Showing 99001 words to 102000 words out of 126208 words
Chapter 34 - ALKAWARIN ALLAH BOOK BY HUGUMA.pdf
ya mara mata baya.
Dukkansu xaman kurame sukayi shida ita cikin motar,kowa ya kama owners corner ya hade
fuska kaman zasu masgi juna,ta cikin glasa muhsin ya qare musu kallo,dariya ta cikashi,ya
girgiza kai kawai,shikam wannan abun yafi masa kama da fadan masoya,sai shine daya gaji da
shurun ya soma sako musu hira don gudun xaman shuru,ba wani hadin kai ya samu daga
wajensu ba na tayashi hirar ba,har gwara ma anwar akan shahidan ta takejin wani abu ya
tokare mata wuya,tunda suka shiga motar sai kace bai santa ba,kai bakace shine a daxun ke
shirin mata daukan amarya ba.
Sanda duka isa muhsin shiya fara ficewa a motar,tana shirin budewa itama ta fita anwar ya
danna lock,waiwayowa tayi ta dubeshi,batason wata magana ko gajerace bare mai tsaho
saboda haka ta kalleshi kawai daidai sanda shima ya kalleta
"Saurin me kikeyi?,kina gudun jerawa ne dani,saidai ni na fiki gudun na jera dake don kar a
dauka nida ke Ali yaga Ali ne"
"Ai baka cika wanda yake gudun jerawa da 'yar maye ba tunda zaka iya aurenta" ta maida
masa amsa idanunta akanshi,saiya dauke kanshi yana cire belt din jikinsa,hakanan ya samu
kansa dajin zafin kalmar 'yar maye data fada din.
Sanda suke shiga wajen babu wanda basu burge ba,duk wanda ya dora idonshi akansu
saiya shagala da kallonsu,perfect martch da yawa suke fada,yayin da duka jama'ar dake wajen
suka miqe don nuna girmamawa a garesu,da yawa wadanda sukasan tsohuwar alaqar dake
tsakaninsu kuwa irinsu anty usaina zunnurah da maqota fuskokinsu sunqi gushewa da
murmushi
"Lallai *ALQAWARIN ALLAH BAYA TASHI* ba wanda ya isa ya canza alqawarin Allah"
zunnurah take fada a bayyane tana kallon maigidanta sanda shahida da anwar suka zauna a
muhallin da aka tanadar musu,tana tuna tsahon zamanin da suka dauka basu tare,tana tuna
yadda kowanne yaqi dan uwansa yake nesanta kanshi dashi,dai gashi cikin qanqanin lokaci
ubangiji ya nuna buwayarsa,ya sake dawo dasu cikin rayuwar juna duk da yadda kowannensu
ke tsaye kai da fata akan qudurinsa amma Allah yayi nasa hukuncin.
Sanda aka fara gabatar da komai akayi kiran dangin ango anty usaina ta fito sai abun ya
baiwa shahida mamaki,ruwan kudin data musu yasa ta sanya ayar tambaya a kanta,wace anty
usaina?ta tambayi kanta lokacin data tsaya gefan anwar suna magana qasa qasa yadda
shahidan bataji,gabanta ya fadi cikin ranta tana addu'ar Allah yasa ba abinda take zato bane.
Saidai kuma addu'ar tata batayi tsaho na aka ware fili na musamman saboda babbar yayar
ango aka bata dama,cikin qananun hawaye da suka kasa riquwa a idanunta ta miqe ta isa inda
anwar da shahida ke zaune,tasa hannunta ta tashesu tsaye gami da dan matso dasu gaban
step din da suke kai kadan yadda kowa zai iya ganinsu,ta karbi abun magana tayi taku biyu
gaba kadan dasu sannan ta tsaya
"Yanzu da zan tambaya cewa suwa kuke gani a tsaye a nan wasunku zasuce amarya da
ango,wasu zasuce masoya,eh....masoya ne saidai ba ordinary masoya da kowa ya sani
ba,masoya ne da kalar soyayyarsu ta bambanta data kowa,masoyan da Allah zai cika
alqawarinsa a kansu koda ba wanda yaso hakan,nasan zaku yarda dani idan kukaga wannan"
saita juya ta kalli masu gabatarwa,cikin sakannin da basu wuce goma ba majigin dake kafe a
bango daban dake hall din ya soma haske wanda hakan yaja hankalin kowa,ciki harda anwar
da shahida,cikin qanqanin lokaci hotuna suka soma bayyana kansu daya bayan daya,hotunan
anwar da shahida shekara biyar zuwa shida baya,mamaki ya kama anwar ni na a ina anty
usaina ta samo wadan nan hotunan?,hotuna ne da sukan dauka lokaci zuwa lokaci shida
shahidan idan yaje zance sanda ya siyi waya torching ya siya mata itama,tana ainihin
shahidarta yana ainihin anwar dinsa,nan fa murmushi ya cika fuskokin al'umma kowa nabin
hotunan daya bayan daya da kallo,abokan tsokana suka samu nayi,yayye da iyaye suka dinga
dariyar hotunan,wasu da hijabai a jikinta,wasu ta sunne kai,shi kuwa yana dan tsirit dinsa babu
wata cika ko kumari tattare dashi,a hankali hotunan suka dinga shiga zukatansu suna tuna
musu wani lokaci can baya,lokutan da sukafi kowanne dadi cikin rayuwarsu,hoto na qarshe ya
soki zuciyarsa shida ita,dukkansu basu manta ba,wannan shine hoto kusan na qarshe da suka
dauka tsakaninsu dab da mai afkuwa zata afku,idanunta ta runtse hawaye nason saukowa tana
hanashi,turota da anwar yayi daga gidansa shine abinda yazo mata a rai,daidai sanda shima ya
dauke kanshi daga kallon hotunan,suna qarewa gurin ya rude da hayaniya da kuma tafu gami
da sowa,saida mc ya daidaita komai sannan anty usaina taci gaba da magana
"Zuwa yanzu nasan kowa ya gasgata maganata ko?"
"Eh..." Duka hall din ya amsa,kaita jinjina sannan ta sake komawa gabansu tana dubansu har
yanzu abun magana na hannunta
"Inason ku sake tabbatarmana da cewa zaku kula dakanku,zaku kula da amanar juna,ga shaidu
nan suna kallo" ta qarashe maganar tana fidda murmushi gami da fatan hakan ya kawo sauyi
tsakaninsu komi qanqantarsa,anwar ta fara miqawa abun maganar tana tsareshi da ido,dole ya
amsa yakai bakinsa,sassanyar muryarshi mai cike da mazantaka ta cika hall din wanda hakan
ya taso da tsohon mikin dake danqare zuciyar nafisa dake maqale ita da mima a wani sashe na
hall din,ji tayi kaman zuciyarta zatayi bindiga,sonshi da qaunarshi ya sake narkewa cikin
zuciyarta,taji inama tun farko batayi sakin bakin cewa ta fasa aurenshi ba?
"In sha Allah zan kula da ita,zan sauke duk wani haqqi nata dake wuyana..."
"Kayi mana qwange....zaka bata soyayya da kulawa?" Anty usaina ta tari numfashinsa ta fada
cikin sauri ta sigar tambata,kasancewar ba abun magana a hannunta yasa wadanda ke zaune
gaba gaba abokanshi su kadai sukaji me tace sai kuwa su,idanu ya fiddo yana kallon antyn ya
tabbatar qure takeson yi masa,cikin qasa qasa da murya yadda su kadai zasuji yace "Idan naga ta cancanta ba" yana miqawa antyn abun maganar,duka takai masa wanda ta manta
ma a inda suka saboda jin haushi ya goce yana dariya,abun ya baiwa mutanen dake wajen
sha'awa suka saka dariya gami da sanya musu tafi,harara ta jefa masa sannan ta juya ta
miqawa shahida abun maganar "Uhmm...uwar gidan anwar,ina naki alqawarin" murmushi ta qaqalo sannan ta jefawa anwar
harara wanda har cikin zuciyarta ita tayi hakan,yayin da sauran mutane suka tsammaci soyayya
ce
"Alqawarin daya dauka baiyimin ba anty,ba abinda ya iya,baisan haqqin soyayya ba baisan
mutuncin masoyi ba,baisan komai ba a soyayya bai iyata ba" tsit kowa yayi yana saurarenta
cikin mamaki,gaban anty usaina ya shiga faduwa,hasina da zunnurah dake zaune cikin mutane
ji sukayi kaman su rugo da gudu su qwace abun maganar daga hannunta,yayin da nafisa ta
tsaya cak farinciki na ratsata,me zai farune?,ba hadin kai tsakaninsu kenan ko jituwa
"Haka kikeso anty na fada irin kalaman da wata amarya da aka yiwa auren dole ta fada?,idan
ban yabi masoyi kamarshi ba me zance?,bashi da buqatar yabo ko daukan alwashi a kansa,shi
yasan komai,duk alqawarin da zan dauka anan na fallasa sirrin soyayyarmu ne,alqawarin daya
dauka duka namu ne mu biyu basai nayi maimaici ba,ni dashi duka abu daya ne" ta qarashe
fada tana murmushi saman fuskarta can qasan ranta kuma tana jin ciwon lafazinta,sowa da ihu
wajen ya kaure dashi,ba wanda ya fuskanci me take nufi daga anty usaina saishi uban
gayyar,sai zunnurah da hasina,kowa ya zaci cewa abinda ta fada din zallar soyayya ce da
qauna,miqawa antyn abun maganar tayi,tana juyowa suka hada idanu dashi saita dauke idonta
gefe guda.
Sosai dinner din ta qayatar ta sanya farinciki cikin zukatan al'umma da dama,takuma
burgesu,komai ya gudana yadda anty zubaida tayi fata shahidan bata bada matsala ba,tayi
qoqarin kula da duk wani motsi nata da action nata.*Alqawarin Allah*
3️⃣6️⃣
Daurin auren da za'ayi sha daya na safe amma tun takwas na safe gidan ya soma cika da
'yan uwa,a sannan tana kwance daga saman gadonta tana kallon yammatan nata hada hadarsu
abinsu suna breakfast,ko sha'awar abincinma batayi bare takai gaci,babu yadda hasina batayi
da ita ba amma ko kallonta batayi ba bare ta tashi,sai juyi take daga nan zuwa can,ji take
kaman zazzabi zai kamata,har goma saura tana kwance tana kallon masu wanka nayi masu
kwalliya nayi.
A sannan ne anty zubaida ta shigo tana dubanta
"Wankanne yau baki da niyyaryi ko kuwa?" Bata amsa mata ba illa miqewa da tayi ta zauna
sosai saman gadon tanajin jikinta a matuqar mace,haka zuciyarta a cunkushe,kanta a qasa anty
zubaida ta aje ledar hannunta
"Ki tashi kiyi wanka ki shirya,mai kwalliya zata shigo tayi miki"
"Anty.." Ta kira sunan anty zubaidan zuciya a karye,juyowa tayi tana kallonta
"Don Allah ki qyale mai kwalliyar nan yau,don Allah" dan shuru tayi sannan tace
"Shikenan zata koma,hasina ta shafa miki ko powder ne" daga haka ta fice daga dakin.
Dariya hasina tayi sosai tana qarasowa inda shahida ke zaune tana tare qwallar idonta,idan
da hali yau batason ko sau daya tayi kuka
"Hajiya shahida,nikam na rasa me kike nufi,don Allah yammata ba kukan dadi wannan matar
take ba?" Ta tambayi sauran yammatan dake dakin tana watsa hannaye,dariya aka sanya
sannan ta dora
"Allah ya baki miji irin wannan da yaji komai da komai amma ki tsaya kina wani nuna qiyayyar
banza,ke idanunsa kawai aka kallah Allah ansan dan soyayya ne na qarshe,baku lura da
yanayin kallonsa bane?" Ta sake jefawa 'yammatan dakin tambaya
"Ashe bani kadai na gani ba,nida daada ta fadamin tun farko aini zan sako kai akwai amanta da
batunki" daya daga cikin cousin sis din shahida ta fada,muryarta kamar ta mutumin daya tashi
yanzu a bacci tace
"Yanzu ma lokaci bai qureba,da zasu taimakeni da sun maida daurin auren kanki,don Allah ki
shaida musu" daya daga cikinsu ta saki dariyahatda qyaqyacewa
"Kuna ganin idonta kunsan qarya take,wannan aka qwace miki shi idan baki kuka ba yanzu
gaba sai hawan jini ya kamaki" dukka suka sheqe da dariya,abun ya bata haushi ganin wai
basu yarda da ita ba
"Nikeson anwar?,amma kun yaudari kanku" daga haka ta zira takalmanta ta shige bandakin
ganin suna sake turata.
Kafin sha daya na rana layin ya dinke tsaf da jama'a,hayaniya ta kowanne sashi,yayin da
fargaba da faduwar gaban shahida suka dadu duk sanda wani minti ko sakan ya
shude,idanuwanta kan agogo,duk surutan da ake cikin dakin bata jinsu bare ta fahimci me suke
fada.
Sha daya da minti goma sha biyar qanwar ummanta ita da wasu yan uwan babanta su uku
suma shigo dakin suna sakin guda wadda ta firgita shahida gamida saka zuciyarta gudu da
matsanancin sauri,inda take zaune suka qaraso hannun daya daga cikinsu na dauke da turare
ta dunfarota tana cewa " *Alqawarin Allah* ya tabbata,yau Allah yayi,shahida ta zama matar anwar"wadda ke tsaye a
bakin qofa qanwar abbanta tace
"Allah ya jiqan habibu,Allah baiyi zaiga aurenki ba shahida,duk qaunar da yake miki Allah bai
nufa ba,Allah ya jiqanka habibu yakai haske kabarinka" kalaman da suka sake tunzura zuciyar
shahida kenan sanda suke fesheta da turaren,ta saki kuka sosai mai sauti wanda ya tunawa da
abbanta yasa taji auren ya sake fice mata daga kai,karo na biyu tun bayan lokacin da al'amarin
ya faru da taji ba zata iya yafewa fiddausi ba wadda ita ta zama sila kuma jagorar afkuwar
komai a rayuwarta,me ta yiwa fiddausi haka dataso tarwatsa mata rayuwa?.
Daada ce ta shigo dakin jin hayaniya da gudar dake tashi a cikin dakin,yawan kukan da
taga shahidan nayi yasa daadan ta fitar da kowa daga dakin taja mata qofar,tayi hakanne donta
bata damar yin kuka sosai ko zataji sanyi a ranta.
Daidai lokacin da nafisa ke kaikawo kaman wadda ta hadiyi kunawa tana zufa,bata tabajin
cewa tayi kuskure ba sai yanzu da labarin tabbatuwar auren shahida da anwar ya ratsa
kunnenta
"Anya banyi ganganci ba kuwa mima?"
"Gaganci kuma na nawa?" Ta fadi a zuciyarta,amma a fili saits iso inda take ta dafa kafadarta
"Babu wani ganganci da kikayi,badai gani na iso ba?zaki shiga gidan anwar a sanda ya dace
dake,ki sawq ranki kamar kin sameshi kin gama" sanyi ya ratsa ranta ta saki ajiyar zuciya
"Please mima,duk wani shiri da zakiyi karkiyi na dogon lokaci,kiyishi a gajeran zango,don
zuciysta ba zata iya jurar tunawa da zan dinga cewa anwar nacan ya kebe da wata macen ba
bayan ni"
"Baki da damuwa fa hajiyata,kisa ido kisha kallo" mima tayi lafazin tana daukan jaka da dan
yalolon mayafinta ta fice daga falon.
*5:00 pm*
Qarfe biyar na yammaci cikin dakin nata da aka gama kwashe komai nata take zaune
saman kujerar madubi,da kanta a yanzu take shiryawa don tasan me afkuwar ta riga data
afku,komai ya qare mata,babu sauran wani abu da zai tasiri koya hanata shiga gidan anwar,ta
gama yankewa kanta gwara ta sassautawa zuciyarta,ta yadda da hakan ta kuma sallama,taci
alwashin samawa kanta walwala da nutsuwa,saidai hawayen da har yanzu ta kasa cin galaba
akanshi gaba daya duk da ya ragu,amma lokaci lokaci yakan sako kai tasa hannu ta daukeshi.
Tsaf ta gama shirin nata hasina da anty xubaida na gyara mata wasu abubuwan har komai
ya kammala,lallai amarya amarya ce,gaba daya kaman sauya shahidan akayi da wata sabuwar
halittar,tayi wani kyau na musamman gami da kwarjini,anty usaina ta zauna daga bakin gado
tana dubanta
"Za'a soma kaiki wajen umma,daganan kuma akaiki gidan yayarshi,za'a barki a nan shi zaizo ya
daukeki ku wuce,munyi magana da ita ta gayan dalilanta nayin hakan kuma na
gamsu,shahida,zamana dake zamane mai dadi wansa nake alfahari dashi,kuma dukkan abinda
ya kamata na gaya kiki koki sani kin riga dakin sani na kuma sake miki tishinsa,abu na qarshe
kawai da zan rufe dashi shine ince miki,shi aure bautar ubangiji ne,hakan ya sanya dadinsa bai
rufewa mace ido ta manta da mahaliccinta,haka dacinsa ma bai sanya mace ta manta da cewa
bautar Allah take,Allah yasa kin shiga a sa'a,ya sauya zukatanku da manufofinku cikin qanqanin
lokaci,ina maraba da tambaya daga gareki duk sanda wani abu ya shige miki duhu,amma ki
sani,dole ki zama jaruma,dole ki koyi hadiye wasu abubuwan ba tare da kowa ya sani kokin
gayawa kowa ba,ciki badon tuwo kawai aka yishi ba,Allah ya sadamu da dukkan alkhairinsa"
daga haka anty zubaida ta miqe don batason tayi qwalla ko daya don karta sake karyawa
shahida gwiwa tunda ta fuskanci kamar ta aro dakiya da juriya,daidai sannan huda ta shigo da
sauri,ta isa gaban shahida ta rungumeta,zata fara kuka anty zubaida ta zare mata ido gamida
korata don karta karyawa shahidan gwiwa,a haka aka fita da ita zuwa gidansu.
Can dinma gidan cike yake da jama'a 'yan yinin biki,uwar dakan ummanta aka ajeta,'yan
uwa suka dinga shigowa aka dinga gaisawa ana yi mata Allah ya sanya alkhairi,tayi qoqarin
tarbar kowa cikin mutuntawa,tunda kusan dangin ummanta ne duka,ba wani bare ko baquwar
fuska.
Sai gab da magariba sannan umma ta zauna da ita ita da sauran yayyenta,fadane dai irin
wanda uwaye kewa diyarsu,daga bisani kuma umma ta taba nata,ta nemi yafiyarta cikin kuka
tana tunawa da abbanta
"Bakiyimin komai ba shahida,saidaima ni nace ki yafe mana nida mahaifinku" kukan da bataso
ba a yanzu shi take haiqan,kaman ba zata fita daga gidan ba haka ta tako suna riqe da ita aka
fito da ita,saitaji wani qauna da kewar mahaifiyarta na ratsata,taji kaman karta tafi,taji kaman
taci gaba da zama dasu,a yanzu bata buqatar anwar sam,bata da buqatarsa cikin rayuwarta.
Tun daga harabar gidan anty usainan zaka gane wata walima ake ta daban saboda yadda
harabar ta qawatu,uwa uba ankon da yake jikin duk wanda ke farfajiyar dama cikin gidan cikin
wata atamfa mai azabar kyau da tsari.
Sabon shagali na walimar da dangin ango suka hada aka bude,nan aka zaunar da shahida
suka dinga mata barin liqi tako ina,ba'a tashi ba saida akayi sallar magariba,anty usaina bata
bari an shiga da ita cikin gidan ba,can wani babban falo dake da daki da bandaki aka kaita,babu
kowa wurin da niyyar ko zatayi sallah,aka aje mata abinci aka barta ita daya donta sake,tuni
'yan uwanta suka koma gida ba wanda ya zauna,fashin sallah take hakanan abinci bata
sha'awarsa,kuma batajin zai iya wucewa ta maqoshinta,saboda haka ta zauna kawai idanunta
kan tv din dake aiki ita daya,volume dinta can qasa don ba'ajin ma me ake cewa,sam ba tv
dince a gabanta ba,sabuwar rayuwar da zata fuskanta itace a gabanta,abu na gaba tsakanin
kunyar anty usaina,ta yaya zata kalleta?,idan ta tuna kalaman data gaya mata na batason dan
uwanta sai taji duk nauyi ya sauko mata,batasan itace wannan yayar tashi qwaya daya da bashi
da kamarta ba,da duk yadda take qin abun ba zata yarda bakinta ya fada ba,addu'a take cikin
ranta Allah yasa kada ta shigo.
Bakwai da rabi zuwa takwas na dare taji hayaniyar gidan ta ragu sosai,da alama masu
tafiya sun tafi kenan,masu shigewa cikin gida sun shige,turo qofar da akayi shi yaja
hankalinta,ta dan dage mayafinta kadan tana kallon mai shigowar,sa'ida ce saidai ita batasanta
ba,fuskarwa a washe ta qaraso falon tana takowa a hankali tana waigawa,da alama ba'asan
tayo.nan ba,dab da shahida ta zauna tana kallonta
"Anty,saike kadai?,nayi nayi da ummi tabarni nazo tace a'ah zamu takura miki kina hutawa
ne,da qyar na samu na sallabo" murmushi shahida tadan saki tana duban sa'ida
"Ina yini anty,ya gajiyar biki"
"Lafiya lau,me sunanki"
"Sa'ida,'yar anty usaina ce ni,kuma qawar uncle anwar" girarta shahida ta dage duka biyun tana
dubanta alamun tambaya,dorawa tayi
"Wallahi kun dace sosai anty keda uncle,uncle ya samu mata me kyau" tana murmushi sosai ta
fada tana kuma sake kallon fuskar shahidan data ji tana