani don GIRMAN ALLAH karkiyi sharing,idan kina da buqata
ki tuntubi wadan nan numbers din*
07067124863
*ko kuma*
09032345899
*Alqawarin Allah*
1️⃣7️⃣
Daga gefan anwar kuwa yaso barin garin ne gaba daya,saboda yadda garin yayi kishi zafi,yaji
ya tsani komai,bashi buqatar duk wani abu daya sani,yana buqatar baqon muhalli,anty husaina
ce ta kafe kai da fata kan bata yarda ba,ganin yadda ya dage kan son tafiya din ta sakar masa
kuka,wanda ya sanya dole ya haqura shima yaci gaba da zaman.
A wannan lokacin da nafisa taga dama tazo mata,taso ta gabatarwa da anwar kanta ne
gaba gadi,taso anwar ya dawo cikin gidansu da zama qarqashin abbanta,ya bashi gida mota da
kuma jari suyi aurensu,saidai yadda labari da halayyar anwar tazo mata ta tabbatar da cewa
aikata hakan babban kuskure ne da zai janyo kwabarta tayi ruwa,wanda daga qarshe suka
gama shawara da mima kan yadda zasuyi.
Alhaji abba kabara mahaifin nafisa mutum ne mai yawan taimako da samawa matasa
ayyukan yi,yana da kamfanoni hakanan yana da shagunan da yake sanya matasa a ciki,duk
matashin da yayu shekara guda riqe da amanar shagon ba tare da an taba kuka dashi ba alhj
abba yakanyi masa kyakkyawar sallama ta hanyar bashi jari mai tsoka,wani lokaci ma bai duba
da abunda aka samu a shekarar,zamanka a shagon iya karantarshi da amanarka kawai ya
nuna idan ya baka jarin ba zasu salwanta ba,wasunsu kuma yakan daukesu ne ya kaisu
kamfaninshi,musamman masu takardun makaranta,dalili kenan sanya sanya ta samu abban
nata
"Uhmm...ya akayi nafi?" Cikin nuna yanayi najin kunya tadan sadda kanta
"Abba dama...dama" sai tayi shuru
"Dama me?" Ya tambayeta yana sauke medical glass dinsa
"Akwai wani marayan matashi ne,abba yana da amana da duk halayen qwarai,ya kammala
karatunsa baida aiki,abba yana shan wuyar rayuwa sanadiyyar haka,idan na masa magana
abba da kaina bazai karbi duk wani abu ba,amma idan kaine da kanka abba zaifi amsar duk
wani taimako" shuru ya danyi yana nazarinta "A ina ke kika sanshi?"
"Abba...a unguwarsu qawata yake,ita take bani labarinsa,na tabbatar zaka yaba da halayenshi
hakanan zaka tabbatar daya cancanci taimako" kai yake gyadawa sannan yace
"Ba damuwa,ki turamin adress dinshi,zamu fidda sanarwar daukan ma'aikata a kamfanina
zansa a duba takardunshi sosai"
"To Abba Allah ya qara budi" amin ya fadi yana daukar jaridarsa yaci gaba da dubawa,yayin da
nafisan ta fita cikin farinciki da walwala.
Randa aka kira anwar aka shaida masa sunan kamfanin da sukeso duba takardunsa yayi
mamaki qwarai,don iya yawon neman aikinsa bai taba bi koda ta titin da kamfanin yake ba,don
bai taba sama ranshi cewa zasu daukeshi aiki ba.
Qarfe taran safe na ranar da zaije kamfanin ya gama shirinsa ya fito yana kulle gidan yaga
mota tsaye a qofar gidan,horn aka danna mishi kana aka jawo motar zuwa gabanshi
"Daga kamfanin alhj abba ne akace muzo mu daukeka" ya kalli motar sosai yaga tambarin
kamfani jiki,hakan ya sanya ba musu ya bishi suka shiga.
Sam bai kula da itaba ashe tana zaune a bayan,sai daya waiwaya suka hada idanu ta sakar
masa murmushi,sam bai ganeta ba,ita ta soma gaidashi sannan ta gabatar mishi da kanta a
matsayin diyar alhj abba,mamaki day ayayi na wanne matsayine dashi da har za'azo har qofar
gida a daukeshi cikin motar kamfani shi da za'a yiwa alfarmar bashi aiki,bashi da amsar wannan
saboda haka shuru shi yafi masa,yana jin nafisan na bashi labarin abubuwan da suka shafi
kamfanin kamar ma an daukeshi aikin ne,shidai nashi kunne ne,don yanzu baya ga anty
husaina baya jin dadin hira da kowacce diya mace,hasalima bayaso su rabeshi.
Bisa jagoranci da shigewar gaban nafisa ya gama komai cikin kamfanin,aka kuma bashi
babban gurbi wanda ko a mafarki bai taba tsammata ba,koda wasa bata nuna ita ta roqa masa
wannan alfarmar ba saboda tasan ba wani abu bane cikin aikinsa yaqi amsar aikin gaba daya.
Lokaci kadan da fara aikinsa alhj abba ya tabbatar da duk maganar da nafisa ta fadi a
kansa,yana da gaskiya yana da amana,hakanan yana da aiki tuquru,baya taba saba lokacin
zuwa kamfani hakanan lokacin tashi,gwara ma lokacin tashin idan akwai wani aikin da kamfani
zaici gaba yakan sarayar da lokacin nashi ya gabatar dashi,dalilin kenan daya sanya alhj abba
da kanshi ya danqawa anwar qaramar motar hawa mai azabar kyau da tsada irin wadda bai
kawo zai mallaketa ba nan kusa,sannan ya nemi daya dawo cikin gidanshi da zama,wanna ne
kuma ya bawa alhjin haquri,saboda yadda nafisa ke shishshige masa sam baya masa
dadi,yana karanta mata ne da daga mata qafa kawai saboda girma da darajar mahaifinta,motat
ta sauqaqa masa sauran ayyuka da zuwanshi ma kamfani gaba daya,hakanan ya dinga barin
motar a wani garage dake farkon layinsu wanda masu abun hawan da basu da muhallin ajesu
suke ajewa a nan su biya wani abu ladan ajiyan.
A sannan rayuwa ta soma mishi kyau,koma ya soma canzawa,kama daga sutura cima da
sauransu,anty husaina ma kanta canji ya soma zuwa mata,a wannan lokacinne nafisa ta kasa
shanye halin ko in kula da anwar ke nuna mata,duk wata alama da ake nunawa mutum ya gane
ana sonshi ta nuna mishi amma a banza wai an mintsini kakkausa,hakan ya sanya tayi
qundunbala taci alwashin sanar mishi wata rana da abbanta ya gayyatoshi cin abincin dare
gidan.
Abban da mamanta sun kammala sun bar wajen saura nafisan da tunda taji labarin
zuwanshi ta kasa zaune ta kasa tsaye,ta tsara kwalliya ta a mutu,sannan ta aro duk wani salo
da tasan zai iya tafiya da d'a namiji,saidai kuma har ya kusa gamawa bataga ya nuna wani abu
game da ita ya burgeshi ba,hakan ya sanya tayi gyaran murya "Anwar....idan ba zaka damu ba don Allah...ina da magana dakai"
"Uhmm...babu damuwa ina jinki" shuru tayi na wasu mintuna sannan ta daga kanta tana
dubanshi sosai
"Tun ranar da Allah yasa na soma ganinka anwar Allah ya dasa min qaunarka...na rasa ta
yadda zan furta maka bansa ya zan gaya maka ka gane ba,wani irin soyayyarka nakejin har
cikin jinina,anwar ina fata da roqon ka soni koda rabin yadda nake sonka ne" tunda ta soma
maganar ya zuba mata idanu yana jin wani abu da baisan meye ba yana taso masa,ko kusa ko
alama baison yaji wannan kalmar daga bakin kowacce diya mace gani yake duk yaudara ce,ba
gaskiya bane qarya ce,yatsunsa ya dinga bugawa a saman teburin kadan kadan har ita sai data
tsargu da kallon da yake matan ta soma kame kamen abunyi,da qyar ya iya hada abun fada
"Nafisa" ya kira sunanta a kausashe,daga kanta tayi ta dubeshi sosai jin yadda sunan nata ya
fito bilhaqqi daga zuciyarsa
"Inason daga yau wannan tunanin yabar qwaqwalwarki,wannan kalmar ta fita daga bakinki,ina
ganin qimarki data mahaifanki,kada ki jawo abinda bazai mana kyau da dadi ba ni dake gaba
daya"daga haka ya miqe ya dauki maqullan motarshi ya wuce ya barta a wajen,kuka ta saki
sosai,bata taba tunanin lamarin zaizo da haka ba,tayi tsammanin yadda yake nuna kulawa a
gareta kaman qanwarshi zata samu soyayyarshi ta sauqi,haka ta miqe ta shiga bedroom dinta
cikin tashin hankali ta dauki wayarta ta kira mima ta zayyane mata komai
"Nafisa kenan,dama ke kina tunanin samun